RASHIN GODIYA ✂ 1
BISMILLAHIR RAHMANIR
RAHIM
Rana ta take sosai duk wanda ka gani a cikinta dole ce ta fito dashi daga gida. Tana zaune a bayan bus ita kadai kamar mayya saboda babu mai zama kusa da ita...karnin da take yi yasa ake gudunta. Daidai asibitin tace da kwandastan akwai na nan. Bai ji abinda tace ba saboda karar horn daga motocin da ke sintiri akan titin. Ai kuwa mutanen ciki kamar hadin baki suka fara cewa akwai na nan, kai baka ji ne ana yi maka magana akwai mai sauka. Kusan duk mutanen bus din fitowa suka yi suka bata hanya ta wuce. Wata dattijuwa ta rike hanci...wai! yarinya a rinka wanka don Allah. Kwandasta yayi dariya ai irin matan nan masu gayu da kazanta suna da yawa. Amma dai gaskiya yanmata idan kika dore a haka sai dai kiji ana biki a makota amma ba naki ba. Aishatu bata ce komai ba har aka bata canjinta tayi gaba.
Wani daci ne ya tokare mata wuya ta kasa hadiyar yawu saboda radadin da zuciyarta ke yi mata. Inda sabo ya kamata ta saba da kyamar da mutane ke yi mata a dalilin ciwon da take fama dashi. Hawaye ne suka sauko mata tayi saurin gogewa da kasan hijab dinta sannan ta karasa gate din asibitin. AMC....Assalam Medical Centre. Tabbas shine asibitin da Anti Lawisa ta kwatanta mata. Daga kanta tayi tana karewa ginin kallo, a rayuwarta tana son gida mai kyau, ba don lalura ce ta kawota ba da ta bawa idanunta hakkinsu.
Tana shiga ciki reception ta wuce ta tarar da mata biyu tsaye. Sallama tayi musu suka amsa tare. Daya daga cikinsu ta kalli dayar, ke Jummai warin me nake ji haka, ko jiya a nan kika bar flask din abincinki ne? Bana son wulakanci ta bata amsa a harzuke, kila ma shegen cover shoe dinki ne da baya samun iska. Ta kalli Aishatu ke baki ji karnin bane don Allah? Ai gara wari akan wannan silent bala'in. Ita dai Aishatu bata ce komai ba don tasan ita ke fitar da wannan abin kyamar. Likita zaki gani ne taji an tambayeta. Eh ta amsa amma ina neman wata nurse ne Risikat. To wanne zaki fara? Likitan ko Sis Risikat din. Daga baya Aishatu taji ance gani meye ake kiran sunana. Hmmmm kai Jummai yau anyi shara kuwa? An fitar da bola da wanke toilets? Wurin nan has a terrible odour. Aishatu suka nuna mata, ga wadda take nemanki. Risikat na matsowa ta tabbatar daga ina warin yake sai tayi shiru don a matsayinta na maaikaciyar lafiya bai kamata tasa mara lafiya yaji ba dadi ba. Haka ta daure ta matso kusa da Aishatu, gani how can I help you?
Dan murmushi tayi tace Anti Lawisa ce ta turo ni. Tuni Risikat ta washe baki Ahh kece yar yayarta ko? Ai ta fada min zaki zo. Kinyi saa Dr Rano bai dade da zuwa ba. Sai dai zaki sami layi ta fada tana nuna matan dake zazzaune a wurin da aka yi domin zamansu suna shan sanyi AC. Ina fata dai akwai kudi ko. Zaki bude file ki biya consultation fee. Nawa ne ta tambaya tana kokarin bude jaka. Jummai tace dubu biyu kudin file sai dubu da dari biyar na ganin likita.
Sai da ta gama biyan kudin Risikat tace ta zauna zaa kira ta. Idan tana bukatar wani abu tayi mata magana. Kinsan farkon zuwana unguwar mu Lawisa ta taimake ni sosai. Bana manta alheri so feel free to ask idan kina son wani abu. Godiya tayi mata sannan ta kara shafa yar jakarta ta tabbatar kudinta yana nan. Sai da babanta ya sayar da tumaki hudu aka bata kudin don ance mata irin lalurarta tana cin kudi sosai.
Kusan mintuna talatin tana zaune saura su biyu a wurin taji ance Aishatu Yusuf. Gabanta ne yayi mugun faduwa ta mike kamar an tsikareta. Yanzu ta yaya zata yiwa likita bayanin ciwonta. Gaba daya ta rude don saboda irin wannan kunyar ta kasa fadawa kowa tana da ciwo har sai da ya bayyana kansa.
RASHIN GODIYA ✂2
Sallama tayi tare da kwankwasa kofa taji muryar namiji ya amsa daga ciki. Hantar cikinta ta sake kadawa da ta shiga taga mutumin ba wanni babba bane. Sai da Aishatu ta kwashi rabin minti a tsaye...malama ki karaso mana akwai taji ya fada yana danne dannen computer.
Aishatu ta karaso gaban table din ta zauna kan kujera. Zumbur Dr Rano ya mike yana kallonta...sorry wani wari nake ji,ina zuwa. Karkashin kujerarsa ya duba da bayan labule. Har wurin gadon da marasa lafiya ke kwanciya ya duba su duk sai da ya leka yana yi yana dan kallonta. Ko dai tusa tayi masa ne tana shigowa ya tambayi kansa. Ganin irin kallon da yake mata yasa ta galla masa harara. Ya dan shafa kansa yana dawowa wurin zamansa tare da karfafa zarginsa na cewa iska ta sakar masa mai wari.
Yana zama ya jawo file din gabansa, Aishatu Ja'afar ko. Kai ta gyada masa kawai. Ya dauko biro ya dora kan wata takarda. Aishatu shekarunki nawa?
Ashirin da hudu.
Kina da aure ne?
Eh...har ya rubuta tayi saurin cewa a'a.
Cikin rashin fahimta ya kalleta. Bangane ba?
Tace wata bakwai kenan da rabuwarmu da mijin.
Sai da Dr Rano ya gama rubuta bayanan da yake da bukata ya ce to me ya sameki?
Kasa dago kai Aishatu tayi tana wasa da wani zobe a hannunta tace kuraje ne suka fito min suna yin ruwa sannan ina fitar da wani ruwa.
Ganin daga nan bata da niyar kara yin wani bayani ga lokaci yana tafiya yasa ya danna wani abu a jikin bango. Ba jimawa wata nurse ta shigo. Gani doctor. Ya tashi daga kan kujerar sa, zan duba patient dinnan ne idan kuma kina wani aikin ki kira wata tazo muyi tare.
A bisa tsarin asibitin idan lalura ta bukaci likita namiji zai duba mace a jikinta sai ya kira nurse mace ta tsaya a wurin saboda kare mutumcin su.
Gadon nurse din ta nuna mata, taso ki kwanta.
Aishatu ta dan zare ido a ina? Dama dai Anti Lawisa ta fada mata da wuya idan ba sai likita ya duba wurin da kansa ba. Shiyasa ma ta jima da ciwon bata yi yunkurin zuwa asibiti ba.
Daga dan guntun bayaninta Dr Rano ya dan gane inda ta dosa. Nurse tana rike da file din ya cigaba da yiwa Aishatu tambayoyi game da abinda idanunsa suka gani a jikinta. Haba dole yaji wari mana. Ita kanta nurse din don bai kamata ta nuna kyamar patient bane amma sai da ta kawar da kanta gefe.
Dr Rano yace Aishatu tun yaushe kika fara ciwon nan?
Wata shida kenan ta amsa daga kwance. Muryarta har rawa take tana magana. Yana kallo ta share hawayen da suka dade cikin idonta tana hanasu sauka.
Tijjani ya cuceta tunda a dalilinsa yau ita ce kwance ana kare mata kallo cike da kyankyami.
Dr Rano ya katse mata tunani...banda kurajen da discharge akwai wurin da ke miki ciwo ne?
Eh marata tana ciwo kuma idan zanyi fitsari da zafi wani lokacin ta amsa idanunta a rufe jin an tura mata wani dogon abu. Bata san nurse din ce ma a kanta ba ba likitan ba. Nurse din tana gamawa tace da Aishatu ta tashi an gama. Dr Rano yace ki kai sample din lab ga request form dinta ki hada dashi.
Wani rubutun yayi sannan ya bata takardar da zata kai wurin ba da magani. Ga wadan nan ki fara sha kafin ayi test din. Ki dawo nan da kwana uku.
Har ta tashi yace Aishatu ki dena sakaci da lafiyarki kinji ko? Rashin zuwanki asibiti da wuri yasa ciwon ya kamaki haka, banda haka da tuni kin manta dashi.
Dan murmushi tayi nagode doctor. Zan kiyaye in sha Allah.
Aishatu na rufe kofa ya dauki wayarsa wadda ta jima tana vibrating lokacin da yake duba Aishatu...sunan Fadila ya gani ta kira sau goma sha hudu. Allah gani gareKa yace don yau kam gidansa bazai masa dadi ba.
RASHIN GODIYA ✂ 3
Shopping yaje yayi mata na tarkacen kayan kwadayi kala kala duk na toshiyar baki. Idan da kayan zaki zaifi jindadin bata hakuri.
Har ya shiga gidan bai ganta ba, yaransa biyu Aliya da Aliyu kadai ya gani suna wasa tare da mai aiki. Da murna suka tare shi ya basu tasu tsarabar...Aliya ina Mamanki? Tana daki ta amsa masa tana barewa kaninta sweet.
Da sanda ya shiga kamar barawo ya tarar da ita a kwance tana kuka. Motsi kadan yasa ta juyo tana kallonsa idanunta jazur sun kankance. Fitar min daga daki munafuki.
Zai yi magana ta hana shi ta hanyar daga masa hannu...wallahi nayi regretting aurenka Huzaifa...ka cuce ni.
A kan gado ya ajiye jakarsa da white coat sannan ya zauna. Yau kuma me nayi Fadila? Meyasa kike son tadawa kanki hankali a banza? Kin san yanayin aikina tun kafin ki aure ni amma ke kullum zuciyarki bata kitsa miki komai sai zargi. Ta ce to ka rasa abinda zaka zama sai likitan mata sai kace wani namamajo. Indai ba tsabar son mata ba meye na specializing akan cututtukansu eyye?
Ledojin da ya shigo dasu ya tura mata. Fadila kiyi hakuri don Allah. Ban taba tunanin cin amanarki ba. Lokacin da kika kira ni dazu ina duba patient ne. Kinga its against dokar asibiti ace kana duba mara lafiya kana waya. Ledojin da ya ajiye ta janyo tana lekawa daya bayan daya...to ai kaine Huzaifa sai ka rinka kula duk wata mace nurse ko patient. Ta dan gutsiri chocolate kaga ai dole na rinka zarginka. Amma komai ya wuce.
Ajiyar zuciya yayi ya tashi zai shiga wanka. Fadila ta bishi har kofar toilet din...Abban Aliya don Allah kada kaci amanata. Ina tsananin sonka shiyasa nake kishinka da yawa. Gefen fuskarta ya shafa tare da daga mata gira..soyayyar da kike min ce ta hana ki ce min sannu da zuwa dana dawo? Sunkuyar da kanta tayi kasa kayi hakuri bazan sake ba. Yanzu ma sharrin shaidan ne. Yayi murmushi haka kika iya ai.
Aishatu kuwa bayan ta karbi magangunanta gida ta tafi. Mamanta Hassana ta gani tare da wasu mata biyu sun zo taya awakin da suka yi mata saura. Da faraa ta shiga gidan ta gaishe su. Sun gama daidaitawa akan dubu shahudu zasu sayi guda hudu. A dole Mama ta amince suka bata kudin suka kada awakin. Duk abinda suke yi Aishatu tana gefe tana kallonsu tana share kwalla. Suna fita tace Mama meyasa kika sayar dasu. Su kadai suka rage fa. Hassana ta yi dan murmushi to Shatu idan bamu yi miki ba waye zaiyi miki? Duk halin da kika tsinci kanki qaddara ce amma laifinmu ni da Babanku. Saboda haka ni dai ina sake baki hakuri ki yafe mana kada mu hadu da fushin Allah. Shatu tace ni ki dena cewa na yafe muku. Kamar yadda kika fada qaddara ce kawai.
To naji yanzu ya kuka yi a asibitin? Kinga likitan da Lawisa ta ke fada. Eh Aishatu ta amsa sannan ta bata labarin yadda suka yi.
Kwana biyu da fara shan magungunan da Dr Rano ya rubuta mata taga kurajen sun fara motsewa da kansu. Hakan yasa kaikayin ya fara raguwa. Babanta Mal Sa'id Jaafar yana ta fafutukar wani abokinsa ya biyashi bashin da yake binsa abin yaci tura. Dan pansho din da ake bashi ma na tsohon malamin makaranta wata na uku kenan shiru. Duk ya damu saboda kanwar matar sa Lawisa ta fada masa ciwo irin na Shatu yana bukatar kudi. Shi kuwa tunda shine yayi silar kamuwarta da ciwon dole yayi iya yinsa don yaga ta sami lafiya. Mashin dinsa ya bugar ya bata wani abin abu a cikin kudin, sauran kuma ya ajiye saboda bukatun gida.
Bayan kwana uku ta shirya ta koma asibitin.
RASHIN GODIYA ✂ 4
Aishatu sammako tayi saboda kada ta tarar da layi,amma duk da haka akwai wurin mutum takwas a gabanta. Hira suke yi abinsu ita kuwa seat din layin karshe taje ta zauna saboda kada a fara gudunta yadda aka saba. Tana nan zaune tana duba wani littafin addu'o'i daga Quran da Sunnah wata mace da a kalla zata bata shekaru goma tazo ta zauna kusa da ita. Kayan jikinta ma abin kallo ne. Kana ganinta kasan akwai wadata. Aishatu na ganin haka ta tashi tsam ta koma wata kujerar nesa da matar. Ga mamakinta sai taga ta taso tazo kusa da ita ta zauna. Aishatu ta sake mikewa sai matar tace haba yar uwa me nayi kike guduna haka. A dan kunyace tace yi hakuri ba gudunki nake ba. Baki ji wari ba da kika zauna kusa dani? Yar dariya matar tayi har hakorin makkanta ya bayyana...kinga yi zamanki nima irin lalurar dake tare dake gareni. Aishatu ta dan gyara zama wa ya fada miki? Risikat matar ta nuna mata. Cewa tayi mu zauna tare tunda duk Dr Rano zamu gani. Aishatu tace au..amma ke banji kina wari ba.
Dariya matar ta zake yi. Ni sunana Sauda ke fa? Sunana Aishatu
Sannu Aishatu. Kin dade da ciwon ne? Kafin ta bata amsa nurse tace Aishatu Sa'id.
Tashi tayi ta tafi room 3 inda Dr Rano yake.
Bayan ya amsa sallamarta a bakin kofa ta tsaya taki karasowa. Fuskarsa ba faraa sosai sakamakon fadan da sukayi da Fadila kafin ya fito.
Ganin da yayi ma Aishatu kamar a tsorace take da dashi yasa ya dan saki fuska. Zo ki zauna, ya dan kalli file din Aishatu ko? ya jikin?
Da sauki Alhamdulillah.
Kina ganin canji da kika fara shan magani?
Eh ina gani
Yayi Bismillah kamar yadda ya saba idan zai fara duba mara lafiya ya dauko result din test din da aka yi mata. Kinga infection kika samu wanda yake barazanar taba miki mahaifa sakamakon rashin zuwan ki asibiti da wuri.
Mahaifa likita ta fada a dan tsorace, yanzu bazan haihu ba?
No ba haka nake nufi ba, da kinzo da wuri dai bazai kai haka ba.
Wasu magungunan ya rubuta mata sannan yace ina bukatar duk panties dinki ki zubar dasu. Ki sayi sababbi kamar shida. Su ma zaki rinka wankesu da ruwan zafi da dettol.
Sai kuma ki rinka amfani da pad saboda discharge din. Kiyi amfani da atleast hudu kullum. Ki yawaita tsarki da ruwan dumi ko da bakiyi abinda ke bukatar hakan ba.
Kanta a kasa saboda kunya ya dan rage murya kina jina kuwa Aisha? Tana dago kai suka hada ido.
A daidai lokacin aka banko kofa da karfi sai da suka mike gabadayansu.
Fadila ce ta shigo a harzuke da wata farar shirt a hannunta...Huzaifa meye wannan? Ta nuna wani jan shati a jikin rigar. Janbakin wace shegiyar ne haka? Da so kayi ka rufe ni ko, to Allah Ya kamaka. Ina hada kayan wanki naganta. Wallahi idan baka nuna min yar iskar da take neman hanani zaman lafiya ba sai na tara maka jama'a.
Aishatu sai ta kalleshi ta kalli matar. Idanunsa sunyi jawur ya rike karfen kujera da hannuwansa. Da gani kasan daurewa yake kada ya karasa gabanta ya shaketa.
A hankali yake magana yanzu Fadila da izinin wa kika fito? Kuma wurin aikina ne kika ga ya dace muyi wannan zancen. zata sake magana ya kama hanunta ya kalli Aishatu idan zaki iya ki dawo karfe biyar, sai in ganki a lokacin. Ya ja hannun matarsa suka fita.
RASHIN GODIYA ✂5
Aishatu ta dade a tsaye tana mamakin wannan al'amari da ta gani, wannan matarsa ce ko budurwa? Nurses din da suka ga fitowar Dr Rano suka sami abin gulma. Ba karon farko ba kenan da Fadila ke zuwa. Ita dai Aishatu fitowa tayi a sanyaye ta koma wurin zamanta ta zauna. Shaf ta manta da Sauda sai da tace mata har kin gama? Tace a'a likitan ya fita ne amma yace zuwa karfe biyar zai dawo.
Sauda ta tashi to ai gara mu tafi gida. Yanzu fa sha biyu da kwata ai kinga akwai zama. Aishatu ta gama yanke shawarar zama a asibitin don kudin hannunta take tsoron yiwa gibi kada ta kasa siyan magani. Sauda ta dan tafa hannu tunanin me kike yi ne? Tashi mu tafi mana.
Uhmm ba komai ki tafi kawai ni zan jira har biyar din.
Sauda tace ko gidanki da nisa ne? Eh Aishatu ta amsa ta dan gyara zama. Kudin da zata kashe daga yan kaba zuwa gwammaja gidansu ai ba kadan bane. Gara kawai ta jira ta gama gabadaya.
Sauda tana ta kallon yadda Aishatu ke zama lost in her thoughts tace kinga layi biyu zaki wuce tsakanin asibitib nan da gidana. So ki zo muje ko don yin sallah. Da farko Aishatu taki yarda sai da Sauda tayi ta roko da magiya.
Wata farar benz taga Sauda ta nufa. Suna shiga ta kunna AC din motar ta ja suka tafi. Basuyi tafiya mai nisa ba suka je gidan Sauda. A ranta Aishatu tace tsabar gata yar wannan tafiyar ma sai an shiga mota. Wani dattijo ya taso ya bude musu gate, Sauda cikin ladabi ta gaishe shi sannan ta shiga tayi parking din motarta.
Yara biyu ne duk yan mata wanda babbar bata wuce shekaru goma ba suka taho wurinta da gudu suna mata sannu da zuwa. A tare suka durkusa suka gaishe da Aishatu ta tambayesu sunayensu. Babbar tace sunana Sajida wannan kuma ta nuna kanwar sunanta Islam. Wadda aka kira Islam ta suma kuka Umma kinga ta fadi suna na bata jira na fada ba ko. Aishatu ta durkusa a gabanta tana rarrashinta ni banji me ta fada ba ma. Islam tayi wa Sajida gwalo Allah Ya kara bata ma ji ba. Sajida tace Umma kin ganta ko. Anti sunana Aisha amma Islam Ummana take kira na. Aishatu tayi murmushi ashe ma sunanmu daya. Islam sai murna ta rike hannun Aishatu. Sauda tace to kaji ya isa haka fadan kun tsare min bakuwa a waje.
Falon gidan Sauda ma abin kallo ne ga Aishatu. Bayan sunyi sallah Sauda ta kawo musu abinci. Da kyar Aishatu taci kadan saboda ta kasa sakin jiki da Sauda. Suna gamawa Sauda tace naga baki kira mijinki kin sanar dashi ba kada yaji shiru. Aishatu ta dauko yar motsatstiyar wayarta da tasha salatif, batir din wayar ma ana ganinsa don bata da cover din baya. Mama ta kira ta sanar da ita. A dan zaman da suka yi Aishatu ta fahimci Sauda tana da kirki shiyasa ta dan saki jiki da ita. Sauda tace mijinki yana karbar treatment kuwa? Don idan ke kadai ke shan magani indai yana da infection bazaku warke ba. Aishatu ta ce auren ya mutu.
Ba dai dalilin ciwon ba ko. Allah sarki. Kinga ni na kawo mana ciwon nan gida gashi watan mu na uku kenan da fara neman magani kuma Alhamdulillah sauki ya fara samuwa. Musamman bayan mun fara ganin Dr Rano.
Aishatu tace ai naga kamar yasan abinda yake yi. Nima kwana na uku da fara zuwa amma kinga kaikayin ma ya ragu sosai.
Haka suka zauna suna ta hira. Har Sauda ta bata labarin yadda ta sami ciwon ta. Wato Aishatu duk macen da bata da godiyar Allah komai kudi komai rashi to tana tare da matsala babba a rayuwa. Ni kinga Baban Sajida babu irin abinda baya min na jindadin rayuwa. Duk kasar da yaje saboda yanayin aikinsa sai ya yi min tsarabar sutura mai yawa. Allah Ya hada ni da wata makociya mai rokon tsiya. Itama fa mijinta nada rufin asiri amma roko tamkar a jininta yake. Kuma aron na kaya ne. Daga hijab zuwa mayafi ta fara. Kafin na ankara mun fara exchanging kaya. Ta karbi nawa taje taro nima na karbi nata. Duk abinda akeyi maigidan bai sani ba. Sai wata rana naje gidan zamu biki tare na fara period duk na baci. Kawai ta dauko min pant a cikin kayanta ni kuma ganin mun zama daya kawai na saka. Wallahi Aishatu sai da baban Sajida yayi kusan wata uku baya fita saboda irin kurajen da muka rinka yi. Ga wani ruwa mai wari...nayi kuka nayi dana sani sosai, baki ga yadda na rinka bashi hakuri ba don na zata saki na zaiyi wallahi. Kinga sai ya gaggauta gama gininsa muka dawo nan don ya raba mu. Shiyasa yanzu ladabin da nake masa ko kadan nasan banyi rabinsa ba ma da.
Aishatu ta jinjina labarin tace amma Anti Sauda gara ke sau dubu akai na. Ni da kika ganni namiji duk kyansa akai kasuwa. Sauda tayi dariya haba kanwata ayi haka kuwa...Aishatu tace ai anyi ma.
Labarin Aishatu Sa'id Jaafar
RASHIN GODIYA ✂6
Iyayen Aishatu duk yan garin Getso ne a jahar kano. Babanta Mal Sa'id yayi karatu har NCE yayi. Bayan ya gama ya sami aikin koyarwa a makarantar gwamnati sannan ya auri Hassana mahaifiyarsu. A Gwammaja ya ke zaune tare da iyalinsa Allah Ya azurta su da 'ya'ya hudu. Aishatu ce babba sai kannenta maza uku Sadiq, Nurain da autansu Mahmoud. Iyayensu suna zamansu lafiya. Hassana tana kiwon awaki da tumaki sannan tana sayar da zobo.
A haka yaransu suka yi karatu. Aishatu tana aji biyar a secondary school ta hadu da Fahad sun tare da iyayensa a kusa da gidansu. Tun da ya ganta yake sonta idan yayi mata magana ko kallo bai isheta ba saboda tana ganinsa da su Garzali daya daga cikin fitinannun unguwar. Babban burinta a rayuwa ta zama lawyer. Lokacin tafiya teaching practice Fahad ya nemi makarantar su Aishatu. Nan fa yan mata da yawa suka nuna mishi so saboda dan gayu ne na ajin karshe. Kullum kayan jikinsa sai kaga karin guga ya saka turare yana baza kamshi. Lifan dinsa kuwa kafin a tashi sai yasa maigadi ya kara wanke masa shi. Duk abinda yake yi don Aishatu tayi noticing dinsa ne, ita kuwa ko a jikinta. Karshe ma tunda ya rinka nunawa kamar kanwarsa ce ita tunda su makota ne sai ta biye masa. Duk yarinyar dake sonsa sai ta rinka kamun kafa da Aishatu.
Duk hanyar da Fahad zai bi don ya sami kan Aishatu yayi amma abin ya faskara. Karshe Fahad dai mahaifinsa yasa yaje gidansu Aishatu nema masa aurenta. Mal Sa'id ya yaba da karamci irin na gidansu Fahad da yadda suka fara tuntubarsa kafin ma yayi magana da yarinyar. Wannan dalilin yasa ya yi alqawarin bawa Fahad auren Aishatu bayan ta gama WAEC. Amma da sharadin zata cigaba da karatu bayan anyi auren.
Tunda Babanta ya sanar dasu Mama ke ta murna. Ko ba komai yaron yana da nutsuwa a ganinsu. Duk kawaici irin na Aishatu sai da ta nuna bata so har ta sanar da iyayenta irin abokansa na unguwar. iyayenta suka ki yarda da maganarta, a ganinsu samun dan mutumci kamar Fahad a irin wannan zamanin sai an tona.
A haka Fahad ya rinka bibiyar Aishatu da dukkan kyautatawa tana wulakanta shi son rai. Idan yazo sai Mama ta fattattake take fita.
Wata rana yana mata hira a soron gidansu ta hade fuska. Ita ko kadan bata son Fahad, taki jinin namiji mai ji da kansa kawai don yana da kyau. Wannan kuwa halin Fahad, suna zaune sai juya wayarsa yake yi. Sabuwar model ce don sai da ya sayar da tv din dakinsa ya cika ya saya. Duk yadda yaso ta nuna tayi noticing wayar ma taki. Can yar karamar wayarta tayi ringing taga sunan dan wan babanta Kamal. Da sauri ta dauka harda kara kashe murya don Fahad yaji haushi. Nan ta rinka magana cikin jan hankali har Kamal sai da yayi mamaki. Kusan minti ashirin yana son ajiyewa tana sake jan hirar. Iyakar kulewa Fahad yayi don shi mutum ne mai tsananin kishin abinda yake so.
Tana gama wayar ta dan kalle shi ni zan shiga gida sai da safe.
Tasss taji ya dauke ta da mari, ni zaki yiwa wulakanci Aisha? Don kinci saa nace ina sonki.
Duk masifar da yake mata bata fahimta saboda yadda marin ya shigeta. Hawaye ne kawai yake wanke mata fuska. A zuciyarta ta kudire bazata taba yarda ta aure shi ba.
RASHIN GODIYA ✂ 7
Ihunta yasa Mama ta fito soron da gudu. Aishatu me ya faru? Ta kalli Fahad ..me ya sameta Fahad. Aishatu zata yi magana ya durkusa har kasa gaban Mama sai ga hawaye a idanunsa kamar famfo, Mama cewa tayi ko zan mutu na dawo bazata aureni ba. Nace ta manta iyayenmu sun riga sun shiga maganar. Shine ta soma kuka ita da ta aure ni gara ta mutu. Ran Mama yayi matukar baci tunda tasan dama Aishatun ba son Fahad take ba.ta dubi yarta da ta rike kumatu kin kyauta Aishatu tunda ke kike da iko akan ki ba mu ba. Bari babanki ya dawo zan sanar dashi gara ayiwa tufkar hanci mara kunyar banza.
Wallahi Mama sharri yake min. Mari na yayi
Wani marin taji daga mahaifinta da ya shigo gidan a lokacin kuma duk yaji abinda suka ce. Wato ke ban isa da ke ba ko. Da ina miki kallon saliha ki rinka mikil mikil da ido kamar mutuniyar kirki.
Fahad ya durkusa a gaban Mal Sa'id yana bashi hakuri. Baba ni na janye gara a bari ta zabi wanda take so. Baba yace ai bazaayi haka ba Fahad, ka turo min Alhajin gobe muyi magana asa lokacin biki. Sai nayi maganin wannan rashin kunyar taki.
Mama tace kayi min daidai, suka shige gida suka bar Aishatu da baki a bude. Fahad ya yi mata wani kallon banza..kadan ma kika gani Aisha. Ni din nan nafi karfin mace ta wulakanta ni. Macen ma irinki wadda bata gama wayewa ba. Yana gama magana ya fice abinsa.
Daren ranar Aishatu tasha kuka. Mama na jinta duk tausayinta ya kamata amma ta share. Yarinya alkhairi na bin ta tana sa kafa tana shurewa. In ba haka ba meye aibun Fahad.
Iyaye maza sun hadu an tsayar da biki wata biyu. Hakan yayi daidai da gama jarabawar qualifying da Aishatu zata yi. Ba karamin tashin hankali ta shiga ba jin cewa ko SS3 baza tayi ba. Wan babanta ba yadda baiyi ba amma Mal Sa'id yaki hakura. Tun wan nasa Alh Dalhatu yana fada har ya koma nasiha saboda yasan kafiya irin ta kaninsa. Suna zaune a dakin mahaifiyarsu a Getso, Alh Dalhatu yace wai Sa'idu shin yaron nan ko iyayensa sun maka wani abu ne da ka kafe sai ka bashi 'ya. Gwaggo Juma tace banda lalacewa ma ai dan uwanka ya dace ya bada ita ba kai ba. Baba gyara zama ni dai kuyi hakuri amma yarinya karama bata isa na rinka sa'insa da ita akan maganar aure ba. Jiya fa a gabana ta kare masa tanadi da yazo. Har tana cewa shi makiri ne. Yaya kaji fa, dama ya fada min a makaranta ake hure mata kunne. Shiyasa nake son cireta kowa ya huta. Duk shawarar da aka bawa Baba sai ya kawo uzurinsa. Dole suka kyale shi da matarsa suka rinka shirye shiryensu na biki.
Lokacin kamar yasan Aishatu gudunsa take ya rinka sauri. Ranar larabar da suka gama jarabawa akayi kamunta. Kawayenta sunyi mamaki sosai don babu wanda ta fadawa. Mamakinsu ya karu da suka ga Uncle Fahad ta aura. Daga masu tayata murna sai yan hassada. Kyakkyawan mutum kamarsa ya kare da Aishatu. Ba wai bata da kyau ba amma kyale kyalen rayuwa basu dameta ba. Ranar asabar aka daura aure da yamma aka kaita dakin mijinta.
RASHIN GODIYA ✂ 8
Aishatu zaune gaban kakarta Gwaggo Juma, tayi kuka har ta gaji. G.Juma ta kawar da kanta gefe ta share yar kwallar da ta taho mata. Ba don Aishatu yarinya ce mai kyaun hali ba da ba zata damu ba saboda irin abinda Baba yayi musu na nuna musu iyakarsu akan yarsa. Kiyi hakuri Aishatun Nabiyy, wadda kika gaji sunanta uwa ce ga dukkan mumini kuma duniya ta shaida mace ce ta kwarai. Aishatu cikin kuka tace ni Gwaggo Allah idan aka kaini guduwa zanyi. Kowa yaki ganewa amma Fahad mugu ne ga iya sharri. G. Juma ta rufe mata baki da hannunta wanda yasha jan lalle gabadayansa, kul kike irin wadannan maganganun. Ya riga ya zama mijinki. Kuma idan har na isa dake zaki yi amfani da shawarar da zan baki. Ki rike Allah ki tsayar da gaskiya a dukkan lamuranki. Kiji tsoron Allah kada ki tarwatsa rayuwarki kawai don ba kya son mijin da Allah Ya rubuta zaki aura. Duk matan da suke guduwa ko kashe miji saboda kiyaya wallahi komai dadewa sai sunyi dana sani. Ki auri mijin da ba kya so ma ai jarabawa ce. Idan kika yi hakuri kuma kika dage da kyawawan halaye sai kiga Allah Ya daidaita ku. Idan ko har babu alkhairi a auren to da sannu Allah zai warware shi Ya baki rabonki. Duk abinda hakuri bai baki ba to rashinsa ma bazai baki ba. Ni so nake ko bayan babu ke idan ana kwatancenki ace ke mace ce mai biyayya ga Allah. Shiyasa kika bi mijinki sau da kafa. Aishatu ta dago kanta ta kalli fuskar kakarta nagode Gwaggo. In Sha Allah zanyi amfani da shawararki. G. Juma da sauran yan uwansu suka tashi suka tafi dama motocin kawo amarya suka biyo.
Fahad da kansa ya shigo gidan ya tarar da yan kawayenta uku da basu tafi ba yace su fito kada su rasa mota. Daya daga cikinsu tace haba ango ai baka sallame mu ba. Dari biyu ya zaro daga aljihunsa ya mika mata, gashi nan ku shiga mota. Allah Ya bamu alkhairi. Ganin yadda ya hade fuska babu wadda ta sake magana suka da uko jakunkunan su suka fice.
Duk muguwar niyar Aishatu na cusguna masa shawarar G. Juma tasa ta watsar. Shiyasa da ya shigo dakin da sallama ta amsa masa fuska a sake. Wuri ya samu ya ajiye ledar hannunsa. Kaza ce guda daya gasashshiya sai juice mai sanyi. Kitchen ya tafi ya dauko plate ya zuba kazar gaba daya ya dan barbada yaji a kai ya fara ci ko kallon Aishatu bai yi ba. Ba dai tace bata son shi ba. Zata gane bata da wayo don yana da mugun riko. Gidan da suke sama da kasa ne da babansu yake ginawa yaransa. Kasa yayansa ne Khalid da matarsa Maryam da yaransu biyu. Saboda riko irin na Fahad ya dena kula wan nasa saboda ya hanashi aron mota.
Aishatu tana ta kallon ikon Allah sai da Fahad ya cinye naman gaba daya ya shanye juice dinsa. Dama karamin kwali ne daidai shan mutum daya. Yana gamawa ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya nemi wuri ya kwanta. Da tana sonsa ba karamin haushi zata ji ba amma yanzu dariya ya bata. Tana nan zaune taga da gaske dai bazai kula ta ba sai ta tashi ta dauki wata doguwar riga da hijab ta shiga toilet ta canja kaya. Da hijab din ta fito a jikinta ya dan tabe baki meye kike ta wani rufe jiki kamar abin arziki ne a ciki. Ita dai bata ce komai ba ta shimfida abin sallah ta tayar. Kafin ta idar yayi nisa a baccinsa. Itama tana idarwa bacci ya dauketa akan abin sallar.
Mafarki takeyi wai kunama ta harbi babban dan yatsanta na kafa wani irin zafi har tsakar kanta. Tayi saurin bude ido da salati ta ga Fahad tsaye a kanta yasa kafa ya take mata dan yatsan kafa. Tayi saurin janye kafar lafiya Fahad taka ni fa kake yi. Karfe nawa yanzu kina kwance kina baccin asara. Ba sallah ba girki bare na ganki kinyi wanka. Tayi sauri ta tashi tana shafa dan yatsanta. Kayi hakuri in sha Allah bazan sake ba. Ki wuce akwai dankali da kwai ki soya kuma kada ki bata lokaci don yunwa nake ji.
Sallah kawai Aishatu tayi ta shiga kitchen din. Dankali ta gani dan kadan an zube a kasa sai kwai gudu biyu a cikin farar leda da bread. Zama tayi ta kirga dankalin, guda ashirin ne cif. Ikon Allah lallai Fahad mutumcinsa ragagge ne...sai tayi saurin rufe bakinta da hannunta Astagfirullah...lallai Fahad mutumin kirki ne.
Ta soya dankali da yayi kukut a plate da kwai guda biyu ta hada da bread din duk ta dora akan tray. Sannan ta zuba ruwan zafi a flask ta kai masa falo. A gabansa ta ajiye komai ya share dankalin da kwai ya rage mata bread. Bata nuna bacin rai ba ta hada tea ta sha da sauran bread sannan ta dan yi gyare gyare a gidan.
RASHIN GODIYA ✂ 9
Dayake aikin ba wani mai yawa bane bata dade ba ta gama tayi wanka. Duk da ita ba mai yin kwalliya bace amma yau ta bata lokaci sosai a gaban madubi. Addua take Fahad ya dena fushin da yake da ita har ta sami damar rokonsa ya barta ta cigaba da karatu.
Riga da skirt ta saka dinkin yayi mata kyau sosai. Jikinta yasha turare kala kala ta fito falo ta same shi zaune yana duba wasu takardu. Wata kujerar ta samu ta zauna Fahad zan sauka kasa mu gaisa da matar Yaya Khalid. Ko kadan bai nuna alamun ya ji ta ba bare ya bata amsa. Fahad magana nake fa...Aisha shiru nake fa ya bata amsa. Tasowa tayi ta durkusa a gabansa...don Allah kayi hakuri da dukkan abinda ya faru kafin muyi aure. Na gane kuskure na kuma in Allah Ya yarda zan gyara. A hankali ya dago suka hada ido....ko baa fada ba Fahad kyakkyawa ne sai dai kuma kyan dan maciji gareshi tunda bashi da halin kirki. Aisha kenan daga kwana daya har kin rissina, ko dai kazar da na ci jiya ban baki bace kike neman yin rigakafi? To bari kiji in fada miki, na so ki sosai da farko amma yanzu kin sire min. Auren ma don na nuna miki kinyi kankanta ki ja dani ne. Duk da ta tsorata da kalamansa bata karaya ba ta rinka bashi hakuri. Kafa yasa ya shureta ya fice.
A haka suka yi sati uku da aure ko matattakalar benen yace Allah Ya isa idan taje. Tana daga sama kamar tsuntsu sai dai ta ji hayaniyar yaran shima ba sosai ba. Wata ranar litinin da safe Fahad yana ta sauri zai je makaranta don a lokacin yake level 4. Lectures gare shi karfe takwas na wani malami mara kirki irinsa. Sai sauri yake kamar zai tashi saboda ya makara. Sai da ya gama shiryawa ya nemi assignment dinsa da ya kai karfe ukun dare yana yi ya rasa. Ga takardu da sauran books dinsa amma babu paper din da yayi aikin. Aishatu tana goge kitchen ya shigo rai a bace..to yar mara mutumci ina paper din da kika sace min? Kallonsa tayi ta watsar ta cigaba da aikin ta. Ya daka mata tsawa Aisha ba magana nake miki ba? Lokaci ya kure wallahi idan har ya shiga ajin bazai karba ba. Nan ma shiru yaji ba magana. Fizgota yayi cikin fushi idan na makara jikinki ne zai fada miki. Naga yana miki kaikayi saboda ban taba dukanki ba. A nutse ta yi masa magana..ni ban taba maka komai naka ba. Gudun kada wani abu ya faru ma yasa ko falon ban gyara ba na bari sai ka fita.
Idan baki taba ba ubanki ne ya dauka?
Ba dai ubana ba ta bashi amsa tana kokarin kwace hannunta da ya murde.
Idanunsa kamar garwashi jin agogon falo yana kara alamun karfe takwas din tayi. Hannunta yaja har falo yayi wurgi da ita akan kujera. Goshinta ya bige da kujerar ta kwala ihu. Bai barta haka ba ya soma dukanta.
Kofin tea din da ke hannun Khalide ne ya fadi da yaji wani gigitaccen ihu da Aishatu ta saka. Mikewa yayi da sauri sai ga Maryam ta fito da gudu. Kaji ihun amarya ko? Don Allah kaje ka duba kada ya kashe musu 'ya. Khalid yace maryam kamar baki san Fahad ba. Yaron nan bashi da kirki ko kadan yanzu ina zuwa sai ya hada ni da Alhaji, shi kuma baya son laifinsa. Matar ma ko sau daya bata shigo nan ba fa. Maryam tace kaima ka biye masa ka hanani hawa saman ba. Wani ihun suka ji tana bashi hakuri ba shiri suka hau saman. A kwance take ya daga kafa zai bige ta Khalid yayi saurin janye shi. Ita kuma Maryam ta daga Aishatu wadda goshinta ya tashi saboda buguwa ga jini a bakinta. Tana kuka ta kankame Maryam tace Fahad Allah zai saka min kuma in sha Allah sai kayi carryover.
Khalid ya kalli kaninsa cike da takaici me tayi maka haka kake dukanta. Yaya ba ruwanka da iyalina,idan ba rainin hankali ba in zauna har karfe ukun dare ina aiki ta dauke takardar don mugunta. Khalid yace ka duba ko ina baka gani ba. Na duba mana yana magana ya dauko jakarsa kinji dadi tunda kin hanani zuwa makaranta zan zauna a gidan muci uwar da zamu ci dake. Kayan jakar ne gaba daya suka zube a kasa saboda zip din a bude yake. Papers dinne suka fara fadowa ya daukosu cike da farinciki...Subhanallahi ashe da na gama a jaka na saka don kada na manta su a gida. Duk su ukun yaga suna masa kallon tuhuma yayo wurin su Maryam. Don Allah Aisha kiyi hakuri wallahi tsautsayi ne. kukanta kawai take taki kallonsa. Daga yau na amince ki rinka zuwa wurin Anti Maryam hira idan na fita. Nan ma bata ce komai ba da yake bashi da kunya yace Yaya ku tayani bata hakuri mana. Shi Khalid ficewa yayi yana sauka ya kwalawa Maryam kira. Aishatu ta kalle shi a tsorace kada ya sake dukanta.
RASHIN GODIYA ✂ 10
Matsowa yayi kusa da ita yaja hannunta suka zauna a bakin kujera. Kana ganinta kasan a tsorace take. Hankici ya dauko daga aljihunsa ya soma goge mata lebenta da ya fashe. Kiyi hakuri Aisha nasan ban kyauta miki ba. Ina da saurin fushi ne da riko amma zanyi kokarin canjawa kinji. Kai kawai ta daga don bakinta ya kumbura. Ya yi dan murmushi kinga bakinki kuwa kamar an cusa fanke. A wahale tayi murmushi yace ko ke fa. Ki daure mu gina rayuwa mai kyau mu manta da dukkan abinda ya wuce. Kin hakura? A yadda ya tsareta da ido ai dole tace ta hakura ko don kada ya sake dukanta.
Tun daga ranar Fahad ya koma lallabata. Sunje gidan iyayenta da nasa sun gaishe su sannan ya barta tana zuwa wurin Maryam ko ita ta zo ko yaranta. Zaman su abin shaawa a lokacin saboda Aishatu ta iya zama da mutane. Kuma ladabin da take masa yasa ya kara sassauta mata.
Matsalar da suka fara fuskanta ta fara daga abinci da suke ci tare. Kullum suka zauna cin abinci ita ce karshen tashi. Tun baya magana har abin ya soma damunsa. idan ta fiye cin abinci kiba zata yi, shi kuma baya son tayi kiba. Dan jikinta a yanzu yayi masa shiyasa ko ciki baya son tayi sai an kwana biyu tunda da kuruciyarta. Wata shawara ya yankewa zuciyarsa washegari ya fara amfani da ita. Dama idan bashi da lectures kasuwa yake tafiya wurin babansa. Ranar zai tafi kasuwa sun gama breakfast tana fitowa daga kitchen taga ya kulle kofar yasa key a aljihunsa. Lafiya ka rufe kitchen din Fahad? Lafiya kalau, kawai na fi son sai na dawo zaki rinka dora abinci sai muci a alokacin. Likitoci sun ce yafi lafiya. Tohhh idan naji yunwa fa ko nayi baki? Kada ki damu zan saka fridge a falo sai a cika shi da ruwa. hannu ta zira a aljihun rigarsa inda ya sa key din...kaga bana son wasa Fahad ka bani don yau sinasir zanyi har da su Anti Maryam nake son aikawa kaga gara na fara da wuri. Hannun nata ya kama ya matse tare da zaro key din Allah da gaske fa nake. Wannan shegen cin da kika tsira kwana biyu kamar gara bazan jura ba. Salon kiyi muni kisa na fara kallon sirara a waje. Abu kamar wasa sai ga Fahad ya fice da key din kitchen. Haka ta koma girki biyu a rana. Daga na safe sai na yamma bayan laasar. Shima da kansa yake auna mata abinda zata dafa. Shi kuwa a waje zai take cikinsa. Babu wanda tayi yunkurin fadawa sirrin gidan ta. Kullum addua take Allah Ya sa ya canja hali. Wata daya da fara horon yunwar da Fahad yake mata ta rame sosai ta kara haske. Anti Maryam tace kanwata ko dai ciki gareki. Dariya kawai tayi ina ciki zai shiga ana fama da yunwa??? Cikinta taji ya fara murdawa saboda tsabar yunwa. Lipton kawai suka sha yau da wani guntun bread. Da farko daurewa ta rinka yi, a hankali abin ya fara tsanani har Maryam ta lura. Aishatu ya dai me ya sameki...jini ta gani yana bin kafar Aishatu ta kamata da kyar suka shiga toilet sai ga wani gudan jini kato ya fado. Anti Maryam ta ce Aishatu bari kika yi fa. Dama ciki ne da ke? Jikinta duk a mace tace ban san dashi ba anti. Anti Maryam ta kira Khalid a waya yazo ya kaisu asibiti lokacin Aishatu ko tsayawa bata iya yi. Likita na dubata yace da Khalid ai dole tayi bari. Mace da ciki ga yunwa tana neman yi mata illa. Ai baa biyewa mata idan suna laulayi mai hana cin abinci. Ko yaya sai a basu wani abin da zai zauna. Shi khalid mamaki ne ya kamashi wai yunwa! A gidan Fahad din? Lallai dole Alhaji yaji wanan magana.
Sai da aka gama komai na asibitin aka sanar da Fahad yazo. Iyayensu da sauran yan dubiya na fita Fahad ya matso kusa da gadon ya rikewa Aishatu hannu. Meyasa baki sanar dani kina da ciki ba Aisha? Hawaye suna zubo mata tace nima ban sani ba. Share mata hawayen dena kuka kinji dama ni ba son haihuwar nake yanzu ba. Sai na gama makaranta nayi service sai ki haihu. Ashe shiyasa kika rinka shegen cin nan kwanaki kamar ahalin yunwa. Kada ki damu zan karbar miki maganin planning. Khalid da ke jikin kofa yana jin abinda kaninsa ke fada yayi tsaki. Allah wadaran halin yaron nan.
RASHIN GODIYA ✂ 11
Kwananta biyar aka sallameta. Kulawa kam tana samu a wurin Fahad sai dai kullum dare kafin su ci abinci zai bata kwayar magani. Lallabata yayi yace maganin zai hanata daukab ciki yadda zata samu damar komawa makaranta tayi WAEC da NECO. Sai dai lokacin yanayi ya tsiri abinda zai hadasu fada yadda bazai biya mata kudin ba sai wata shekarar. A haka suka zauna har yayi jarabawarsa ta karshe. Da murnarsa yaje makaranta duba result. Abin bakin ciki yana da spillover a course din da Aishatu tayi masa addua ranar da yayi mata duka. Da bacin rai ya nufi gida yau jikin Aisha zaiyi tsami ya fada a ransa. Muguwar yarinya ashe da gaske tayi masa wannan adduar.
A tsorace ta fito daga bandakin da PT strip a hannu, Anti Maryam kin gani layi biyu ne. Maryam ta rungumeta tana murna Alhamdulillah Aishatu Allah Ya raba lafiya. Aishatu kuwa jikinta har rawa yake tace na shiga uku na yau me zan fadawa Fahad? Bangane ba Maryam ta tambayeta. Abin arzikin ne kike cewa me zaki ce masa? Karar babur dinsa ta ji yana turo shi cikin gate din. Cikinta yayi wani mugun murdawa don tsoro. Sosai Fahad yake jaddada mata rashin son haihuwa a yanzu. Gashi ta dan samu saukin irin yadda yake zama da ita. Ta fara zubar da hawaye ba kakkautawa Maryam ta rike hannunta suka zauna. Aishatu ko planning kuke yi ne? Ita dai bata bada amsa ba ta tashi ta hau sama a sanyaye.
Irin kallon tuhumar da yake mata yasa ta kara tsorata kamar yasan abinda ya faru. Suna shiga falo ya kama kofar ya kulle ya zaro belt din wandonsa. Akan gwiwarta ta durkusa tana bashi hakuri. Wallahi Fahad bansan haka zai faru ba. Tsautsayi ne kayi hakuri.
Bai ko saurareta ba ya fara tsula mata. Har ni zaki yiwa cuta irin wannan. Ta bude baki zata kara magana yace rufa min baki makira. Dama nasan har yanzu ba sona kike ba ahiyasa kike min muguwar addua. To burinki ya cika na sami carryover saboda haka kema haihuwarki ta kara nisa. Sai na gama makaranta kamar yadda na fada miki nayi service kuma sai na sami aiki. Ai fadan da taji yana yi yasa ta fasa fada masa tana da ciki. Gara tayi shiru kawai idan ya fito idonsa ya gane masa.
Tun daga ranar aka koma gidan jiya. Ga rashin wadataccen abinci ga wulakanci kala kala. Ko kadan bata fada masa tana da ciki ba.
Wata alhamis ya dawo daga kasuwa a gajiye ga yunwa bazai iya jira ya auna abincin da zata dafa a lokacin ba. Indomie biyu ya dauko mata yace ta dafa masa. Tun da ta dora amai yake taso mata tana daurewa. Da kyar ta gama ta kai masa ya bata guda daya yace ta dafa tace ya kula jikinta ya fara budewa. Tana mikewa amai ya kwace mata ta rinka kwarawa a wurin. Ya tashi a fusace wai me kike nufi dani ne Aisha? Ya zaki rinka min amai don ki haramta min abinci. Abba dan maryam yana bakin benen ya jiyo kakarin amanta ya ruga wurin mamansa. Anti Aishatu zata yi amai Mummy. Da sauri ta hau saman ta bude kofar falon. Aishatu ta gani tana amai tana gyara wurin da ta bata. Duk tayi kaca kaca da wurin. Maryam ta harare shi amma kai dai Allah wadaran halinka. Mace na fama da ciki kana kallo ka zuba mata ido tana wahala. Ya kalli Aishatu da ta tsure ya kalli Maryam. Ciki kuma??? Garin yaya? Me yasa baki fada min ba. Baki na rawa zata yi magana Maryam tayi saurin gyara zancen...dama surprise zata maka to kuma yadda kayi mata yanzu ne ya bani haushi shine na fasa kwan.
Sai da ta gyare wurin ta sauka a ranta tana fargabar abinda zata jawowa Aishatu. Ai kuwa taba fita sabanin ya nuna fushi sai ya nuna kamar yana murna da cikin. Ai da kin fada min da wuri saboda zuwa asibiti. Wata nawa ne yanzu. Kai a kasa tace nima ban sani ba. Amma ina jin zai kai uku. Masha Allah sannu kinji.
Sai dare yace ta dauko masa maganin da yake bata na planning. Ya duba ya tabbatar bata fashin shan maganin. Dan murmushin yake yayi yana tunanin yadda zaiyi yasa cikin ya zube. Ina shi ina 'ya'ya yanzu. Kuma sai ya rama abinda tayi masa na muguwar addua. Ita kuwa Aishatu ta gama saka rai da abinda ke cikinta. Duk abinda Fahad ke yi mata bata damuwa burinta ta haihu lafiya. Su Mama sai murna da ganin cikin wanda har ya kai wata hudu. Fahad na kwance akan gado lokacin ya rasa me ke masa dadi don mamansa tace ya bawa Aishatu dubu hamsin ta fara siyan kayan haihuwa. Sassaken maganin daya karbo ya dauko yana kallo. Gaskiya bazai iya bari ta haihu ba. Baya kaunar 'ya'ya yanzu ko kadan. Falo ya bita ya mika mata jikon. Aisha ga wannan kisha saboda saukin haihuwa. ta karba da hannu biyu nagoda Allah Ya saka da alkhairi. Amin, bari na dauko miki cup. Da kansa ya zuba ya bata. bata kawo komai a ranta ba ta shanye shi tas. Cikin dare suna kwance cikinta ya soma murdawa. Ta dan taba shi Fahad cikina ciwo...wani murmushi ne ya kwace masa yayi wata munafukar mika sannu ko inyi miki tausa ne? Tana yunkurin tashi daga kan gadon jini ya balle mata.
RASHIN GODIYA ✂ 12
Kuka Aishatu tasa masa Fahad don Allah ka taimakeni kada na rasa wannan ma. Tasowa yayi kamar gaske duk a rude. Bari na shiga toilet gani nan zuwa. Bandaki ya shige ya bata lokaci sannan ya fito. Zuwa lokacin Aishatu har ta fara fita hayyacinta. Kinkimarta yayi kasa ya bugawa su Khalid kofa Yaya don Allah ka taimaka ka zo muje asibiti Aishatu ce ba lafiya. Su ma duk sun rude haka Khalid yazo ya fitar da mota suka tafi asibiti. Kafin su karasa Aishatu tayi karamar haihuwa tayi barin cikin wata hudu.
Likitoci sun bata dukkan taimako don har wankin ciki aka yi mata. Sai gabanin asuba ta farka taga Mama da Hajiyan su Fahad a dakin. Suna hada ido da Mama ta fashe da kuka. Hajiya ta zo ta rungumeta...yi hakuri Aishatu qaddara ce wadda bawa ba yadda zaiyi da ita. Ita dai Aishatu kuka take yi kawai Mama tana bata hakuri. Sai dare Fahad ya shigo...Hajiya ta fara masa fada yace Hajiya ni bazan iya ganin Aishatu a wannan yanayin ba. Duk mun gama sa rai...sai hawaye sharr kamar yaro. Har kudi na hada zan bata ta fara siyayya ashe ba rabonmu bane. Mama tace haba Fahad kaine ya kamata ka bata hakuri. Ku karfafi zuciyarku. Haka suka yi ta basu baki. Baban Aishatu shima yaji tausayin Fahad sosai don abinci ma baya ci a cewarsa duk jikin matarsa ke damunsa.
Kwanaki uku da kwanciyar Aishatu tana bacci dakin shiru Maryam ta tafi gida dama mata kunu. Su Mama basu karaso ba sai ga Fahad ya shigo. Ganin tana bacci ya hakince akan kujera yana waya da Audu Kulli mai magani. Audu yace mutumina kuma sai naji ka shiru ko maganin baiyi bane.
Fahad yace inaaa mutumina ai gamu a asibiti ma magani yayi kyau. Wallahi a ranar ma cikin ya zube da daddare. Ai wannan karon allura zansa ta rinka yi don naga maganin baya hana daukar ciki. Da su na taho ma zan mayar da sauran.
Sai da ya gama maganarsa Aishatu ta tashi rai a bace. Allah Ya isa Fahad kuma wallahi sai na fadawa su Hajiya. Ni ba karatu ba ni ba ga haihuwa ba. Wace irin rayuwa ce wannan? Gara ka sake ni in huta.
Mama ce ta bude kofar ta shigo...Aishatu ashe baki da hankali har yanzu? Har yanzu baki kwantar da hankalinki a gidan mijinki ba shine kike cewa ya sake ki. Hajiya da ke bayanta tace Hassana baki san halin Fahad ba. Allah kadai yasan me yayi mata. Cikin kuka tace Hajiya magani ya bani cikina ya zube.
Laaaahhhhh haba Aisha kada ki tona sirrinmu a wurin nan. Mu bar zancen nan kawai bana son abinda zai hada iyayenmu. Mama tace ko meye Fahad ka fada don a gyara idan ma matsala ce da ku ai gara kowa ya sani a daidaita ku. Ba komai fa mama rigimarta ce kawai. Aishatu da tayi saroro tana kallon Fahad don ta rasa inda ya dosa. Hajiya ta ce kaga ba sa'anninka a wurin nan ka fadi me ya faru ko mu fita mu barka da matarka.
Hannunsa yasa a aljihu ya fito da maganin planning da yake bawa Aishatu. Wanda ya dauko ma har ya kusa rabi ya mikawa Mama. Dazu da zan dauko mata kaya naga maganin. Ashe shi take sha don kada tayi ciki. To da Allah Ya kawo kuma shine suke zubewa. Ya fara kuka....tace bata sona bazata yarda ta hada zuria dani ba. Aishatu tasa ihu wallahi karya yake min. Mama ta bige bakinta rufe min baki mutuniyar banza. Duk abinda kika fada naji kafin na shigo. Mungode tunda kin nunawa duniya bamu isa ba. Hajiya ma bata ji dadi ba amma ta daure kiyi hakuri Hassana mu bita a hankali. Fahad yace banso fada ba don Allah kada baba yaji zancen nan. Zamu daidaita a tsakaninmu.
Zance dai bai kare ba har aka sallameta. Kowa ya juya mata baya banda Khalid da matarsa. Har fadawa Alhaji abinda yaji Fahad na fadawa Aishatu game da hana haihuwa yayi aka karyata shi a gida. Sai da akayi mata fada sosai sannan ta koma gidanta. Haka ta koma cikin rayuwar kunci da bacin rai don wulakancinsa yafi na da saboda goyon bayan iyaye da ya samu.
Wata shida da dawowarta yanzu ko abincinta baya ci. Idan ya dawo gida zai auna mata abinda yaga dama ta dafa taci sauran taci da safe. Duk ta kara ramewa ga rashin kwanciyar hankali. Wata rana tana zaune tana jin radio taji ana bada labarin wata mata da ta zane mijinta saboda baya bata abinci. Tayi dariya sosai taji ina ma ita ce ta zane Fahad. Ai kuwa daren ranar ya auna mata wake wai ta dafa taci da mai. Yanzu don Allah a daren nan zanci wake? Kaga fa tara da kwata idan naci cikina zai baci. Daki yayi shigewarsa idan bazaki dafa ba ki barshi mana. Nan take dabara ta fado mata, tana jin alamun ya fara wanka ta tsala ihu iya karfinta. shiru bai fito ba ta kuma yin ihun ga maciji nan zai shigo bandakin ka fito Fahad. Bata rufe baki ba ya fito jikinsa duk kumfa. Akan kujera ya ganta a tsaye tana tsalle. Yana ina ya rinka waige waige. Karkashin kofar daki ya shije. Ni dai bazan kwana a nan ba kasa zani. Ke bana son shirme bari na nemo maza a waje su kore shi. Tace kai ma namiji ne...sarai tasan ko a tv aka nuna maciji canja tasha yake saboda ya taba saransa yana yaro a yadda ya bata labari. Duk inda yaga abu a dan murde a kasa ko tsumma ne ya rinka fada kenan.
RASHIN GODIYA ✂ 13
A baibai ya saka doguwar riga jikinsa duk yayi jirwaye saboda kumfa da ta fara bushewa ya ce ke ki tsaya a nan zan nemo masu taya ni fitar dashi. Tace nima sauka zanyi, ko ka tsaya ka fitar dashi kawai. Sai dai naga kato ne jikinsa har sheki yake. Tsawa ya daka mata don a tsorace yake yana ta waige waige...malama kiyi min shiru kuma ban yarda ki sauka kasa ba, ya fita da sauri. Tana jin ya sauka kasa ta kyalkyale da dariya. Amma Fahad ya shahara a keta, shine zai barta ita kadai da gaske ne ma sai dai ya cutar da ita. Dakin ta shiga ta lalubu keys din kitchen da yake fita dashi kullum ta shiga toilet ta dauki sabulun wanka ta manna a jiki yadda shatin key din zai fito a jikin sabulun sannan ta mayar da key din inda ta dauko shi. Wani bakin mayafinta ta dauko mai ratsin ja ta murde shi sosai sannan ta jefa karkashin kujera. Bayan ta gama ta ta koma falo ta cigaba da ihun maciji.
A haka suka dawo suka tarar da ita. Ku shigo tace hanyar daki yayi. Maza biyu ne bai damu ba ya nuna musu hanyar dakin ya haye kan kujera ya tsaya kamar yadda Aishatu tayi yana bada umarni. Ku duba har karkashin gado da cikin toilet din kunji ko? Ba kyauta zaku min ba zan biya wallahi.
Dariya ta rinka cin Aishatu tana ta gimtsewa. Can ta sauko kaga kamar gashi nan a kasan kujera. Tana mika hannu ya sona ihu ki barshi su zo su dauke kar ki taba. Ko sauraronsa bata yi ba ta janyo mayafin tayi cilli dashi kansa. Ihu ya kwalla tare da faduwa kasa a sume. Mazan da ya kira kira suka fito tace ai ya fita ta taga amma sai da ya fado masa a jiki. Suka taimaka mata aka kai shi daki ta yayyafa masa ruwa ya farfado. Tun daga ranar ya wani kara hade rai kada ta raina shi, a nata bangaren kuwa dariya yake bata sannan ta kai an yanko mata irin key din kitchen da rana tana diban abinci kadan yadda bazai gane ba ta dafa ta ci. Lokacin horon yunwa ya kare.
Haka Aishatu ta rinka cin karenta ba babbaka har na tsahon sati uku. Ranar alhamis da tsakar rana tana zaune tana cin shinkafa da mai da yaji ya shigo gidan ba ko sallama dama bai fita da wuri ba duk yunwa ta isheta ga fushin ya hanata zuwa Getso duba G. Juma. Tana cin abincin tana mita ita kadai sai ganinsa tayi a gabanta. Kallon da yake mata ba karamin tsorata ta yayi ba. Cikinta ya dori ruwa....ya kalleta sai ki fada min gidan uban wa kika sami abincin nan? Bara kika fara ko roko, ko kuwa aljanu sun fara ciyar dake? Nan take idea tazo kanta ta yi wani murmushi sannan ta cigaba da cin abincinta.
RASHIN GODIYA ✂ 14
Ya sake cewa Aisha ba magana nake miki ba. Nan ma bata kula ba ta cigaba da cin abinci harda fara 'yan wake wake. Rai a bace ya kai hannu zai dauke plate din ta fizge. Dama kanta ba kitso sai kawai ta jefar da dankwalinta ta canza murya. Tunda bazata iya yin ta maza ba sai ta kara rage ta ta...idan ka taba mata abinci zamu tabbatar munga bayanka Fahad. Dan ja yayi da baya don idanunta ta kafe a kansa ita a dole aljanu take yi. Ya danyi ta maza ke ni zaki yiwa aljanun karya? Lallai tunda rashin kunyarki har ta kai ga haka dole zanyi maganinki mara kunyar banza. Aishatu dama ta samu! ta cakumi wuyansa ta kwada masa mari wanda yayi matukar shigarsa. Kumatunsa ya rike da kyau idanunsa sunyi ja ya rasa tantacewa gaske ne ko gangan. Sai dai Aishatunsa matsoraciya ce bazata taba iya yi masa haka ba. Yarinyar da sai yadda yayi da ita kuma ta kasa fadawa kowa a gidansu. Baya ya kara matsawa Aishatu tana kallon yadda jikinsa ke bari tace mu sittin ne a jikinta. Munzo kwatar mata 'yanci ne saboda irin cutar da kake mata. Ka zubar mata ciki har sau goma...bakinsa na rawa yace wallahi biyu ne kawai kiyi hakuri. Ta sake make murya kai ni namiji ne ba mace ba. Kuma bazan hakura ba sai ka gyara halinka. Idan ba haka ba zamu dawo Fahad,idan muka dawo rayuwarka zamu nema. Wayar chaja ta dauko ta rinka zambada masa yana ihu har waje ana jinsa.
Tana jin takun Maryam ta dena dukansa ta samu daidai kan kujera ta kwanta tana fitar da wani irin sauti. Maryam ta shigo a tsorace Fahad ihunka naji. Me ya faru? Jiki a sanyaye yace Anti ashe aljanu gareta. Ji yadda ta rinka duka na. Ki dauke ta kawai ku sauka kasa. Anti maryam ta samo ruwa ta tofa addua ta shafa mata. Ka kaita daki ka kwantar da ita ina jin abin ya sauka. Amma me ya faru har suka tashi? Yace daga yi mata wasa fa...abinci take ci nace zan dauke plate din shikenan. Aishatu tana kwance tana jin yadda yake karya. Kadan ma ka gani ta fada a ranta. Daki aka kaita bata dade da kwanciya ba sai bacci. Tana farkawa Mama ta gani a kanta da Anti Lawisa suna mata sannu. Har ta ma manta abinda tayi da farko ta dan kalle su Mama me ya faru? Anti Lawisa tace kwanta abinki sannu. Allah Ya kara sauki. Mama dai bata yi magana ba sai kallon Aishatu take tana tausaya mata.
Jinya sosai tayi har sati biyu. Abinci da kayan kwadayi kala kala Fahad yake kawo mata saboda yan uwanta da ke zama a gidan kullum. Anti Maryam ma tana nata kokarin sosai.
Shi kuwa Fahad tsoronta yake ji don baya yadda su kadaice a daki.
Ya dawo gida a gajiye ya nufi kitchen dibar abinci don yanzu baya yadda ya takura ta. Ciwon karyar ya sake tashi cikin dare ta masa duka shiyasa ya fita harkarta. Yana kofar kitchen din ya ji muryarta tana waya da kaninta sadiq da baya gari tana fada masa abinda tayiwa Fahad harda zancen macijin karya. Shi kadai take iya fadawa sirrinta, tana magana yana dariya. Kofa taji an taba ta juyo. Fahad yaji duk yunwar da yake ji ta tafi ya ce mata ta shirya su je gidansu gaida G. Juma yaji ance ta shigo kano. Murna ta kama ta suka tafi ko abincin bai ci ba. Gidansu Fahad suka fara shiga yace da iyayensu su biyo su zasu gaishe da kakarta.
Suna zazzaune a falo Baba yace ni fa bangane wannan tara mu da kuka yi ba Fahad. Me yake faruwa ne? Fahad yace babu abinda ke faruwa ina so in sanar daku na saki Aishatu saki uku!!! Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Hajiyan Fahad tace ka fara shan kwaya ne? Saki uku kamar baka da hankali. Aishatu bata san lokacin da tace Alhamdulillah a fili ba. Mama ta magareta baki ji sakinki yayi ba kike hamdala? Iyayensu babu wanda yaji dadin abinda ya faru. Fahad dan sarkin kuka ya fara hawaye. Ashe Aishatu ba aljanu gareta ba, na karya tayi kawai don ta doke ni. Kwanaki ma macijin karya ta jefa min na suma. Babu abinda bana yi mata amma yarinyar nan na fuskanci rayuwata take nema. Kowa yayi mamaki amma tunda ansan ba sonsa take ba sai suka yarda. Aishatu kamar an cire mata kaya tace ni bazan taba tona maka asiri akan irin abinda kake min ba,amma idan na cuceka Fahad Allah zai saka maka idan kuma ni...Baba ne ya rufe ta da duka bata gama magana ba. Ke dai anyi mutuniyar banza. Ki dawo gidan sai muci abinda muke ci tare.
RASHIN GODIYA ✂ 15
Iyayen Aishatu sam sun ki fahimtarta. Bata da wani sukuni indai ba tana tare da yan uwanta su Nurain ba. A haka ta gama iddarta cikin kunci da tsangwama. Mama har hantarar take idan tayi magana, a dole suna bayan Fahad.
Da kyar da sidin goshi Baba ya biya mata kudin WAEC. Ta dukufa karatu sosai saboda shekararta uku rabonta da makaranta gashi ko aji shida ma bata yi ba. Lokacin da result ya fito tayi saar samun credits takwas da pass a history. Baba duk abinsa yayi murna amma dai ya kafa mata sharadin bazata cigaba da karatu ba sai ta sake aure. A haka Aishatu ta kwashi shekara daya da rabi babu abinda take yi sai zuwa islamiyya da yin zobo da meatpie wanda almajiri yake sayar mata tana biyansa. Shi kuwa Fahad watansu biyu da rabuwa ya sake aure. Matarsa yar kanin Alhaji ce wai nan anyi masa auren huce haushi tunda Aishatu ta ki shi. Yahanasu amarya dai bata da matsala da yan uwansa. Hatta anti maryam da basu dena mutumci da Aishatu ba suna zaman lafiya da ita. Da yake ya saba da keta lokacin da ya fara kokarin kwatanta mata irin zamansu da Aishatu. Ranar da ya kulle kitchen yana fita tasa tabarya dama turminta a baranda yake tayi rugu rugu da kofar. Da ya dawo zai fara fada tace kar ma ya soma idan ba yana so ta fada a gida bane. Irin kayan ciye ciye da yake shigowa dasu da ya cinye gaban Aishatu kuwa da karfi take kwata. Tun yana hakuri har aka fara jin kansu. Bata shiru yana fada tana fada. Karshe ma Alhaji ta fadawa karya da gaskiya akan Fahad to sai tayi rashin saa son dansa ya rufe masa ido yaki yarda. Wata rana suna fada ta biyoshi har kasan bene da tabarya saboda yaki siyo mata naman miya. Da rarrashi Khalid ya samu ta hakura ya aika aka siyo mata naman. Suna zaune a falonsa Fahad ya dora kankara akan kumburarren goshinsa Khalid ya rinka masa nasiha. Fahad rayuwa fa bazata taba tafiya a haka ba. Banda keta da hada sharri baka iya komai ba. Hakika Allah SWT Yayi gaskiya da Yace idan muka gode Masa zai kara mana, idan muka ki kuma to azabarSa mai tsanani ce. Ka fini sanin tun bata sonka Aishatu aka tilasta ta aure ka har ta kwantar da hankalinta don ku zauna lafiya amma kiriri ka rinka cutar da ita. Ko sau daya bata taba fada min abinda kake mata ba amma ai ina da idanu. Duk ta rame kamar wata kazar mayu. Shiyasa idan ka fara wannan kukan ko kadan bana yarda da kai tunda tun muna yara ka iya wannan sharrin. Fahad ya dan harare shi yana magana da kyar saboda ciwo yace yanzu dai Yaya me kake son cewa? Khalid yace abu daya ne kawai. RASHIN GODIYA ga Allah akan ni'imomin da Yayi mana komai kankantarsu masifa ne a garemu. Ya baka mace tagari mai hakuri da sannin hakkin aure amma sai da ka kaita bango ta yi maka bore. Sau nawa kake dukanta da yin abubuwan da zasu saka ta a cikin matsala da iyayenta? Duk ta shanye saboda ka iya toshe duk wata kofa da zata yiwa wasu bayani su fahimta. Bansan cikakken abinda ya faru ba amma nayi imanin laifinka yafi nata. Abinda kayi mata ne Allah Ya baka mace irin yahanasu wadda bata barin ta kwana. A sanyaye fahad ya tashi don ya san gaskiya dan uwansa ya fada masa.
Cikin ikon Allah sanaar Aishatu tayi albarka dan kudin da take samu ta ke tarawa a banki. Sauran kuwa gidansu take taimakawa da kanta duk da iyayenta basa gani bare su yaba. Maza suna ta neman aurenta saboda yadda ta murmure tayi kyau. Lokacin shekarunta ashirin da biyu. Wani ma bazai yarda ba idan aka ce ta taba aure. Rannan ta kira Maryam a waya su gaisa khalid ya dauka yace suna asibiti ne anyi mata aiki ta haifi mace. Aishatu tayi murna sosaita tambaye shi asibitin don bazata iya zuwa gidansu ba saboda surutun mutane. Atampa tasa mai kyau wanda aka yiwa riga da wrapper skirt sai mayafi babba da ta yafa. Fuskarta kwalliya tayi kadan tasa takalmi mai dan tudu sai yar purse dinta da ledar kayan barka. Tayi kyau sosai ta fito tayiwa Mama sallama zata fita...tabe baki tayi haka dai aka iya sai yawon tsiya an kasa aure. Koda yake waye zai auri mai dukan miji. Zuciyarta ba dadi ta fita ta tafi. Sun sha hira sosai da maryam. Suna zaune Khalid da Fahad suka shigo tare da Yahanasu tayi wa maryam girki. Yaran maryam na ganinta suka rungumeta suna murna. Yahanasu ma sun gaisa lafiya ta gaishe da khalid tare da dauke kanta daga Fahad tayi musu sallama ta fice. Tunda Fahad ya ganta gabansa ya fadi. Gaba daya ta canja ta kara kyau. Fita yayi yabi bayanta yana kiran sunanta. Kamar yana magana da dutse bus na tsayawa a gabanta ta haye ba ko waige. Daga ranar Fahad ya soma wani tashen sonta, zance kadan sai ya sakota. Abu kamar wasa sai gashi bashi da wani sukuni idan baije gidansu ba duk da bata fitowa. Da baba yayi masa magana ma cewa yayi saki uku cikin fushi ai a matsayin daya yake. Baba yace abu daya zaisa ka kuma aurenta sai idan ta auri wani ta fito. Shi dai yana kaunar Fahad. Duk da baya son ya ganta da kowa dole ya karbi shawara. Ganin bata sauraron kowa Fahad ya tura mata kanin abokin shi Audu mai suna Tijjani suyi auren kisan wuta ba tare da ta sani ba. Anyi saa ta damu da rashin karatu babu wani bincike iyaye suka shiga maganar duk da ba wani sonsa take ba ta amince aka yi aure saboda su baba sunce idan ta wuce wannan shekarar ba aure zasu yi fushi da ita. Duk abinda ake Baba da Fahad suke shawara yasan auren kisan wuta ne. Amma idonsa ya rufe shi dai a mayar da aurenta da fahad musamman da yaga kudi sun fara zauna masa har ya sayi mota. Anyi aure ita dai Aishatu tana zaune ne kawai saboda biyayyar iyaye. Bayan wata daya Fahad ya hurawa tijjani wuta ya sakota tare da infection din da ya sa mata. Tana gama idda Fahad ya dawo. Sai dai kafin ta bashi amsa ciwo ya bayyana a jikinta. Hajiya tace bazata yadda a mayar da aurensu da fahad ba. Da kansa yace ai shi ya jawo mata har ma ya fadi duk irin zaman da suka yi a baya duk don a bari ya aureta. Shi da gaske yanzu sonta yake. Su baba sunji kunya sosai tare da tsanar fahad. Shiyasa duk yan kudin su da nata a neman lafiyarta suke karewa domin sunyi nadama. Alhaji da Hajiya ma sun bata hakuri sannan Alhaji yace idan ya kuskura ya saki yahanasu zaiyi fushi da shi.
Aishatu ta numfasa ta kalli Sauda wannan shine labarina wanda da zan buda miki sosai sai mun kwana a nan. Fahad yasa na tsani maza saboda muguntarsa da tsantsar iya sharri. Sauda tace Aishatu tabbas kinga rayuwa Allah Ya baki wanda zai zama haske a rayuwarki.
RASHIN GODIYA✂ 16
Sai da suka yi sallar laasar suka koma asibitin. Sajida da Islam basu so Aishatu ta tafi ba har gate suka bisu suna daga mata hannu. Sun zauna har shida saura babu Dr Rano babu dalilinsa. Karshe Sauda ta ce mata gara su tafi gida, nurse suka tambaya tace sai wani satin ranar talata zai shigo. Suka yanke shawarar dawowa ranar. Har phone number suka yi exchanging.
*
Tamkar wata jaka haka Huzaifa ya rinka jan hannun Fadila har suka shiga dakinsa ya bude drawer din da yake ajiye kayan wanki. Wata farar leda ya dauko ya bude ya fito da wando da safa wadanda duk suke da digon ja a wurare daban a jikinsu. Saboda bacin rai da kyar yake iya magana ita kanta fadila ta gama tsorata da yanayinsa..ba a nan kika dauko rigar ba. Kai ta daga masa a hankali. Ya ce saboda kin gama ginawa zuciyarki zargi baki dauko sauran kayan ba kika fito da shirt din ita kadai ko. Sabo mai wanki ne ya fada min ya jika su da wasu kayan masu zuba wadannan sun baci shine na hadasu a leda zan bayar. Idan baki yadda ba na yarje miki ki dauki wayata ki kirashi ki tambaya. Yana gama magana ya fice daga dakin ya koma falo zuciyarsa na kuna ta rufe idanunsa. Hasbunallahu kawai yake karantawa don a yadda yake ji idan Fadila ta shigo hannunsa zai iya yi mata rauni da duka.
Inda ya barta haka ta tsaya kusan minti goma ta kasa fitowa daga daki. Wani irin so take yiwa Huzaifa wanda bazata iya hada shi da komai ba. Shiyasa take tsananin kishinsa. Duk irin yadda mata suke nuna sonsa musamman abokan aikinsa bai taba tunanin biye musu ba. Idan har zai kula mace sai ya tabbatar aurenta zaiyi. To bai tashi aure ba tunda ko shekara biyar baiyi da auren fari ba shiyasa yake kama kansa. Hakuri yake sosai da Fadila saboda irin yadda take yawan zarginsa da yi masa rashin mutumci idan abin ya motsa. Falon ta biyo shi ta durkusa a gabansa tare da rike masa hannu. Abban Aliya don......daya hannun nasa ya daga ya dakatar da ita. Kada ma kice don Allah don baki san girmanSa, isarSa da buwayarSa ba. Fadila ba kya gode masa duk abinda ya baki sai ki rinka hangen wani abun daban kawai don ayi ta zama cikin tashin hankali. Bakin gwargwado ina kokarin kyautata miki amma na rasa dalilin da yasa ba kya kyautata min zato. Ko dai kin taba ganina da wata a zahiri, waya ko text? A'a wallahi duk sharrin shaidan ne kayi hakuri. Yace ke zan bawa hakuri tunda kice aka yiwa laifi. Abu daya nake so ki sani wallahi idan kika kaini bango bazan nemi matan banza ba amma sai na cika gidan nan da matan da suka fiki komai. That is a promise. Baki bude ya barta a zaune ya dauki key din motarsa ya fita.
Gidansu ya tafi ya shiga dakin Umma mahaifiyarsa ya tarar tana sallar laasar. A kan kafet ya zauna ya jingina bayansa da gado yana jira ta idar. A nan bacci ya dauke shi saboda gajiya da tension da suka yi masa yawa. Tana idarwa ta kalle shi cike da tausayinsa. Filo ta dauko zata gyara masa kwanciya yayarsa Kubra ta shigo. Aurenta ne ya mutu ta dawo gida suna ta rigimar wanda zai rike 'ya'ya ita da mijinta. Sauri tayi ta karbi filon ta saka masa ya gyara kwanciya ya cigaba da bacci. Tace yanzu Umma wannan katon magidancin kike gyarawa kwanciya sai ya karasa ki. Umma tace ina ruwanki, danki ko nawa?
Wai ina ni ina wannan zabgegen dan kalen hanjin. Nasan bazai wuce yar banzar yarinyar nan bace ta bata masa rai. Kina ganinsa kinsan bashi da kwanciyar hankali. Mtswww ina ma ya saketa kowa ya huta. Umma ta harareta ke bana son rashin hankali don kin kaso naki auren sai na kowa ma ya mutu. Yaya Kubra tayi dariya umma kinsan dai ba laifina bane. Umma ta ce haka kuke fada ke da mijin naki magulmata kuna so kuna kaiwa kasuwa. Dariyar Yaya kubra ce ta sa Huzaifa ya farka. Yana tashi ya gaishe su Umma tace autan umma yau ba aiki ne ka dawo wuri? Wallahi umma akwai, wata yar matsala ce ta....idanunsa ne suka kai kan agogon dakin ba dai biyar da rabi ce zata yi ba? Yaya Kubra tace ya lafiyar idon ne likita. Da sauri ya tashi yana saka takalmi zan dawo ko zuwa gobe ne umma yau na kusa karya alqawari . Yana tuki yana adduar Allah Yasa yarinyar bata jira shi ba. Sai yanzu ya tuna ma a gabanta Fadila tayi wannan tsiyar. Karshenta ma ta gama baza labarin kowa ya ji a asibitin. Wani tsakin yayi ya cigaba da tukinsa.
A bakin gate ya ganta tana kokarin tare mota ga wata mata daga cikin motarta suna hira. Har ta samu za ta shiga yayi saurin tura maigadi ya tsayar da ita. Kafin ya karaso ta shige mota ita ma Sauda taja tata motar ta tafi. Hannu ya buga kan sitiyari duk Fadila ce ta ja masa. Allah kadai Ya san patients nawa ne suka tafi da haushinsa a rai.
RASHIN GODIYA ✂ 17
Magungunanta na farko ta cigaba da sha sannan ta rinka yin yadda likita da Anti Sauda suka bata shawara. Ita kanta taji dadin jikinta kuma wannan karnin ya ragu sosai ga kurajen duk sun mutu. Mama sai washe baki take don murna 'yarta ta fara samun lafiya. Da yamma tana sharar tsakar gida yaro ya shigo yace wai Aisha tazo inji Fahad. Sai da gabanta ya fadi don rabonta da shi zai kai wata shida. Daga bakin yan unguwa taji wai aiki ya samu a Abuja. Likafa ta cigaba ta fada a ranta. Ta san dole ya karo wulakanci. Da can ma yana fama da lifan ya aka cika. Mama tana daga daki tayi saurin fitowa ta kalli dan aiken, kaje ka fada masa babanta yace duk ranar da ya sake zuwa kofar gidan nan hukuma ce zata rabasu. Dan banzan yaro ga karyar tsiya. Aishatu ta kwashe da dariya kai Mama sirikinki ne fa Fahad. Ni gaskiya ki barni inje. Biyota tayi da maficin hannunta tana cewa kaniyarki Shatu. Ita kuwa daki ta ruga tana yiwa Mama dariya don ba karanar tsanarsa tayi yanzu ba. Yadda yake iya tara hawaye a idonsa ya fadi karya da gaskiya yasa Mama tace ita tsoronsa ma take ji.
Yaro ya maimaita sako yadda aka fada masa Fahad yace to nagode. Kofar gidansu ya koma ya zauna har ya hango Mal Sa'id ya dawo zai shiga gida. Sauri yayi ya tarar da shi suka gaisa fuskar nan ta Baba a hade. Har mamakin kansa yake yadda ya tsayawa Fahad akan Aishatu kamar wani wawa. Yarinya duk tabi ta motse amma a lokacin gani yake kamar ita ta jawowa kanta. Fahad yace Baba don Allah kuyi hakuri ku bari nayi magana da Aishatu ita ma na roketa tayi hakuri.
Ba sai ka ganta ba inji Baba, zan fada mata kuma tunda yarinya ce yar albarka nasan da gudu za ta yafe maka. Kai ka sawa ranka ta yafe amma wallahi ka nesanta kanka da gidana. Duk irin magiyar da zaiyi yayi amma sam baba yaki amincewa. Karshe ma dai shigewa cikin gidansa yayi ya bar fahad a tsaye.
Sunyi waya da Anti Sauda har sau biyu. Mama ma tayi mata godiya saboda yadda ta ke nuna kulawa ga Aishatu. Ana gobe zasu koma asibiti ta sake kira tayi mata tuni. Aishatu tayi mata godiya sosai.
Sai karfe tara na dare ya dawo gida a gajiye. Shopping din kayan abinci da sauran kayan bukatun gida yayi. Boot din motarsa a cike har seat din baya. Shi da maigadin gidansa suka rinka jidar kaya suna shiga dasu store. Motsinsu yasa Fadila fitowa da doguwar rigar bacci. Huzaifa yayi mata muguwar harara saboda tana ganin maigadi amma taki komawa ta sa ko da mayafi ne. Sai da suka gama ya ce cikin fada yanzu don Allah Fadila kin kyauta kenan? Ki fito gaban M. Bala da irin wannan shigar ba ko baki da aure ai kinsan tsiraici haram ne. Zumbura masa baki tayi to ba gidana bane. Duk wanda ya kalla yayi wa kansa, ta wuce shi ta shiga kitchen. Tsaki yayi ya bi bayanta ga kaya nan ki jera yadda ya kamata. Kinyi min papper soup din kuwa? Dan tsaki tayi banyi ba wani film ne ya dauke min hankali yanzu aka gama. Nayi tunanin za ka yi aikin dare ne shiyasa ban yi ba. Huzaifa girgiza kansa yayi kawai yace to ki fito da kazar daga fridge ta dan saki kafin ki dafa.
Ai ban saka ba ma, ni tunda ka fita ban shigo kitchen din ba. Yace a takaice dai kina nufin tana cikin sink tunda na ajiye miki da azahar. Bata kula shi ba ta dauko tukunya zata dora yace ta barshi ya fasa zai sha tea kawai. Tace to babu bread mantawa nayi ban kira ka ba.
Fadila what is wrong with you, me Aliyu zai ci gobe? Kinsan baya cin komai sai bread da safe. A hasale ya fita don ya gama kulewa.
Haka yasha tea da madara ya shiga wanka. Yana fitowa wayarsa na soma ringing. Lokacin shadaya saura. Kafin ya dauka Fadila ta riga shi. Tana dubawa taga ansa lady K tasan mace ce ta dauka ta fara masifa....to kadangarun bariki masu hana matan aure sakewa da mazansu. Me zaiyi miki da tsohon daren nan kike kiransa. Muryar Yaya Kubra taji tace Fadila rashin da'ar taki har yazo kaina? To tun wuri ki shiga taitayinki ko na saba miki, shashashar kawai. fizgar wayar taji yayi yana magana yana harararta.
RASHIN GODIYA ✂ 18
Daren ranar damuwar Fadila tasa da kyar bacci barawo ya dauke Huzaifa. Gari na wayewa tun bakwai da rabi ya fice. Fadila tana tambayarsa ko zaiyi breakfast bai kulata ba ya tafi.
Sai da ya gama ward round a asibitin sannan ya shiga office wurin karfe goma. Lokacin Aishatu da Sauda suna zaune a baya suna ta hira. Yau Sauda aka fara kira, bayan sun gaisa ya tambayeta progress din da ake samu game da jikinta ta sanar dashi. Yace to ya akayi baki zo ba last week. Ko lafiya ta fara samuwa zaki fara wasa da ita. Murmushi tayi haba Dr ai kasan ina kulawa. Nazo last week kana cikin duba Aishatu sai ka fita ita ma baka gama dubata ba. Mun dawo around 5 muka jira shiru sai aka ce sai yau za ka sake zama. Dafe kansa yayi da yake masa ciwo, ta fada muku dalilin fitar da nayi ko? Sauda tace eh to, cewa tayi kace idan zamu iya mu dawo karfe 5. Sai da ya gama yi mata tambayoyi ya kara mata wasu maganin ya ce ta turo next patient. Har ta je bakin kofa taji yace ita dayar kin santa ne? Sauda tace ai tana nan ma muna tare. Na dai riga ta zuwa ne kawai.
Mutum uku ya gani bayan Sauda kafin Aishatu ta shigo. Yau sai yaga tayi fes ba kamar zuwanta na farko ba. Fuskarta dauke da murmushi tayi sallama. Bin ta ya rinka yi da ido har ta zauna bayan ya amsa sallamar. Dr ina kwana
Ajiye biron hannunsa yayi sannan ya amsa lafiya kalau. Ya jikin ina fata kina samun sauki.
Alhamdulillah da sauki. Yace to yanzu me yake damunki? Yadda ta sunkuyar da kanta bata iya bashi amsa sosai saboda kunya yana burge shi. Gata kyakkyawa sai yau yayi noticing....she looks so innocent.
Zafin bai tafi ba.
Kamar daga sama yaji muryarta a kunnensa. Sai a lokacin ya dawo hayyacinsa. Ya kama zancen zuci..amma Fadila kin cuce ni, ace daga ganin patient na fara wasu irin tunani a kanta.
Hmmm kika ce zafin bai tafi ba ko? Eh ta amsa.
Allurai ya rubuta mata da wani magani na shafawa. Ki cigaba da shan wadancan har su kare. Wayarsa yaji an kira sai ya share ya cigaba da bayani don yayi tunanin Fadila ce.
Godiya tayi masa ta tashi zata tafi aka sake kiran wayar sai ya dauka. Abokinsa ne Abdul wanda shi kadai Huzaifa ke iya sanarwa matsalolin gidansa. Alama yayi mata da hannu kada ta fita.
A yadda yake kallonta kamar wadda batayi karatu ba sai kawai ya rinka magana da turanci yana bawa Abdul labarin irin kuncin da yake ciki a dalilin Fadila. Duk maganar da yake idanunsa basu bar Aishatu ba. Ita kuwa kasa take kallo amma tana tausayawa likitan da baiyi dacen mata ba. Ko da yake samun wuri tayi. Ita idan taga mace na yiwa miji iskanci har mamaki take. A hankali taji ya ce Abdul i need a second wife. Bata san me abdul din ya fada ba amma dai ta ga Dr Rano ya sake kallonta yayi murmushi.
Ajiye wayar yayi...kiyi hakuri na bata miki lokaci sosai ko. Dama ina son baku hakuri ne game da abinda kika gani wancan zuwan naki.
Murmushin da ya soma jindadin gani a fuskarta tayi masa sannan ta mike tsaye. ba komai Dr nan gaba dai ka dena hirar sirri a gaban patients don da yawanmu muna jin yare daban daban. Ba shiri ya tashi yana kiran sunanta ta yi gaba. Maimakon yaji ba dadi sai ya sami kansa cikin nishadi. Sai da ta fita ya tuna ashe kansa na ciwo kuma yana jin yunwa.
Kai Aishatu kamar bazaki fito ba. Ina jin matan can suna korafi wai ko hira kuke yi. Aishatu tayi dariya ko daya Anti Sauda bari na karbo magani mu tafi.
RASHIN GODIYA ✂ 19
Suna wurin karbar maganin suka ga sauran likitoci da nurses duk suna ta tafiya hanyar consultation rooms din da suka baro. Wata nurse ta leko wurin mai bada maganin wanda tuni dama ya tashi daga kan kujerar sa yana kokarin fahimtar abinda ya kawo rudu haka a asibitin. Tace masa Huzaifa ne yayi collapsing yana cikin duba wata mata. Saurin tura kujerarsa yayi baya yace da su Anti Sauda dake tsaye jikin window ina zuwa don Allah. Da gudu suka fice Aishatu ta kalli Anti Sauda da fuskarta ta nuna alamun damuwa kin san wanda suke fada ne? Eh likitan da muka gani ne. Aishatu tace Huzaifa naji ance fa Anti ba Dr Rano ba. Anti Sauda tace sunansa kenan ai. Amma kinga bai kamata mu tafi ba ace daga fitowarmu wani abu ya same shi. Duniya à bin tsoro, irin haka ne sai kiji ana yanzu fa muka rabu. Aishatu tace ai tunda bamu karbi magani ba dole mu jira.
Wuri suka samu suka zauna suna kallon yadda ake ta kai kawo akan Dr Rano. Matar da yake dubawa bayan fitar Aishatu sai bada labarin abinda ya faru take. Yana cikin tambayata me ya same ni sai naga ya rike kansa. Yayi kokarin tashi kawai sai naga ya fadi kasa. Aishatu na jin haka ta fara bawa Anti Sauda labarin da taji yana yi a waya. Har cewa yayi rabonsa abinci sosai tun shekaranjiya. Anti Sauda ta rike baki wasu matan basu da godiyar Allah. Irinsu ya kamata Fahad dinki ya aura. Uhmm uhmm Fahad dinsu dai Aishatu ta fada tana dariya.
Sai bayan wurin minti talatin likitoci suka fito daga emergency inda ake saka masa ruwa suka koma bakin aikinsu. Sai ga patients suna shiga da kadan kadan suna duba likitansu. Anti Sauda ta ja hannun Aishatu tashi muje mu duba shi. Mata uku ne a dakin suna fitowa suka shiga. Yana ganin Aishatu gabansa ya fadi. Zaune yake akan kujera ana masa karin ruwa. Sis Risikat tace lallai Dr Rano ka tsorata mata irin wannan yan dubiya haka..to gaskiya kowa ta shigo mana da kaji da lemo sai mu san kun damu da Dr dinku. Anti Sauda tace harda dawisu ma. Dr Allah Ya sauwake. Risikat ta kalle Aishatu kece niece din Lawisa ko? Ya jikinki kuwa kwana biyu bamu hadu ba. Jiki yayi sauki all thanks to Dr Rano. Tana magana yana kallonta yarinyar nan ta gama sanin sirrinsa tunda yayi waya a gabanta. Anti Sauda ta ce mu zamu tafi Allah Ya kara sauki. Amin suka amsa shi da Risikat.
Kofar dakin aka turo da karfi Fadila ta shigo...idanunta kan Sauda da Aishatu suka tsaya Risikat wadannan su waye? Me ya kawo su dakin da aka kwantar da mijina?
Anti Sauda tace dazu ya gama duba mu kafin mu karbi magani aka ce yayi collapsing shine muka zo duba shi. Huzaifa ta kalla da tun shigowarta ya rufe idanunsa don yasan sai tayi wani abin da zai kara bata masa rai. Kaga irin abinda bana so ko, idan nayi magana ace na fiye kishi da zargi. Idan ba haka ba meye dalilinsu na zuwa dubiya. Anti Sauda ta ce kiyi hakuri fita ma zamuyi. Wasu matan ne biyu suka bude kofar zasu shigo Fadila ta daka musu tsawa suka koma ba shiri. Aishatu sai kallonta take yi. Wace irin mace ce wannan da kishi ya fiye mata akan lalurar mijinta. Risikat ta nuna mata bakin gado zauna duk fita ma zamuyi Allah Ya kara sauki Dr. An duba shi dai stress ne da yunwa suka masa yawa. Fadila ta watsa mata harara to na tambayeki ne uwar kinibibi. Dama ance haka kuke yarbawa da shigewa mutane jarababbu. Huzaifa hakurinsa ya kusa karewa ya bude idanunsa da suka yi masa nauyi a hankali...Fadila don Allah kiyi shiru. Risikat da fuskarta ta kwabe kamar zata yi kuka ya kalla. Ko shi ta girme shi bare Fadila. Aishatu ta tare shi kafin yayi magana kiyi hakuri, ku zo ku tafi. Fadila daga zaune tace umma ta gaida Aisha. Risikat tace ni fa na fada miki ne don ki sa shi dole ya rinka cin abinci kada yunwa ta sa masa wani ciwon. A tsiwace Fadila tace ai ban tambayeki ba. Ku kuma tsayuwar me kuke yi ne haka, a tafi mana. Anti Sauda har ta bude kofa Aishatu ta dawo ciki ta dan durkusa a gefensa. Tun kafin tayi magana Fadila ta miki kamar an tsikare ta. Aishatu ta wani kara rage murya baby bari naje gida inyi maka kunu don ruwan nan kadai bazai dauke maka yunwa ba. Ko akwai wani abin da kake so? Zo ku ga idanun Fadila...baby? baby fa ta kira ka Huzaifa. Shi kansa da su Anti Sauda fuskarsu ta nuna mamaki sosai suka tsaya kallon ikon Allah. Aishatu ba kula ba don itama a tsorace take kada Fadila ta rotsa mata wani abin a kanta. Amma wani haushinta ne ya kamata tana zuba iskanci an rasa mai nuna mata kurenta. Ganin ya kasa magana tace baby ko jikin ne? Anti Risikat ki fadawa dr azo a sake duba min shi. Hawaye ta soma yi a hankali bana son ganinka a wannan yanayin..ina ma ciwon ya dawo jikina. Kifta masa ido Aishatu tayi don yasan wasa take yi. Fuskar Fadila ya kalla. Ta gama hade rai sosai ga hawaye kamar famfo a idanunta. Sai kawai ya biyewa Aishatu. ki dena fadin haka idan kika kwanta ciwo ya zanyi. A kasalance yake maganar ki tashi ki je gida kinji Aish amma da gaske ina jiran kunun kafin su Umma su zo. Ta mike a hankali sai na dawo baby na. Yaya Fadila ki kular mana dashi sosai. wani irin riko taji fadila tayi mata tana ta zuba ashar irin wanda kunne bai kamata yaji ba. Ni zaka yiwa karya kace min baka da budurwa. Ke kuma yau sai naga abinda kike takama dashi. Hannu ta daga zata mari Aishatu wadda ta gama kidimewa sai Anti Sauda ta rike ta. Idan kika taba mij kanwa ni bazan kyaleki ba. Banza wadda ta rako mata duniya. Kanina sai anjima ta fada suka fita ita da Aishatu. Dariya sosai suke yi Sauda tace dama haka kike? Aishatu ta share hawayen idonta na dariya ke kuwa zama da Fahad wasa ne. Kawai ji nayi gara in dan nuna mata yadda ake tarairayar miji. Anti Sauda ta yi murmushi dama na bari ta dan mareki. Ai nasan bazaki fara ba. Don bakiji yadda cikina ya kada ba da naji ta damko ni.
Fadila kuwa dirar wa Huzaifa tayi da masifa da zagi yaci amanarta budurwarsa tayi mata rashin mutumci yana kallo. har waje ana jin muryarta saboda fada na cinta ko sau daya tunda ta shigo bata ce masa ya jiki ba. Sai da ta gaji don kanta ta dena. Kuma ba inda zani wallahi zan gani idan zata dawo. Kunun ma in ta kawo sai nayi mata wanka dashi. Tana cewa baby kana kiranta Aish. Tayi kwafa wallahi har yau baka sanni bane. Kuma sai na fadawa Daddy.
Huzaifa rufe idonsa yayi tana ta fadanta ita kadai saboda bacci dake dibarsa yana murmushi. Who is Aishatu ita ce tambayar dake yawo a zuciyarsa.
RASHIN GODIYA ✂ 20
Anti Sauda ki gaishe min da su Sajida ni zan wuce gida, Aishatu ta dan yi gaba. Bangane zaki gida ba Sauda ta fada tana rike mata hannu. Kizo muje gida ki dama kunun, anjima da kaina zan kaiki gida mu gaisa da Mama.
Kunu kuma Anti Sauda, wane kunun?
Au har kin manta yanzu kika gama kiran mijin wata baby har kina masa alqawarin kunu.
Dariya sosai Aishatu ta rinka yi. Amma dai Anti Sauda ba kya sona. Wato na koma wannan matar tayi min duka kenan. Ai ni ina tunanin daga yau na dena zuwa asibitin nan don nasan da ganinta za ta sa ayo mata farauta ta. Sauda ta dage ita dai sai sunje an dama kunun..kika sani ma ko daga nan abin arziki ya tabbata. Aishatu ta girgiza kai rufa min asiri ina fama da wari ko ta ina. Ni da aure ai munyi hannun riga. Sauda bata hakura na tayi ta insisting ita so take taga yadda Dr Rano zasu kwashe da matarsa. Karshe dai Mama ta kira da wayar Aishatu ta fada mata zasu zo gidan tare amma sai sun fara zuwa nata. Mama ta ce to ba matsala.
Aishatu dai a sanyaye ta bi Anti Sauda don ita ko Huzaifan bata san da idon da zata kara kallonsa ba. Su Sajida sunyi murnar ganinta sosai. Anti sauda ta nuna mata komai na damun kunun tace to sai ki dama yadda idan munje kinga zanji dadin cewa ke kika yi. Cikin damuwa tace ni dai Anti Sauda da mun bar wasan nan haka kada shima yazo yana tunanin ko ni irin matan nan ce marasa kamun kai. Anti Sauda ta dafa kafadarta...Aishatu kinga dai bamu dade da haduwa ba amma ina kaunarki tsakani da Allah. Haka kawai naji ina sonki da Dr Rano. Auren mazan da basa jin dadin matansu na gida yana da riba idan kin iya takunki. Aishatu tace to Anti me ya kawo zancen aure kuma. Zan dama kunun amma bazan shiga asibitin ba. Ki kai musu ki zo ki muje gida kawai. Anti Sauda tace naji nagode.
Kafin ta gama Sauda ta shiga dakinta ta duba kaya har kala biyar masu kyau da mayafai uku duk masu kauri tasa a leda. Sai body spray kala kala da turare mai kamshi har da panties sababbi duk ta hada. A falo ta sameta su Islam tana yi mata surutu. Korarsu tayi suka tafi suna turo baki ta mika mata ledar. Aishatu ta duba kayan da suke ciki ta bude baki tana kallon Anti Sauda. Ni dai kafin kiyi tunanin na raina ki wallahi duka kayan nan basu dade ba kuma ina saka su. Sauran tarkacen kuwa duk sababbi ne duba ki gani. Aishatu tace kada muyi haka dake Anti Sauda. Ban baki don komai ba sai kawai don na dauke ki kanwata. So nake ki gyara jikinki muje asibitin nan...Aishatu ta daga gira Anti kinki hakura da zancen Dr dinnan. Shine kika hado ni da kaya, idan na saka naje gida Mama zata yi fada. Anti Sauda tace zanyi mata bayani da kaina. Kinga jikinmu kusan daya so rigunan zasu miki daidai. Kuma duk wrapper skirt ne don kada skirt din yaki yi miki daidai. Da lallami da magiya ta samu Aishatu ta shiga wanka. Irin kallon da ta ga Huzaifa na yi mata tana fatan kwalliya ta biya kudin sabulu. Aishatu ta sami sabulu mai kamshi tayi wanka ta gyare jikinta sosai. ta fesa body spray kala kala sannan ta saka daya daga cikin kayan da aka bata. Falo ta fito Anti Sauda ta bita da ido...kanwata Allah kinyi kyau sosai. Wannan karon inajin rodi matar nan zata biyoki da shi. Suka yi dariya sannan sauda ta kira mijinta ta sanar dashi zata koma asibiti daga nan ta kai Aishatu gida.Idan ya dawo kuma akwai labari.
Umma da Yaya Kubra sunyi sunyi Huzaifa yaci abinci yaki wai bakinsa ba dadi. Ya Kubra ta kira kanwarta Saddiqa tace ta taho masa da kunu ko zai sha. Suna zaune suna taba hira umma nayi masa fadan zama da yunwa. Fadila dai bata yi magana ba don a cike take fam. Ganin idon umma yasa ta dena masifar da take masa. Daga baya ma ta fita waje yin waya. Kwankwasa kofa akayi Yaya Kubra ta ce a shigo. Anti Sauda ce ta shigo da dan kwandon abinci wanda aka saka flask din kunu da cups sai fruit salad da tayi mai sanyi. Ko baa fada ba tasan dattijuwar da ta gani mai cike da kamala babar Dr Rano ce. Sauda karasawa tayi gaban Umma ta gaisheta sannan ta gaida Yaya kubra. Harda dan sunkuyar da kai tace Dr ya jikin? murmushi ne a fuskarshi ya amsa mata Alhamdulillah da sauki. Hankalinsa duk yana kan kofa ya ga ta inda Aishatu zata bullo. Sauda tace ga kunun da kace kana so inji Aishatu, Allah Ya kara sauki. Gidana nan kusa ne ko gobe na dawo na dauki flask din. Mamakin dawowarta yayi sosai Yaya Kubra tace baiwar Allah bamu ganeki ba. Ni yayarsa ce ga umma kuma mahaifiyarmu. Anti sauda tayi tsuro ta rasa abin fada yau ake yinta...Aishatu na can waje ita ana yi mata yar kure. Yadda tayi yasa Huzaifa ya kusa dariya duk da bai yi tsammanin zasu dawo ba. Ta fara cewa uhmm, uhmm dama. Ya kubra tace ko dai karin aure zaiyi dake. Ta firfito da idanu ni??? Da aurena wallahi. Huzaifa yayi gyaran murya kanwarta ce ba ita ba. Umma tayi murmushi Allah sarki yar albarka shine ta aiko da kunu. Auta kace aure zaka kara...kana ganin fuskarta kasan labarin yayi mata dadi. Kara kawai take yiwa Fadila. Yaya Kubra baki yaki rufuwa tace tana ina yanzu? Anti Sauda tace waje....wai kunya take ji. Yaya Kubra ta tashi muje mu shigo da ita su gaisa da Umma. Huzaifa na tsoron kada karyar ta kara gaba yace ki bari kawai zancen baiyi nisa ba. Bata saurare shi ba suka fita. A cikin mota suka ganta zaune, yays kubra tace kanwata fito mu gaisa. Gaban Aishatu ya fadi taji ko'ina a jikinta ya soma rawa. Kai karya ba kyau!
RASHIN GODIYA ✂ 21
A sanyaye ta bude kofar ta fito ta durkusa ta gaisheta. Dadi ya kama Yaya Kubra ta kalleta, dole Huzaifa ya so ki. Ina fata zaki rike min dan uwa amana. Aishatu a rikice take kallon Anti Sauda da ke faman kifta mata ido akan kada ta ce komai. Ku zo muje ki gaisa da Umma, mungode sosai da abinda kika kawo masa ba irin wasu ba. Har sun kama hanyar komawa Aishatu tace ammm don Allah tsaya kiji. Anti Sauda ta rike mata hannu har tana matse shi duk don tayi shiru. Aishatu ta girgiza mata kai alamun bazata yi ba sannan ta sanar da Yaya Kubra komai. Ji tayi ta rungumeta sosai. Allah Yayi miki albarka Aisha. Kin yi min daidai wallahi, ni da igiyar aurensa a hannu na take da Fadila bata shekara a gidansa ba. Ba karamin so yake mata ba, tun yana kau da kai har suka fara fada sosai. Daurewa kawai yake da rabon 'ya'ya. Kuma Umma tana hana shi daukar mataki. Duk kawaici irin nata baki ga farinciki a fuskarta ba da taji zancen nan. Indai ba wani gareki ba ki yarda kawai. Anti Sauda tace nima haka na fada mata . Kuka kawai tasa musu, ni fa ba cewa yayi yana sona ba. Ga lalura ina fama da ita. Kuma bazan sake aure ba har abada. Yaya Kubra tace kada ki kuma fadin haka. Kuma ke da kike da lalura har akwai wanda ya dace dake kamar likita ne. Suna ta magiya ita dai jinsu kawai take har suka ja ta zuwa dakin da aka kwantar dashi.
Mayafi tasa ta rufe fuskarta sosai. Ba umma ba shima kansa kunyarsa take ji. Wani irin relief yaji da ya gansu sun shigo tare. Ta gaishe da umma shi kuwa ta kasa kallonsa ma. Yaya Kubra tana dariya tace amaryar auta baki gaishe da angon naki ba ko don kinga umma ne? Da sun san yadda ta gama tsurewa babu wanda zaiyi mata magana. Umma tace bari in fita naga auta shima yau wai kunyata yake ji. Huzaifa yayi murmushi cikin shagwaba haba Ummana jira nake ta zuba min kunu in sha sai na farfado sosai. La'ila ha ilallah. Sun gama rudata karshe don maganarsa ta karshe sawa tayi ta fadi zaune daga tsugunawar da tayi. Umma ta jefe shi da mafici kuga min mara kunyan yaro zaka sa taji ciwo. tashi tayi ta fita ta barsu. Yaya Kubra tace to dan nema duk naji bayani daga Aishatu amma ina so kuyi tunani kafin nan da ka warke son mu san abin yi. Anti Sauda tace baki ga da yadda na samu muka dawo ba. Huzaifa ya dubi idanunta da suka yi ja fuskarta kamar zata yi kuka yace Aish zo ki bani kunun soyayya yunwa nake ji. Hawayen idanunta ne suka sauko cikin kuka tace ni dai don Allah abar zancen nan kada umma ta zata gaske ne. Na nawa kuma inji Anti Sauda. Ai yanzu sai maganar sa rana kawai. Huzaifa yace ai tunda kika kawo kanki Aish kinzo kenan. Kubra ta mika masa hannu yauwa dan gari. Zama suka yi suna ta rokonta ta amince ta aure shi ko don Fadila ta dena abinda take yi. Budar bakin Aishatu sai cewa tayi ni ina da wanda zan aura. Anti kizo mu tafi don Allah....Fadila ce ta shigo dakin rai a bace. To munafukai har kun dawo? Ashe yarinya ba kya son kanki da arziki. Flask din kunun ta suntuma su Yaya Kubra suna mata magana bata saurari kowa ba ta bude ta soma watsawa Aishatu a jiki. Ihu tasa iya karfinta tana kuka. Su Anti Sauda suka janyeta. Allah Yasa mayafinta da girma jikinta bai kone sosai ba sai kafarta. Huzaifa ya fizge drip din hannunsa ya ture Fadila. Kina hauka ne zaki kona ta. Umma ta bude kofar tare da wata nurse lafiya me ya faru? Yaya Kubra tace kinga abinda Fadila tayiwa Aishatu. Banda rashin mutumci irin naki ko ruwa baki yi tunanin bashi ba tunda aka kwantar dashi sai tsabar balai da yake cin ki. Umma ta riko Aishatu da ke kuka rai a bace tace Fadila na gaji da wannan halin naki. Ta dubi Huzaifa shima ransa ya baci tace ka shirya wallahi don daga nan gidansu yarinyar nan zani na bawa iyayenta hakuri sannan zan fadawa Yaya Babba yaje ya nema maka aurenta.
Fadila sai kuka wai shi da yan gidansu sun hade mata kai idan ya gaji ne ya saketa kawai. Fita tayi ta tafi gidan kawarta Wasila.
Ita kuwa Aisha tayi kuka tayi dana sanin shiga sabgar da babu ruwanta. Sai da aka duba mata wurin da ta kone aka bata magani sannan Umma ta ce da Yaya Kubra ta ja mota su bi bayan su Sauda sai gwammaja gidan Mal Sa'id.
RASHIN GODIYA ✂ 22
Aishatu kamar wadda tayiwa sarki karya haka ta shiga soron gidansu tana ta rabe rabe. Anti Sauda tana ta yi mata dariya tun a mota ta dena kula ta wai duk ita ta jawo mata.
Su Umma suka fito suka shiga gidan tare. Mahmoud kaninta ne ya fara ganinta jikinta duk kunu. Yaya Shatu lafiya kinga jikinki kuwa? Mama ta fito daga daki da sauri me ya faru? Matan da ta gani ya dan tsorata ta. Wani abin kika yi ne Shatu? Kuyi min bayani don Allah. Fashewa Aishatu tayi da kuka ta rungume mama. Yaya Kubra tace ashe ma raguwa ce ke, har ta fara saki kuka tun yanzu. Umma ta ce da mama ki kwantar da hankalinki babu abinda ya faru sai alkhairi. Tabarma Aishatu ta shimfida musu a tsakar gidan ta kawo musu ruwa sannan ta koma cikin daki. Tana jin muryar umma tana mata bayani danta ne yake son Aishatu yanzu daga zuwa duba shi matarsa ta zuba mata kunu a jiki. Ni dai nazo baki hakuri ne sannan in fada miki wan babansa zai zo nema masa aurenta. Mama gaba daya ta kasa fahimtar zancen, abu daya ta kula da shi yadda Umma ta damu da abinda aka yiwa Aishatu. To ni bani da abinda zance muku yanzu. Idan babanta ya dawo zan sanar dashi.
Sai bayan fitarsu Mama ta tsare Aishatu da tambayoyi. Bata bata lokaci ba wurin labartawa Mama komai...ta rike baki lallai Shatu ina ke ina shiga irin wannan rigimar. Wallahi nima mama nayi dana sani amma yayar nan tasa da Anti Sauda sun ki yarda a fadawa Umman gaskiya. Mama ta ce to kinsan babanki bazai yarda yayi gangancin sake yi miki zabe irin na da ba. Kinga ko zancen aure baya yi miki yanzu. Haka suka yi ta tattaunawa har Baba ya dawo.
Kwana biyu a tsakani Huzaifa yaji sauki sosai Umma ta takura masa da zancen Aishatu. Ga Fadila tayi yaji daga gidan Wasila kawarta mai bata shawarar mata basa zamewa mazansu bayi. Dole miji yabi matarsa kuma ya kyautata mata sosai. Gidansu ta tafi tana kuka wai su Yaya kubra sun dake ta a asibiti. Ko kadan babanta bai yarda ba don yasan halinta na rashin bawa komai mahimmanci in ba kanta ba. Maminta kuwa ta hau magana ta zauna suna jiran Huzaifa yazo biko. Su Aliyu ma ya mayar dasu wurin Umma kullum shima acan yake cin abinci. Ya dawo daga asibiti umma ta takura masa akan yaje Rano wurin wan babansa ya fada masa zancen auren. Umma yarinyar nan fa bamu gama daidaitawa da ita ba. Tana daga kan kujera tace to kaje ku daidaita mana. Nifa tunda naje na bawa iyayenta hakuri magana ta kare. Duk da yana fata Aishatu bata da wani tsayayye amma yana tsoron yadda abin zai kasance. Umma ta katse masa tunani kaga auta ka tashi ka shirya bayan magriba ka je gidansu. Sannan gobe da rana Haj Rabi zata zo muje bikon Fadila. To kawai yace ya tashi ya fita falo inda sauran yayyensa mata suke zaune. Babansu Dr Aliyu Ahmad Rano ya shekara goma da rasuwa. Su biyar Haj Gaji ta haifa wadda suke kira umma. Akwai Zainab, Kubra, Shukriya sai Saddiqa wadda Huzaifa yake bi. Dukkansu suna gidan mazajensu da yara banda Kubra da suke ta rigima da mijinta akan babarsa da ta takura mata. A halin yanzu yayi mata saki biyu tana gidansu.
Wani sky blue din yadi yasa wanda yayi masa kyau sosai. yasa hula da takalminsa yana fesa turare yana tunanin yadda Aishatu ta kira shi baby a gaban fadila. Murmushi yayi shi kadai da ya tuna yadda fuskar Fadila ta canja saboda kishi. Tabbas zai san yadda yayi ya auri Aishatu don ya sami kan matar da yafi so banda ummansa....FADILA.
RASHIN GODIYA ✂ 23
Bai sha wahalar kwatancen da Yaya Kubra tayi masa ba ya gane gidan su Aishatu. Wurin parking ya nema sannan ya fito ya karasa kofar gidan. Yana zuwa ya aika wani almajiri a fada mata Dr Rano yana sallama da ita don bashi da numbar wayarta.
Fahad na kofar gidansu tare da wani abokinsa suna zaune kan boot din motarsa yaga lokacin da motar Huzaifa ta wuce su har yana fadawa abokin nasa kaga wannan motar ina sa ran karshen shekarar nan irinta zan siya. Wannan kuma sai na barwa Aishatu. Yahanasun kuma fa ko ka siya mata wata ne? Bai kai ga amsawa ba yaga wani kyakkyawan mutum ya fito daga motar ya tsaya kofar gidansu Aishatu. Ita kadai ce mace duk gidansu saboda haka ya tabbatar wurinta mutumin yazo. Sauka yayi daga kan motar yace kai ina zuwa ya karasa kofar gidan ya tsaya. Huzaifa na ganinsa ya karaso gabansa ya mika masa hannu suka gaisa. Kowa cikinsu na ji da kyau da kudi ga shiga ta alfarma.
Sai da Mama tayi da gaske Aishatu ta gyara jikinta ta fito. Mama tace kije don baki san inda alkhairinki yake ba. Tunda yazo da kansa ai kinsan ba da wasa yake ba. Ba a son ranta ba ta kimtsa ta fita. Turus ta tsaya har sai da gabanta sai da ya fadi. Huzaifa da Fahad ta gani a tsaye. Fahad ya matsa mata sosai yan kwanakin nan. Ba karamin so yake nuna mata ba ga siyayya kala kala. Komai ya bayar mayar masa take yi. Anti Maryam ma tazo kamfen don tana son Aishatu ta dawo gidansa. Fahad din yanzu dana da fa ba daya bane. Aishatu tace na yanzu yafi cutata tunda ya jawo min wannan mugun ciwon. Sai dai yau da gobe tasa kiyayyar ta ragu har tana tsoron kada wata rana yaja raayinta ta amince da aurensa. Tafi kowa sanin Fahad green snake ne.
Wurin Huzaifa ta nufa yana jingine da motarsa, Fahad ya biyo bayanta da sauri Aisha don Allah ki tsaya. Ga mamakinsa dana Huzaifa sai ji yayi tana cewa Huzaifa...baby na yi hakuri na barka a tsaye. Ya kalli fuskar Fahad da ta canja lokaci guda ya gano saboda shi tayi haka. Sai kawai yace take your time my luv. Nasan kwalliya kika tsaya yi min, and you look so beautiful. Tana matsowa Fahad na binta a baya. Huzaifa yayi kissing hannunsa yayi hura mata. Kunya taji sosai tayi saurin rufe fuskarta. Tunda Fahad yake baya jin ya taba ganin bacin rai irin wannan. A fusace ya zo gabansu ke Aisha iskanci kike a titi duniya na kallonki. Wane dan iskan ne wannan yake biyoki har gida. Huzaifa yace who gave you the right to insult my wife? Fahad ya rinka kallonsu yace matarka kuma? Wallahi Aisha as long as I live baki da miji sai ni. Me zaki ci da wannan mutumin. Tace Fahad ka fita harkata ko in hada ka da Baba. Huzaifa ya dan bata rai yanzu ina kusa kike sa'insa da namiji...haba Aish. Fahad ji yake kamar ya rufe mutumin nan da duka sai dai yana tsoron kada sauran chance dinsa na samun soyayyar Aishatu ya rasa. Yace kaga malam yarinyar nan matata ce so ka kyale mu muyi settling problems dinmu. Tana daga gefen Huzaifa tace a da ba. Saki uku ai ya yanke duk wata alaqa tsakaninmu. Ran maza ya baci Fahad yayi kan huzaifa yana neman suyi fada. Abokinsa ne yazo ya janye shi da kyar yana ta zage zage wai babu mai raba shi da matarsa. Suna tafiya ta janyo mayafi ta rufe fuskarta. Ina zata kai kunya a wurin Huzaifa. Yau ma ta sake maimaita abinda tayi rannan. Kallonta Huzaifa yake yi, tayi kyau sosai duk da ba wata kwalliya tayi sosai ba. AISH!!! Yadda ya kirata yasa taji wani iri a jikinta..
We need to talk, ina zamu zauna? Soron gidansu ta kaishi don zance a cikin mota ba mutumcin mata bane. Nesa dashi ta zauna kanta a kasa. Shiru babu wanda yayi magana cikinsu. Can yace ya jikinki ko akwai matsala? A'a ina shan maganin da ka rubuta min. To kada kiyi wasa dasu kuma duk wanda ya kare kafin ki sayi sabo ki fara sanar dani. To kawai tace ta sake sunkuyar da kanta. Aish kinga ta yadda Allah Ya hada mu ko. Kin taimakeni nima na taimake ki. Umma ta dage sai naje Rano na sanar da wan baba maganarki. Aishatu ta dago kai ni dai tsautsayi ne ya sa nayi abinda nayi. Ka bata hakuri kawai ko kace ni nace na fasa. Its not that easy Aish. Waye wannan mutumin da na dazo? A takaice ta fada masa tarihin aurenta da Fahad. duk da yaji haushin irin abinda yayiwa Aishatu sai da yayi dariya sosai da tana fada masa irin ramuwar da tayi. Kafin ta gama labarin duk sun sake da juna. Shima nasa labarin ya bata ta kara tausaya masa. Indai bazaki damu ba Aish ki amince muyi aure. I believe love will find its way idan muka fara zama a matsayin maaurata. Ta dan kalle shi saboda a hankali yake magana. Ta lura sam baya son tashin hankali. To ka bari muyi shawara da su Mama zuwa gobe. Ba damuwa ya amsa mata, Ina wayarki? Kankame abarta tayi don da kunya ta bari ya gani. Yayi yayi taki bashi wai dariya zaiyi mata. Yace to shikenan dama number dinki zan dauka. Tace bari na fada maka a haka. yace naki wayon nima bazaki ga tawa wayar ba. Sai goben zan dawo in sha Allah. Tare suka tashi tana nade tabarmar duk soron ya cika da kamshin turarensa yace Aish kafin muyi auren zanso mu zama abokan shawara. Tace ba komai mun zama ma. Har zai fita ya waigo tana tsaye tana kallonsa. Saurin kawar da kanta tayi yace baki ce goodnight baby ba? Da gudu ta shige gida. Shima dama tsokanarta yake. Cike da nishadi yaja motarsa ya tafi gida.
RASHIN GODIYA ✂ 25
Kamar yadda ya fada a daren ranar yazo. mama tana yiwa Aishatu kitso don yan unguwa sun dena yi mata, nurain ya fada mata tayi bako. Mama tace saura daya mu gama ka kai masa tabarma soro tana zuwa. Tunda aka ce yazo Aishatu ta kasa sukuni. Wani irin dadi taji a zuciyarta. Ana gama kitson ta gyara jikinta don yanzu ta dage wurin tsafta.
Kamshin turarensa wanda ta fara ganewa taji tun kafin ta gama shiga. Da sallama ta shiga ta samu wuri ta zauna daga gefe. Huzaifa ya bita da kallo har ta zauna. Me yasa yarinyar nan take affecting dinsa haka...ita ta fara gaishe shi ya amsa sannan Mahmoud ya kawo ruwa da kunun aya a jug. Kunun ya kalla zuba min wannan Aish. Murmushi tayi ta kasa kallonsa...ai da ka zuba da kanka. Why ya tambaya yana kokarin hada ido da ita. Saboda bani da lafiya mana. Ni banda yan gidanmu babu wanda yake cin wani abu nawa. Aish! Ta dago kai a hankali jin yadda ya kira sunanta. Ni ba dan gidanku bane? Ta soma inda inda ba haka nake nufi ba ai...yace to indai dan gidanku ne zaki zuba ki miko min da kanki. Da ta mika masa cup din idanunsa cikin nata ya shanye tas. Wasu hawaye masu zafi ne suka sauko mata yayi saurin ajiye cup din. Nayi wani abu da zai bata miki rai ne Aish? Sai da ta gama kukan tace tunda na fara ciwon nan banda yan gidanmu kai da Anti Sauda ne kadai baku nuna kyama gareni ba. Ta sa gefen mayafinta ta goge idonta tana dan murmushi koda yake ranar da ka fara ganina a asibiti....ya katseta kada ma ki fara lokacin fa kina yar kazamarki ne. Tare suka yi dariya sannan ya gyara zama. So what do you think about us? Dan turo baki tayi a take yaji wani abu a ransa sai ya wayance da dauko waya a aljihu. Sai da ta rufe fuskarta sosai sannan tace na amince. Alhamdulillah taji yace...Aish na rasa abubuwa da dama a rayuwar aure wanda sai mun zauna zaki fahimce su da kyau. Amma a yanzu ina son kiyi min alqawarin zaki yi kokarin zame min garkuwa a gidana. Ki zama matar da babyn ki zai gani yaji dadi. Kunya sosai ta rinka ji ta tashi zata gudu. Yace dawo please ga wannan kuma kada kice min bazaki karba ba. Ai kuwa kin karbar sabuwar wayar da ya bata tayi. Yayi ta magiya amma taki. Sai yace to ni gobe zani Rano muyi magana da Kawu. Ina son inji muryarki kafin na dawo. Wayarta ta mika masa wai ya sa number dinsa ya yi ta dariya don baka ce tana amsa kira ba. Tana kallo ya bude wayar ya zaro sim dinta yasa a sabuwar wayar. A rikice tace Dr babana zaiyi min fada fa. To ai bazan tafi ba ma sai mun gaisa dashi. Ba haka kawai zan turo masa iyayena ba bai sanni ba. Zan bashi wayar ya baki da kansa. Ko an fada miki ke kadai ce yarsa? Haka suka zauna suna taba hira har Baba ya dawo ta tashi ta basu wuri.
Washegari da sassafe Huzaifa ya tafi rano. Gidansu baban shi yaje, family house ne mai dauke da barin duk 'ya'yan gidan harda na babansa inda suke zuwa sallah a lokacin yana da rai. Yanzu kuwa sai dai idan wani sha'ani ya kaisu saboda kowa yayi aure. Umma kuma bazata ji dadi zuwa ta zauna ita kadai ba. Gidan nasu akwai hadin kai da zaman lafiya. Wurin babban wansu ya fara zuwa ya sanar dashi maganar aurensa. Matarsa Hajjo tayi murna sosai ai gara ka kara aure ko ma cigaba da zumunci da iyalinka. Aure shekara hudu amma mu da matarka sai dai idan ta haihu. Kawu yace mata iyayen zance kishiya indai ba taku bace taje gidan kowa ma. Sun daidaita magana ranar jumaa su kawu zaso zo kano. Huzaifa bai tafi ba sai bayan laasar ya shiga sashen sauran yan uwansa.
su umma sunje bikon fadila amma taki amincewa ta koma. Yaya Zainab da aka je da ita duk ta kule. Dama Yaya Kubra ta labarta musu yadda ya hadu da Aishatu, Yayarsa shukriya tafi kowa nuna son auren har da kubra da aka yi komai a gabanta. Lefe suke hadawa na gani a fada ko kwandala basu nema a wurin autan umma ba. Su kawu sunje har Getso neman aure Alh Dalhatu yaji dadin yadda dan uwansa ya bashi girma wannan karon. G Juma kuwa sai tsokanar baba take wai duk wanda ya tuba don wuya ba lada. An tsayar da biki bayan sati uku saboda dangin Huzaifa sunce basa son a dauki lokaci sosai. Fadila ganin da gaske auren nan ba fashi ta tattara ta koma gidanta ganin mijinta ko waigenta baya yi ta yanke shawarar maganin Aishatu idan aka yi auren. Abinda bata sani ba duk abinda yake don ya sami damar dawo da soyayyarsa da matarsa ne. Kulawa dai sosai yana nunawa Aishatu kuma ko da wasa baba yace kada ta taba nuna masa Fadila tazo gidansu. Yace ai irin wannan zaman iyawa ne Shatu. Bana so miji ya sanki da kai kara tun yanzu. Kaji su Mal Said!!!
RASHIN GODIYA ✂ 24
Aishatu tana shiga gida ta fadawa mama duk yadda suka yi da Huzaifa. To ke Shatu kin tabbata kin amince da auren nan? Zaki iya zama da kishiya? Aishatu ta ce ni dai Mama kuyi shawara da Baba zuwa gobe. Basu bar wurin ba ya shigo. Mama nayi masa bayani yace ba dashi ba. Aishatu indai ba kina sonsa bane to bazan yarda kiyi irin wannan auren ba. Ga ciwo a jikinki yaje yana wulakanta ki ma. Bata nuna masa damuwa ba, kullum adduarta akan zabin Allah ne. Zuwa yanzu ta damu da lamarin Huzaifa amma bazata iya yiwa baba musu ba idan har yaki amincewa ta tabbatar babu alkhairi. Sai dai tun da ta shiga daki take juyi akan gado. Hirarsu da Huzaifa take tunawa ita kadai tana murmushi.
Washegari da safe Mal Sa'id yana zaune a gefen dakalin gidansa suna hira da wani makocinsa sai ga mota ta zo kusa dasu da gudu har tana watso musu kwata. Tare suka mike suna fada matan dake cikin motar ko a jikinsu. Sai da tayi parking suka fito. Kamar bata san abinda tayi musu ba tace sannu baba ina neman gidansu wata Aishatu ne. Baba yace ke mahaukaciyar ina ce zaki bata mana jiki amma ki kasa bada hakuri. Fadila ta yatsina fuska kaga malam tambaya nake ka bani amsa idan ka sani. Wasila tace ba kince kin biyo shi jiya ba kinga gidan da ya shiga. Fadila tace ai kinsan dare ne ga uban duhu. Ga gidajen kusan duk iri daya. Baba ya kare musu kallo lallai yaran nan suna da karancin tarbiya. Kofar gidansa ya nuna musu ku shiga nan ne gidan su Aishatu. Hannafi makocinsa yace ya ka nuna musu baka san da me suka zo ba. Baba ya karkade rigarsa so nake naga a inda shatu ta kwaso mana wannan gayyar tsiyar. Bayansu ya bi shima ya shiga gidan.
Mama na ta yiwa su Nurain fada sun ki tashi daga bacci kosan da Aishatu ke soya musu na safe ya soma hucewa. Fadila da Wasila suka shigo gidan ba sallama. Aishatu na ganinta jikinta ya fara rawa ai bazata taba manta fuskar nan ba. Fadila ta kalli mama nazo baku shawara ne ke da matsiyaciyar yarki. Kada tayi kuskuren shiga gidana don kishi dani sai an shirya. Mama tace to Allah Ya baki hakuri amma bazata aurar miki miji ba. Wasila ta tabe baki an ga mai kudi za a like masa. Ku siyawa yarku mutumci ku bata miji daidai da ita. Aishatu sai basu hakuri take Fadila na kiranta mara kunyar karya. Baba yana tsaye a bakin kofa sai da suka gama rashin kunyarsu suka wuce shi ko kallo bai ishe su ba. Aishatu tana ta kuka don da gaske tsoron fadila take. Baba ya yi gyaran murya...Aishatu na ganinsa ta ce me ya sami kayanka? Bai bata amsa ba yace da mama ku fara shiri in Allah Ya yarda sai Shatu ta auri likitan nan. Har ni wata yarinya zata yiwa fitsara don mijinta na neman yata. Ya girgiza kai bata sanni bane wallahi banda girma ya kamani da sai....
Mama tace yi hakuri malam. Aishatu tana hawaye dob duk ita ta jawo wa kanta da iyayenta wannan masifar tace baba kuyi hakuri amma bazan yarda na aure shi ba tazo tana ci muku mutumci. Baba yace ni bazan takura ki ba kada a maimaita irin na da. Amma tunda ni naki amincewa da fari yanzu na baki dama. Idan kin amince ki sanar dashi ya turo iyayensa can Getso gidan Yaya Dalhatu.
RASHIN GODIYA ✂ 25
Kamar yadda ya fada a daren ranar yazo. mama tana yiwa Aishatu kitso don yan unguwa sun dena yi mata, nurain ya fada mata tayi bako. Mama tace saura daya mu gama ka kai masa tabarma soro tana zuwa. Tunda aka ce yazo Aishatu ta kasa sukuni. Wani irin dadi taji a zuciyarta. Ana gama kitson ta gyara jikinta don yanzu ta dage wurin tsafta.
Kamshin turarensa wanda ta fara ganewa taji tun kafin ta gama shiga. Da sallama ta shiga ta samu wuri ta zauna daga gefe. Huzaifa ya bita da kallo har ta zauna. Me yasa yarinyar nan take affecting dinsa haka...ita ta fara gaishe shi ya amsa sannan Mahmoud ya kawo ruwa da kunun aya a jug. Kunun ya kalla zuba min wannan Aish. Murmushi tayi ta kasa kallonsa...ai da ka zuba da kanka. Why ya tambaya yana kokarin hada ido da ita. Saboda bani da lafiya mana. Ni banda yan gidanmu babu wanda yake cin wani abu nawa. Aish! Ta dago kai a hankali jin yadda ya kira sunanta. Ni ba dan gidanku bane? Ta soma inda inda ba haka nake nufi ba ai...yace to indai dan gidanku ne zaki zuba ki miko min da kanki. Da ta mika masa cup din idanunsa cikin nata ya shanye tas. Wasu hawaye masu zafi ne suka sauko mata yayi saurin ajiye cup din. Nayi wani abu da zai bata miki rai ne Aish? Sai da ta gama kukan tace tunda na fara ciwon nan banda yan gidanmu kai da Anti Sauda ne kadai baku nuna kyama gareni ba. Ta sa gefen mayafinta ta goge idonta tana dan murmushi koda yake ranar da ka fara ganina a asibiti....ya katseta kada ma ki fara lokacin fa kina yar kazamarki ne. Tare suka yi dariya sannan ya gyara zama. So what do you think about us? Dan turo baki tayi a take yaji wani abu a ransa sai ya wayance da dauko waya a aljihu. Sai da ta rufe fuskarta sosai sannan tace na amince. Alhamdulillah taji yace...Aish na rasa abubuwa da dama a rayuwar aure wanda sai mun zauna zaki fahimce su da kyau. Amma a yanzu ina son kiyi min alqawarin zaki yi kokarin zame min garkuwa a gidana. Ki zama matar da babyn ki zai gani yaji dadi. Kunya sosai ta rinka ji ta tashi zata gudu. Yace dawo please ga wannan kuma kada kice min bazaki karba ba. Ai kuwa kin karbar sabuwar wayar da ya bata tayi. Yayi ta magiya amma taki. Sai yace to ni gobe zani Rano muyi magana da Kawu. Ina son inji muryarki kafin na dawo. Wayarta ta mika masa wai ya sa number dinsa ya yi ta dariya don baka ce tana amsa kira ba. Tana kallo ya bude wayar ya zaro sim dinta yasa a sabuwar wayar. A rikice tace Dr babana zaiyi min fada fa. To ai bazan tafi ba ma sai mun gaisa dashi. Ba haka kawai zan turo masa iyayena ba bai sanni ba. Zan bashi wayar ya baki da kansa. Ko an fada miki ke kadai ce yarsa? Haka suka zauna suna taba hira har Baba ya dawo ta tashi ta basu wuri.
Washegari da sassafe Huzaifa ya tafi rano. Gidansu baban shi yaje, family house ne mai dauke da barin duk 'ya'yan gidan harda na babansa inda suke zuwa sallah a lokacin yana da rai. Yanzu kuwa sai dai idan wani sha'ani ya kaisu saboda kowa yayi aure. Umma kuma bazata ji dadi zuwa ta zauna ita kadai ba. Gidan nasu akwai hadin kai da zaman lafiya. Wurin babban wansu ya fara zuwa ya sanar dashi maganar aurensa. Matarsa Hajjo tayi murna sosai ai gara ka kara aure ko ma cigaba da zumunci da iyalinka. Aure shekara hudu amma mu da matarka sai dai idan ta haihu. Kawu yace mata iyayen zance kishiya indai ba taku bace taje gidan kowa ma. Sun daidaita magana ranar jumaa su kawu zaso zo kano. Huzaifa bai tafi ba sai bayan laasar ya shiga sashen sauran yan uwansa.
su umma sunje bikon fadila amma taki amincewa ta koma. Yaya Zainab da aka je da ita duk ta kule. Dama Yaya Kubra ta labarta musu yadda ya hadu da Aishatu, Yayarsa shukriya tafi kowa nuna son auren har da kubra da aka yi komai a gabanta. Lefe suke hadawa na gani a fada ko kwandala basu nema a wurin autan umma ba. Su kawu sunje har Getso neman aure Alh Dalhatu yaji dadin yadda dan uwansa ya bashi girma wannan karon. G Juma kuwa sai tsokanar baba take wai duk wanda ya tuba don wuya ba lada. An tsayar da biki bayan sati uku saboda dangin Huzaifa sunce basa son a dauki lokaci sosai. Fadila ganin da gaske auren nan ba fashi ta tattara ta koma gidanta ganin mijinta ko waigenta baya yi ta yanke shawarar maganin Aishatu idan aka yi auren. Abinda bata sani ba duk abinda yake don ya sami damar dawo da soyayyarsa da matarsa ne. Kulawa dai sosai yana nunawa Aishatu kuma ko da wasa baba yace kada ta taba nuna masa Fadila tazo gidansu. Yace ai irin wannan zaman iyawa ne Shatu. Bana so miji ya sanki da kai kara tun yanzu. Kaji su Mal Said!!!
RASHIN GODIYA ✂ 26
Shirye shirye ya kankama a gidansu Aishatu. Zuwa yanzu Anti Sauda ta zama yar gida komai da ita ake yi. Mal Sa'id ya dage karshe don yaga ya fito da yarsa. So yake ya wanke duk abinda ya faru a baya. Maimakon mama ta bata shawara da kansa yake sa yarsa a daki yana bata shawarar yadda zata tafiyar da sabuwar rayuwarta. Sai ya gama kuma sai yace kiyi hakuri Aishatu na bi son zuciya a baya na cutar dake. Murmushi take yi tace babu komai. Kayan kamshin jiki dana daki kala kala Anti Sauda ta hada mata ga shi tana matsa mata taci abinci sosai saboda jikinta ya ciko. Tace sauran sai kin sami lafiya kanwata. A son ranta basai anyi wani biki ba ita da zata yi aure na uku. Gidansu Huzaifa suka ce basu yarda ba. Ko walima ne ayi suna son gayyatar mutane kuma ya kamata ango yazo suyi hoto. Har mai gyaran jiki aka dauko ta dan gyara mata shima dai Anti Sauda tayi alqawarin da lafiya ta samu jikin nan zai kara shan gyara.
Iyayen Fadila ma sun yi mata fada tare da bata shawara akan ta gyara zamanta da mijinta, ta kiyaye maimaita abinda yasa shi neman aure da wuri haka. Jinsu kawai take, da idanunta taga yadda mijin wasila yake mata. Tamkar ma tsoronta yake ji sannan baya kafa mata takunkumi akan duk wani abu da ta bukaci yi. Girki kuwa na masu aiki yake ci hankali kwance. Ita dai tana son mijinta amma ko kadan bata son aiki kuma ga korafi idan abu baiyi mata yadda take so ba. A son ranta ta zauna suyi soyayyarsu da mijinta amma ya dena expecting wani abu daga gareta na daga aikin gida. Sun riga sun gama shawara ita da wasila...yanzu ne lokacin da zata nunawa kowace mace Huzaifa bazai iya rayuwa babu ita ba. Ba karamin so yake mata ba. Tasan da haka shiyasa take ta tsiyarta son rai don tasan bazai iya sakinta ba.
Saura kwana hudu biki Huzaifa ya shigo gida da kaya a wata karamar jaka. Sako ne daga yar uwarsa Saddiqa da ta dinka musu shi da Aishatu na fitar biki. Shadda ce tashi ash anyi mata aiki mai kyau da silver zare sai wani hadadden ash lace. Dinkin buba akayi da zani. Sai head da wani silver mayafi. Hatta sarkar da Aishatu zata saka Saddiqa ta hado a ciki don ita yar kasuwa ce. Yawancin kayan lefen da suka kai akwati takwas duk ita ta hado kayan. Ya tafi duba aikin fetin gidan da akeyi Fadila ta zo ta dauki jakar ta bude tana kallon kayan. Tabe baki tayi zaku ci ubanku daga kai da amaryar taka. Wato har anko zaku yi. Wata irin dariya tayi wadda tafi kuka ciwo.
Huzaifa ya fito daga kitchen din da ake yiwa Aishatu ya nemi jakar ya rasa. Dakinsa ya shiga yaga Fadila ta saka kayan tana kokarin saka sarka. Tana jin motsinsa ta juyu da sauri fuskarta dauke da kayataccen murmushi tana juyi a gabansa Abban Aliya nayi kyau??? Baki bude ya tsaya yana kallonta. Fadila waye yace ki taba min kaya? Gabansa tazo ta tsaya ta rike masa hannu kayi hakuri Huzaifa da dukkan abinda nayi maka. Kuma nagode sosai da kayan nan. Nasan dai sai ranar biki zamu saka ko. Thank you dear sai tayi masa kiss. Kasa magana yayi har ta fita zuwa dakinta bari na duba idan bani da matching shoe and bag sai muje mu siyo wani anjima ko.
Tausayinta yasa ya kasa cewa ba kayanta bane. Sai da ta fita ya fara tunanin yadda zaiyi don a hanya har yayi wa Aishatu waya yana kwantanta mata kayan. Saddiqa ya kira ya fada mata abinda ya faru. Kin ga ita ma Fadilan abar a tausayawa ce, baki ga yadda take kokarin kyautata min ba yanzu. Tsabar takaici ya hanata magana ta kashe masa waya tun bai gama bayani ba. Fadila da ke labe a jikin kofa ta toshe bakinta tana dariya. Sai ta nuna musu itama mace ce.
Yaya Shukriya ta kira tana ta fada. Ke saddiqa lafiyarki kuwa? Me ya faru kike ta masifa kamar wadda ta zauce. Ta fadawa yar uwarta abinda Huzaifa yayi. Sai kace wanda aka asirce Yaya. Lace din dubu arbain ne wallahi na ajiye ma Aishatu banda sarkar dana saka mata. Shima tasa shaddar mai tsada ce ga kudin dinki. Haba don Allah. Yanzu ma Yaya kubra zan fadawa. Shukriya tace kada ma ki soma don sai taje gidan ta karbo kayan. Kinsan halinta sarai. Su biyu suka yanke shawarar yadda zasuyi. Kudi suka hada suka kaiwa wani tela dinkin wani lace din fari wanda yafi nada tsada da farin yadi na maza shima mai tsadar gaske aka sake dinkawa express. Kusan dubu tamanin suka kashe sannan suka kira Huzaifa yazo ya dauka a gidan Shukriya. Duk abinda suke ita dai Aishatu bata sani ba. Godiya yayi musu sosai akan irin yadda suke masa. Saddiqa tace Allah idan ka sake bata Huzaifa sai na maka rashin mutumci. A take ya kira Aishatu yace zai kawo mata kaya da daddare amma farare ne. Tayi amfani da light green shoe and bag saboda head da sarkar light green din ne. Ita dai godiya sosai tayi masa tace sai yazo. Lokacin saura kwana biyu ayi bikin.
RASHIN GODIYA ✂ 28
Ran Huzaifa yayi matukar baci da ganin Fahad. Hannun Aishatu ya ja suka koma wurin zamansu yana ta bata rai. A haka dai taro ya tashi zukatan maauratan babu walwala. Fadila tana shaaninta amma tana lura da fuskokinsu. Dadi ne ya kamata har suka fito zasu tafi tana faraa. A bakin motarsa suka tsaya zasu tafi Kubra ta taho rike da hannun Aishatu. Fadila tana saka yara a mota zata shiga ita ma kubra tace ku fito fadila sai ku tafi a motar Yaya Zainab. Fadila ta hade fuska yaya bangane ba. Gida fa zamu tafi. Huzaifa da ke gaisawa da abokansa ya nufo su.. Fadila ta ce yaya kubra ce tace mu koma motar yaya zainab. Na zata gida zamu tafi yanzu. Kubra ta fara fada yau daya dai Huzaifa kamata yayi ace kai kazo da Aishatu nan wurin , to tunda baka dauko ta ba ai sai ka mayar da ita gida. Huzaifa ya tsaya yana kallon Yaya kubra tana fito dasu Aliya daga motar. Ta ce muje yaran albarka mu tafi motar Anti. Ba musu yaran suka tafi suna murna saboda ga yan uwansu a motar. Huzaifa ya kalli Yaya kubra ta hade rai bai ga alamun wasa ba. Kuma shima yana son tafiya da Aishatun. Aishatu tana kallon yadda hankalinsa ya rabu biyu sai da ta ga Fadila ta bude gaban motar zata shiga wai zasu tafi da Aishatu su ajiyeta a gida sai su wuce, har da yiwa Aishatu gwalo. Yamutsa fuska Aishatu ta soma yi har Yaya kubra ta kula. Lafiya dai Aishatu me ya sameki? Cikinta ta nuna ta fara cijewa kamar dauriya take. Huzaifa duk ya rude Aish sannu ya sata a bayan mota ya taimaka mata ta kwanta. Fadila ki bisu su ajiye ki a gida bari na je asibiti da ita. Yaya Kubra tace idan muka ajiye yaran zamu taho muma. ta leqa ta window Aishatu Allah Ya sauwake. Tana soma tafiya fadila ta ce huzaifa yarinyar nan fa kalau take. Tsabar iya barikanci ne yasa take karyar ciwo. Hankalinsa gabadays yana kan Aishatu yace kinga bana son surutu ki bi su Yaya ku tafi. Nan ya barta a tsaye yaja mota yayi gaba.
Basu yi tafiyar mintu biyu ba Aishatu ta tashi zaune abinta tana kallon titi. Ba tare da ya juyo ba yace Aish ashe kema kin iya rigima? Shiru bata amsa masa ba. Yayi murmushi naga tunda nazo ko magana baki min ba. Laifin me nayi? Nan ma shiru ba amsa. Sai da yaje kofar gidansu ta kama kofa zata fita taji ta a rufe. Ka bude min na fita ta fada rai a bace. Ace ranar aurenta har sai an fada masa abinda ya kamata yayi mata, banda wulakancin da yayi mata na sa kaya iri daya da uwargidansa kamar ba ita ce amaryar ba.
Shiru yayi shima yaki kulata, ta soma dukan kofar ni ka bude min sai kuka ya kwace mata. Sai da tayi mai isarta fuska sharbe da hawaye sannan ya fito ya bude mata kofa amma ya tsaya ya tsare wurin fitarta. Gani tayi ya sake cika mata ido kuma yayi matukar kyau. Sai ta kawar da idonta don bazata juri hada ido dashi ba. Aish kiyi hakuri don Allah nasan fushinki harda na kayan dana saka da fadila ko? Ba musu ta gyada kai. Kuma ciwon cikin ma na karya kika yi don kawai ki rama ko? Nan ma kai ta daga. Yayi ajiyar zuciya to kiyi hakuri haka halinta yake. Duk abinda tayi don ta baki haushi ne kuma tayi nasara tunda ko sau daya banga fara'arki ba yau. Wayarsa ya dauko ya rinka daukarta hoto tun tana turo baki har ta soma dariya. Sai da ya tabbatar ta hakura yace to bari na wuce gida kinga muna da tafiya Getso da wuri gobe. Ta dan bata fuska ni fa abar lallabawa ce yau tunda kayi min laifi. Ka bari sai na ce ka tafi don kaina. Dariya yayi yana mamakinta. Wani lokacin kunyarta har yawa take. Wani lokacin kuma sai ta zama bold, wanda hakan ma yana burge shi game da ita. Rike kofar yayi har ta sauko ana jin hayaniyar yan biki daga gidansu. Tace bari na karbo key din nan, ta nuna masa kofar wani daki da ya ke ta wajen gidansu. Bata jima ba ta dawo ta bude masa. Dakin a gyare yake kuma dama don hakan ta gyara shi. Bata jima ba ta dawo da buta a hannu. Kayi alwala ga masallaci can a kasan layi kaje kayi sallar isha. Ya dubeta da kyau yau bazan tafi gida ba kenan. dariya kawai tayi ta koma cikin gida. Itama sallar tayi kafin ya dawo ta kai masa abinci. Tuwon masara ne da aka kulla a leda da miyar kuka, ta sha wake da naman kaza. Sai man shanu da yajin daddawa. Tun kafin a fara shirin bikin tayi ta ajiye saboda ta tuna a wata hirarsu ya fada mata irin tuwon da yafi so. Ta hado masa da ruwa mai sanyi sosai. A cikin gida ana ta tsokanarta ta fice abinta tana dariya.
Yana dawowa dakin kofar a bude take sai labule da ta saki. Ya shiga da sallama ya ganta da kwanukan abinci. Wayarsa ta mika masa wadda take ta ringing a cikin hularsa da ya bari a dakin. Ya duba Fadila ce ta kira sau takwas. Yana karba wani kiran ya shigo ya dauka yana kallon fuskar Aishatu. Tuni ta gane ko waye mai kiran sai ta dauke kai. Yana dauka yaji sautin kukanta tana ta mita wai ina ya tsaya daga kai Aishatu asibiti. Aishatu sai ta matsa kusa dashi ta dan daga murya wayyo baby cikina. Sakin baki yayi yana kallonta bai san lokacin da dariya ta kwace masa ba. Yace Fadila kada ki damu taji sauki na kaita gida. Dariya ya cigaba da yi Aishatu ta kasa kallonsa, yayi nuni ga abincin zuba min tunda yau rigimar fadila kike son ja min. Tace rigima har ta wuce ta saka kayan da kace za'a aiko min ranar bikina. Ya dan rage murya kice kin fara kishina Aish...a'a ni ba kishi nake ba. Murmushinsa ya kayatar da ita ta zuba masa abinci yana ci suna yar hira yana mata santi ya dade bai ci tuwo irin haka ba . Bai ankara ba yaga karfe goma da kwata na dare. Wayarsa da ya saka a silent yaga missed calls din farida kusan dari. Kamar kada ya fita yace Aish zanyi missing din rigimarki, da kunyarki da wannan murmushin. Suka fita ta raka shi har mota. Ya tafi yana zulumin tashin hankalin fadila. Ita kuwa Aishatu a ranta tace Fadila kinyi da yar halak. Kowa yaci bashina sai ya biya. Duk da bata fada ba amma ranta yayi matukar sosuwa da wulakancin da aka yi mata a wurin bikinta don tasan bazai wuce sharrin fadila ba. A haka zata taimaka masan yana biyewa Fadila blindly?
RASHIN GODIYA ✂ 27
Asibitinsu sun bashi hutun sati biyu yaje ya kai musu invitation cards sannan ya wuce gida. Mai kunshi ya gani ta gama yiwa Aliya ana yiwa Fadila a falo akan karfet ko leda ba'a sa ba. Ranshi ya baci sosai ya shige daki. Dama a hannu daya aka yiwa Fadila tace da mai lallen ina zuwa. Ledar da ya shigo da ita a hannunsa ta nema ta rasa. Idonta tabbas ya gane mata kamar kaya ne a ciki ta dan laluba wardrobe dinsa bata gani ba. Jin motsin sa zai fito daga toiley yasa tabar abinda take yi. Abban Aliya sannu da zuwa...kin kula ta yayi ya dauko jallabiya zai saka. Me nayi maka ne? yace ba komai kawai. Wato bata ma san me tayi ba. Fita tayi abinta ta koma aka cigaba da lallen. Idan ya fita zata sake dubawa taga abinda ya boye daga shigowarsa daki.
Ranar jumaa bayan laasar su Anti Lawisa da sauda suka dauko mai kwalliya aka yiwa Aishatu. Lallen kafarta da hannu ya fito sosai. Mama sai kallon yarta take cike da kulawa. A ranta tace Allah Yasa gidan zamanta ne. Amarya tayi kyau har ta gaji. da yake ba fara bace sosai kayan jikinta sun fito da ita sosai. Tana ta kamshi...Anti Sauda da su Islam anko suka yi suma duk sunyi kyau. Hudu da kwata suka tafi wurin bikin. hall ne da yasha kwalliyar da ta dace da kayan amarya da ango. A Jeep din Yaya Zainab aka dauko amarya. Lokacin da zata shiga mota Fahad yana kallonta daga kofar gidansu ya yi sauri ya shiga mota. Gidansa yaje ya saka farar shadda da light green din hula irin kayan Aishatu ya dauko card din bikin wanda da kyar ya samu daya ya shigo hannunsa tunda bikin card admit ne ya fice. Huzaifa ya fito daga wanka yana fesa turare Fadila ta shigo. Ba karamin kyau tayi masa ba ya rinka kallonta har tazo ta karasa fesa masa turaren a singlet dinsa. Ya kalleta, uwargida ran gida. Kinga yadda kika yi kyau kuwa? Ita dai dariyar keta take masa a zuci. Jakar kayansa ya dauko tunda ya riga ya kaiwa Aishatu nata. Ya bude wandon yasaka ya bude rigar yaga wani abu kamar miyar kuka. Meye wannan haka? Fadila ta nuna tsoro ta ta karba tana kai rigar hancinta. Kamar warin lalle fa. Ya fizge rigar da sauri, lalle kuma? Me ya kawo lalle nan. Ya fara kallonta cikin tuhuma Fadila wane irin wulakanci ne wannan. Ban gane wulakanci ba. Wallahi bani na taba maka kaya ba. Aliya ta kira suma duk an shirya su sunyi kyau. Tace Aliya kece kika bata kayan Abbanki da lalle? Aliya tace tsumma ne fa Mummy na goge lalle dashi. A leda na gani. Huzaifa ya kara harzuka yanzu Aliya drawer din kayana ne wurin goge lalle? Ta kalli mamanta sai ta soma kuka. Ita dai mummy ce ta nuna mata ledar tace ta goge hannunta kafin a wanke. Zata yi magana Fadila ta mareta tare da korarta daga dakin. Huzaifa har yana hanata. cikin bacin rai tace to yanzu wane kayan zaka saka? Ya ce ina da fararen shadda da yadi bari na duba. Sai dai ko daya bai samu ba Fadila tace ni duk na hada su wanki jiya. Yanzu ma naga yana shanya. Iyakar kulewa Huzaifa yayi amma sai ya daure. Ta shiga duba kayansa wai bari ta samo masa wani. Shi kuwa tunanin fadan da zasuyi da Saddiqa yasa ya hakura yasa ash. Zuciyar Fadila fes suka fito tare da mijinta.
Taro yayi taro amarya tana zaune ana jiran shigowar ango sai gashi da abokansa sun shigo. Wasila tasa Aliyu da Aliya daga gaba suma ash din shadda aka dinka musu sunyi kyau sai bayansu iyayensu ne Fadila da huzaifa suma shigarsa iri daya. Sunyi kyau sosai sun kuma burge mutane sosai. Aishatu tana hango su hawaye suka cika mata ido...tabbas kayan da ya kwatanta mata ne daga baya ya kawo mata wasu daban. Hawaye taji ya taru a idanunta suna barazanar fitowa. Hannu taji a kafadarta ta dan dago kai. Saddiqa ce ta ke girgiza mata kai alamun kada tayi kuka. Ita kuwa shukriya da tafi kowa rauni sai da hawayenta suka sauko. Saboda wulakancin da akayiwa Aishatu. Yaya Kubra da yaranta suka zagayeta taca a hankali sai kan uba. Amma Huzaifa sai na koya maka hankali.
Har seat dinsa Fadila ta rako shi sannan ta sauka ta zauna wurin kawayenta. aishatu fuskarta ba yabo fa fallasa. Tun yanzu ta fara sanin matsayinta...ana tsaka da taro aka bukaci ango da amarya a filin rawa. Daga shi har Aishatun da tunda yazo bata ce masa ko sannu ba babu wanda ke rawar. Fadila kuwa ta cashe tayi musu barin kudi sosai. Suna haka sai ga Fahad from no where shima yazo yana rawa yana kallon Aishatu. Sonta ke kara shigarsa yana tunanin yadda zaiyi ko anyi auren ya rabata da huzaifa.
RASHIN GODIYA✂ 29
Aishatu tana shiga gida ta kira Anti Sauda ta fada mata yadda suka yi da Huzaifa. Yaba mata tayi sosai tace ta cigaba kuma kada ta bari tsoron fadila yasa ta dena abinda take yi. Shi kuwa Huzaifa bai isa gida ba sai shadaya saura. Ledojin biskit da robar lemo yayi karo dasu an baza su a kasa. Fadila bata falon amma Aliyu da Aliya suna zaune akan kujera suna kallo a waya. A dan tsorace ma ya karaso ya gansu. Suna masa oyoyo yace Aliya me kuke yi har yanzu baku kwanta ba. Ya mika masa wayar Fadila kallo mummy ta bamu muyi. Aliyu yace sunan film din zaman auye. Aliya tace kai zaman aure ake cewa. Ta cigaba da kallon babanta, wata mata ce suka yi aure da wani mutum tare ma suke kwana a gado fa abba. Ni dai na fadawa Aliyu wuta zasu shiga. Karbe wayar yayi hankalinsa a tashe ya kai su daki. Kowa gadonsa daban yace su cire kayan jikinsu don tun wanda suka je biki. Kunyi sallah kuwa? Suka ce a'a. Zama yayi suka yi alwala ya nuna musu suka yi magriba da isha. Aliyu yace Abbana cikina yana ciwo, yunwa nake ji. Aliya tace nima haka Abba. Lemo muka sha da biskit.
Zuciya ba dadi yace musu yana zuwa ya fita ya tafi dakin Fadila. A takure ya ganta akan gado taci kuka ta koshi. Itama bata cire kayan jikinta ba ya soma mata fada. Yana yi tana yan wake waken rashin mutumci. Ba abinda yafi bashi haushi irin kallon da yaga yaransa suna yi gashi an barsu a falo cikin dare. Dama mai aiki ke dawainiya dasu gashi ta tafi gida neman saurayi. Gajiya yayi da fadan ya koma dakin yaran ya taso su ya basu tea sai ya tarar sunyi bacci. Tare dasu ya kwanta a dan gadon Aliyu.
Bayan asuba ya shiga kitchen da kansa ya dafa zuwan zafi ya soya kwai ya hada ma yaransa da bread. Shiru Fadila bata fito ba har yayi musu wanka ya shirya su suka ci abinci. Babu wanda yayi cigiyarta ma. Dakin ya leqa tana baccinta hankali kwance. Yayi tsaki suka fita. Gidansu ya kai yaran suna ta murna Umma tace gandoki ai ka riga duk masu zuwa getson zuwa. Sai karfe goma aka gama taruwa suka dunguma zuwa Getso. Shabiyu da rabi na rana aka daura auren Dr Huzaifa Muhammad Rano da Aishatu Sa'id. Fahad yana jin an daura auren hawaye ya sauko masa. Yana kallo Huzaifa bakinsa har kunne yana ta gaisawa da mutane. Aishatu tasa ce shi kadai ko zata yi aure goma sai yasan yadda zaiyi ya sake aurenta.
Gidansu Aishatu anyi yini su Anti Sauda aka zauna sake bitar karatun zama da mijin Fadila. Wanka Aishatu tayi aka kawo mata garwashi ta sake turara jikinta. Idan bata fada ba yanzu babu mai sanin bata da lafiya. Jikinta duk ya ciko ga kamshi duk karni da warin discharge babu. Pad take sakawa yanzu saboda discharge kuma tana canjawa akai akai. Atampa tasa wadda tasha dinki mai kyau sai katon mayafi. Baba ya dade yana mata nasiha ita kuwa Mama sai kuka. Anti maryam ma matar khalid tazo da ita aka kai amarya gidanta. Tun daga waje ake yaba kyan gidan, side dinta aka wuce da ita mata suna ta guda. Yaya Kubra tasa key zata bude kofa yaki shiga. Tayi tayi abu ya gagara yan kawo amarya suka zauna ana kallon kallo. Waya ta kira Huzaifa ko yayi mistake din key yace ya tabbatar shi ya bata. Fadila bata gayyaci kowa ba sai Wasila suka wuce su Anti lawisa suna dariya har Wasila na cewa idan kofar taki sai ku mayar da ita gida. Yaya Zainab ta shigo kira Huzaifa tana ta fada don cikinsu akwai tsofaffi harda kakar Aishatu G Juma. Kuka kam Aishatu tayi Yaya Shukriya ta bawa mutane hakuri daga baya suzo suga dakin amarya. Da daidai aka tafi mata an sami na surutu. Daukar Aishatu suka yi zuwa gidan Umma. Tayi ta bata hakuri itama don sun gano Fadila ce tasa aka canja key din kofar gaba daya. Waya suka yi masa yazo gidan ya dauki matarsa. Sai bayan isha ya sami zuwa lokacin tana zaune kan abin sallah tana addua. Sai da ya jira ta idar umma ta sake musu nasiha suka tafi. Yau ma kin kula shi tayi don abin na fadila ya fara yawa. shima baiyi attempting jan ta da zance ba. Grand square ya shiga yayi yar siyayya ya fito. Wani irin kamshi take mai dadi da kwantar da zuciya. Ya kalleta yayi murmushi Allah kadai Yasan me zata yiwa Fadila ra rama. Sai ya sami kansa da son ganin abinda zata yi.
Fadila na jin shigowar motarsa ta fito da gudu. Rigar bacci ce wadda da ita da babu duk ta rungume shi tana kuka. Haba Abban Aliya yau ka ja min zagi ka bada wrong key aka kasa budewa amarya. Yanzu dole ta kwana a gidansu ko gidan Umma ko. Zuwa gobe sai a canja wani. Tureta Huzaifa yayi a hankali yana kallon kofa suka hada ido da Aishatu. Ranta ya gama baci ta daure sai ta shigo da sallamarta murya kasa kasa. Katon mayafin jikinta ta cire, rigar jikinta fitted ce ta kamata tsam da skirt din. Ta kwance dankwali gashinta ya zubo har baya. Kukan shagwaba ta saka tun kafin ta gama shigowa Huzaifa yayi murmushi yasan ramuwar ce ta tashi. yau da wata ya aura kila sai ya zane fadila amma Aishatu ma ta isheta. Yace Aish me ya faru ne? Miko masa mayafin tayi da dankwali...ba kaine ka barni da kaya ba. Kuma duk sunyi min nauyi. Ni dakin ma bazan iya karasawa ba. Karbar kayan yayi tana ta kwarkwasa....tana kara shiga zuciyarsa. Fadila ta soma zage zage shegiya karuwa. Don bakin naci da kika biyo shi ina zaki kwana. Huzaifa zaiyi magana Aishatu ta girgiza masa kai...babyna mu tafi daki ni na gaji. Ya rike mata hannu suka wuce dakinsa wanda Fadila ta gama gyarawa sosai ya sha turaren wuta. Suna tafiya fadila ta fizgo mata riga ta baya wallahi baki isa ki shiga ba. Huzaifa bafa zan yarda da wannan rashin mutum....tas taji ya dauke ta da mari. Fadila ki kiyayeni wallahi. Kin fara kai hakurina karshe.ke dai ki kuntata min shine jindadin rayuwarki. Akan Aish zan miki abinda baki taba tunani ba. Tunda suke bai taba daga murya yana mata fada kamar yau ba. Wannan munafukar yarinyar bazata zo ta hanata zaman lafiya ba. Tana kallo suka shiga dakinsa harda sawa kofar key.
RASHIN GODIYA ✂ 31
Juye yuye Huzaifa ya rinka yi bacci ya kauracewa idanunsa, ya cire rigarsa don ya ragewa kansa nauyi amma duk a banza. Bai taba tunanin zai kara aure ba saboda Fadila dai gashi yau saboda itan dai yana kwance gado daya da wata a matsayin matarsa. Ya rasa dalilin da yasa ya kasa bacci. Aishatu kuwa tsabar gajiya ce tasa ta baccin dole. Idan ya tuna yadda yaji lokacin da ya rungumeta sai yaji kamar ya janyota jikinsa yanzu ma. To amma ya Aish zata dauke shi? Yayi dan tsaki indai yayi sharing gado da ita bazai jure nisanta daga gareta ba. Shi kadai yake ta saka da warwara, karshe dai filo ya jefa kasa ya kwanta.
Kiran farko na asuba ne ya tasheta. Kanta yaso ya juye har ta manta inda take. Ta duba gadon da kyau ta tabbatar ita kadai ta kwana a kai. Zuciyarta taji tayi mata nauyi da tayi tunanin ko kyamarta tasa yaki kwana akan gadonsa. Kawai sai bata ji dadi ba.
Tana sauke kafarta daga kan gadon ya fito daga toilet. Ganinsa ba riga yasa taji kunya sosai tayi saurin dauke idonta. Gani tayi ya kara mata girma da kwarjini. Ya kawar da shirun dake tsakaninsu kin tashi lafiya Aish. Ta gyada masa kai ba tare da tayi magana ba. Yanayinta ya canza idan ya dawo daga masallaci zai tambayrta abinda ke damunta.
Yana bude kofar dakin yayi karo da abu a dunkule a kasa a cikin falonsa. Ya dan ja da baya sannan ya shuri abin da kafa. Muryar Fadila yaji tana cewa wallahi Huzaifa baka isa ba. Ya kara shurinta ta tashi a firgice. Tsabar masifa na cinta mafarki take wai Huzaifa ya kara auro wasu matan. Yace me kike yi a kofar dakina ko a nan kika kwana? Ban sani ba ta amsa tare da tashi tayi hanyar fita. Ya dan riko mata hannu sannan yayi magana daidai saitin kunnenta ki dena labe saboda kada kijiyo wa kanki sirrin boye. Yadda yake maganar yana lumshe ido yasa ta ture shi ta fice.
Wurin karfe tara ya fito ya shiga wurin Fadila. Akan doguwar kujera ya tarar da ita a falonta tana zaune. Ko da ta ganshi kawar da kai tayi. Ya karewa falon kallo Allah kadai yasan rabonshi da shara. Kila tunda mai aikinta ta tafi. Ga dukkan alamu ma akwai wani abu mai tsami a dust bin din falon don ana shigowa zai daki hancin mutum.. kusa da ita ya zauna kinci abinci kuwa? Tace cikin tsiwa bana son gulma don nasan cin nawa ba damunka zaiyi ba. Yaji zafin abinda ta fada sai ya share. Ki tashi ki zo falo an kawo abinci daga gidan umma. Idan kin gama kizo dakina ina son magana dake. Bai jira amsarta ba ya tashi.
Ya rasa wannan tura baki na Aishatu tun asuba da ta tashi. Tayi wanka babu kayan sawa saboda nata suna kulle a side dinta. Ya zauna a kusa da ita a kan gado sai yaga ta dan matsa. Yayi dan murmushi A haka zamuyi kawancen kina zumbura min baki Aish, Ko dai nayi laifi ne ban sani ba? Eh .....subhanallah me nayi miki. Ta sake turo baki, hakan yana bashi shaawa game da ita. Tace kana kyamata ko? Tambayar yaji ta wani iri yace me kika gani? Sai ta dukar da kanta saboda ya kafe ta da ido...gani nayi ka kwanta a kasa. Sai tayi tunanin kada ya fassarata kuma da wata manufa. Uhmm ina nufin da ka barni a kasan ko...ba komai dai abar zancen. Hancinta ya ja har ta danyi kara. Ki dena irin wannan tunanin Aish. Ko har kin manta maganarmu ta jiya? naga duk kin ruda kanki ,tambayar ma kin kasa yinta sosai. Kina son sanin ko ina kyamarki ne ko amma kina tsoron kada nace kina son kwana kusa da mijinki. Murmushi ne ya kufce mata ta kasa dago kanta. Bana son takura miki shiyasa amma da ina kyamarki ai bazan aureki ba. Amma yau haka zamu kwana ya nuna mata yatsunsa guda biyu a hade. Ba shiri ta tashi ni ba nufina kenan ba. Ni kuma nufina kenan my dear best friend. Amma seriously ya kike jin jikinki yanzu? Babu kurajen sai kaikayi wani lokacin. Yace discharge fa? Akwai amma bai kai na da ba. To Alhamdulillah sauki ya fara samuwa. Irin wannan infection din naci gare shi ki cigaba da shan magani. Kuma tsaftar nan kada ki sassauta mata. Anjima zan siyo miki wani ma. Godiya sosai tayi masa yana dariya yace kinga fa bana son godiya malama kawai ki kawo kudin consultation. An fada miki ana ganin Dr kyauta ne? Aishatu tace to da me zan biya Dr Rano? Bugo kofar dakinsa kamar zaa balleta yasa ya fasa magana. Fadila ce ta shigo da alama har yanzu batayi wanka ba. Ganinsu da tayi zaune kusa da juna yasa ta harari tace Aishatu to jarababbu da sanyin safiyar ma. Huzaifa ya daka mata tsawa kina hauka ne zaki shigo min ba sallama..kuma ki kiyaye abinda ke fita bakinki kada ranki ya baci. Samu wuri ki zauna mana kin tsaya min a ka. Aishatu tace ina kwana? Fadila ta yatsina fuska a hankali tace yana wurin uwarki. Sarai tasan sunji. Huzaifa ya yunkura zai tashi cikin fushi Aishatu ta rike masa hannu. Baby dan karasa shafa min man a bayana mana. Dama wata jallabiyarsa ta saka Fadila tana ganin ya mika hannu ta tashi wannan karuwancin ba dai a gabana ba. Dama kiran na wulakanci ne? Ya ce ga wanda ya wulakanta kansa ba.
Bayan yan mintuna dakin yayi shiru Huzaifa yayi musu nasihar zaman lafiya sannan yace idan Aishatu ta gama kwana ukunta a matsayinta na bazawara zasu raba kwana two-two days. Sannan ya gargadi Fadila akan rufe kofar side din aishatu. Zansa a saka sabun handle yanzu amma Allah kika sake a gidanku zaki kwana. Itama tayi dana sanin yin hakan don gashi dakin da take jimawa bata gyara ba ta zage ta gyara wata daban ta kwana a kai.
RASHIN GODIYA ✂ 30
Huzaifa na rufe kofar gaban Aishatu ya fadi. Wani tsoro ya saukar mata ta kasa karasa shiga dakin. Irin kallon da Huzaifa ke yi mata yasa taji kunyar kayan jikinta ta mika hannu zata karbi mayafinta da ta bashi. Boye shi yayi a bayansa tace don Allah ka bani...kwaikwayonta yayi yace don Allah naki. A hankali ya matso kusa da ita... har suna jin sautin numfashin juna yace ba don ni kika yi wannan kwalliyar ba. Tayi dan murmushi tare da sunkuyar da kanta kasa. Hannunta ya rike ya ja ta har bakin gado sannan ya zaunar da ita. Ya zauna a daidai saitin kafafunta daga kasa. Ya kallonta yace Aish you always amaze me. Nayi mamakin yadda mijinki na fari ya kasa fahimtar ki har ya rabu dake. Maganar Huzaifa tasa hawaye ya cika mata ido....muryarta tana rawa ta soma magana. Shekarata 17 aka yi min aure. Kuma kamar yadda na fada maka Fahad mugun mutum ne. Bazaka fahimce shi ba sai zama ya hadaku. Sau tari mutum baya gane ni'imar da Allah Yayi masa sai ya rasa ta. Duk musulmin kwarai yana da kyau yayi godiya ga Allah a halin samu ko rashi domin duk abinda Ya bamu yana tafe da alkhairi. Rashin godiya ga Allah akan kyautarSa garemu yana jawo mana asara mai yawa. Kaga dai yadda Fadila ta gigice akan auren nan wanda ita ta jawowa kanta. Shima Fahad har yau bai fidda ran sake aurena ba. Kaga a da basu nuna damuwarsu yadda ya kamata ba sai yanzu da suka ga zasu rasa abinda da basa bashi mahimmanci. A shekaru ashirin da hudu nayi aure uku, ina fata ka zama mijina na karshe...ta dan numfasa, nasan cewa ours is not a love marriage amma ina fata zaka rikeni amana ka zama mijina na karshe.
Maganganun Aishatu sun shige shi sosai amma kalmarta ta karshe ta dan daga masa hankali har yayi saurin rufe mata baki da hannunsa. Murmushi ta sake yi masa....Dr nasan kana matukar son Fadila kuma kana son ku zauna lafiya da ita. Nima ina so maka hakan shiyasa zan taimaka maka har ta gane rashin dacewar abinda take yi. Amma ina rokonka alfarma daya....ya kura mata ido yana jiran yaji abinda zata ce. Nasan ina tare da ciwo don Allah kada ka bari kowa ya sani. Sirrina ne wanda bana son ya zama sanadin da za'ayi min gori watarana. I just want a home to call my own.
Zuciyar Huzaifa ba karamin karyewa tayi ba. Sai yau ya kara yadda Aishatu mace ce mai hankalin. Hawayen da yaga tana shirin yi ne yasa ya janyota jikinsa ya rungume. Sun jima a haka yana shafar gashin kanta wanda yasha gyara. Kanta a kasa ta fara kokarin tashi ya ce tsaya mana ai nima ina da abin fada. daga yau you are my best friend, my sister and.......shiru tana jiran taji me zai ce har ta gaji ta dago kanta. Kissing dinta yayi a baki kafin yace my wife yana mata murmushi. Har ya tashi ya shiga wanka bata iya tashi ba saboda yanayin da ta sami kanta. Anya Aish ko dai son Dr H.M Rano kike yi?
wasu riga da wando na bacci ya bata ta dauka ta shiga toilet. Wanka tayi da alwala ta fito suka yi nafila. Ya fita samo plate da zai zuba musu naman da Saddiqa ta gasa masa. Yana dawowa ya tarar ta jingina da gado tana bacci. Tausayinta yaji ya kara kamashi ya dauketa a dora ta akan gado. Sai da ya gama abinda yake yi ya kashe fitila ya kwanta shima.
Fadila dake zaune a kofar dakin tun bayan ya fita dauko plate tana ganin duhu ta karkashin kofar taji kamar zuciyarta zata buga saboda kishi. Tana kuka tace na shiga uku. Nan ta zauna tana ta rusa kukanta har asuba babu wanda yasan tana yi.
RASHIN GODIYA ✂ 32
Huzaifa ya kira mai gyaran kofa kamar yadda ya fada an gyarawa Aishatu kofarta. Bangarenta akwai kitchen, parlour da dakuna biyu. Daya an saka mata gado mai tsada irin na zamani har kuka sai da tayi. Iyayenta suna iya kokarinsu wurin kyautata mata. Daya dakin kuwa kayan turare ne da hadadden kafet da pillows. Ga shi akwai wadatar iska a wurin. Sai ta mayar dashi wurin shan iska kawai. Falonta ma ya hadu ga kitchen wanda Huzaifa ya wadata store din cikinsa da dukkan kayan abinci. Ya kuma sanar dasu kowa zatayi nata abincin ne wadda take da girki ranar ta hada dashi. Hakan yayiwa Aishatu dadi don tana gudun abinda zai hadata da Fadila.
A kwanaki ukun da Aishatu tayi sun kara sabawa da Huzaifa. Banda masallaci babu inda yake zuwa. Idan ya dawo kuwa hira suke yi da bawa juna labarai akan rayuwarsu. Lokacin bacci kuwa a kasa yake kwanciyarsa tana daga kan gado. Haka zasu cigaba da hira har suyi bacci. Abinci kuwa kullum zaa kawo safe ,rana da dare daga gidan umma. Aishatu tace wannan wahala ce zata rinka dafawa da kanta. Yaya kubra da ta ji sakonta ta kira ta a waya...ke dan kwana ukun nan ai lokaci na baki ki kara sace zuciyar mijinki. Duk abinda nake dafawa irin wanda yake so ne so kada ki damu. Kullum aka kawo sai Aishatu ta buga waya tayi godiya. Ita kuwa Fadila an ga bulus itama dena girkin tayi. Wani lokacin ma kafin Aishatu ta debarwa Huzaifa ita zata fara diba duk ta tsince naman ta bar musu kada. Ana gobe Aishatu zata fita girki Huzaifa yana aiki akan computer a dakinta tana zaune daga gefensa tace yaushe zamu je gidan Umma ne da Rano? Wani murmushi yayi wanda ya nuna yaji dadin abinda ta fada sosai. Aish harda Rano zaki je? Tace eh mana. Ba garinku bane kuma akwai yan uwanka a can. Ni kazo ka fada min su waye closest to you ma a can tun wuri. yace mai yasa? Murmushi tayi tace sirri ne. Lumshe idanunsa yayi cike da nishadi. Yan kwanakin da suka yi tare damuwarsa da yawa ta ragu sosai. Ya dan jima a haka yana jindadin kamshin falon nata sannan yace ki bari sai kin sake karbar girki. Ta bata fuska har gidan Umman? Kinga yanzu aiki nake dan dubawa kuma gobe ba ke ce da girki ba. Kema bazaki so ranar girkinki na fita da Fadila ba. Aishatu tayi dariya bazan hana ba amma ka tabbatar idan kuka dawo sai dai ka koma dakinta don ban san abinda zan maka ba. Dariya sosai yayi ya kura mata ido har sai da ta kawar da nata tana murmushi. Aish kina kishina??? Muryarsa can kasa yayi maganar ta tashi da sauri uhmm bari naje na gyara maka daki. Amsar da bata bashi ba kenan.
Sai da ya dawo daga masallaci da magriba yace ta shirya su je gidan Umma da gwammaja. Murna a wajen Aishatu baa cewa komai. Yau zata je taga su mama, dama kullum sai sunyi waya har da baba ma. Huzaifa yana kallon yadda take ta shiri cike da doki har yar waka ta rinka yi a gaban madubi. Wani turare ta dauko mai matukar tsada. Anti Sauda ce ta bata kyauta tun kafin tayi aure, tsaraba da mijinta ya dawo daga Dubai. A ledarsa ma yake ta saka a jakarta. Lace tasa mara nauyi riga da zani sai mayafinta babba wanda ta dora a kanta bayan ta kashe dauri. Kallonta kawai yake tana saka takalmi yace Aish kinyi kyau kamar amarya. Ta dan tura baki me kake nufi, ni ba amarya bace? Kinfi kama da.....ta koma gaban mirror tana sake kallon kanta. Da me nayi kama please? Ko dai kayan basuyi ba na canja. To sarkin rikicewa wasa nake. Komai yayi banda abu daya. Ta dago idanuwanta menene baiyi ba? Baki fesa min turare ba. Kinsan idan mutum baby ne babu wanda ya kaishi shagwaba. Ta rasa me yasa Huzaifa yake son sata jin kunya.
Tare suka fito duk sunyi kyau kana ganinsu kaga masoya masu kaunar juna. Ya shiga dakin Fadila yace mata sun fita. Naman gabanta ta cigaba da ci hankali kwance. Suna fita ta shiga kitchen ta dauko tabarya sai kofar bangaren Aishatu.
Gwammaja suka fara zuwa suka tarar da Baba da abin sallah a waje zai tafi masallaci sallar isha. Huzaifa ya bishi ta shiga ita kadai. Mama da kannenta sunyi murnar ganinta sosai har Huzaifa suka dawo suna ta hira. Baba yayi musu nasihar da ya saba akan rikon amana da kula da addini. Ga mamakinta kaya ya debo daga booth dinsa masu yawa ya basu. Suka yi ta godiya. A mota suna hanyar zuwa gidan umma yace Aish ina son Baba. Yana da kirki ga saukin kai, sai yake tuna min da nawa mahaifin. Tace Allah Yayi masa Rahma ni na hakura ya zama babanka daga yau. Shan miya amma. Meye kuma shan miya Aish? Tace dama ranar da na fara ganinka nasan kai dan kauye ne, ta rike haba ace dan kano bai san shan miya ba. To me ka sani? Ya kashe mata ido nasan yadda ake...in fada? Fadi mana nasan bazai wuce kace ka iya lomar tuwo ba. Sai da maigadi ya rufe gate din gidan yace mata nasan yadda ake kissing bakin Aish. Duk da sau daya hakan ta taba faruwa tsakaninsu ranar da aka kaita amma babu ranar da bata tunawa. Kafin ya gama kashe motar ta fice ta shiga gidan da gudunta..wannan kunya ta Aish. Ya shafi sumarsa yabi bayanta. Umma tayi murnar ganinsu sosai, tace autan umma har ka fara kiba. Aishatu tace dama sunanka kenan? To daga yau na samu. Yace haba umma meyasa kika fada a gabanta salon ta raina ni. Yaya kubra tace sai kai dai ka fiye son girma. Aishatu zo muje kici abinci. Aishatu tace ni dai daga yau umma nice autarki kinga ai girmeni. Duk suka yi dariya, ta tambayi su Aliya akace Shukriya ta tafi gidanta dasu. Sunyi hira sosai da zasu tafi ta bawa umma turaren da taho dashi. Tana son kamshinsa duk da yana kwali ana ji. Umma tayi ta sa mata albarka. Yaya Kubra kuwa sai washe baki kanninta ya auro yar arziki irin albarka. Sai goman dare suka koma gida. Sai dai tun daga kofar falo suka ga wurinta a bude. Kusan komai na falon an fasa shi babu wani abin mora hatta kafet da kujeru an tsaga su da wuka.
RASHIN GODIYA ✂ 34
Ranar har dare Aishatu bata ga fara'ar Huzaifa ba. Gaba daya hankalinsa ya koma kan gyaran dakin ta. Samarin unguwar ya samu su biyu suka share dakin aka fitar da duk abinda bazai moro ba. Ganin shima ya zage ana aikin dashi Aishatu ta gaji da zaman dakin ta shigo wurinsu harda dan murmushinta. Da me zan tayaku ko in kawo muku ruwan sanyi? Hannu kawai ya nuna mata alamar ta tafi. Haushinsa ya kara kamata, wai meye laifinta ne da zai tsiri sha mata kunu. Daki ta koma ta kunna tv tana kallo sai gashi ya shigo. Dauke kanta ma tayi don kada su hada ido. Ya dawo gefenta zai zauna ta matsa tare da kawar da kai daya gefen. Sai ya koma gaban tv ya tsaya ita kuwa ta runtse ido a dole bazata kalle shi ba. Yayi murmushi ya shiga toilet yayi wanka. Kafin ya fito ta tashi ta tafi dakinta. Kayan da ya debo ta duba babu undies a ciki shine ta tafi nema. Yana ganin bai ganta ba ya fita daga shi sai dogon wando. Bazai wuce ta koma dakinta ba, sai taje wani abin ya ji mata ciwo. Kawai sai yabi bayanta.
A durkushe ya ganta tana kuka sosai. Jikinsa a sanyaye ya karasa inda take. Ji tayi ya rungumeta ta baya, duk yadda taso ta kwace ta kasa. Shima kansa haushinsa take ji. Allah kadai Yasan da yadda Baba ya siya mata wannan kayan. Huzaifa ya juyo ta ita lokacin ta dena fizge fizgen don tasan yafi karfinta ko motsi ya hanata yi. Sake rungumeta yayi yana shafa mata baya..a hankali taji yana cewa Aish ki kara hakuri. Tun haduwarmu dake kike fuskantar matsaloli amma you always find a way to make things better. Wannan karon fadila ta wuce gona da iri amma i promise you bazan barta haka ba. Aishatu ta dago kanta a hankali suka hada ido....wani irin abu da bazata iya fasaltawa ba taji a wannan lokacin. Ga dukkan alamu Huzaifa ma yaji don wani irin murmushi ya sakar mata da ya kara narkar mata da zuciya. Hannunta ya rike suka koma dakinsa. Aishatu tace Dr...harararta yayi wai sai kinga fadila zaki kirani baby, ni nayi fushi. Ya bata dariya tace to yi hakuri baby. Amma seriosly magana zamuyi. Banga dalilinka na cewa fadila bata da girki ba har sai an gama gyaran dakina. Zaiyi magana tayi saurin cigaba Wallahi hakan daukar hakki ne. Abinda ya faru zargi ne muke tunda ido bai gani ba. Huzaifa yace Aish ya wuce zargi fa. Ke kinsan babu wanda zai miki haka sai ita. Aishatu tace ni dai ka je ka fada mata zata karbi girki ni bazan yi ba. Huzaifa ya ce Aish har zaki fara musu dani? Ta zauna bakin gado ba haka bane...lahirarmu nake dubawa. Me zamu ce idan Allah Ya tambayemu hujjar mu ta hukunta bisa zargi? Nasan kana mata uzuri amma please ka kara. Haka tayi ta bashi baki ko kadan bai so ba amma yasan gaskiya take fada masa. Rai a bace yaje ya sanar da Fadila ta shirya karbar girki da daddare.
Shawarar Wasila ta karba ta bashi hakuri sosai tana kuka. Ya dai ji amma bai sakar mata fuska ba. Kafin ya fita ya dawo ta gyara dakinta da falo. Yau harda wankin toilet. Sai da yayiwa Aishatu sai da safe ya fita...abin haushi hawaye taji ya sauko mata. Meye na kuka Aish ta tambayi kanta. Its not like kuna soyayya da angon naki. Sauran abincin da Yaya Kubra ta aiko mata taci. Shi kuwa Huzaifa yana ta cika da batsewa ya shiga falon Fadila. Ba yabo ba fallasa ta gyara dakin. Rigar jikinta kuwa iyakarta cinya. Tayi kyau sosai don ta iya kwalliya. Indomie ta dafa masa ya kalli abincin a wulakance amma dole yaci don yunwa yake ji. A hankali Fadila ta rinka jan hankalinsa har ya sakar mata jiki. Ranar zuciyarta fes ta kara tabbatarwa tana son mijinta kuma shima yana sonta. Dole ta yi gaba da Aishatu don bata ga matar da ta isa suyi sharing miji ba.
Fahad yana zaune gaban likita yana kara karanta report din test din da aka yi masa. Ya dago kai yanzu dr ka tabbatar ni da yahanasu duk bamu da problem? Dr ya gyara zaman glass dinsa yace kwarai kuwa Fahad. Komai lafiya hakuri kawai zaku kara. Kasan haihuwa lokaci ne. Amma na rubuta maka magani da zakuyi trying. Fahad ya daki table din dr din ya mike cikin fushi. Magani! Magani ! Magani! Na gaji. Ka bar maganinka kawai ba yau na fara zuwa test ba akan fertility ana bani. Ransa a bace ya fita....ya gaji da trying result yake son gani. Ba abinda yake so kamar haihuwa yanzu ido rufe. Idanunsa yaji suna masa zafi alamun hawaye na shirin zuba. A hankali yace Aisha I miss you.
RASHIN GODIYA ✂ 33
Saboda tsabar tashin hankali Aishatu ta kasa cewa komai. Kofar dakinta ta kalla an rotsa ta duk da katakon mai kwari ne. Da sanyin jiki ta karasa ciki abin mamaki baa taba komai ba. Karamin falonta kuwa cike yake da kamshi saboda komai na show glass dinta ya fashe rugu rugu. Bakinta ta toshe saboda kukan da yake neman fin karfinta. Sai hawaye kamar famfo. Huzaifa kuwa jingina yayi da abinda yayi saura na kofar falon ya runtse idonsa. bazai iya kwatanta yadda ransa ya baci ba. A hankali ya bude idonsa yana kallon Aishatu...mayafin da tasa ta toshe bakinta ne ya hana kukanta yayi karfi. Tausayinta yaji sosai kukanta yana kara daga masa hankali. Zuciyarsa kamar ta fashe don tsananin bakinciki. Fita yayi yana kwalawa Fadila kira cikin daga murya. Ko ita Aishatu da take daki sai da ta tsorata. Tare ya sun shigo da Habu maigadi. Mal Habu yace yallabai kaga barnar da ta faru ko? Fadila ta ruga da gudu ta rungume Huzaifa tana shesshekar kuka. Abban Aliya kaga girman mutumin kuwa? Allah ne ya rufa min asiri da kila ma yanka ni zaiyi. Iyakar karfinsa ya tureta don bai shirya jin karyar da zata yi masa ba. Mal Habu yace na zaga bayi kenan na rinka jin kamar ana buga wani abu. Ina zuwa naga Hajiya tana ihu tana kuka tace wani ne ya hauro yake fasa kayan hajiya amarya. Rainin hankali Huzaifa ya fada a zuci. Da kyar ya iya cewa to kai ka ganshi ne Mal Habu....ehhh, to na dai ga kamar giftawar inuwa dana leqa ta taga. Ba don girmansa ba da babu abinda zai hana Huzaifa dauke shi da mari. Amma sai yace runda baka da tabbas ina ganin gara a hakura da aikin nan naka idanunka sun fara samun matsala. Mal Habu yace a'a yallabai banga komai ba. Amma ita Haj a gabanta abin ya faru. Huzaifa bai tsaya sauraronta ba ya koma dakin Aishatu. Tana nan inda ya barta a tsaye tana zubar da hawaye. Dakinta ya shiga ya rinka fito da akwatunanta yana kwashe kayan wardrobe din yana zubawa a ciki. Sai da ya kwashi wanda zai iya sannan ya fara kaisu dakinsa daya bayan daya. Fadila tana falo tana dariyar mugunta. Ba don shigowar habu maigadi ba har dakin sai ta lalata. Ganin Huzaifa da akwatuna ta ce lafiya ina kuma zaka kai kayan? Shiru ma magana ce. Sai da ya gama kwashesu tsaf Aishatu dai bata iya cewa komai. Ya koma ya rufe kofar gidan sannan ya sake shiga dakin Aishatu. Ji tayi Huzaifa ya daga ta cak kamar jaririya yazo ya wuce Fadila dake matsar kwallar karya a falo. Bai ajiyeta ko ina ba sai akan gadonsa. Ruwa mai zafi sosai ya tara mata a toilet ya sake daukarta ya kaita sannan ya rufo mata kofa. Kofar dakinsa kowa key yasa ta waje ya rufeta sannan ya tafi dakin Fadila.
Waya ya tarar da ita tana yi. Jin alamun da mutum a bayanta yasa ta koma muryar kuka. Ai wasila na auna arziki da yau kunji mummunan labari. Wani kato ne.....wayar ya fizge kafin ta tashi ya fara zabga mata belt dinsa. Sai da yayi mata lilis ya kyaleta tana ta kwarma ihu. Mal Habu har ya gaji da buga kofar gidan. Itama Aishatu ihun Fadila yasa tayi saurin fitowa daga toilet taji kofar dakin kam a rufe. Bugu take iya karfinta ta kasa budewa.
Huzaifa ya kalli Fadila da jikinta yayi rudu rudu. Cikin fushi yace baki fi karfina ba Fadila, kina cin darajar aure ne kawai nake raga miki. Amma tunda kin zabi haka mu zuba ni da ke shege ka fasa. Kuma wallahi baki da girki har sai na gama gyarawa Aishatu dakinta. Idan zaki gyara halinki ki gyara otherwise ki kama hanyar gidanku. Haba na gaji da masifarki. Tun kafin nayi aure kike hura min wuta. Nayi auren ma ban tsira ba. Ki guji ranar da zaki kaini bango sai na miki fiye da wannan. Wai ni zaki rainawa hankali. Ki yi min barna a gida kice wani ne. Da gaske ne ai so zanyi ya hada dake a fashe fashen. Fadila cikin kuka take masa Allah Ya isa. Yayi gaba abinsa zuciyarsa ba dadi.
Yana bude kofar dakin ya tarar da Aishatu zaune a bakin kofa tana rusa kuka. Tana ganinsa tace me yasa ka dake ta? Yace kinga ki sami wuri ki kwanta raina a bace yake i dont want to talk now. Bata sake tanka masa ba ganin ya dau zafi sosai kamar ba yanzu suka shigo gidan cikin nishadi ba. A haka ya kwanta wurin da ya saba a kasa yana ta adduar neman sassauci a zuciyarsa har bacci ya dauke shi. Washegari da sassafe ya kira Yaya Zainab yace suzo gidansa ita da sauran yan uwansa. Aishatu tunda ta tashi take rakube a gefe. Fushin Huzaifa yana neman shafarta duk da ita aka yiwa laifi. Kafin tara na safe dukkan ninsu sun iso harda Yaya kubra da tayiwa umma karya ta fito. A gigice suke saboda kiran yayi wuri. Basu kara gigicewa ba sai da suka ga dakin Aishatu. Saddiqa tace ko baka fada ba auta nasan Fadila ce da wannan aikin. Wallahi sai naci ubanta a gidan nan. Yaya zainab dama halin umma suka yo ita da Huzaifa wurin hakuri tace ba haka zaayi ba saddiqa. Ina Fadilan take? Yaya kubra tace Allah Yaya indai zata fito babu abinda zai hanani dukanta. Ya take so ayi mata ne....fadila na jin muryarsu ta kama kofar dakinta ta rufe da key. Wurin Aishatu ya kaisu wadda tunda ta tashi take kuka. Tana ganinsu ta fada jikin Yaya kubra tana ta kuka. Gaba dayansu ta basu tausayi. Yaya Zainab tace to yan uwa lokacin zumunci yayi. Ya kamata duk mu hadu mu gyarawa Aishatu daki ba tare da sanin Umma ko su Mama ba. Itama Fadilan ka barni da ita zan bata last warning. Ta koma ga Aishatu kiyi hakuri kanwata don Allah kada ki daga maganar nan. Kai kuma na yarda ka hukunta ta duk yadda kake so amma banda saki please. Da fadila taki bude kofa daga waje tayi mata fada da nasiha. Huzaifa duk haushi ya ishe shi har wani lallaba ta ake. Ai bata ga komai ba a gashin kumar da zai mata. Aishatu kuwa ta rasa bakin yi musu godiya. Yaya shukriya tace ai yiwa kai ne.
Yaya Zainab na tafiya gida ta fadawa mijinta. Managing director ne a wani travel agency ya ce gaskiya yarinyar nan bata kyauta ba. Amma nasan maganinta....ya kira waya yayi wa wani magana sannan yace da Yaya zainab ki fada ma Huzaifa yayi wa amarya passport next week zasu tafi Umra. Yaya zainab ta washe baki lallai Aishatu yar gata ce.
RASHIN GODIYA ✂ 34
Ranar har dare Aishatu bata ga fara'ar Huzaifa ba. Gaba daya hankalinsa ya koma kan gyaran dakin ta. Samarin unguwar ya samu su biyu suka share dakin aka fitar da duk abinda bazai moro ba. Ganin shima ya zage ana aikin dashi Aishatu ta gaji da zaman dakin ta shigo wurinsu harda dan murmushinta. Da me zan tayaku ko in kawo muku ruwan sanyi? Hannu kawai ya nuna mata alamar ta tafi. Haushinsa ya kara kamata, wai meye laifinta ne da zai tsiri sha mata kunu. Daki ta koma ta kunna tv tana kallo sai gashi ya shigo. Dauke kanta ma tayi don kada su hada ido. Ya dawo gefenta zai zauna ta matsa tare da kawar da kai daya gefen. Sai ya koma gaban tv ya tsaya ita kuwa ta runtse ido a dole bazata kalle shi ba. Yayi murmushi ya shiga toilet yayi wanka. Kafin ya fito ta tashi ta tafi dakinta. Kayan da ya debo ta duba babu undies a ciki shine ta tafi nema. Yana ganin bai ganta ba ya fita daga shi sai dogon wando. Bazai wuce ta koma dakinta ba, sai taje wani abin ya ji mata ciwo. Kawai sai yabi bayanta.
A durkushe ya ganta tana kuka sosai. Jikinsa a sanyaye ya karasa inda take. Ji tayi ya rungumeta ta baya, duk yadda taso ta kwace ta kasa. Shima kansa haushinsa take ji. Allah kadai Yasan da yadda Baba ya siya mata wannan kayan. Huzaifa ya juyo ta ita lokacin ta dena fizge fizgen don tasan yafi karfinta ko motsi ya hanata yi. Sake rungumeta yayi yana shafa mata baya..a hankali taji yana cewa Aish ki kara hakuri. Tun haduwarmu dake kike fuskantar matsaloli amma you always find a way to make things better. Wannan karon fadila ta wuce gona da iri amma i promise you bazan barta haka ba. Aishatu ta dago kanta a hankali suka hada ido....wani irin abu da bazata iya fasaltawa ba taji a wannan lokacin. Ga dukkan alamu Huzaifa ma yaji don wani irin murmushi ya sakar mata da ya kara narkar mata da zuciya. Hannunta ya rike suka koma dakinsa. Aishatu tace Dr...harararta yayi wai sai kinga fadila zaki kirani baby, ni nayi fushi. Ya bata dariya tace to yi hakuri baby. Amma seriosly magana zamuyi. Banga dalilinka na cewa fadila bata da girki ba har sai an gama gyaran dakina. Zaiyi magana tayi saurin cigaba Wallahi hakan daukar hakki ne. Abinda ya faru zargi ne muke tunda ido bai gani ba. Huzaifa yace Aish ya wuce zargi fa. Ke kinsan babu wanda zai miki haka sai ita. Aishatu tace ni dai ka je ka fada mata zata karbi girki ni bazan yi ba. Huzaifa ya ce Aish har zaki fara musu dani? Ta zauna bakin gado ba haka bane...lahirarmu nake dubawa. Me zamu ce idan Allah Ya tambayemu hujjar mu ta hukunta bisa zargi? Nasan kana mata uzuri amma please ka kara. Haka tayi ta bashi baki ko kadan bai so ba amma yasan gaskiya take fada masa. Rai a bace yaje ya sanar da Fadila ta shirya karbar girki da daddare.
Shawarar Wasila ta karba ta bashi hakuri sosai tana kuka. Ya dai ji amma bai sakar mata fuska ba. Kafin ya fita ya dawo ta gyara dakinta da falo. Yau harda wankin toilet. Sai da yayiwa Aishatu sai da safe ya fita...abin haushi hawaye taji ya sauko mata. Meye na kuka Aish ta tambayi kanta. Its not like kuna soyayya da angon naki. Sauran abincin da Yaya Kubra ta aiko mata taci. Shi kuwa Huzaifa yana ta cika da batsewa ya shiga falon Fadila. Ba yabo ba fallasa ta gyara dakin. Rigar jikinta kuwa iyakarta cinya. Tayi kyau sosai don ta iya kwalliya. Indomie ta dafa masa ya kalli abincin a wulakance amma dole yaci don yunwa yake ji. A hankali Fadila ta rinka jan hankalinsa har ya sakar mata jiki. Ranar zuciyarta fes ta kara tabbatarwa tana son mijinta kuma shima yana sonta. Dole ta yi gaba da Aishatu don bata ga matar da ta isa suyi sharing miji ba.
Fahad yana zaune gaban likita yana kara karanta report din test din da aka yi masa. Ya dago kai yanzu dr ka tabbatar ni da yahanasu duk bamu da problem? Dr ya gyara zaman glass dinsa yace kwarai kuwa Fahad. Komai lafiya hakuri kawai zaku kara. Kasan haihuwa lokaci ne. Amma na rubuta maka magani da zakuyi trying. Fahad ya daki table din dr din ya mike cikin fushi. Magani! Magani ! Magani! Na gaji. Ka bar maganinka kawai ba yau na fara zuwa test ba akan fertility ana bani. Ransa a bace ya fita....ya gaji da trying result yake son gani. Ba abinda yake so kamar haihuwa yanzu ido rufe. Idanunsa yaji suna masa zafi alamun hawaye na shirin zuba. A hankali yace Aisha I miss you.
RASHIN GODIYA ✂ 35
Haka Aishatu ta cigaba da zaman hakuri da Fadila don bata fasa halin neman tsokana ba. Tsakaninta da Huzaifa suna hira sosai. Dakinsa kuwa ya bar mata sai dai ya je daukar kaya. Ranar da Aishatu zata karbi girki tun da ya farka da safe ya sami kansa cikin nishadi. Fadila tana kwance gefensa ya dan taba ta...a hankali ta bude ido saboda baccin da take ji. Yace fadila tara da rabi fa...kinsan dai daren jiya cornflakes nasha. Please ki tashi ki bani abinci. Ta juyar da kanta ni ka kyaleni na dan kara kadan, goma ma bata yi ba.
Yace idan baki tashi ba zanje wurin Aishatu nasan....kamar an tsikareta ta tashi naji naji bari nayi brush. Ta fita yabi bayanta da dariya. Fadila kishi.
Bayan laasar ya tafi dauko yaransa don sati daya ya rage Aliya ta koma makaranta. Sunyi murnar ganin Abbansu sosai suna ta bashi labarai. Har yar kiba yaga sunyi...ba dole ba tunda suna samun abinci ba kame kame ba.
Aishatu tun asuba ta hau gyaran daki. Har mamakin kanta take irin wannan zumudi kada ma Huzaifa ya gane. Ita dai tasan ta damu sosai da shi...muryarsa kadai idan taji sai gabanta ya fadi. Garin yaya ta soma sonsa ne? tun a kan fahad ta sallama maza shima bazata bari ya sani ba har sai ta tabbatar da matsayinta a wurinshi. Kamar kullum ya shigo su gaisa bayan ya dawo ya ganta tayi kwalliya sosai kamar mai zuwa biki. Sai dai ya kula bata rabo da mayafi. Tun zuwanta sau daya ya ganta ba mayafi ranar da aka kawota. Toilet take shiga ta shirya kullum ta shirya. Yana ta binta da ido ta fada masa abinda take bukata na cefane don girkin rana washegari. Yace ko in samo miki yar aiki ne Aish? Hankalinsa yana ga kyakkyawar fuskarta kamar bai taba ganinta ba. Ta danyi murmushi bana bukata gaskiya. Ina su Aliyun ne ina ta jiran ganinsu. Yaji dadi sosai ya ce suna dakin Fadila bari na kira su. Tace ka bari zani da kaina muje kayi introducing dina dai. Zan fada musu ke ce maman kannensu 12 masu zuwa nan gaba. Zaro ido tayi tana dariya sai kace wata bera? Yace to wa ya sani ne abu a duhu? Filo ta dauko ta jefa masa sannan suka fita suna dariya.
Fadila tana rungume da Aliyu tace kada ku manta sunan da na fada muku dai kunji ko? Aliya tace ai ni Abba zan fadawa ya koreta kada ta sha min jini. Karaf maganarta a kunnen Huzaifa yace wace zata sha jininki kuma Aliya..kinje kin koyo zance a wurin su hidaya ko? Aishatu na shigowa Aliya da Aliyu suka yo kanta har ta fara murmushi sai suka cire takalma suka fara jifanta. Huzaifa ya daka musu tsawa meye haka Aliya? Ta kyabe baki ta soma kuka Anti Mayya ce ta shigo zata shanye mana jini. Huzaifa ya tsaya yana mamakin wannan magana ta yaran shi. Aishatu ta dafe goshi inda takalmin Aliya ya sameta ta juya zata fita su Aliyu suna mata ihun Anti Mayya. Sai da ta fita Huzaifa ya janyo Aliya yar shekara hudu da rabi da Aliyu dan shekara uku. Wa ya fada muku sunanta kenan. Aliyu yace Mummy tace mana itama ta sha mata jini jiya da straw ko Yaya ya tambayi yar uwarsa. Kuma da zafi kamar allura. Fadila ta kwashe da dariyar mugunta. He should have known mai hali baya canjawa. Yaran yayi wa fada sosai yace da Fadila kin kyauta sannan ya fita cikin fushi.
A kitchen dinta ya sameta tana kwashe tuwon shinkafa. Yayi saurin zuwa zai karba ta hana shi. Tana gama zuba tuwon a leda ta kulle ta rufe flask din. Sai ta hau gyaran gas cooker din. Yana magana taki kula shi sai aiki take kawai. Miyar agushin da take yi ta zubawa ganyen ugu ta cigaba da aiki. ya gaji da kallom yadda take yi ita a dole bazata karaya ba. Riko ta yayi ta karfi Aish listen to me please. Ta fizge hannunta kaje daki na kusa gamawa kitchen din akwai zafi. Janyo ta yayi ta karfi ya matseta a jikinsa. Kuka mai tsuma zuciya ne ya kwace mata ta rinka yi bai ko yi yunkurin bata hakuri ba. Gara tayi kukan ko zuciyarta ta sassauta.
RASHIN GODIYA ✂ 36
Kusan minti biyar tana abu daya bai kosa da ita ba har ta gaji ta dena don kanta. Tana dagowa ta ga gaban farar shirt dinsa duk bakin kwallinta ya bata masa. Idanunta yabi yaga abinda take kallo...ya dan shafi fuskarta stop looking worried indai akan wannan bakin ne za'a wanke. Ta kirkiro murmushi ni kwallin da nayi asara ne ya dameni. Duk ya kare a gaban rigarka. Har zuciyarsa take burge shi, a wannan yanayin take iya wasa dole ya jinjina mata. Sai Fadila tayi dana sanin abinda tayi don bazai kyaleta ba. Amma yanzu burinsa bai wuce yaga farincikin Aish ba.
Da taimakonsa suka kai kwanukan abincin falo tunda nasa dakin babu. Ta kawo masa fruit juice wanda ta hada da kwakwa, kankana, dabino da ayaba tayi blending ta tace. Sugar kadan ta kara tasa a fridge yayi sanyi. Komai nata a nutse take yinsa yaji ta kara shiga ransa sosai. Love will find its way tabbas haka ya taba fada mata...ko dai har ya iso ne bai sani ba? Shi kadai yayi murmushi tare da lumshe idanunsa. plate ta dauko zata yi serving dinsa abinci tana kallonsa. Bata gajiya da kallonsa...sai ta tuna abinda Fadila tayi mata....a sannu zan rama ta fada a ranta. Fahad ma ta koya masa hankali bare mace yar uwarta.
Yaji dadin abincin sosai yayi ta mata godiya akan yadda ta iya bata lokaci tayi masa girki. Ya so nuna mata godiyarsa fiye da haka don shi da samun abincin kirki dai yaje gidan Umma. Sai dai kuma yanayin da suke yasa bazai iya ba. Fadila tayi nasarar bata musu mood dinsu. Kafin ya gama cin abincin ma tayi tafiyarta daki. Wanka ta sake yi ta tsaftace jikinta ta kwanta. Kanta taji yana mata matsanancin ciwo. Ta kasa tashi ma bare ta nemi Huzaifa ya bata magani. Wasu hawayen ne suka fara zuba...yanzu ita haka rayuwarta zata kare kullum cikin bacin rai. Anti Mayya da 'ya'yan mutumin da sonsa yayi mata mugun kamu suka kirata yafi komai kona mata rai. Tun yanzu kenan ina ga idan suka kara girma Fadila tana musu hudubar tsiya. Huzaifa kuwa da ya gama cin abinci dakin fadila yaje. Yaran sunyi bacci Aliya tayi cuku cuku da rigar shaddar dake jikinta wadda Fadila ta gagara cire mata. Shi kuwa Aliyu duk sanyin AC da fanka daga shi sai pant ta kwantar dashi. Fadila na ganinsa ta ce yau ma dukan nawa kazo yi a gaban 'ya'yana? Bai kulata ba ya saka musu kayan bacci ya gyara musu kwanciya. Ya dubeta da kyau...ki sani Fadila duk mai hankali yana gudun ranar dana sani. Duk abinda kike shukawa da hannunki ba na wani ba zaki girbe wata rana. Auren mace sama da daya ba kaija farau ba so duk wani haukanki bazai sa na saki Aish ba. Na fada miki ina raga miki ne darajar aure to ki sani duk wanda bai godewa ni'imar Allah ba wata rana zai godewa azabarSa. Naso yi miki hukunci mai tsanani sai gashi wadda kika cutar ta nuna min komai a sannu ake binsa. Yanayin da na ganta bayan ta fita dazu ya sa zan barki da halinki. Yana juyawa zai fita ta yi shewa ta tafa hannu Ahayye yaro
Ahayye ba yaro ba
Iyye nanaye
Duniya bata bar kowa ba hatta wanda baa auri uwarsa ba ma jiransa take. Ki ji tsoron Allah Fadila.. tace ina ji Huzaifa, dole kake ganin laifina tunda ka hadu da annoba, ka auri karuwa ragowar mazan titi. Itakar karfinsa yasa ya mareta sai da taga haske ya fita cikin bacin rai.
Dakinsa ya shiga yaji zafi don babu abinda ke kunne na sanyaya daki. Hatta windows duk an saki labule. A tsakiyar gado ya ganta ta rufa da bargo. Yayi saurin yaye bargon yana cewa lafiya Aish? Rawar sanyi take yi sosai jikinta ke karkarwa. Ga wani katon hijab ta saka, yana kokarin cirewa tana kara rike abinta. Idanunta sunyi ja sosai da gani ta dade tana kuka. Ba don Umma ba yau Fadila sai dai ta kwana a gidansu a yadda yake ji a ransa. Da kyar ya iya cire hijab din tan masa wani kukan ita sanyi take ji. doguwar rigar bacci ce a jikinta ta cotton. Ya kai hannu kai da wuyanta. Jikinta yayi mugun zafi, Oh my God ya fada yana tashi ya tsaya yiwa wadda bazata dauka ba nasiha ga Aish tana kwance. Ruwan famfo ya debo a wata roba ya hado da karamin towel. Jikinta ya rinka bi yana gogewa tun tana cewa ya bari har ta dena. Shi har mamaki ta bashi a wannan yanayin wai har tasan kunya don rufe jikinta ta rinka yi ita a dole kada ya ga jikinta.sai da ya gama ya zubar da ruwan ya dawo ya bude wata drawer ya dauko first aid box. Idanunta duk sun mata nauyi da kyar take bude su. Amma tana ganin ya fito da syringe ta fara kokarin tashi. Kayi hakuri don Allah Dr bana so...hawayen da ya tsani gani take yi. Yace kema kiyi hakuri nayi miki don ki sami lafiya. A hankali ta fara kokarin gudu yace bazan miki da zafi ba kinji. Tace to tsaya na shirya...a zaune nake ma ya fada. Ganin dai shirin yaki karewa sai kawai ya rungumeta yadda bazata motsa ba har yayi mata. Ai kuwa wata kara ta saki tare da cigaba da kuka mai sauti. Yana sakinta ta soma dukansa. Shima yasan ruwan allurar akwai zafi. Ya tashi ya kawo mata ruwa tasha magani. Sai dai tana sha shima da kyar ta fara kakarin amai. da gudu taje toilet ta amayar da maganin. Duk tausayinta ka kamashi ya gyara mata jiki kuma ya gyara wurin sannan ya sake kwantar da ita. Sai da yayi nafila har ya jefa pillow kasa inda yake kwana sai ya dawo dashi gadon. Gefe dai ya kwanta yana kallonta cike da tausayi da tsantsar so. Ya tabbatar bazai taba jindadin rayuwarsa ba idan babu Aishatu a ciki. Ta soma bacci yaga tasa kafa tana ture bargon. Gumi take sosai hakan ya tabbatar masa zazzabin ya sauka. Haka yayi ta kallonta har bacci ta dauke shi.
RASHIN GODIYA ✂ 38
Tuni Huzaifa ya tattaro dukkan nutsuwarsa. Idanunsa sun kasa barin Aishatu. Ita kuwa ba don kada Fadila tayi saurin gano ta ba da ko kadan bazata iya jurar kallonsa ba. Ya juga ga Fadila wadda kuka yaci karfinta sosai, bari na gama na dawo zan kira Baban gandu na sanar dashi abinda yake faruwa. Ko sakin da Huzaifa yayi mata bai kada mata ciki kamar sunan Baban gandu da huzaifa ya fada ba. Wan mahaifinta ne wanda tun suna yara suke tsoronsa. Mutum ne mai tsayar da gaskiya amma yana da fada sosai. Idan laifin mutum ya tsananta ba bakon abu bane a gareshi ya dake shi.
Aishatu ta dauki mayafinta ta yafa tare da bin bayan mijinta. Falon Huzaifa na waje wanda yake tarbar baki suka shiga. Bata ma san dashi ba sai ranar. Mal Habu yayi wa Baba da Mahmoud kaninta jagora ya shiga. Murnar a wurinta ta kasa buya, ta durkusa su gaisa sai kuka. Baba yayi saurin yiwa Huzaifa kallon tuhuma. Har abada bazai kara bari wani namiji ya wulakanta masa 'ya ba. Yana son abarsa sosai. Huzaifa ya wayance kinga dai Mahmoud yana kallonki kina hawaye. Baba ya dubi dan autansa kai fita waje kafin ka sami labarin kaiwa gida. Duk suka yi dariya harda ita mai kukan. Huzaifa yace Baba ai tunda aka ce kazo ta fara kwallah wai bata taba tsammanin ganinka ba a gidanta. Mal Said yayi yar dariya yau ma hanya ce ta biyo dani kuma dai kaninki dana aiko ya nace sai munzo. Huzaifa ma ya durkusa Baba ya taro shi da hannu ya bashi hannu suyi musabaha. Haba Huzaifa ai kai dana ne. Dana da ya kira shi yasa yaji dadi. Wani karamin buhun da Mahmoud ya ajiye Baba ya nuna musu. Ga tsarabarku daga Getso. G Juma ce tace ki raba har su Hajiya kwan zabi ne. Bakar Ledar kuwa na yar uwarki ne. Aishatu tace wacce Baba? Yace yayarki mana, ya dan kalli Huzaifa sunan ne ya dan kwanta min. Huzaifa da Aishatu suka yi shiru sai can tace mungode Baba. Da ganinsu yasan akwai matsala yace Aishatu kada kiyi kuskuren yi min karya menene? Naga kuna yiwa juna kallon kallo ko zuwan nawa ne bai kamata ba. Huzaifa yace Subhanallah Baba ba haka bane. Sallamar Fadila ce tasa hankalinsu ya koma ga kofar falon.
Bayan fitarsu ta kira wasila a firgice tana kuka tana fada mata abinda ya faru. Wasila na shiga uku Huzaifa ya sake ni. Tace ke kwantar da hankalinki yar uwa. Kije ki bashi hakuri sosai a gaban Aishatun. Itama ki bata ni kuma ki bar sauran a hannuna zam nemo mana Fahad dinnan duk inda yake. Nayi miki alqawari ta inda ta shigo zata fita. Fadila taji dadin zancen wasila tace bari su dawo baban shegiyar ne yazo. Wasila tace to zama bai kamaki ki ba. Kije ki bada hakurin a gabansa. Ki tabbatar yasa baki Huzaifa ya mayar dake.
Fadila ta karaso cikin falon lullubinta har ka. Gaban Aishatu ta fara durkusawa ki yafe ni Aisha. Nabi son zuciya na cutar dake. Wallahi ina son mijina bazan iya rayuwa babu shi ba. Ta koma kan Huzaifa ka yafe min Abban Aliya nayi maka alqawarin ganin sauyi a halayena. Huzaifa duk kunya ta kamashi a gaban suriki. Ta tashi ta koma gaban Baba. Ka yafe min abinda nayi maka kwanaki kuma ka taimakeni ka sa baki ya mayar dani. Saki daya yayi min dazu. Ta kuma rushewa da kuka kamar wata zautacciya. Huzaifa ya harzuka me ya hadaki da Baba kuma? Duk suka yi shiru ya sake maimaita tambayarsa da tsawa ga Fadila a tsorace tace kwata na watsa masa kuma na gargade shi kada ya bari ayi auren ku. Huzaifa ya yo kanta zai doketa da kafa. Tashi ki fitar min daga gida.
Baba yace ashe zamana anan bai kara komai ba dana? Ina gabanka kana korar mace. Wata rana Aishatu zaka koro min kenan. Cike da kunya da takaici Huzaifa ya labartawa baba irin cin kashin da take yiwa Aishatu. Kwarai ran baba ya sosu saidai yana tsoron Allah Ya kamashi da laifin kin bada shawara tagari. Na yarda kaddara ce ta kawo ni gidanka a yau. Indai ina da mutumci komai kankantarsa a idonka ka mayar da ita yanzu. Huzaifa yace haba baba kafi karfin haka ma. Aishatu taji dadin yadda ta kasance. Bata da burin zama sanadin fitar wata mace daga gidan mijinta. Baba ya yi musu nasiha sosai akan hakuri da juna. Shi da yazo ya da niyar su gaisa sai gashi sun kusa awa daya. Huzaifa ya harari Fadila bayan tafiyar baba kinci sa'a yau. Amma next time you won't be so lucky. Ta tashi a sanyaye kamar gaske...babu next time Huzaifa. Aishatu duk da taji dadi amma a tsorace take, ta tabbatar mutum baya canja hali lokaci daya. Sai dai zata yi mata uzuri da adduar su sami zaman lafiya mai dorewa.
RASHIN GODIYA ✂ 37
Ita ta fara tashi da asuba jikinta yayi mata nauyi amma zazzabin da ciwon idon duk yayi sauki. Sai idanunta da suka kankance ita da kanta taji hakan. Tana juyawa ta ga Huzaifa yana bacci....kasa dauke ido tayi daga kansa ta fara tunanin me ya kawo shi gadon. A hankali ta tuna abinda ya faru a daren sai kunya ta kamata. Rufe ido tayi da hannuwanta kamar yana kallonta. Sai kuma ta cigaba da kallon fuskarsa....Huzaifa irin mutanen nan ne masu kwarjini da daukar hankali. Kyakkyawan sajensa ya zagaye habarsa zuwa saman bakinsa. Ji tayi sonsa yana karuwa a zuciyarta sosai. Ta shagala da kallonsa kamar daga sama taji yace nayi miki kyau ne cikin sanyin murya. Dama gadon ya tsage ta fada ciki haka taji don kunya. Zata gudu yayi saurin riko ta. Zama yayi suna fuskantar juna amma ta runtse idanunta yace ki bude ido mana Aish. Ta girgiza kai da sauri. Yayi murmushi to bari nima na kare miki kallo yadda kika yi min. Kokarin noke kai yaga tana yi sai ya tashi bari nayi alwala kada kisa mu makara sallah.
Ko da ya dawo daga masallaci bata dakin. Ya zauna karatu ita kuwa tana kitchen. Sauce tayi da mince meat wanda yasha albasa, attaruhu, koren tattasai, da caras. Sai ta kwaba flawa da ruwa da kwai daya sai dan gishiri. Haka ta rinka soyawa da mai. Yayi fari kuma yayi kyau sai ta dama kunun gyada ta kai masa dining table. takwas ta kusa lokacin da ta gama ta same shi yana bacci. Bandaki ta shiga tayi wanka ta shirya. Har ta gama yana bacci ta dan kwanta itama don jikinta babu kwari sai. Basu tashi ba sai shadaya da rabi. Ta rinka salati wai ta makara. Yace to aikin me zaki yi? Tace to tashi kayi wanka kazo kaci abinci. Wai yaushe rabon duniya...tun Fadila na amarya ma sai ta gama bacci take dora abinci. Yace ki kawo min daki kawai I am feeling lazy. Tayi dariya ta fita main falon gidan inda ta ajiye abincin. Aliya ta gani akan kujera shi kuwa Aliyu akan dinning table din suna cin abinci. Wurin kaca kaca sun zubar da miya. Kuma abin takaicin ma ba'a plate suke ci ba. Flask din suka bude suna tsoma hannuwansu. Yau da ita ta haifesu kila sai tayi musu duka. Hawayen ma sunki zuwa. A hankali ta karasa gaban table kafin tayi magana Aliya ta sauka da gudu tana kiran mummy. Shi kuwa Aliyu akan table ya kasa sauka sai ihu yake wayyo Abba ga Anti Mayya. A tsaye yake yana ihu sauran kadan ya fado Aishatu tayi saurin daukansa. Kafin ta ajiye shi sai dukanta yake da hannuwansa. Fadila da Huzaifa kusan a tare suka fito. Yaro kuwa ihu yake kamar ya shide. Fadila ta karbe danta kaga ni ko Huzaifa ka dauko matar da zata kashe min yara. Huzaifa yayi mata tsawa shut up fadila! . Aishatu kujera kawai ta dafe don kada ta fadi. Bazata iya kwatanta bacin ranta ba. Huzaifa yace Aish me ya faru Aish? Cikin rawar murya tace na fito daukar abincinka na tarar suna ci. Wallahi banyi musu magana ba ma. Aliyu naga yana ihu shine na sauke shi fa. Fadila ta kalli wurin da suka bata ta rinka dariya. Aliya tace Mummy ce ta bude mana tace muci. waya Huzaifa ya kira dreban Umma yace yazo gidansa yana jiransa. Duk a falon suka zauna wurin shiru banda kukan Aliyu. Kusan minti ashirin sai ga dreban ya iso. Hannun Aliyu da Aliya ya kama ya kaisu mota..ka kaisu wurin umma ka fada mata zanzo anjima. Fadila tana ta masifa a bata yaranta ko sauraronta baiyi ba. yana shigowa ya sami takarda da biro ya zauna kan kujera ya fara rubutu Aishatu tazo ta karbi biron. Gwiwarta a kasa tace don Allah Dr kada kayi haka. Ya dagota a hankali Aish mutuwa ce kawai zata hanani abinda nayi niya. Fadila kije na sakeki saki daya. Huzaifa me kace? Cikin fada da kuka take maganar. Yace ki fice min daga gida Fadila na gaji. Ta cigaba ni zaka saka saboda wannan karuwar? Har dame ta fini? Matar da ta gagara zaman gidan miji. Kaine mijinta na uku fa.
Aishatu dama ta gama kulewa sosai tace Fadila kinsan da me na fiki? Fadila ta jefa mata harara. Aishatu ta rinka tafiya a hankali tana juya jiki. Jikin da yake tada hankalin Huzaifa. Yana ganin ta fara tafiya yace a ransa abin yazo. Bata tsaya ko ina ba sai gabansa ta kashe masa ido. A hankali take magana amma yadda fadila zata ji. Da irin wannan karuwancin na fiki sai ta hura masa iska a fuska, ya lumshe ido har yaso ya manta a gaban Fadila suke ta sake hura masa a kunne. A hankali tace I love you baby...sai ta karasa rage tsazarar dake tsakaninsu ta hanyar hada bakinta da nasa. Wani shock yaji har kafarsa ya biye mata. Ita kanta ta manta a inda take. shima kamar mai rada yace I love you too Aish.
Kiris ya rage zuciyar Fadila ta buga ta dafe kirji tsananin kishi na damunta. Kujera ta dauko zata kwada musu sai suka ji sallamar mal Habu mai gadi. Faduwar kujerar hannun Fadila yasa suka kula da abinda tayi niyya ma. Da kyar Huzaifa ya iya cewa Mal Habu ya akayi. Yace Yallabai ana sallama da kai ne a waje. Ya ce sirikinka ne Mal Sa'id.
RASHIN GODIYA ✂ 40
Yinin ranar har Huzaifa ya dawo ko kallon banza Aishatu bata samu daga Fadila ba. Sai dai ta kasa sakin jikinta da ita. Sai da ta gama abincinta na dare ya dawo lokacin tana wanka. Dakin yasha gyara da turaren wuta mai dadin kamshi. Jikinta ma sai da ta dade tana turara bayan tayi wanka. Ciwonta yayi sauki sosai don babu kuraje ko kaikayi. Discharge ne ya rage shima kuma bashi da yawa kamar da. Shiyasa bata wasa da shan magani ko kadan. Sanin baya gida yasa bata shiga toilet din da kayan da zata chanja ba. Fitowarta tayi kai tsaye da kaskon turaren wuta a hannu. Ai tana ganinsa ta koma da gudu saboda towel ne kadai a jikinta. Ta dan leqo da kai Dr...sai ya harareta tayi saurin gyarawa baby don Allah ga hijab dina can akan abin sallah. Yayi mata murmushi ni na gaji hijab din nauyi kada na fadi garin dauka. Sai ta koma ciki ta rufe kofar. Shiru shiru yaji bata fito ba ya dauki hijab din ya mika mata. Haka ta fito tana sunne sunnen kai ta kwashi kayan shafe shafenta da kayan bacci zata koma toilet. Huzaifa yayi saurin tashi kinga shirya abinki kada kije ki kwaso mutanen bandaki ki rinka dukana cikin dare....tasan tsokanarta yake saboda labarin fahad da ta bashi. Tayi dariya duk mijin da baya jin magana ake zanewa ai. Shi dai Huzaifa sai ya fita ya barta ta shirya.
Yana cin abinci yana kara godewa Allah da Ya hada shi da Aishatu. Komai nata tsaf sabanin yadda ya saba gani a nasa gidan. Yau ba yadda bata yi ba akan ya kwanta a kasa yaki. Tace to ita zata koma kasan nan ma yaki. Suna ta rigima da wasa ta sauke pillow kasa yace indai zaki kwanta a kasa kizo na rama abinda kika yi min. Kafin ya gama magana ta dawo dashi kan gadon tayi kwanciyarta a can gefe. Kusan awa daya da kwanciyarsu amma babu wanda yayi bacci. Juye juye kawai yake tsakanin hannunsa na hagu da dama baccin yaki zuwa. Duk da duhun dakin ya san itama ba baccin take ba shiru kawai tayi ta kasa juyawa ma kada su fuskanci juna. Bargon da ya rufa dashi ya yaye duk a banza yayi tsaki kawai yasa hannu ya janyo Aishatu jikinsa. Ta fara kokarin zillewa yayi mata rada a kunne lets stop pretending ko Aish. This is what we want. Yayi ajiyar zuciya sweetdreams my Aish. Amma kiyi addua kinji ko. Daga haka bai sake magana ba sai kankameta da yayi ta kwanta kan kirjin shi. A haka suka yi bacci......
Daga ranar suka kara shakuwa da juna sosai. Idan ya fita aiki sun rinka waya da text kenan. Sabon jere su Yaya zainab suka yi mata wanda dole yafi na da kyau da tsari saboda tsadar kayan. Ana aikin jeren Fadila ta shigo suka gaisa karshe ma dai da ita aka karasa aikin. Su Saddiqa sunyu mamakinta sosai. Aka gama Aishatu ta koma side dinta. Bayan kwana biyu Anti Sauda tazo da su Islam suka yini a gidan. Sunsha hira sosai don Aishatu da kyar ta bari suka tafi. ita dai Anti Sauda shawar zaman lafiya da rike gaskiya ta bawa Aishatu. Kuma ki dage da yawan godiya ga Allah bisa niimar da Yayi miki sai kiga Ya kara miki. Kuma ki kasance harshenki baya rabo da azkar. Da zasu tafi kayan kwalliya ta hadawa yaran suka tafi cike da murna.
Tsakanin Fadila da Huzaifa ma zaman ya dan daidaita tunda yaga ta dena abubuwan da take masa. Hatta bangarenta ma tana gyara shi sama sama. Main falon gidan kuwa Huzaifa ya kafa dokar duk mai girki ita zata gyara shi. Ana haka mai aikin Fadila ta dawo. Ba karamar murna tayi ba don dan gyaran da take yi ji take kamar ta shekara tana abu daya.
RASHIN GODIYA ✂ 39
Suna shiga gida Aishatu ta fara tattara kwanunkanta da su Aliya suka bata. Huzaifa na ganinta ya kwalawa Fadila kira ta fito a sanyaye ita a dole ta shiryu. Ya sha kunu wa kike jira ya gyara wurin nan? Kizo ki dauke ki wanke mata kayanta. Fadila tace dama tsintsiya zan dauko..Aishatu bari zan karasa. Itama Aishatu tace haba ki bari kawai ta cigaba da tattare kayanta. Sai da ta gama gyara wurin sannan ta koma kitchen ta dumama sauran sauce din. Ragowar wainar da ta ajiye saboda su Aliyun ta hada masa a tray daban ta kai masa. A kwance ta same shi ya rufe idanunsa. A bakin kofar ta tsaya ta kasa shiga dakin. Wannan kunyar tasa da take ji kada ace ta munafurci ce shine tunaninta. Lokaci daya take ajiye ta a gefe sai bukatarta ta biya kuma kunyar ta rufe ta. Anya yau bata zake da yawa ba kuwa? Da wane ido zan sake kallonsa ma. Zancen zuci ne ya fito fili don bata san maganarta ta karshe ta fito ba. Ji tayi yace da wadannan idanun masu rikitawa Huzaifa lissafi mana. Yana maganar yana tahowa gabanta. Tray din hannunta ne ya fara rawa saboda yadda ta rude da irin kallon da yake mata. Ba tare da ya dena kallonta ba yasa hannu ya dauke mata tray din. Gaba daya ta karasa rikicewa ta soma in'inar karfi da yaji. Uhmm dama...dam...dama na..nace. Ya dan kalleta kika ce me? Uhmm nace kayi..ko zakayi hakuri akan dazu. Huzaifa ya jawo hannunta ya zaunar da ita akan kujerar table din da yake aiki. Ya zauna a gabanta amma ya juya mata baya. Duk a takure take jin kanta sai ya kwantar da kansa a cinyarta. You were saying nayi hakuri. Hakuri akan me? Ta yaya ma zata iya magana a yadda suke dinnan. Tayi shiru kamar ruwa ya shanyeta. Daga kwancen yace na dauka ma zaki bani hakuri ne for kissing me. A ranta tace ashe yaji haushi...da saurinta ta daga kai sama eh shine dama nace kayi hakuri ai. Huzaifa yana lura da reaction din Aish dinsa. Komai nata yana bashi shaawa yace kada ki damu fa zan rama ne kawai. Tace zaka rama kuma? Eh yanzu if you dont mind. Bata san lokacin da ta ture masa kai ta rufe kanta a toilet ba. Dariyarsa ta rinka ji daga ciki yace ki fito ki bani abinci kafin na suma.
Sai da yayi laasar ya tafi gidan Umma. Ta matsa masa da tambaya auta me ya faru ne, jiya ka dauko yaran nan daga gidan Shukriya yau ka turo su kafar Aliyu ko takalmi babu. A takaice ya sanar da ita abinda fadila tayi amma bai sanar da zancen saki ba. Umma duk hakurinta tayi ta fada. Tace ni sai inje har gidan naka wallahi. Haka kawai daga yin aure wannan da iyayenta sunji ai rai zai matukar baci. Kuma shine ka rufe min. Bansan an fasa mata kayan daki ba sai yau. Yaya kubra tace Umma mun kusa gama komai don gobe zamu karbo kayan ayi jere. Fadan sai ya dawo kan kubra haka kika iya ke kuma gyara gidan wani. Tun wuri ki daidaita da mijinki ki koma. Kubra tayiwa Huzaifa alama da ido.. mu bar wurin nan tun wuri don ran umma ya baci.
Wasila bata sha wuyar samun number din Fahad ba don akwai ta da shige shige. Yadda ta dau zafi ko mijinta ne ya kara aure sai haka. Ana turo number din ta kira shi. A lokacin sun gama fada da yahanasu duk akan rashin haihuwa. Kowa yana ganin laifin dan uwansa. Wasila ta kira bai gane ko wace ba tace bazai gane ba tana son su hadu ne akan maganar Aishatu ne. Nan da nan ta samu attention dinsa yace zai zo kano ranar asabar suka tsayar da wurin haduwarsu. Da murna ta kira Fadila ta sanar da ita tayi mata godiya sosai. Tana ajiye wayar tayi dariya sai na nuna miki Fadila ba saar yinki bace.
RASHIN GODIYA ✂ 40
Yinin ranar har Huzaifa ya dawo ko kallon banza Aishatu bata samu daga Fadila ba. Sai dai ta kasa sakin jikinta da ita. Sai da ta gama abincinta na dare ya dawo lokacin tana wanka. Dakin yasha gyara da turaren wuta mai dadin kamshi. Jikinta ma sai da ta dade tana turara bayan tayi wanka. Ciwonta yayi sauki sosai don babu kuraje ko kaikayi. Discharge ne ya rage shima kuma bashi da yawa kamar da. Shiyasa bata wasa da shan magani ko kadan. Sanin baya gida yasa bata shiga toilet din da kayan da zata chanja ba. Fitowarta tayi kai tsaye da kaskon turaren wuta a hannu. Ai tana ganinsa ta koma da gudu saboda towel ne kadai a jikinta. Ta dan leqo da kai Dr...sai ya harareta tayi saurin gyarawa baby don Allah ga hijab dina can akan abin sallah. Yayi mata murmushi ni na gaji hijab din nauyi kada na fadi garin dauka. Sai ta koma ciki ta rufe kofar. Shiru shiru yaji bata fito ba ya dauki hijab din ya mika mata. Haka ta fito tana sunne sunnen kai ta kwashi kayan shafe shafenta da kayan bacci zata koma toilet. Huzaifa yayi saurin tashi kinga shirya abinki kada kije ki kwaso mutanen bandaki ki rinka dukana cikin dare....tasan tsokanarta yake saboda labarin fahad da ta bashi. Tayi dariya duk mijin da baya jin magana ake zanewa ai. Shi dai Huzaifa sai ya fita ya barta ta shirya.
Yana cin abinci yana kara godewa Allah da Ya hada shi da Aishatu. Komai nata tsaf sabanin yadda ya saba gani a nasa gidan. Yau ba yadda bata yi ba akan ya kwanta a kasa yaki. Tace to ita zata koma kasan nan ma yaki. Suna ta rigima da wasa ta sauke pillow kasa yace indai zaki kwanta a kasa kizo na rama abinda kika yi min. Kafin ya gama magana ta dawo dashi kan gadon tayi kwanciyarta a can gefe. Kusan awa daya da kwanciyarsu amma babu wanda yayi bacci. Juye juye kawai yake tsakanin hannunsa na hagu da dama baccin yaki zuwa. Duk da duhun dakin ya san itama ba baccin take ba shiru kawai tayi ta kasa juyawa ma kada su fuskanci juna. Bargon da ya rufa dashi ya yaye duk a banza yayi tsaki kawai yasa hannu ya janyo Aishatu jikinsa. Ta fara kokarin zillewa yayi mata rada a kunne lets stop pretending ko Aish. This is what we want. Yayi ajiyar zuciya sweetdreams my Aish. Amma kiyi addua kinji ko. Daga haka bai sake magana ba sai kankameta da yayi ta kwanta kan kirjin shi. A haka suka yi bacci......
Daga ranar suka kara shakuwa da juna sosai. Idan ya fita aiki sun rinka waya da text kenan. Sabon jere su Yaya zainab suka yi mata wanda dole yafi na da kyau da tsari saboda tsadar kayan. Ana aikin jeren Fadila ta shigo suka gaisa karshe ma dai da ita aka karasa aikin. Su Saddiqa sunyu mamakinta sosai. Aka gama Aishatu ta koma side dinta. Bayan kwana biyu Anti Sauda tazo da su Islam suka yini a gidan. Sunsha hira sosai don Aishatu da kyar ta bari suka tafi. ita dai Anti Sauda shawar zaman lafiya da rike gaskiya ta bawa Aishatu. Kuma ki dage da yawan godiya ga Allah bisa niimar da Yayi miki sai kiga Ya kara miki. Kuma ki kasance harshenki baya rabo da azkar. Da zasu tafi kayan kwalliya ta hadawa yaran suka tafi cike da murna.
Tsakanin Fadila da Huzaifa ma zaman ya dan daidaita tunda yaga ta dena abubuwan da take masa. Hatta bangarenta ma tana gyara shi sama sama. Main falon gidan kuwa Huzaifa ya kafa dokar duk mai girki ita zata gyara shi. Ana haka mai aikin Fadila ta dawo. Ba karamar murna tayi ba don dan gyaran da take yi ji take kamar ta shekara tana abu daya.
RASHIN GODIYA ✂ 41
Aliya da Aliyu sun dawo gida Huzaifa ya kaisu dakin Aishatu da kansa. Aliya sai rabe rabe take a jikin bango don tafi Aliyu wayo. Huzaifa yace musu wannan itama mamanku ce kunji ko. Daga yau nan ne gidanta kada na sake jin kun kirata da wani suna mara dadi sai na zane ku. Aishatu tayi murmushi ta mika musu hannu ku zo mu gaisa. A dan tsorace suka karasa gabanta suka mika mata hannu. Ta basu sweets harda ice cream.. daga nan suka saki jiki har da cin abinci. Tana ta musu wasa Aliya tace mummy tace mu rinka kiranki Maama. Abin yayi wa Aishatu da Huzaifa dadi suna cin abincin Aliyu yace maama abincinki yafi na mummy dadi, zaki dawo dani nan dakin? Huzaifa yace kana son dawowa ko. Yace eh Abba ita Aliya sai ta zama yar mummy ni kuma ga maama na. Ya koma cinyarta ya zauna. Huzaifa ya rada mata maaman Aliyu yaushe zaki masa kani ne? Kai ta sunkuyar tace ba rana bare wata. Yayi dariya kin kusa gama shan magani dai. Saboda haka ku fara saka rana.
Fadila ke ta kai kawo a daki tun rana da taji labarin tafiyar Aishatu da Huzaifa Umra ta nuna bacin ranta a fili. Ba Umrar bace ta dameta kamar tafiyar da zasuyi tare. Duk inda Huzaifa zaije tare suke zuwa ko bayan ta fara haihuwa baya yarda ya tafi ya barsu a gida. Yau ga tafiyar tana ji tana gani zaiyi da Aishatu. Hawaye mai zafi ya sauko mata ba karamin daurewa take ba da tana gani Aishatu ke shigar mata dakin miji.
Huzaifa na daki shiru har shabiyu saura na dare Fadila bata shigo ba. Ya kira wayarta yaji shiru bata dauka ba har sau uku sai ya tafi dakin nata. Bata cikin falo ya duba dakinta har da nasu Aliya bata nan. Hankalinsa ya dan tashi ya tafi dakin Aishatu. Da sallama ya shiga ya ganta tsakiyar yara suna bacci. Dadi da son Aishatu ya karu a zuciyarsa. Cikin kankanin lokaci ta siye zukatan yaran. Rufe musu kofa yayi ya koma.
A tsakar falo ya ganta ta bude baki ganin daga ina ya fito ta fara halin. Kuka take yanzu Huzaifa ranar girkina ma sai ka shiga dakin Aishatu? Ya ce Fadila kenan, dakinki na duba ban ganki ba. Suma yaran basa nan shiyasa nazo dubawa. Tayi gaba kawai ta shiga dakinsa yabi bayanta wai meye yake damunki ne Fadila. Dole kace meye yake damuna mana. Don cin amana sai ka biya muku zuwa Umra ku kadai. Idan adalcin zaka yi ai dani zaka fara zuwa sannan wani lokacin kaje da ita. Huzaifa yayi ajiyar zuciya Fadila rigima to ai bani na biya ba. Alh Sabiu ne ya biya mijin Yaya Zainab. Kuma idan baki manta ba munje hajji da umra dake. Wace kasa na taba zuwa batare dake ba ma. Harararsa tayi kafin tace karyar banza yanzu ka fara aure da bai taba biya maka ba sai yanzu. Kunje kun gama kulla munafurcinku shine zaka fada min son ranka. To dole kasan yadda zaka yi dani wallahi don bazan zauna gadi ba. Zancenta ya fara kular dashi ya dai daure yaki magana. Wuri ya samu ya kwanta ta fita tare da bugu kofa. Bata jima ba ta dawo da sauri Huzaifa ina 'ya'yana? Na duba basa dakinsu. Yana daga kwance yace suna dakin Aishatu. Fita tayi da gudu wallahi bazasu kwana a can ba. Haka kawai kai din na hakura kuma yaran ma namu ne yanzu mu biyu? ta haifi nata mana tunda ta ita zuwa dakin miji. Huzaifa yace na rantse miki idan kika fita daga dakin nan sai ranki ya baci. Sai ki rinka abu kamar wata jahila. Ki fitan na gani. Dole ta hakura ta kwanta tana bambami. Can yaji ta dan matso kusa dashi Abban Aliya kayi bacci ne? Uhmm Abban Aliya kayi hakuri da abinda nayi. Ji yayi ta rike masa hannu yayi dan murmushi ya sake rintse ido. Shiru yayi mata yar rainin hankali kawai...ta iya shafawa idonta toka sai tata ta kawota ta shiga kwantar da kai.
Kafin ya dawo daga massalaci da asuba Fadila ta bude wata drawer zata dauki dan kudi yadda Wasila ta bata shawara. Wai idan bata dauka ba Aishatu zata kwashe. Tana cikin nema ne tayi karo da kwalayen magungunan Aishatu. Ta dauka tana jujjuya su a hankali ta rasa gane ko na meye. A iya saninta Huzaifa baya shan wani magani wadannan kuma an sha da yawa a ciki. Tana ta juyayin abin a ranta sai ta bude takardar cikin daya tana karantawa taga ance kada mai ciki tasha. Sannan an ce idan an dena ganin dischage sai mace ta dena sha. Hannunta har yana rawa ta kwafe sunan maganin a wayarta don ta tabbatar na Aishatu ne tunda mace ake ta ambata.
Haka Huzaifa ya dawo ya sameta akan gado tana browsing. Bakinta bude ciki da mamaki da fargaba. Yanzu Aishatu na fama da mugun ciwo irin wannan shine ya aurota. Kuma dole yasan da ciwon tunda haka kawai Aishatu bazata bar magani a dakinsa ba. Huzaifa na dawowa tayi saurin jifa da wayar ta mike da sauri. Yace ina zaki tace alwala. Yanzu bakiyi sallah ba kika zauna duba waya da asuba. Allah Ya shiryeki. Tace amin amin dai, a ranta kuwa murna tayi don wannan sirrin kamar ta baza shi ta gama. Kai anya kuwa Huzaifa zai kusanci Aishatu da ciwo........no wonder ta taba shigowa taga pillow da abin rufa a kasa. Kai wannan abu yayi dadi wasila zata sha labari.
RASHIN GODIYA ✂ 42
Wasila a kashingide kan gadon Fadila tace ai ko kadan kada ki tona mata asiri ta hanyar baza zancen nan. Komai a hankali ake binsa. Ni yanzu kirawo min ita mu gaisa kiga yadda zanyi sai ki dau course. Koda yake gara naje da kaina sai taga kamar an bata mahimmanci. Wasila tayi sallama a kofar falon Aishatu Aliyu ya amsa. Fadila tace kinga yadda ta raba ni yarana ko. Wasila tace su Aliyu manya har ka iya amsa sallama haka kamar babban mutum. Ya durkusa Anti ina wuni, maama na ce ta koya min. Su ka sake hada ido lallai da sake. Aisha ce ta fito daga daki sanye da dogon skirt baki sai wata farar sleeveless riga. Gashinta ta daushe shi da ribbon daga gefe sai kamshi take, hannunta duk kumfa. Tace bismillah ku zauna mana baki ne damu. Daga ciki suka ji muryar Aliya tana cewa Maama in goge jikina kafin kizo. Aishatu tace eh ga towel nan ki dauka. Fadila ta dan wayance wanka tace kiyi mata ko? Tsifa na turata wurin Laure fa. Aishatu tace lauren ce ta yanke a hannu shine na karasa mata tsifar aka wanke kan. Nan da nan Fadila ta hade rai har sai da wasila ta dan take mata yatsa alamun ta saki fuska. Aishatu ta mayar da hankalinta ga wasila sannu da zuwa ina wuni. Wasila ciki da faraa tace lafiya kalau amarya ya gida da kiriniyar yara? Ai basu da kiriniya Aishatu ta amsa tana shafa kan Aliyu yaran albarka ne. Wasila tace sannu Aishatu kin sha aiki ga jiki kina fama dashi. Cak Aishatu ta tsaya a jikin fridge da take shirin daukowa wasila lemo. A sanyaye ta waigo jiki kuma? Wasila tace kinsan masu lalura irin taku suna bukatar hutu sosai. Kuma dai a rinka hankali kada wasu su dauka. Cup din hannun Aishatu a take ya fado bakinta har yana rawa tace wane ciwo? Sai Fadila tace rabu da ita kinji kanwata wai ta dauka ciki gareki kada nima na samu. Na fada mata ai ke da ciki ba yanzu ba sai nan gaba. Aishatu zancensu yana kara kidimata ta danyi yake ta zauna. Fadila tayi murmushi ina nufin sai kin gama cin amarci. Aure wata biyu ai baki fara komai ba a amarcinki. daga nan suka tashi suka fita har tana jin dariyarsu. Gaba daya sai ta rasa nutsuwa. Ta kasa gane hasashe suke na cikin ko kuwa dai zancen lalurarta ne ya fito fili. Haka ta gaji da tunani ta hakura.
A daki wasila tace to kawata kinga yadda ake yi dai. Daga mata hankali zakiyi ta yi daga baya sai ki fasa kwan kowa yaji. Haka kuwa akayi Fadila sai tayi ta shagube idan taga Aishatu. Abin ya rinka damunta sosai, dan sakin jikin da take tare da Huzaifa ya fara ja baya. Ana haka wata jumaa Huzaifa ya sanar dasu zasu je Rano gaba dayansu. Fadila har tace bazata ba sai ta tuno maganar wasila tace zata bisu. Ranar asabar kafin karfe tara sun kama hanya. A mota suna ta hira Aishatu da Fadila kamar wasu yan uwa. Hirar ma Fadila ke kawo ta.
Gidan kowa murna anga iyalin Huzaifa. Fadila dai ta kasa sakin jiki sosai dasu. Ita kuwa Aishatu da yaran kamar wadanda suka saba. A falon wan baban Huzaifa duk yawancin matan yan uwa da 'ya'yansu suka taru ana ta tsokanar juna. Wata abokiyar wasan Huzaifa ta dubi Aishatu...anti amarya ina fata mun kusa zuwa suna ko. Murmushi tayi cike da kunya don akwai manya a wurin Huzaifa yace kin tanadi shanun suna ko, baki ji an hana yanka rago ba sai shanu. Duk aka yi dariya Fadila tace rabu dasu kanwata ke ina kika ga lafiyar yin cikin yanzu. Duk kuyi ku gama sai nan gaba. Aishatu da Huzaifa suka yi saurin kallon Fadila ita kuwa ta basar. Matan wurin sai suka mayar da maganar wasa. Har suka dawo gida Aishatu bata da nutsuwa.
Ba jimawa da faruwar haka kuma Nurain yazo gidan kanin Aishatu na biyu. Tayi murnar ganinsa sosai, da yake yana da saukin kai har kasa ya gaishe da Fadila. Da taimakon Habu maigadi ya kinkinmo kwandon tumatir masu kyau ya shigo dashi main falo. yace baba ne ya dawo daga getso jiya gonarsa tayi albarka. Aishatu ta kira babanta tayi masa godiya. Da ta gama tana durkushe da ledoji a hannunta tana rabon tumatir din har da yan uwan Huzaifa saboda manya ne sosai masu kyau. Tace Baba yasan ina son tumatir shiyasa yayi min wannan babbar kyautar. Fadila ta yatsina fuska sai ta ce ai da yake ance ana son irinku su rinka shan tumatir sosai yana da sinadarin kariya daga kamuwa da cancer. Aishatu da Nurain suka kalleta cikin rashin fahimta. Aishatu tace ban fahimci maganarki ba. Fadila ta dafa mata kafada ba wani abu nake nufi ba. Kinsan shi tumatir yana da sirruka masu tarin yawa. Zai miki amfani sosai lokacin da kika warke. Ta tashi ta shige daki. Nurain yace anya Yaya matar nan kalau take kuwa. Ni duk zancen nata na kasa ganewa. Aishatu bata ma jinsa sosai hankalinta ya tafi ga tunanin da take. Wai yan kwanakin nan meye yake damun Fadila take mata irin maganganun nan. Banda iyayenta da Anti Sauda, Huzaifa ne kadai yasan lalurarta. Gabanta ya fadi....Allah Yasa ba fadawa Fadila yayi ba. Sai tayi saurin kwabar kanta. Dr Rano is a good man bazai taba tozarta rayuwarki ba.
RASHIN GODIYA ✂ 43
Aishatu ta tambayi Huzaifa zuwa gidan Anti Sauda ta yini ya amince. Tace nagode Allah Ya saka da alkairi. Cikin mamaki ya kalleta don na baki izinin fita kawai kike min wannan godiyar? Ta na bude masa maballan rigarsa tace ai ya wuce kawai. Ya rike hannuwanta biyu yanzu idan nace bazaki ba zaki hanu? Sosai ma kuwa. Haram ne mace ta fita ba tare da izinin mijinta ba. Huzaifa ya rungume ta sosai na sani Aish amma banyi tsammanin akwai macen da fitarta ta dogara da izinin mijinta ba. Allah na gode maKa da Ka bani Aishatu a matsayin mata. A hankali itama tace Alhamdulillah. Yace kinsan kin kusa dena shan magani ko. Idan kika shanye dose din da na siyo jiya zamuje ayi miki pap smear. Yana dakina idan kin shigo anjima zan baki. Ya daga gira... Hopefully zuwa time din kin gama warkewa sai ki zama amaryar gaske. Murmushi suka yiwa juna Ya saita bakinsa a kunnenta did I tell you how much I love you? Tana dariya tace noooo. Wani irin kallo yake mata tana ja da baya yace zo na fada miki....suka ji an bude kofar dakin. Fadila ta yi saurin ja da baya kuyi hakuri wallahi ban san kuna ciki ba. Huzaifa ya daka mata tsawa wane irin iskanci ne wannan Fadila. Ta dan nuna alamun rikicewa to ai bansan ka dawo ba ne. Kuma naga nan dakinta ne. Yace shi dakin nata bazaki iya yin sallama ba. Fadila tana bashi hakuri Aishatu na bashi. Yayi tsaki ya cewa Aishatu idan kun gama ki sameni a daki. Kuma kiyi sauri. Har ya rufo kofar Aishatu tana murmushi....tana son mijinta fiye da tunaninta.
Ta dubi Fadila da ta tsaya jikin kofa ki zauna mana ko mu koma falo ne. Fadila ta sunkuyar da kai kasa sai ga hawaye yana zuba. Aishatu na gani ta dawo kusa da ita. Subhanallah me ya faru? Fadila ta shaki hanci nasan Huzaifa ba karamin fushi yake dani ba akan abubuwan da nayi masa a baya shiyasa baya min uzuri yanzu. Haba ki dena kuka tunda mune a karkashinsa hakuri zaki sake bashi. Fadila ta goge ido to nagode sosai Aishatu Allah Ya barmu tare. Dama jiya ne da ya dawo lokacin kin kwanta ya bani wadannan maganin na kawo miki sai bacci ya dauke ni. Zuciyar Aishatu sai harbawa take da sauri da sauri don bakincikin da ke cin ranta. Fadila tana kallon yanayin Aishatu tace ga maganin ki taimake ni kisha yanzu kuma don Allah ki rufa min asiri kice tun a jiya na baki. Kinsan lalurar shan magani kullum babu dadi. Amma yace daga wannan kin gama ai. Shiru Aishatu bakin magana. Fadila tayi alamun tausayi da fuskarta baki ga yadda ya damu da lalurar nan taki ba. Nima duk na damu bayan ya fada min. Ta tashi tsaye bari naje daki...af! Ai kuwa ina da kawa mai gyaran jiki idan kin warke sai muje. Tana fita Aishatu ta fashe da kuka ita kuwa Fadila ta kwashe da dariya. Kadan kika soma gani yarinya.
Huzaifa har ya gaji da jiran Aishatu yace ko dai Fadila ta ja ta da zance ko kuma bacci ya dauke ta. Yayi ta kiran wayarta a kashe. Yaje dakin kuma tana sallah. Haka ya zauna yana jiran ta idar har kusan minti talatin taki idarwa. Ta sallame raka'a ta takwas a kirgensa yayi saurin tsayawa gabanta. Muryarta har rawa take ta daga hannuwa sama zata yi kabbara ya rike su. Haba Aish tun dazu nake jiranki. Ki duba time har daya saura baki bani abinci ba. Kukan da take rikewa ya kwace mata. Ya rungume ta yana rarrashi me aka yi miki. Fadila ce ko? Cikin kuka tace bani da lafiya ne. Sai tauyinta ya kara kamashi kuma shine zaki yi shiru tun dazu. Ita dai kukanta take yi. Sai da tayi shiru yace Aish yaushe kika koyi karya ne. Ki fada min gaskiya me aka yi miki. Tace tausayin kaina nake ji. Huzaifa ya riketa sosai Aish this is so unlike you. Ki fada min gaskiya. Sai ya fita kawai yana kiran Fadila. Aishatu ta na riko shi yaki sauraronta. Duk da dare ne Fadila ta jima tana kasa kunne taji lokacin tashin bomb.
RASHIN GODIYA ✂ 44
Kafin ya shiga dakinta Fadila ta shige cikin bargo tana baccin karya. Da karfi ya buga kofar ya bude. Ta tashi tana murza ido ita ga mai bacci me ya faru Abban Aliya? Yace ki taso ki biyoni daki yanzun nan sannan ya koma. Da bin bango ta shiga a dan tsorace ta ga Aishatu ta takure a kasa tana kuka. Tayi kwafa a ranta lallai tarkonta yayi kamu. Huzaifa sai kai kawo yake a dakin yace kinga samu wuri ki zauna zaki wani tsayawa mutane a ka. Sai da ta zauna shima ya zauna akan kujera Fadila ki fada min gaskiya me ya hadaki da Aishatu. Ai itama sai kukan Aishatu ba dai kin masa zancen maganin ba, ke da na rokeki ki rufa min asiri kada yasan yau na baki. Tuni Aishatu ta karasa yarda da cewa Huzaifa ne ya fadawa Fadila tunda gashi bata ji tsoron maimaita zancen a gabansa ba. Dan zaman da tayi daga gefensa a kasa ta tashi ta canja wuri gaba daya. Shi kuwa ya kasa gane inda su biyun suka dosa yace Fadila wane maganin. Ta kalli Aishatu ina ledar? Aishatu ta nuna mata tana kan bedside drawer. Fadila ta dauko ta durkusa a gabanshi ta mika masa. Yana gani yayi saurin tashi Fadila a ina kika dauko ledar nan? Dan kukanta ta cigaba kayi hakuri Abban Aliya nasan tun daren jiya kace na bata shine na manta sai dazu da na shiga dakinta. Dama ni nace ta sha na yau yadda bazaka gane ba. Ta kalli Aishatu nasan ba fada masa kika yi ba, ganewa yayi na kwana daya ne ko. Huzaifa yace ke ni ban fahimce ki ba. Aish yi min bayanin abinda ya faru. Fadila tace ni dai na fuskanci kamar baki so ya sanar dani ba ko? Shima ai ba son ransa bane. Shimfida na gani a kasa na tambayeshi shine yayi min bayanin infection dinki. Yace saboda karnin discharge ma shiyasa ba kya rabo da turaren wuta da air freshner. Nasan ba dadi miji ya nuna kyamar matarsa shiyasa na bashi shawarar ya daure ya kwana tare dake. Ta dan masa kallon tuhuma dont tell me baka dauki shawara ba.
A lokaci Huzaifa ya tabbatar Fadila makira ce ajin farko. Yana kallo ta tashi ta rungume Aishatu kiyi hakuri kinji kanwata. Nasan da ciwo amma kamar yau ne komai zai daidaita tsakaninki da mijinki. Duk mace ai tana son ganin danta bayan aure. Burina ki warke yadda zaki iya samun ciki ki cika gidan nan da yara. Aishatu fuskar Huzaifa take kallo yadda ya saduda cewa ta gama dashi. Har gumi yake saboda yadda hankalinsa ya tashi. Aishatu duk fushinta a take ya sauka. Idan Huzaifa yana son tona mata asiri ko kyamarta bazai aureta ba. Kuma tun yaushe suka fara kwana wuri daya ma. Tuntuni baiji kyamar ba sai yanzu? Ta yaba da kyaun halin Huzaifa da na yan gidansu. Hakika kullin Fadila ne wanda ta jefa mata shakku a zuciyarta game da mijinta.
Tana tunaninta taji yace Fadila abin har ya kai ga ki yi min sharri haka. Aish wallahi karya take min. Yadda yayi maganar ya kara bata tausayi sosai. Hawaye ya zubo mata ta share da bayan hannunta, gabanta yazo ya tsaya a sanyaye zai sake magana tasa hannu ta rufe masa baki. Cike da tsantsar so tace Babyna did I tell you how much I love you? Yayi murmushi mai cike da takaici saboda Fadila ta masa wulakanci sosai. Yace No. Ta rungume shi ta baya to muje muyi wanka sai na fada maka. Huzaifa da Fadila gaba dayansu sunyi matukar mamakin abinda Aishatu tayi. Tamkar Fadila bata dakin ta dawo gabansa ta tsaya tana masa shagwaba ni ka zuge min zip din na kasa. Bai iya cewa komai ba ya zuge zip din doguwar rigar atamfar dake jikinta. Ta ja hannunsa suka shige toilet suka bar Fadila a tsaya baki bude.
Bata san lokacin da tace kan uba anya yarinyar nan mutum ce kuwa? Ta fita ta bugu musu kofa da karfi. Bata kula da lokaci ba ta kira wasila tana kuka, dama itama jiran feedback take bata kwanta ba..tsam ta tashi daga daki ta koma wani dakin ta amsa wayar. Ni na rasa yadda zanyi da yarinyar nan. Ta bata labarin duk yadda suka yi Wasila tace kwantar da hankakinki next week Fahad zai zo. Su Aishatu kuwa suna jin ta fita suka fito. Huzaifa zaiyi magana ta ce kada kace komai. I trust you. Kissing dinta yayi tare da godiya ga Allah.
RASHIN GODIYA ✂ 46
Fadila ta aikawa Fahad text tana son su hadu ranar litinin da safe a kofar makarantar su Aliya. kamar yadda ta sani wannan litinin Huzaifa yana da call wato aikin kwana a asibiti. Da wuri ta tashi ta shirya Aliya harda yi mata girki ita da duk ranar girkinta sai dai ta bata biscuit da lemo.
Ta shiga dakin Aishatu ga yarki zata tafi school tace bata ga Maama ba. Aishatu ta gyarawa Aliyu kwanciya ta dauko homework din Aliya ta saka mata a jaka. Sai kun dawo Aliya Allah Ya bada saa. Fadila tace amin maaman yara. Lokacin sati uku kenan da faruwar rikicin da ya jawowa Fadila saki na biyu. Tun lokacin take neman shiri da Aishatu. Tana dai kokari su zauna lafiyan amma ta gagara sake mata. Mutum kamar Fadila ba haka kawai ake sakewa dashi ba. Kamar maciji take mai jiran sara da ya sami dama.
Aliya na fita daga motar ta fara neman numbar Fahad zata kira shi. Seat din gaba taji an bude sai ta ga mutum ya zauna a gefenta. Bude baki tayi zata yi ihu yace shut up and drive. Kamar tasan muryar amma bata tantance ba jiki na bari tace tare muke da mijina. Yayi yar dariya irin wadda ta taba ji a waya. Sai yanzu ta gane shi...Fahad? Yace eh. Bata sake magana ba ta rinka bin hanyar da ya nuna mata sai da suka je gate din central hotel yace ta shiga. Jikinta ya danyi sanyi kana hauka ne? Hotel ne fa sai wani ya gan mu. Fahad ya bata rai sosai idan kin fasa ne shikenan. Aikin banza kai, ki neme ni sannan ki nuna tsoro. Ai na zata mijin naki dan gwal ne zaki iya komai dominsa. A harzuke tace kada ka gaya min magana mana. Mijina yafi karfin ka zage shi. Fahad yace eyye kaga mai miji...yana magana yana tafa hannu. Fadila a tsorace take da shi tace muje amma kayi sauri kada ya koma gida bana nan. Har dakin da yayi masauki ya kaita duk da ta san hakan bai dace ba amma tana ji a ranta babu abinda bazata yi ba akan raba Huzaifa da Aishatu. Mijinta ne ita kadai. Sun hada plan din duk yadda zasu bullowa lamarin yace to sai naji daga gareki. Fadila tace shikenan.
Tana fita ya koma kan gadonsa ya zauna. Yahanasu ya kira a waya tace ya aikin kayi breakfast kuwa? Ya gyara kwanciya banyi ba na dan soma abinda ya kawo ni ne. Tace to Allah Ya dubi niyya my dear. Yace amin Yaha....yana jin ihunta tana cewa Allah bana so, wane irin Yaha kamar a kauye. To ba yar kauyen bace ya amsa yana dariya.
Huzaifa daga wurin aiki gidan Umma ya wuce. Yaya kubra tace to meye kuma kayi mana sammako yau kamar wani gwauro? Yayi murmushi yau a waliyinki nazo. Ta jefa mishi dankali Umma kinga autanki zai min rashin kunya ko? Umma tace rashin kunya ko gaskiya kaga shigo daga ciki autan umma muyi magana. Yaya kubra ta tsaya daga jikin kofa tana jin bayanin Huzaifa akan yadda suka yi da mijinta. Yayi alqawarin raba musu gida da mahaifiyarsa tunda ya tabbatar zaman tare ne yasa Hajiyar ta koyi sa wa iyalinsa ido. Gobe zasu je Rano tare ya biya sadaki. Yaya kubra ta ce duk yaushe aka gama wannan shawarar ina cikin gidan nan. Nifa ba cewa nayi ya rabu da Haj ba. Kawai abinda take yi ne bana so. Umma tace ya rage naku ni dai wannan zaman naki ya isheni a koma ayi bautar aure. Daga nan Huzaifa ya wuce gida. Sai da ya shiga dakin Aish suka gaisa sannan ya tafi dakinsa. Fadila yanzu kwantar da kai take sosai shi dai yana zaune da ita ne kawai saboda Allah amma duk ta fice masa a rai.
Aishatu kuwa gyaran jiki suke zuwa da Anti Sauda sauki ya samu. Anti Sauda har tsokanarta take wai tana sheki saboda zata fara amarci. Tace kai antiña ni kunya nake ji. Ta kai mata duka a baya kyaji da gulmarki bayan nasan kwana bakwai dinnan sunyi miki nisa. Aishatu ta sake dariya. Wayarta ce tayi ringing gashi duk jikinta an shafe shi da wani abu an rufeta da bargo ga garwashi da turaren wuta mai matukar kamshi. Ta kalli wayar da kalar tausayi alamun anti sauda ta saka mata. Anti Sauda tace kaji min yarinya fa. Tun dazu yake bugowa ku gaisa kamar na sato ki. Aishatu tace na karshe ne Anti daga wannan zan fada masa yayi hakuri sai an goge min yadda zan dauka da kaina. Anti Sauda da mai gyaran jikin suna ta dariya. Daga lokacin da suka fara Huzaifa ya kira sau hudu duk Antin ke saka mata wayar a kunne. Wannan karon tana dora mata tace baby kaji Anti Sauda ko.....muryarta da yaji tayi masa dadi. Yaushe rabon da yaji wannan muryar mai taba masa zuciya. Shiru taji tace baby ko baka ji na ne. Yace ina jinki Aisha....Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun. Da karfi tace FAHAD? Anti Sauda ta yar da wayar ba shiri.
RASHIN GODIYA ✂ 45
Kasa bacci Huzaifa yayi a daren saboda bacin rai. Hakika ba don Allah Ya taimake shi Aishatu mace ce mai fahimta da yin uzuri ba bai san da yadda zai fitar da kansa ba. Zama da Fadila bala'i ne, sai yanzu ma ya kara tabbatar da hakan. In Allah Ya yarda sai ya toshe duk wata kofa da zata sake kawo musu matsala.
Yana dawowa daga sallar asuba ya tafi dakinta. kwance tace hankali kwance tana bacci. Lallai bata da kunya duk abinda tayi har ta iya bacci haka. Takardar da ya rubuto tun kafin ya shigo gida ya ajiye a karkashin wayarta ya fita. sai yanzu yaji wani dadi kamar an sauke masa katon dutse. Yaransa yasan ko bashi da rai Aishatu zata rike su amana. Ya koma daki suka koma bacci bayan sunyi karatu don bacci bai ishesu ba a gidan. Wurin karfe takwas suka ji wani gigitaccen kuka. Aishatu ta farka a tsorace baby waye wannan? Kaji wani irin ihu kuwa. shi kuwa ko yunkurin tashi baiyi ba tunda yasan mai kukan da dalilin kukan. Aishatu ta dan jijjiga shi don Allah ka tashi ka duba. Yayi murmushi na duba wato idan dodo ne ya cinyeni ni kadai ko? To anki wayon. Tace to ni bari naje ya cinyeni tunda haka kake so. Ya janyo hannunta dawo ki kwanta kinji Aish. Fadila ce take yi. Ai tuni ta mike shine kake kwance bayan kasan mai yi. Idan wani abin ne ya faru a gidan fa. Huzaifa ya juya baya ya gyara kwanciya sai ya cinyeta ita kadai. Ganin da gaske bazai fita ba sai ta tashi ta tafi dakin fadilan. Kuka take sosai tana fizge fizge. Aishatu dai sai taki karasawa ciki don tsoro ta bata. Fadila me ya sameki? Da katon zaginta ta juyo zata fara sai ta tuna yadda suka yi da uwarta wasila. Ta rarrafa ta rike kafar Aishatu ki min rai Aishatu kingani. Abban Aliya ya sakeni, na biyu kenan. Duk abinda nayi jiya sharri ne da karya. Ni kadai nayi bincike na batare da ya sani ba. Daga yau na dena na hakura na tabbatar aurenku babu mai iya raba shi. Wannan masifaffen kishi ta fada tana dafe kirji ki tayani addua Allah Ya yaye min. Dama tsoro nake kada ki rabani da mijina to gashi da kaina nake sawa ya nisance ni saboda halaye na. Kayya na cuci kaina na biyewa kishin banza. Tausayi sosai ta bawa Aishatu tace nawa yayi miki. Fadila a ranta tace ji kamar ba ita ta zuga shi ba. Daya ne ta fada tana ta matsar kwalla. Ki rufa min asiri yadda Allah Ya rufa miki. Tare suka juya zasu dakinsa suka ganshi a tsaye. Yace Aish zo ki wuce daki. Kin zauna tana fada miki karya da gaskiya kina ji. Zuwa yanzu ya kamata kisan halin Fadila. Tafiyarta ita ce alkhairi garemu. Fadila ta fara bashi hakuri kawai sai ta fadi kasa. Huzaifa yayi dariya yana kallonta. Yace kin gani ko Aish, idan bata yi abin kallo ba bata jindadi. Idan kin farfado ki kira mutanen gidanku suzo daukarki don wallahi bazaki min idda a nan ba. Zan baki ci da sha duk inda zaki. Aishatu ta sake kallon Fadila wadda taki motsi duk da yadda kanta ya soma kaikayi kamar mai kwarkwata. Tace babyna kayi mata afuwa for the last time. Nasan dacin saki da rayuwar da ke biyo bayansa ga wanda ya zalumci dan uwansa. Ta dan shafa mata ruwa a fuska sai gashi ta farfado huzaifa yace ai na zata kin tafi kenan. Fadila cikin kuka tace ku taimake ni ko albarkacin cikin dake jikina. Duk sunyi mamaki sai dai Huzaifa yasan bazata masa karyar ciki ba. Don tasan zai iya dubawa ya tabbatar. Aishatu tace Fadila nasan zan dade ban kara yarda dake ba don na biyu kenan abinda kika yi min. Amma darajar abinda ke cikinki muna rokonka ka taimaka maganar sakin ka janye. Idan ta sake yi maka laifi nayi alqawari bazan shiga ba. Fadila ta rungumeta ta tana ta godiya. Shi kuwa fita yayi.
A sanyaye ta bishi daki yana zaune bakin gado ya dafe kai. Aishatu ta zauna a kusa dashi ta dafa masa kafada. Baby ka gode Allah sharrinta baiyi tasiri a kanmu ba da yanzu zuciya ta debe ni kila nice zan nemi sakin. Yayi saurin rufe mata baki. Allah Ya kiyaye Aish...tace to tunda hakan bai faru ba ya kamata mu nuna godiyar ga Allah ta hanyar yafe mata. Ka kara hakuri ko don darajar yara. Yace yanzu kin yarda na dawo da ita. Ta gyada kai don tsakani da Allah tana tsoron Fadila. Amma tana kwadayin ladan da ake bawa mai yawan afuwa idan an cutar dashi. Ya kankameta yana mata magana a kunne Aish it seems kina so sonki yayi min yawa a raina. Ke wace irin mace ce? Ya shafi fuskarta...you are too nice, too good. And Dr Rano loves you so much for that. Ita ma tace and I love you too. Ban taba tunanin zanyi aure namiji yaga darajata ba sai gashi ka zama sanadin gushewar duk bacin ran da na kwaso a baya. Duk da halin da nake ciki baka guje ni ba baby ta yaya zanyi sanadiyar raba maka iyali? Yace Alhamdulillah itama ta maimaita suka manta da Fadila da ke daki tana waya da Fahad.
Wasila ce ta turo mata numbarsa ta kira. Cikin isa da gadara tace masa sunana Fadila matar mijin tsohuwar matarka. Idan har kana sonta har yanzu ka zo mu hadu. Fahad yace ke kinsan da wa kike magana kuwa kike nema ki rinka bani order kamar yaronki? Ta tabe baki ba Fahad bane. Yayi wata yar dariya shine, ya kamata ki san ba'a yiwa fahad magana a haka. Idan kin shirya ki sanar dani wurin da zamu hadu. Sai kawai ya kashe wayar. Ta tsaya tana kallon wayar a hannunta tana juyata. Shi kuma wannan waye ta fada a zuciyarta.
RASHIN GODIYA ✂ 47
Aishatu ta rude jikinta na rawa tace Anti Sauda me zai sa ya kira ni haka kawai. Anti Sauda tace kinga kwantar da hankalinki in Allah Ya yarda ba komai. Ita dai Aishatu hankalinta bai kwanta ba sai da aka goge mata jiki ta tashi jikinta duk ba kwari. Anti sauda tace kina zuwa gida ki sanar da Dr don daga labarinsa ni ko kadan ban yarda dashi ba. Aishatu tace ai dole anti. Ni sam ban yarda da rufa rufa ba. Fahad mugun makiri ne ga iya hada sharri. Suna magana suka fito waje, dama gidan babu nisa da na Anti sauda a kasa suka je.
Fadila tana zaune gaban motar Huzaifa ya daukota daga gidansu tace Abban Aliya mu biya mu dauko Aishatu naga jiya irin lokacin nan ta dawo. Huzaifa yayi tsaki bana son iyayi, ta sanar dake inda zata ne da kike cewa a daukota. Ko kuwa son jin kwaf ne ya motsa kike neman bugun cikina. Fadila ta sunkuyar da kai, nasan duk abinda nayi ne a baya yasa komai nayi yanzu sai ka fassara shi da wata manufa. Shareta yayi don yasan son jan zancen take. Ya dauki wayarsa ya kira Aishatu dama niyarsa kenan su biya a daukota tunda yamma tayi. Ta fada masa ta gama zata jira ta koma gidan anti Sauda. Fadila na jin haka ta dauko wayarta ta tura text.
(Tana gidan nan da na kwatanta maka a yan kaba. Kayi sauri muna hanya)
Baiyi mata reply ba ya cigaba da kallon gate din gidan da Aishatu ta shiga daga cikin mota. Ta kara kyau da haske...sai yanzu ya kara ganin wautarsa akan yadda yayi treating dinta a gidansa. Yaro ya gani zai wuce yayi saurin fita daga mota ya tsayar dashi. Don Allah kace Aisha tazo inji Huzaifa. Ka fada mata tayi sauri wayata ce ta mutu. Yaron ya shiga ya fadawa Sajida sakon ta shiga dakin mamanta ta fada musu. Aishatu ta tayi saurin gyara fuska Anti Sauda sai dariya take...na dai fada miki amarcin nan sai an gama gyaraki. Na fuskanci Huzaifa ya gama koya miki rashin kunya idan ban kaiki ba zaki kai kanki. Aishatu ta rinka dariya suka fito tare. Anti Sauda tace gori zan masa har yau bai taba shiga gidana ba.
Basu ga motarsa a bakin gate ba har Anti Sauda na cewa ko dai tafiya yayi wani wurin kila yanzu zai dawo. Sam bata kula da yadda Aishatu ta sandare a tsaye ba. Hannunta taji ta damka har ta danyi ihu ke lafiya zaki karya ni. Kamar me rada ta nuna mata mutumin da yake tahowa wurinsu. Anti Sauda tace waye wannan? Ko Fahad ne? Aishatu ta gyada kai alamar eh.
Assalam alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Anti Sauda ta sha kunu ta amsa da kyar sannan ta rike Aishatu shige muje ciki. Fahad yace don Allah Haj ki daure ku saurare ni. Abinda ya kawoni yana da matukar mahimmanci. Aishatu ta juya a fusace yayi saurin cewa don girman Allah ki tsaya. Ba tare da ta juyo ba ta tsaya. Kan gwiwoyinsa biyu ya durkusa ki yafe ni Aisha. Ni mai dumbin laifi ne a gareki kuma wallahi ban taba jin son mace ba sai da na rabu dake. Nayi nadama mara iyaka kuma tun a duniya naga sakayyar abinda nayi miki tana faruwa a kaina. Sai hawaye suka fara zuba a idanunsa. Ya kalli Anti Sauda ki taimaka ki bata hakuri ko zanga sassauci a rayuwata. Bani da wani burin da ya wuce ki furta da bakinki kin yafe min. Duk maganar da yake kin juyowa tayi. Tana tuna irin wahalar da ya rinka bata ciki harda zubar mata da ciki sau biyu. Anti Sauda tace ni abinda ya bani mamaki ya akayi kasan tana gidan nan. Yayi murmushi ki roketa ta yafe min sai kuji abinda ya kawo ni. Wallahi Aishatu bazan kara cutar dake ba. Ina tsoron lahirata, ina tsoron wutar Allah, ina kunyar haduwa da Mahaliccina. Ta dan juyo na yafe maka amma don Allah ka dena bibiyata haka. Ya tashi yana kade rigarsa nagode sosai Aisha. Sai kuma mu koma ga abu na biyu da ya kawo ni....kafin yayi magana suka ji wani mahaukacin horn. Dukkansu basu tun san lokacin da Huzaifa yayi parking mota yana kallonsu ba. Ransa ya gama baci ji yake kamar ya shake fahad don ya tabbatar shine saboda haduwar da sukayi a kofar gidan su Aishatu. Zuciyar Aishatu kuwa don tsoro da fargaba kamar ta fito waje
RASHIN GODIYA ✂ 48
Gaba daya Aishatu ta rikice ta ma kasa motsawa. Huzaifa ya fito daga motarsa a fusace ya janyo hannun Aishatu. Anti Sauda tace Dr kayi mata a hankali bamu san yana wurin nan ba. Tamkar ba da shi take magana ba haka yayi gaba abinsa. Fahad bai ce masa komai ba har ya tada kura suka wuce. Anti Sauda ta yiwa fahad kallon banza. Ince ko kaji dadi ka hada rigima. Aishatu tana fada min sharrinka sai yau na tabbatar. Mai yasa baka yi masa bayanin abinda ya kawoka ba. Fahad yayi murmushi tare da dan tabe baki saboda kishi mana. Anti Sauda ta yu hanyar gate din gidanta a fusace Allah wadaran halinka. Fahad yace please ki saurareni. Maybe na iya fitar da kawarki daga zargi. Na tsaya sauraronka nima nawa mijin ya dawo ko. Sannu mugu to ta Allah ba taka ba. Ta shige tare da bugo gate din da karfi.
Kana ganin yanayi Huzaifa kasan bashi da kwanciyar hankali. Babu abinda shaidan bai kitsa masa ba a zuciyarsa. Wai garin yaya ma Fahad yasan gidan Sauda? Kuma ya akayi yasan inda Aish take a wannan lokacin? Fadila ta dan juya baya inda take jin sautin kukan Aishatu a hankali. Aishatu wai me ya faru ni kun sani a duhu. Kaima Abban Aliya meye na fushi bayan baka kirata ko kayi mata horn ba tunda muka zo. Ai kaga ba laifinta bane don bata taho da wuri ba. Mtsw kuma maza da rigimarku. Shiru babu wanda ya kula ta. Ta sake cewa Aishatu waye mutumin nan ko dan uwanku ne. Na tuna shi a wurin walimarki yana ta miki liki. A fusace Huzaifa yace to uwar jaraba kina mota har kin kare masa kallo...tayi saurin daga hannuwa sama yi hakuri na yi tunanin ko dan uwanta ne ko mijin wannan matar. Daidai lokacin da ya shiga gidan mal habu na rufe gate Fadila tace kai amma fa Aisha jininku mai karfi ne don kuna dibar kama da mutumin nan. Hancinku yayi....wani irin burki Huzaifa ya taka saboda yadda ya harzuka. Yace Fadila idan bakiyi min shiru ba zan tattaka ki wallahi. Tayi dariya Aishatu yau angonki sai a hankali bari na barku. Ta fice abinta ta shiga ciki. Aishatu ta dago kai suka hada ido ta mirror din gaba yace kema ki fita. Ta soma magana baby ka saurare ni wallahi...katse ta yayi da tsawa Aishatu ki fita nace, am not in the mood. Bai taba fadar sunanta ba sai yau. Yau ma cikin bacin rai. Ba musu ta fita yayi ribas da motar ya rinka danna horn har mal habu ya fito da gudu daga bandaki ya bude masa gate ya fice.
Aishatu ta shiga ciki tana kuka. Komai yayi mata zafi. Ta tabbatar plan Fahad ya hada tunda cewa yayi tazo inji Huzaifa. Komai yayi mata zafi ta shiga daki ta takure akan gado tana kuka a hankali. Ba ita ta tashi ba sai da taji kiran magriba.
Fadila tana kallon yadda Huzaifa ya fita ta tafa hannuwa. Wannan karon ko kinfi kuda naci Aishatu sai kin koma inda kika fito. Ta kira wasila suka sha hira hankali kwance.
Masallaci daya suka yi sallah. Sai da ya jira ya gama gaisawa da mutane ya fito sannan ya biyo shi waje. Sallama yayi masa mutum ya amsa cike da nutsuwa. Sai yace kamar Dr Rano ko mijin Aishan Sauda? Eh nine ya dan saki fuska. Don Allah magana nake son muyi. Gefe suka koma Huzaifa yace kaine mijin Haj Sauda ko? Babban su Islam yace eh nine lafiya dai? Huzaifa yayi masa bayanin abinda ya gani. Yace to ni bana son aiki da zargi, nasan halin mutuminan amma ina neman izini muyi magana da Saudan ta fada min gaskiyar abinda ya faru. Alh Adam yace kayi tunani mai kyau Dr. Allah Ya tsare mana iyali daga sharrin shaidan. Muje gidan..Huzaifa yayi masa godiya yace haba har daurin aurenka fa nazo. Rashin zamana yasa bama haduwa sosai.
RASHIN GODIYA ✂ 49
A falon gidan suka zauna Anti Sauda tayi musu gamsasshen bayani game da zuwan Fahad. Ta kare da cewa wallahi Dr matarka tana sonka kuma tana da rikon amana. Bai kamata zargi ya shiga tsakaninku akan abinda ka gani kawai baka bincika ba. Idan da tana son komawa gareshi ai bazata aureka ba. Huzaifa ya dafe kai ya kasa magana. Garin yaya ya nuna bacin rai sosai ga matarsa wadda take yiwa mai lafi uzuri. Alh Adam yace Sauda kibar kishi, babu abinda baya sawa. Tace hakane kaga ko ba komai nasan kanwata tana da babban gurbi a zuciyar Dr. Murmushi Huzaifa yayi yace nagode sosai da yadda kike kula da Aish, Allah Ya saka da alkhairi. Ya tashi zan tafi don Allah idan ya sake contacting dinku sai ki sanar dani tunda kince ya fada muku akwai abinda ya kawo shi.
Har bakin motarsa Alh Adam ya rako shi. Sai da ya fita sannan maigadin ya biyo Alh Adam. Uhmm Alh ga wannan takardar. Wani mutum ne dazu ya bani yace na bawa Hajiya sai na manta yanzu na tuna da na sake gani bako. Alh Adam yace kuma bai fadi suna ba? Maigadi yace na tambaya yace idan na bata zata gane. Alh Adam ya bude takarda ya karanta.
(Nasan ba lallai ku yarda dani amma akwai bayanin da nake son yi Aisha ko mijinta. Ga numbar wayata pls contact me.
Fahad)
Alh Adam yayi tsaki kuma shine sai yanzu zaka bani? Gashi wanda abin ya shafa yanzu ya tafi. Gida ya shiga ya nunawa Anti Sauda tayi ta salati ta kira Aishatu wayarta a kashe, ita kuma bata da numbar Dr Rano. Dole suka hakura sai washegari.
Huzaifa bai koma gida ba sai da ya nemo wata kaza da Aish ke so. Duk ranar da rigimarta ta tashi ta rinka nacin sai ya siyo mata ga layi da akeyi a wurin. Haka ya zauna yana ta tunanin halin da take ciki. Fatansa daya ba kuka take yi ba. Gashi ta kashe waya ya kasa samunta. Hudu ya siya ya wuce gida. A falonta ya ajiye nata ya wuce dakin Fadila ya kai mata biyu. Nata daya na yara daya, ta karba cike da murna, ita dai ta ga kayan kwadayi kawai. Har zai fita tace Abban Aliya ina na kanwata? Yana jin yadda tayi maganar yasan gulma ce kawai. Yace ban siyo ba ki kyale ta kawai. Ta ce gaskiya irin haka ba dadi ai sai ya zama rashin adalci. Ya dan kalleta to ko zaki dibar mata ne. Tuni ta hade rai kai ne hakkin ciyar da ita ke wuyanka ai. Kuma nasan idan ka koma kila ya tashi mai naman ko? Ba komai amma dai ka rinka adalci. Yace naji kije ki kwanta ki kular min da baby. Ta sake jindadi ta rufe kofa tana tsalle da murna. Aiki ya fara kyau saura na gobe ma.
Huzaifa yana mamakin hali irin na Fadila, ya tabbatar da ita ce a wannan yanayin Aish bazata nuna farinciki haka ba. Da sallama ya shiga dakinta ya tarar bata ciki. Allah sarki Aish yasan dakinsa ta tafi duk don kada ta nunawa mutan gidan halin da suke ciki. Can gefen gado ya hangota tana bacci akan abin sallah. Zuciyarsa tayi masa zafi ya kara jin tausayinta. Shiyasa Annabi SAW ya hanemu da daukar mataki cikin fushi. Ya ajiye ledar naman ya zauna a gefenta tare da dora kanta a cinyarsa. Motsinsa ne ya tasheta tayi saurin mikewa tana murza ido. Tana ganinsa ta soma kuka wallahi ban san shine yazo ba. Cewa akayi nazo kana jirana wayarka ba chaji kuma. Kamshin turaren da take yini ana yi mata ya doki hancinsa....bakinsa yasa ya hanata magana. Sun jima a haka hawayenta bai dena zubowa ba. Ya dago habarta da hannu biyu yana kallonta...kiyi hakuri nayi kuskure da ban tsaya sauraron hanzarinki ba. Kishi ne ya rufe min ido tare da mamakin abinda ya kawo shi har nan. Wani kukan yaga zata fara yayi saurin rungumeta, gaba daya ya zaunar da ita akan cinyarsa yace Aish I love you so much, bana son tuna kin taba auren Fahad bare na ganshi. Ya cutar min da ke sosai kokari nake na mantar dake duk wannan mugun experience din. Tana kukan tace kai kadai na taba so a rayuwata baby. Idan ka kasa amincewa dani bansan yadda zanyi ba. Duk wani farincikina ya danganta da kai. Haka suka yi ta kara jaddadawa juna so. Can yace wai kinyi wanka yau kuwa? Tsami nake ji. Dundu tayi masa a baya ba kaine ka sani kuka ba. Kuma wallahi bana tsami duk turaren nan da nake yini a ciki. Yayi dariya to kauri kike yi no wonder naji dakin kamar ana girki da itace. Hawaye ta soma tana kukan shagwaba ta tashi tana tura baki haka ma zaka ce ko? Duk gyaran nan da nakeyi saboda kai, to na dena kuma wankan ma na dena gaba daya. Yana mata dariya yace ashe haka kike da nauyi cinyata kamar ba a jikina take ba. Yana murza wurin da ta zauna daga yanzu idan zan rarrasheki daga nesa nesa zanyi. Kara shan kunu tayi tana masa mita nima bazan kara zuwa kusa da kai ba. Ta dauki mayafinta sai da safe na dena zuwa dakin nan. Ya dago ledar kaza ga wannan bari na cinye sai kisa a shara. Yadda tayi murmushi ya burge shi ta dawo da sauri wasa fa nake yi. Ai duk macen kirki a dakin mijinta take kwana. Yayi dariya sosai sannan suka zauna suka ci abinsu. Bayan sun gama suka yi wanka ya janyota jikinsa suka kwanta. Aish taji ya kirata a hankali. Naam babyn Aish ta amsa masa. Wai sai yaushe za'a gama gyara jikin nan? Naga ya gyaru sosai tun yanzu. Tayi murmushi sai nan da sati uku. Dan murmushin fuskarsa ya dauke ki manta da wani sati uku don bazan bari ba. Wai baki san medically bai kamata a rinka yawan shakar hayaki ba. Shi kanshi turaren da kuke yi ba'a so yayi yawa saboda kada yayi wa jiki illa. Aishatu ta gane abinda yake nufi tace to ai kaga ba laifina bane. Wato shi irin wannan gyaran idan ba'a jira an gama ba to baci zaiyi. Jinsa kawai tayi ya kara matseta cikin kunnenta taji yace wannan dai yau zai baci gobe sai a sake wani. Tace to ai Anti Sauda tace........maganar da bata sami damar karasawa ba kenan sai da asuba.
Washegari tana kitchen wayarta ta rinka ringing. Huzaifa da ke shirin fita asibiti ya dauka yaga ko waye. Sunan Anti Sauda ya gani ya duba time bakwai da yan mintuna. Sai kawai ya dauka. Tana jin muryarsa ta gaishe shi sannan tayi masa bayanin sakon Fahad. Yayi mata godiya sosai ya fita kitchen wurin Aish ya sanar da ita. Suna maganar text ya shigo da numbar da ya rubuta musu. Huzaifa ya kwafa a tasa wayar ya kira.
RASHIN GODIYA ✂ 50
Yanayin canjin fuskar mijinta yasa ta fara tsorata ta kagu ya gama ya sanar da ita abinda ya fada masa. Bayan sun gama yace mata ta zai je wurin Fahad a hotel din da yayi masauki. Aishatu ta ce kada ka je idan don nasan karshe ranmu ne zai baci. Huzaifa ya shafi fuskarta kada ki damu duk wanda ransa ya baci shi yaso. Tace ban gane ba. Zaki gane bari nayi sauri. Kafin ya fita ya kira wani abokin aikinsa ya nemi alfarmar ya kama masa aiki kafin ya zo.
Fuskarsa a hade ya bi bayan Fahad ya shiga dakin. A jikin kofa ya tsaya ya rungume hannuwansa a kirji. Fahad tace don Allah ka zauna Dr. Magana nake so muyi ta hankali. Huzaifa yace nan ma ya isa. Fahad yace suit yourself.
Fahad yace nasan ka sanni ka san wasu abubuwa da dama akaina. Bayan rabuwata da Aisha na so ta kamar inyi hauka. Kuma har yanzu ina sonta. Huzaifa ya daure fuska abinda ka kirani ka sanar dani kenan? No bashi bane amma ka sani son da nake mata ne yasa zan sanar da kai. A shekaru uku da nayi da matata ta yanzu naso haihuwa sosai. Duk lokacin da naje asibiti sai likitoci suce lafiyarmu kalau lokaci ne kawai baiyi ba. A lokacin na rinka tunanin yadda zanyi na rabaka da Aisha. Sai watarana naji waazi da ya tayar min da hankali. Ga tsananin mamakin Huzaifa hawaye ya gani a idon Fahad. Nayi nadamar zama sanadin zubewar cikin Aisha har sau biyu. Nayi roki iyalina, iyayena da sauran yan uwana gafara game da irin zamanmu da su. Aisha kadai ta rage min da hakkin rai biyu. Huzaifa abin ya fara isarsa. Kaga malam ni fa ba tarihin rayuwarka nazo ji ba. Fahad yayi murmushi ni kuma sai kaji tarihin zaka fahimci inda na sa gaba. A halin yanzu dai na shiryu daga munanan halaye na. Sai dai kwatsam wata rana wata mata mai suna wasila ta kirani a waya. Suna neman hadin kaina ne a rabaka da Aisha ni na aura tunda sun sami labarin ina sonta. Sai a lokacin Huzaifa ya zauna. Fahad ya cigaba tun lokacin na amsa mata amma banyi niyar yin komai ba sai da matarka Fadila ta kirani a waya da wannan bukatar dai. Naji tsoron idan ban amsa ba zata iya neman wata watar ko wani mutumin shiyasa nazo. Tare da sannin matata don ita ta bani shawarar yadda zanyi. Huzaifa ya tashi tsaye kana son kace min fadila ta sanka ne,wato sharri kake son kulla mata. Dama nasan zuwa wurinka will be a complete waste of time. Hotuna Fahad ya baza masa akan table din gabansu. Wasu shi da fadila ne a wajen makarantarsu Aliya. Sai wasu a gate din hotel din,wasu kuma a kofar dakin. Jikin Huzaifa ya soma rawa a sanyaye yace Fahad ka nemi matata ne? Fahad yace ka kwantar da hankalinka ko a da ni ba mazinaci bane. Magana tazo muyi akan yadda zamu bata tsakaninka da matarka. Ta yaya nasan gidan da Aisha take jiya?
Huzaifa gumi ne ya jika shi lokaci guda. Wane irin tashin hankali ne wannan. Ina Fadila zata kai mugun halinta. Bata laakari da kullum tayi sai asirinta ya tonu. Wannan yafi komai kure shi tunda har zata iya kebewa a dakin hotel da mutumin da ba muharraminta ba. Ya ce da Fahad to meye next plan dinku. Fahad ya dauko waya a gabansa ya kira Fadila yasa a speaker.
Tana dauka tace ,yauwa tun dazu nake jiran wayarka, ya fita itan ma dreban gidan uwarsa yazo ya dauketa. Huzaifa ya rike baki wai uwarsa.
Fahad yace to yanzu ya zaayi?
Ta cigaba na gano gyaran jiki take zuwa. Na riga na yanki key din dakin nata. Fahad da Huzaifa suka hada ido. Jin anyi shiru yace Fahad kana ji na?
Eh ina jinki yanzu ya zaayi na shiga dakin yadda wannan mijin naku zai ganni.
Fadila tayi dariya kada ka damu. Kazo bayan laasar sai na bude maka dakin. Zan tabbatar yau ni na daukota ba shi ba. Daga nan sai ka buya kada ka kuskura ka fito sai kaji muryarsa. Idan da hali ka rungumeta ma komai ihunta. Tana dariya fahad ya biye mata suka yi tare.
Huzaifa kirjinsa ya dafe zuciyarsa kamar ana hura wuta. Fadila ta fi karfinsa yanzu mace me irin halinta zaman aure ba nata bane sai dai idan hali ya dace da na mijin. Huzaifa yace Fahad meyasa ka zabi ka fada min gaskiya? Fahad yace baka ji lokacin da na ce maka nayi nadama ba? Da ban amince ba Fadila zata iya neman wani. Dukkansu suka ajiye kishinsu a gefe suka tsara plan din yadda zasu bullowa Fadila. Ita wadda ake yi dominta bata san me sukeyi ba. Tana can cike da farinciki tana karasa gyara jikinta domin neman yardar Allah da ta mijinta.
RASHIN GODIYA ✂ 51
Huzaifa ko aiki ya kasa zuwa saboda yanayin da yake ciki. Duk cikin 'yan uwansa babu wadda zai iya fadawa tayi shiru ba tare da ta sanar da umma ba. Shi kuwa yafi son sai ya kashe gobarar ma sannan za ta san abinda yake faruwa. irin wannan sirrin kuwa ba abu bane da zai iya fadawa aboki. Ciki ba don abinci kawai aka yi shi ba, wani idan ya sani ma dariya zai masa ace ya kasa rike mace. Daga karshe dai office ya wuce amma ya sanar yau bazai iya ganin marasa lafiya ba. Maaikatan asibitin sunyi mamaki domin hakan ba halinsa bane. Bai dade da zama ba sai ga wayar Fadila. Gabansa har faduwa yayi ya dauka ya kuma yi kokarin nuna mata komai lafiya yake. Sai da ta gama yi masa hira tace Abban Aliya kaga wasila ce tazo nan aka bugo waya yayarta ta karye a kafa. Na fita rakata muka ga tayarta daya tayi paci. Naga hankalinta duk ya tashi shine nake son in kaita. Hmmm kawai ya ce, yanzu ba don yasan gaskiya ba haka zata raina masa hankali. A fili kuwa cewa yayi mal Habu ya cire ya daura mata spare mana. Kukan wasilar yaji fadila ni na tafi kawai don bansan halin da take ciki ba. Fadila tace kaji ta ko duk a rude take. Huzaifa yace to ba komai ki kaita. Allah Ya kiyaye gaba. Fadila ta ajiye wayar suka tafa da Wasila. Tace kai amma fadila mijin nan naki akwai matsi sosai. Ni Kamilu bai isa na tambayeshi fita ba. Fadila ta ce uhmm nima da bana tambaya, zuwan shegiyar nan ne naga tanayi shiyasa na fara. Sake tafawa suka yi sannan ta kira Fahad tace yazo yanzu.
Basu dade ba kuwa sai gashi kamar yadda ta fada masa kada yazo da mota bai zo da ita ba. Ya kira ya sanar da ita yana bakin gate. Sai ta fito ta ce Mal Habu ya duba mata baya tana jin kamar motsi, kafin ya dawo ta shige da Fahad. Wasila ta kare masa kallo tace gaskiya Fadila na kyasa. Ko kadan bata ji kunyar yana jin abinda ta fada ba. Fadila ta ce ke duk namijin duniya ai yayi miki. Fahad yana jinsu dai bai kula ba. Wasila ta sake cewa ita kuma Aishatu duk mazan da ke sonta haka suke kyawawa in dai bazaka damu ba Fahad ina son zama friend dinka. Yadda take masa kwarkwasa ya bata masa rai. Wasu matan basu san darajar da Allah Yayi musu ba. Fadila dai ta dauki key din mota ta rike mayafi a hannu. To zamu tafi zan tabbatar ni na dauko ta. Ga dakin ka shiga na hada maka da keys din falo da na daki. Yace to nagode amma kuyi sauri. Wasila dai kamar kada ta fita. Ta dade tana son Huzaifa ma amma saboda Fadila take hadiye wa.
Ana yin laasar ta sake kiran Huzaifa ta sanar dashi zata koma gida amma taga wurin yayi kusa da inda Aishatu take zuwa za ta biya ta dauko ta. Yace ai yau da wuri ta gama ta tafi. Ina jin ta isa gidan ma. Amma dai nagode da kike wannan kokarin na ganin kun daidaita. Fadila dadi ya isheta dama bukatarta Aishatu ta riga Huzaifa zuwa gida.
Huzaifa ya ajiye wayar ya kalli Aishatu da ke zaune a gabansa tana sharbar hawaye. Idanunta sunyi ja sun kumbura sai ajiyar zuciya take yi. Yau bata gama gyaran jikin ba yaje ya daukota. Ya gama yi mata bayanin yadda suka yi da Fahad kenan Fadila ta kira. Kallonta kawai Huzaifa yake yi yace Aish menene abin kuka kuma? Bayan Allah SWT Ya fitar dake ba tareda anyi nasara akanki ba. Tace hakane amma me na tsarewa Fadila haka? Idan da Allah bai kaddari zamanmu ba da tuni mun rabu. Tashi yayi ya rungumeta yana ta rarrashi ni bana son zancen rabuwa kinji ko. Duk bawan da ya dogara da Allah kuma yake gode Masa a kowane hali bazai tabe ba. Allah bazai dora mana jarabawar da tafi karfin imaninmu ba. Shiryuwar Fahad ai ba kokarinmu bane. Ina so ki kara inganta imaninki ki kasance mai hakuri da juriya sai kiga rahmar Allah tana bibiyarki. Aishatu ta kalli Huzaifa tana murmushi tace Alhamdulillah. Ya rike hannunta ko ke fa. Tashi mu tafi gida.
RASHIN GODIYA ✂ 53
Kowa na binsu da ido ya kaita gaban mahaifiyarsa ya zaunar da ita sannan yace mata Aish bani key din dakinki. Ba musu ta dauko ta mika masa, yace guda nawa ne mukullan? Ta ce hudu ne biyu suna jakata biyu kuma suna wurinka. Huzaifa ya shiga daki ya fito da su. Ya hada ya ce da Baban gandu ai sun cika hudu ko? Yace hudu ne zahiri. Wai ni kadai ne kaina ya kulle a wurin nan? Umma tace nima jira nake su yi min bayani. Idanun fadila kamar zasu fado kasa. Ta riga ta gama tsurewa tunda taga ya shigo da Aishatu tasan abinda zai biyo baya bazai mata kyau ba.
Huzaifa ya tashi yaje ya bude dakin Aishatu sai ga Fahad ya fito. Nan fa kowa ya tashi tsaye ana kallon kallo. Umma tace auta don girman Allah me yake faruwa? Huzaifa yace su zauna yanzu zaiyi musu bayani. Suna zama yace Fahad bismillah. Nan da nan fahad ya fara bayanin abinda ya faru tun daga wayar Wasila ta farko. Kowa da abinda yake fada game da Fadila da kawarta. Aishatu kuwa sai kuka take yi. A wurin Huzaifa ya fadi wasu daga abubuwan da fadila tayi masa a baya tun kafin aurensa da Aishatu. Fadila ta soma kuka Huzaifa sharri zaka yi min ko har ka iya hada baki da tsohon mijin matarka don kawai baka so na. Baban fadila ya tashi ya hau dukanta. Fadila ke wace irin yarinya ce yanzu da ke zaa hada baki a kawo namiji dakin wata don miji ya saketa. Kuma da yake baki da tsoron Allah har ki kirawo dangin mijinki su zo kallo ko. To gashi ramin da kika gina kin fada ciki. Tana kuka tace Abba wallahi sharri ne. Tunda yarinyar nan tazo take kulla min sharri. Huzaifa kawai sai ya jefa mata hotunansu ita da Fahad a mota da hotel. Wannan karon Baban gandu ne ya kai mata duka. Kin cucemu kin cuci kanki Fadila. Umma ta ce Aishatu iyayenki sun san abinda ke faruwa...ta girgiza kai a'a Umma. Tace Allah Yayi miki albarka da kika rufa sirrin gidanki. Fahad ya tashi zai tafi suka yi masa godiya da bai biyewa son zuciya ya fada ga halaka ba.
Ana ta yiwa Fadila fada tana rusa kuka wasila ta sabi jakarta zata gudu Huzaifa yace dawo nan. Ki jira mijinki zai zo daukarki. Wasila ta soma matsar kwalla tana bada hakuri. Babu wanda ya saurareta har Kamilu ya iso bai tsaya gama jin bayani ba ya ce ta tafi ya saketa saki uku. Nan kuma manya suka soma yi masa fada yayi aika aika. Shi dai murna yake yau ya sami kwarin gwiwar rabuwa da matar da ta zame masa karfen kafa. Dama iyayensa basa son auren. Haka wasilq tabi bayansa tana ta kuka har waje ana jin muryarta. Hankali ya dawo ga Fadila, Huzaifa yace Baba dama na kiraku ne don ku zama shaida saboda kada magana ta fito ta karyata. Ku gafarceni amma bazan iya sake zama da Fadila ba. Fadila ta taso tana ihu don Allah kada ka karasa sakina Huzaifa. Igiya daya ce ta rage min. Wayyo na shiga uku Aishatu kice kin yafe kada ya karasa sakina. Huzaifa ya dauko takarda ta tashi ta fizge wallahi baka isa ka sakeni ba. Kayi kadan Huzaifa dama nasan duk bakwa sona ta nuna su Yaya Zainab. Wallahi zama daram a gidan nan babu inda zani. Baban gandu ya kwada mata wani mari ba shiri ta nutsu. Yace bazan hanaka sakinta ba Huzaifa. Fadila kin zalunci kanki don Ubangijinmu sarki ne mai adalci. Kin zama daga cikin mutanen da basa iya godewa Allah. Godiya ga Allah fa ba ta tsaya a cewa ALHAMDULILLAH bane. Idan kika yi abinda ya dace ma kin nuna godiyarki. Fadila kina sabawa mijinki yana hakuri baki gode ba, kin kullawa matar abubuwa da dama wanda ya kai a saki a tsakaninku har sau biyu tana sawa ya yafe miki baki gode ba, Allah Ya baki rai da lafiya, gidan aure da zuria nan ma baki gode ba. Mijinki da abokiyar zamanki basu taba tunanin tona miki asiri ba sai gashi rashin godiyarki ya janyo naki asirin ne ya tonu. Me kike nema ne a rayuwa Fadila? Babanta cikin kunan rai yace me take nema kuwa Yaya banda ta jawo mana zagi da bacin suna. Babu abinda Allah bai baki ba na jindadin rayuwa Fadila sai dai zuciyarki bata da godiyar Allah. Duk macen da zata kasa sauke nauyin mijinta kuma ta nuna kishin banza don zaiyi aure bata da maraba da jaka. Fadila tayi saurin kallon mahaifinta yace kwarai kuwa. Baki da maraba da jaka mana. Kina zaune wata can tana koya miki yadda zaki zauna da mijinki. Ke kuma kamar mara hankali duk abinda ta fada ya zauna miki a ka. har ki fasa kayan dakin kishiya dangin miji su biya ba tareda an neme mu ba. Haba Fadila! Indai hakan riba ne yau idonki ya gane miki ai.
Umma ta ce Fadila yau kinga sabanin abinda kika so ya faru. Da yanzu wannan baiwar Allah zamu saka a gaba da fada da zagi. Ki sani zaman gidan miji iyawa ne. Kissa da kike ji ana fada ba hauka bace. A yadda kika iya kulla abubuwa haka da kinyi amfani da basirarki wurin kyautatawa miji da tuni bamu zo ga yau ba. Ni shaida ce auta ya so ki sosai sai gashi abin mamaki aure bai rufa shekara biyar ba ya kara wata. Zamanin daga ni sai mijina ya wuce. Yanzu fatanmu kawai idan tazo a zauna lafiya idan kuma ita muka tarar ma dai a zauna lafiya. Rayuwar har nawa take da zamu batawa kanmu lokaci da neman ganin bayan wasu. Shawarata ta karshe gareki shine kiji tsoron Allah ki gyara halinki. Su Yaya shukriya duk suna da abin fada a bakinsu amma tarbiyar umma ta hanasu magana idan manya nayi. Dole dukkaninsu suka yi shiru. Huzaifa ya dubi iyayen fadila...Baba ku yi hakuri ku yafe min amma bazan kara iya zama da ita ba. Ina tsoron abinda zaije ya dawo nan gaba ne. Baban gandu yayi ajiyar zuciya Huzaifa kayi hakuri gaskiya kuma bazan goyi bayan ka zauna da ita a wannan yanayin ba. Duk macen da zata iya shiga hotel da mutumin da ba muharraminta ba har daki dole aji tsoron zama da ita. Huzaifa ya kalli Aishatu wadda tun zamansu bata yi magana ba. Kawar da kai tayi gefe alamun yau babu ruwanta sai kawai ya tashi ya dora wa Fadila takardar da tun bayan da ya baro wurin fahad ya rubuta.
Kukan da take yi ya bawa mutanen wurin tausayi sai dai duk bawan da bai godewa rahmar Allah ba,wata rana bazai ki godewa azabarSa ba. Haka iyayenta suka saka ta a gaba tana hawaye suka tafi gida. Umma ta sake yiwa su Aishatu nasiha suka tafi.
RASHIN GODIYA ✂ 52
Kafin Fadila ta karasa gida Fahad ya tura mata text akan cewa kada tayi masa text ko waya saboda Aishatu tana dakin. Hankalinta kwance ta yi masa reply akan za ta kiyaye. Sai bayan rabin awa da komawar Fadila gida sannan Huzaifa ya dauko Aishatu suka taho. Da ya iso a waje yayi parking din motar suka shigo ciki sai Aishatu ta tsaya a falonsa na waje. Shi kuma yayi sallama ya shiga ciki.
Ciki da nishadi ya shiga gidan yana ta faraa. ba shiri ya tsaya da yaga Fadila da Wasila a tsakar falo suna ta kai kawo. Ya sake maimaita sallama Fadila ta amsa da kyar, muryarta har rawa take yi. Huzaifa ya kallesu kamar mai mamaki yace lafiyarku kuwa ko yayar taki ta mutu ne wasila? Ta ja dogon numfashi jikinta da sauki. Gidanka ne dai a cikin matsala. Fadila ta share hawayen munafurci kinga ki iya bakinki kawai idonsa ya gane masa.
A can waje kuma motoci biyu ne suke horn a bakin gate. Mal Habu ya bude musu suka shigo. Daya Yaya Kubra ce tare da Umma. Dayar kuma dreban yaya zainab ne ya daukosu ita da Yaya shukriya da Saddiqa. Aishatu ta leka ta window ta gansu hankalinta ya kara tashi me ya kawosu gidan a lokaci daya ta tambayi kanta. Su dinma a cikin tashin hankali suka shiga gidan. Huzaifa da yake tsaye a falo yana jiran amsar su Fadila ya juyo a tsorace yana tambayarsu ko lafiya. Saddiqa tace kai zamuyi wa wannan tambayar auta. Fadila ta kira dukkanmu tace muzo gidan nan akwai matsala. Yace nima shigowata kenan bata fada min komai ba. Umma ta kalleta ke Fadila ko dai yaran ne? Wasila tace yara Laure ta rakasu islamiya. Za ta sake magana sai ga sallamar baban Fadila da yayansa Baban Gandu. A take cikin Fadila ya bada wani mugun sauti tace Baba daga ina kuke haka? Baban gandu yace kaniyarki, ba amsa sallama ba gaisuwa sai daga ina muke? To daga inda kika aikemu muke mara kunya. Huzaifa da sauran suka gaisa dasu. Umma tace ni ku fada min abinda ke faruwa fadila ce ta kira mu. Baban gandu yace mu kuma Huzaifan ne ya kiramu da kansa. Yace lallai yana bukatarmu a gidan nan saboda wani abu mai matukar mahimmanci. Yaya Zainab tace wai ni ina Aishatu ne. Fadila ta durkusa gabansu dama dalilin nawa kiran kenan. Nasan duk abinda zan fada zaku ga kamar kishi ne yasa na fada shiyasa na kiraku ku zama shaida. Ban dade da dawowa gida ba munje duba yar wasila sai nake jin kamar maganar mutum sama da daya a dakin Aishatu. Da nayi zaton baki ne da ita sai kuma naji muryar ta namiji ce. Duk da haka nace ko kannenta ne. Ta kalli Huzaifa nasan dai ka hana maza wuce falon nan amma sai nace kila wani abin ne daban. Baban gandu yace ke kuma uwar shisshigi sai kika dorawa kanki damuwar da ba taki ba ko? Umma tace haba Alh kyaleta ta gama bayaninta. Fadila ta sake sauke murya tace to daga nan nace da wasila tazo muje mu gaisa sai naji kofar a kulle ta ciki. kuma na tabbatar da mutane a ciki. Na buga baa bude ba shine hankalina ya tashi na zaga tagarta ta baya. Wayyo Allah sai kuka ya kwace mata Abban Aliya ha'intarka Aishatu take yi. Ta window din tagar na hangota ita da wani suna.....Baban Fadila ya daka mata tsawa bana son zancen banza. Su Umma kuwa sai salati suke. Wannan wane irin tashin hankali ne. Jinkin kowa a mace suna kallon Huzaifa wanda ya dafe kai yana hawaye. Kowa ya tausaya masa basu san kukan tsabar bacin rai bane na irin halayyar Fadila. Falon yayi tsit can Huzaifa ya ce Fadila kin tabbata kin gansu tare. Tace wallahi na gansu a mugun yanayi. Ai wasila ma na wurin, ban bari sun ganni ba dai. Kasan yau baka dawowa da wuri kuma na mata waya cewa na fita. Kila shiyasa ta kirawo shi. Yayyan Huzaifa suna ta juyayin zancen. Kawai suka ga ya tashi. Waje ya fita har umma na cewa a bishi kada yayi wani wurin. Bai dade ba sai gashi ya dawo rike da hannun Aishatu. Fadila ta tashi da sauri jikinta na bari.
RASHIN GODIYA ✂ 53
Kowa na binsu da ido ya kaita gaban mahaifiyarsa ya zaunar da ita sannan yace mata Aish bani key din dakinki. Ba musu ta dauko ta mika masa, yace guda nawa ne mukullan? Ta ce hudu ne biyu suna jakata biyu kuma suna wurinka. Huzaifa ya shiga daki ya fito da su. Ya hada ya ce da Baban gandu ai sun cika hudu ko? Yace hudu ne zahiri. Wai ni kadai ne kaina ya kulle a wurin nan? Umma tace nima jira nake su yi min bayani. Idanun fadila kamar zasu fado kasa. Ta riga ta gama tsurewa tunda taga ya shigo da Aishatu tasan abinda zai biyo baya bazai mata kyau ba.
Huzaifa ya tashi yaje ya bude dakin Aishatu sai ga Fahad ya fito. Nan fa kowa ya tashi tsaye ana kallon kallo. Umma tace auta don girman Allah me yake faruwa? Huzaifa yace su zauna yanzu zaiyi musu bayani. Suna zama yace Fahad bismillah. Nan da nan fahad ya fara bayanin abinda ya faru tun daga wayar Wasila ta farko. Kowa da abinda yake fada game da Fadila da kawarta. Aishatu kuwa sai kuka take yi. A wurin Huzaifa ya fadi wasu daga abubuwan da fadila tayi masa a baya tun kafin aurensa da Aishatu. Fadila ta soma kuka Huzaifa sharri zaka yi min ko har ka iya hada baki da tsohon mijin matarka don kawai baka so na. Baban fadila ya tashi ya hau dukanta. Fadila ke wace irin yarinya ce yanzu da ke zaa hada baki a kawo namiji dakin wata don miji ya saketa. Kuma da yake baki da tsoron Allah har ki kirawo dangin mijinki su zo kallo ko. To gashi ramin da kika gina kin fada ciki. Tana kuka tace Abba wallahi sharri ne. Tunda yarinyar nan tazo take kulla min sharri. Huzaifa kawai sai ya jefa mata hotunansu ita da Fahad a mota da hotel. Wannan karon Baban gandu ne ya kai mata duka. Kin cucemu kin cuci kanki Fadila. Umma ta ce Aishatu iyayenki sun san abinda ke faruwa...ta girgiza kai a'a Umma. Tace Allah Yayi miki albarka da kika rufa sirrin gidanki. Fahad ya tashi zai tafi suka yi masa godiya da bai biyewa son zuciya ya fada ga halaka ba.
Ana ta yiwa Fadila fada tana rusa kuka wasila ta sabi jakarta zata gudu Huzaifa yace dawo nan. Ki jira mijinki zai zo daukarki. Wasila ta soma matsar kwalla tana bada hakuri. Babu wanda ya saurareta har Kamilu ya iso bai tsaya gama jin bayani ba ya ce ta tafi ya saketa saki uku. Nan kuma manya suka soma yi masa fada yayi aika aika. Shi dai murna yake yau ya sami kwarin gwiwar rabuwa da matar da ta zame masa karfen kafa. Dama iyayensa basa son auren. Haka wasilq tabi bayansa tana ta kuka har waje ana jin muryarta. Hankali ya dawo ga Fadila, Huzaifa yace Baba dama na kiraku ne don ku zama shaida saboda kada magana ta fito ta karyata. Ku gafarceni amma bazan iya sake zama da Fadila ba. Fadila ta taso tana ihu don Allah kada ka karasa sakina Huzaifa. Igiya daya ce ta rage min. Wayyo na shiga uku Aishatu kice kin yafe kada ya karasa sakina. Huzaifa ya dauko takarda ta tashi ta fizge wallahi baka isa ka sakeni ba. Kayi kadan Huzaifa dama nasan duk bakwa sona ta nuna su Yaya Zainab. Wallahi zama daram a gidan nan babu inda zani. Baban gandu ya kwada mata wani mari ba shiri ta nutsu. Yace bazan hanaka sakinta ba Huzaifa. Fadila kin zalunci kanki don Ubangijinmu sarki ne mai adalci. Kin zama daga cikin mutanen da basa iya godewa Allah. Godiya ga Allah fa ba ta tsaya a cewa ALHAMDULILLAH bane. Idan kika yi abinda ya dace ma kin nuna godiyarki. Fadila kina sabawa mijinki yana hakuri baki gode ba, kin kullawa matar abubuwa da dama wanda ya kai a saki a tsakaninku har sau biyu tana sawa ya yafe miki baki gode ba, Allah Ya baki rai da lafiya, gidan aure da zuria nan ma baki gode ba. Mijinki da abokiyar zamanki basu taba tunanin tona miki asiri ba sai gashi rashin godiyarki ya janyo naki asirin ne ya tonu. Me kike nema ne a rayuwa Fadila? Babanta cikin kunan rai yace me take nema kuwa Yaya banda ta jawo mana zagi da bacin suna. Babu abinda Allah bai baki ba na jindadin rayuwa Fadila sai dai zuciyarki bata da godiyar Allah. Duk macen da zata kasa sauke nauyin mijinta kuma ta nuna kishin banza don zaiyi aure bata da maraba da jaka. Fadila tayi saurin kallon mahaifinta yace kwarai kuwa. Baki da maraba da jaka mana. Kina zaune wata can tana koya miki yadda zaki zauna da mijinki. Ke kuma kamar mara hankali duk abinda ta fada ya zauna miki a ka. har ki fasa kayan dakin kishiya dangin miji su biya ba tareda an neme mu ba. Haba Fadila! Indai hakan riba ne yau idonki ya gane miki ai.
Umma ta ce Fadila yau kinga sabanin abinda kika so ya faru. Da yanzu wannan baiwar Allah zamu saka a gaba da fada da zagi. Ki sani zaman gidan miji iyawa ne. Kissa da kike ji ana fada ba hauka bace. A yadda kika iya kulla abubuwa haka da kinyi amfani da basirarki wurin kyautatawa miji da tuni bamu zo ga yau ba. Ni shaida ce auta ya so ki sosai sai gashi abin mamaki aure bai rufa shekara biyar ba ya kara wata. Zamanin daga ni sai mijina ya wuce. Yanzu fatanmu kawai idan tazo a zauna lafiya idan kuma ita muka tarar ma dai a zauna lafiya. Rayuwar har nawa take da zamu batawa kanmu lokaci da neman ganin bayan wasu. Shawarata ta karshe gareki shine kiji tsoron Allah ki gyara halinki. Su Yaya shukriya duk suna da abin fada a bakinsu amma tarbiyar umma ta hanasu magana idan manya nayi. Dole dukkaninsu suka yi shiru. Huzaifa ya dubi iyayen fadila...Baba ku yi hakuri ku yafe min amma bazan kara iya zama da ita ba. Ina tsoron abinda zaije ya dawo nan gaba ne. Baban gandu yayi ajiyar zuciya Huzaifa kayi hakuri gaskiya kuma bazan goyi bayan ka zauna da ita a wannan yanayin ba. Duk macen da zata iya shiga hotel da mutumin da ba muharraminta ba har daki dole aji tsoron zama da ita. Huzaifa ya kalli Aishatu wadda tun zamansu bata yi magana ba. Kawar da kai tayi gefe alamun yau babu ruwanta sai kawai ya tashi ya dora wa Fadila takardar da tun bayan da ya baro wurin fahad ya rubuta.
Kukan da take yi ya bawa mutanen wurin tausayi sai dai duk bawan da bai godewa rahmar Allah ba,wata rana bazai ki godewa azabarSa ba. Haka iyayenta suka saka ta a gaba tana hawaye suka tafi gida. Umma ta sake yiwa su Aishatu nasiha suka tafi.
RASHIN GODIYA ✂ 54
Kwana biyu da faruwar wannan al'amari aka kira Huzaifa daga gidansu Fadila kan cewa tayi bari cikin dare. Ko da ta fice masa a rai yaso kwarai ta haihu don yana son yara. Ranar da yaje dubata ta bashi tausayi sosai kuma ta bashi hakuri. Har ta roki ya tayata bawa Aishatu ma hakuri.
Bayan sati biyu Aishatu da Huzaifa suka tafi Umra. Bakinta ya kasa rufuwa lokacin da ta ga Ka'abar Allah. Daga inda ta ganta ta durkusa tayi sujjada ta kara godewa ALLAH SWT bisa ga niimoninsa gareta. Sunyi sati biyu banda ibada babu suke yi. Sai soyayyarsu da shakuwa da suke karuwa kullum. Basu da burin da ya wuce kyautatawa juna. Nan suka yi azuminsu har sallah. Ranar da zasu dawo tun safe Aishatu tace jikinta ba dadi tana ta narkewa. Huzaifa ya ce nasan ciwon bakya son komawa gida ne. Tayi murmushi wa yake son yin nisa da kasa mai tsarki? Ya ja hancinta babu.
Suna jirgi ta dan kwanta jikinsa ta tashi ba shiri saboda amai da yake damunta. Kafin jirginsu ya sauka tayi sau biyar. Duk ta bashi tausayi haka suka tafi gida jikinta ba kwari. Su Aliya sun sha tsaraba ta dame shi sai an dauko mata su a daren yaki amincewa. Ke kin fiye rigima Aish. Kina fama da kanki kina kiran yara. Ki bari gobe na dauko su. Yau naga alama kwanan jinya zanyi. Ta dan turo baki please baby. Nayi missing din su sosai. Ya janyota jikinsa ni bakiyi missing dina ba ko. Ta gyara kwanciya ba ina ganinka ba kullum. Yace su ma yaran ai kullum kina waya dasu. Gobe zanyi musu albishir mai dadi. Tayi kara riko shi don Allah ka fara yi min kaji. Ya noke kafada haba babyn Aish. Huzaifa ya kura mata ido yana kare mata kallo....shi dai yana sonta. Ta hura masa isa a fuska me kake kallo ne baby? Yadda kika ciko mana 'yan kwanakin nan. Gobe zanyi miki pregnancy test. Naga alama yarinyar nan ciki gareki. Kunya tasa ta kara shigewa jikinsa taki yarda su hada ido. Yayi yayi taki dagowa haba Aish meye na jin kunya kuma. Ko kunyar karyar ce ta motsa. Ta na dariya tace ta gasken ce baby.....shima dariyar yake yace indai ita ce to bari nayi maganinta.
Bayan wata hudu kowa yasan Aishatu tana da ciki don ya fito ya fi watanninsa girma ma. Kulawa take samu sosai daga iyayenta da umma. Su Yaya Zainab ma duk sun gama yankewa yan biyu ne a cikin yadda yayi girma shiyasa suke kara shagwabata. Duk da haka ita ke yiwa mijinta girki kullum. Tun yana hanawa har ya hakura, yace da kanta zata dena idan jikin ya kara nauyi. Rayuwarsu abin shaawa suna kula da su Aliyu sosai. Yaya Kubra ma ta koma gidanta sun dena fada da uwar mijinta.
Wata talata Huzaifa na asibiti ya gama duba patient an kira next one sai yaga Fahad tare da wata mata ta sha katon mayafi. Tun ranar da aka tona Fadila basu sake haduwa ba. Huzaifa ya yi murnar ganinsa don kuwa yayi ta kiran wayarsa baya samu. So yake suyi zumunci saboda taimakon da yayi masa. Shima Fahad din da faraa ya shigo suka gaisa. Fahad yace Dr ga madam fa Yahanasu. Ta sake gaishe shi Fahad yace duk abinda ya faru kwanaki da taimakonta ne. Huzaifa yana ta murmushi yace kawai kace kanwata ce. I hope ba problem dai. Fahad yace akan matsalar haihuwa ne Dr. Ya nuna masa medical reports dinsu na wasu asibitocin. Bayan dogon nazari ya tura su yin wasu gwaje gwajen tare da basu wasu magungunan. Suka rabu cikin mutunta juna.
Daren ranar suna kwance da Aish yake bata labarin zuwan Fahad. Tace ikon Allah kenan da yana gudu yanzu yana nema. Huzaifa yace haka rayuwa take. Allah Yayi mana jagora. Wai kinsan labarin da na ji yau kuwa? Fadila ta auri mijin Wasila suna ta rigima da wasilan don itama har tayi auren kashe wuta. Aishatu tayi mamaki to Allah Ya kyauta. Ya sake cewa ai akwai wani labarin...Aishatu ta ce yaushe ka zama mai labarai ne. Tun da na auri Indo Aisha mana...my one and only Aish. Ta rungume shi sosai ai kuwa Aish tana da labari mai dadi da zata baka. Suka ja bargo suna dariya.
Ko da Huzaifa yayi mata scanning yan biyu ya gani amma basu fadawa kowa ba. Cikin na da wata bakwai ta dena fita ko'ina saboda girmansa. Mama bata zance sai na tausayin Aishatu har Baba yana mata tsiyar bata jin kunyar yar fari.
Wata rana Huzaifa ya dawo daga gidan Umma ya tarar da Aishatu tana ta kai kawo a cikin gida. Dama ya barta da safe tana complain din mararta ta rike. Yana ganinta yasan haihuwa ce ya dauko akwaitin da ya hada mata suka tafi asibiti. An shiga da ita labour room suka hanashi shiga. Ya zauna a waje sai ga su Yaya Kubra dukkanninsu. Mama ma tazo tare da kanwarta lawisa sai Anti Sauda. Wurin awa uku suna ciki kana kallon Huzaufa sai ya baka tausayi. Da an fito ya rinka tambayar ko lafiya kenan. Karshe har wani fada fada ya koma yi musu. Dr Abida ita ta hana ya shigo ganin yadda Aishatu ke wahala. Da fargaba ta ishe shi a waje ya shiga kawai ana ta kiransa yaki sauraronsu. Aishatu na ganinsa ta soma kuka don ta sha wahala. Dr Abida tace Dr Rano ina jin ko CS zamuyi mata ne cibiya ta nade baby daya. Safar hannu ya saka ya tsaya gaban matarsa. Yana yi yana karfafa mata gwiwa ya yi dabararsu da likitoci ya warware cibin. Kusan rabin awa yana kanta kukan ma ta dena sai ga kan da ya fito. Dr Abida tana gefe tana kallon yadda Dr Rano ke lallaba matarsa. A hankali ya taimaka dan ya fito ya mikawa nurse, sai ga na biyun shima ya fito da taimakon Allah. Yana yi mata sannu ta sake wani nishin sai ga na uku. Bakinsa yaki rufowa cewa yake ku sa musu shaida. Aish har uku kika haifa. Ya koma ya rungumeta...i love you. Sannu yanzu ki rufe idonki a hankali zanyi miki dinki kinji ko. Ihunta yasa Dr Abida da nurse din fita.
Gidan Mama a cike da yan uwa da abokan arziki yan barka don taki yarda Aishatu ta koma gidanta. Huzaifa yayi ta mita har ya hakura. Ranar suna kuwa a gidan Mama akayi saboda yafi fili. Jamaa sun taru sosai harda su Yahanasun Fahad da Anti Maryam matar wansa. Itama Yahanasu da karamin cikinta. Yara sunci sunan Abdulrahman, Abdulrahim da Abdulrashid. Anyi taro lafiya an tashi lafiya. Bayan wata shida Yahanasu ta haifi yarta mace. Bakin fahad kamar gonar auduga. Ya fidda rai da samun haihuwa a da. Aisha ya sawa babyn bisa shawarar Yahanasu. Suna ta zumuncinsu. Itama sunje suna Aliyu ya kankame baby Aisha har yana cewa Maama wannan ce baby Aish dina ko irin yadda Abba yake fada miki. Aka yi dariya ita kuwa sai kunya.
A gida tana bawa Huzaifa labari yace ai kyan da ya gaji babansa. Amma dai tun wuri ya sake sunan nan. Huzaifa ne kadai mai Aish. Suka rungume juna tace Babyn Aish....a hankali yace naam. Tace yau na fada maka ina sonka kuwa? Yace eh amma yana da kyau a yawaita maimaitawa. Allah Yasa mu dace.
ALHAMDULILLAH
Godiya ta musamman gareku yan uwana wadanda suka bani kwarin gwiwar rubutun nan.
💞 Zainab, Shukriya, Rumanatu, Sadiya and Ibtihal.
Nagode sosai Allah Yabar zumunci.
Sai kuma yan uwana dukkan masu karanta books dina. Wadanda na sani da wanda ban sani ba. Fatan alkhairi garemu baki daya. Kamar su Rufaida Omar's fans, Matan Albarka, Mu kula da addininmu mata, Classic Ladies Novel, home of novels, modern hausa writters da sauran yan uwa da abokan arziki. Allah Ya bamu rayuwa mai albarka.
Batul Mamman💖