Sunday, 29 May 2016

MEYE DALILIN KA

  MEYE DALILINKA ๐Ÿ’ž 1

Bismillahir Rahman Rahim


Haj Munnira ta tsaya ta karewa dakin kallo cikin takaici komai a hargitse gado kamar yara biyar ke kwana, filo daya a kasa da kayan bacci sai ledojin sweet dana capri sonne. Gefe kuma wardrobe shima a bude duk an hargitsa har wasu kayan sun fado kasa. A takaice dai dakin tamkar yayi sati baa gyara shi ba. Me zan mata ne idan ta dawo abinda take ta tambayar kanta kenan.  Can dai ta kwalawa Inno kira Inno yaushe rabon da a share dakin nan? Inno tana raba idanu tace Hajiya yau ne kawai ban share ba kuma zan gyara shi tas kafin ta dawo har bandakin duk zan wanke.
Hajiya Munnira tace ni ba dalilin da yasa na tambayeki ba kenan jiya ba tare muka gyara ba dake har na shirya mata wardrobe? Haka yake Hajiya ta bada amsa. Hajiya tace to wallahi idan ta dawo kika nemi hanani dukanta zamu saba dake na fada miki tun wuri. Tana gama magana ta fita. Nan da nan Inno ta hau kwashe kaya zata fara gyara.

Da gudu ta shigo tayi jefa da school bag dinta a kasa, lunch box ma ya bi shi sai takalmi wanda ta rinka  cilla kafafunta sai da suka fita da kansu. Na kafar hagun yana fita sai a kan fuskar Haj Munnira. Ai tana ganin haka tayi saurin durkusawa kasa tace Assalamu alaikum Ummana na dawo na sameki lafiya? Ko kulata batayi ba don in da sabo to ta saba da halin Khairi na bada hakuri da nutsuwa idan tasan bata da gaskiya wayar rediyo ta ciro tayi kan tilon yar tata. Tsoron duka ne da Khairi kamar me don haka iyakar muryarta ta bude tana ihu. Ummana kiyi hakuri kada ki dokeni wallahi na dena jifa da takalmina. Inno ta fito da sauri Hajiya kiyi hakuri. Ya mukayi dake Inno? Ta tambayeta cikin fushi sannan ta cigaba. Yarinya ita kadai ta rinka caja min kai. Ke ba namiji ba Khairi amma gara wasu mazan da ke. Dakinki kamar filin dambe ga kazantar tsiya. To daga yau babu me sake yi miki shara ko wankin toilet da gyaran kaya kuma kullum sai na tabbatar kin gyara zaki fita makaranta. Khairi ta kalli Umman tata tace na dena Umma daga yau Allah kuwa. Ni tashi ki bani wuri. Tana tafiya Umma ta lura hijab dinta ya yage ta baya tace Khairi me ya sami hijab din? Umma kusa ce a seat dina ina tashi ji kike kyeeeet. Inno abin dariya ya bata ita kuwa Umma bata jira ta rufe bakinta ba ta bi ta tace sai dan banzan baki kamar reza zo nan ta sake daga wayar zata dake ta.

Yi hakuri Anti taji an fada daga bakin kofa. Da gudu Khairi taje ta rungume shi. Umma tace ai yau ko zaka ari baki Ahmad sai ta zane yarinyar nan. Khairi wadda tuni ta fara hawaye ta kankame shi Uncle Ahmad don Allah ka bata hakuri. Dan murmushi yayi wanda ya kawata kyakkyawar fuskarsa yace Anti Munnira kiyi hakuri kinga yarinya ce idan ta girma zata dena.
Umma tace kayya dai ai ba alama ta maida kallon ta ga Khairi tace idan kika girma a haka bana jin zaki sami mijin aure.

Subhanallahi Inno tayi saurin fada tace haba Hajiya kada kiyi wa yar tawa baki mana. Umma ta tabe baki ta zauna bakin kujera tace yo yar shekara tara tana wannan abin ai ban ga ranar girman ta ba. Ahmad shima zaman yayi yace ni ina sonta Anti so bata da matsalar miji. Ya kama hannun Khairi kinsan bana son kazanta ko? Eh ta bashi amsa. To daga yau kada ki bari na sake jin zancen rashin tsaftarki. Tayi murmushi har gibinta ya fito. Ai na dena daga yau Uncle Ahmad. Tashi tayi taje ta cire uniform dinta sai dai kafin ta kai dakin yana kallonta tasa hannun damanta a hanci ta share hannun a rigarta. Wayar hannun Umma ya karba ya bita yana cewa ashe ni zan fara zaneki tana gudu. Umma dariya tayi tace wai! Gaskiya Ahmad kayi sa'ar mata.




Batul Mamman

 ๐Ÿ’•  MEYE DALILINKA ๐Ÿ’ž 2


Filo ta jawo ta dora kanta ta cigaba da karanta wasikar jaki. Gadon duk books ne da handouts ko ta ina amma yau ma tunanin Uncle Ahmad ta tashi dashi ta kasa mayarda hankali tayi karatu gashi test gareta gobe.

Kausar ce ta shigo dakin ta daka wa Khairi doka a cinya ba shiri ta tashi zaune tana murza wurin. Tace to muguwa me nayi miki. Kausar ta zauna kan gadon tace tun dazu nake sallama baki amsa ba kina ta juyi kamar waina. Nasan bazai wuce tunanin Uncle Ahmad ba. Har kin manta muna da test gobe ko? Ni karatu nazo muyi malama tashi ko na kara miki ta sake daga hannu.

Wani hoto ta nunawa Kausar din wanda Uncle din ya turo mata ta whatsapp. Shi da yaransa ne Iman da Sadiq a bakin ruwa. Komai hassadar mutum dole ya yaba domin duk sunyi kyau. Kausar ta ajiye wayar a gefe tace Khairi har yaushe zakiyi ta son wanda bai san kinayi ba? For God's sake he is married with two kids. Murmushin yake Khairi tayi tace Allah Kausar ban damu na zama ta hudu a gidansa ba. Ni tunda yace wa Umma shine mijina nake gina rayuwata dashi. Tun bansan so ba har na sani duk akansa. Kausar ta tabe baki to zan cigaba da taya ki addua idan ya dawo kasar hankalinsa ya dawo kanki. Allah Ya amsa Khairi tace sannan suka fara karatu.

********************

A falo ta hadu da Malam yana ta rubuce rubuce ga Qur'ani da sahihul muslim a gabansa yana kokarin hada  khudbar juma'a ya turo glasses dinsa can karshen hanci. Tsugunawa tayi ta tura masa shi ciki sannan tace Malam ya aiki? Lafiya kalau ya bata amsa yana murmushi Ummulkhair kin mayar dani kakanki ko? Tace to idan babu kaka ai da uba ake yi. Ajiye biron hannunsa yayi yace tun jiya nake aikawa kizo kina wasan buya dani. Keya ta sosa to ai nasan dalilin kiran. Umma wadda ta shigo falon lokacin tace to sarkin zance meye dalilin. Shiru tayi ta sunkuyar da kanta kasa Malam yace zauna ayi maganar a gabanki Munnira.

Ya ce to a ajiye wasa a gefe Ummulkhair ina zancen miji ya kwana? Na baki dama ki fitar da miji amma abin mamaki duk yadda ake zuwa samuna akan maganarki har yau babu wanda kika amince dashi. Umma tace to ai Malam irinsu Khairi ba'a basu wannan damar ko cikin almajiranka kawai ka bawa daya. Almajiri kuna Umma? Khairi ta fada tana zaro idanu sannan tacewa Malam ya kara mat lokaci. Ni dai ba haka naso don a yadda na tsara kina gama secondary zan aurar dake amma tunda hakan bai samu ba gaskiya bana son ki cika shekara 23 a gabana. Alh Mahe yazo dazu kina makaranta akan maganarki da dansa Tahir kuma na amince. Gabanta ne yayi mummunan faduwa

********************

Kuka take a daki Inno tana ta bata hakuri Khairi tace Inno ta yaya zan fada musu Uncle Ahmad nake so? Inno ta cigaba da share mata hawaye kiyi hakuri 'yata da yardar Allah komai zai zo da sauki. Yau kwana hudu da maganar nan amma baki da aiki sai kuka? Ina baki shawara da kada ki taba bijirewa Malam domin sabawa mahaifi ba karamin hatsari gareshi ba.

A daidai wannan lokacin Dr Ahmad ke saukowa daga jirgi shi da matarsa Mufida da yaransa guda biyu bayan shekaru uku da yaje yayi wani course a kasar Singapore.





Taku Batul Mamman ce


๐Ÿ’• MEYE DALILINKA ๐Ÿ’ž 3

Ko da wasa babu wanda ta bari ya san sirrin dake boye a ranta daga Inno sai aminiyarta Kausar Mukhtar wadda makota suke tun suna yara. Tare suka yi secondary sai kuma suka nemi course daya a jami'ar Bayero. Khairi da Kausar wadanda kawayensu ke kira da 2K basa boyewa juna komai. Tsayinsu kusan daya sannan dukkansu suna da matsakaicin haske. Khairi akwai kyau kuma akwai fara'a idan ka cire lokutan da take tunanin Uncle Ahmad da wuya ka ganta fuskar nan babu murmushi. Da kuruciya dai anyi fitina yanzu da ake ji da 'yan matanci kuwa nutsuwa ta danzo musamman da take 'yar daya taga cikin malaman da ake ji dasu a kano Dr Abdallah Saraki. Sai dai ba'a raba ta da tsokana da tara shirgi a dakinta. Ummulkhairi Abdallah Saraki.

Ta gama kukanta na yamma yau saura na darw kamar yadda ta tsarawa kanta kullum tunda Malam yayi mata zancen Tahir. Idar da sallar ishan takeda wuya Inno ta shigo dakin da sauri har tana tuntube da takalman da Khairi ta cire a bakin kofar daki. Albishirinki 'yata ta fada tana wangale baki. Goro Inno ta amsa mata a sanyaye. Inno tace tunda naga kamar ban burgeki ba to kije falon Malam ana kira. Dammm taji gabanta ya fadi. Har tasa hijab wanda ya dace da kayan jikinta sai ta fasa ta jawo wani a kayan wanki ya gama yamutsewa ga manjan wainar filawar da suka ci ita da Kausar a gidan Lami makociyarsu. Tasa ta fita idan Tahir ne tasan dole ya ce ya fasa. Yau kazanta zata yi mata rana ta fada a ranta tana murmushin mugunta.

Qamshi ne mai dadi ya bugi hancin Khairi tana daga labule suka hada ido. Yarrr taji a jikinta kamar wuta ta ja ta. Ta bude baki galala tana kallosa...wallahi ya kara kyau da haduwa ta fada a ranta. A zahiri kuwa ta kasa magana tana karasa shigowa ya mike kamar an mintsine shi. Kada ki karaso wurin nan ya fada yana mata wani irin kallo. Umma ma cewa tayi Khairi meye wannan? Sai a lokacin ta kula da umman ta. Tace Umma me kika gani? Uncle Ahmad yayi tsaki ni duk na zata zanzo naga kina ji da gayu kin girma ashe kina nan a Khairin kazanta. Subhanallahi ta fada sannan ta koma ciki da gudu. Ba komai bane illah hijab din korar Tahir da ta saka sai dai tana dawowa falon Umma tace ya tafi gida domin dare yayi dazu jirginsu ya sauka.

Da wani kukan ta koma daki tana share kwalla taga bakuwar number na kiranta. Tana dauka bayan tayi sallama taji muryar dake sanyaya mata zuciya. Khairi ya kira sunanta (kai sunan ma daban yake a bakin Uncle ta fada a zuci). Naam Uncle shine ka tafi kafin na dawo ko? To ai kece kanwata ina ta dokin surprising dinki shiyasa ban fada miki ma zamu dawo ba kawai sai na ganki kamar anyi wasan kura dake. Murmushi tayi ai na zata Tahir din da Malam yace zai aura min ne yazo. Yanzu dai a bar maganar hijab mai datti don yanzu na zama yar gayu. Ina Anti Mufida da su Sadiq? Lafiya kalau suke ya bata amsa. Gobe kizo ku hadu dasu Umaima ku taya Mufida gyaran gida zan turo azo daukarki da safe nasan sunday ne ba school.

Ranar Khairi bacci mai dadi tayi harda mafarki ta haifawa Uncle Ahmad yan biyu. Gari na wayewa ta kira Kausar a waya ta bata kyakkyawan labari. Suna ta shirmen murna domin kuwa dai ba'asan suna yi ba. Kafin takwas na safe ta gama shiryawa taje ta gaishe da itayenta. Malam ya kalli Umma yace yau lafiya kuwa Ummulkhair take? Ina wucewa naji tana share dakinta. Umma tace ai tun jiya Ahmad yace zai turo a dauketa shine take ta doki.

Abincin ma da kyar taci tana ta kallon agogo shi kuwa driver din gidan Alh Aliyu wanda wan mahaifin Khairi ne baizo ba sai 9:30. Kafin yazo kuwa ta kira Umaima da Ummi yafi a kirga su gane mata ko ya taho. Hijab dinta yau light blue ne kamar atampar jikinta. Ba wata kwalliya sosai tayi ba tunda Malam bazai yarda da hakan ba amma ta tabbatar tayi fes yadda Uncle zaiji dadi.




4rm Batul Mamman

 ๐Ÿ’• MEYE DALILINKA ๐Ÿ’ž 4

Gidan Baba Aliyu ya wuce da ita suka dauki Umaima suka wuce sabon gidan Uncle Ahmad a unguwar 'yan kaba. Mufida tayi farinciki da ganin su tare suka hadu da kannenta suka share gidan tunda kafin su dawo an riga an gama jeren komai.

Baba Aliyu shine babba a gidansu, Malam ke binsa sai Hashim wanda ya gamu da lalurar paralysis sakamakon fadowa da yayi daga bene shekaru 35 da suka wuce. Baba babban dan kasuwa ne yana da mata biyu da Hajiya Karima wadda ake kira Hajiya shekararsu 5 da aure sannan ta haifi Ahmad daga shi bata sake haihuwa ba. Sai Hajiya Zainab wadda ya aura daga baya ta haifi Amina, Rahma, Umaima da Hashim.  Suna kiranta da Momi. Suna zaune ne tare da matar babansu Yakumbo. Ita bata taba haihuwa ba amma ko da iyayensu suka rasu ta kula dasu sosai musamman Baba Karami wato Hashim  wanda ya gamu da lalura. Haj Zainab amaryar Baba 'yar kanwar Yakumbo ce.

********************

Khairi tana yiwa Umma tsifa Inno ta shigo cike da fara'a tace Hajiya yanzu mai gadi yace na sanar ana sallama da 'yata. Shiru tayi kamar bata ji me akace ba sai da Umma  tace Khairi bazaki tashi bane? To sakar min kaina ta fada tana kokarin daura dankwalinta. Tashi Khairi rayi taje ta dauko hijab ta saka. Tana dawowa falon Umma tace kije falon bakin Malam ki same shi. Tahir ne wanda an sanar dake babansa ya yi magana.

Sallama tayi ta shiga falon hannunta da tray wanda ke dauke da juice, ruwa da meat pie. Bayan ta ajiye masa a kan centre table ta sami kujera can nesa da shi ta zauna ta hade fuska ita kada ma ya kawo mata wargi. Yanayin Khairi dariya ya bawa Tahir amma sai ya gintse yace mun wuni lafiya? Lafiya ta bashi amsa a dakile.

Haka suka zauna suna kallon kallo. Tahir yana karanta wata journal da ya gani a kan kujera ita kuwa Khairi waya ta dauko tana dannawa.

Kusan mintuna 15 suna haka daya gaji da shirun ya ajiye jaridar ya dubeta. Ina fata Malam ya sanar dake dalilin zuwana. Gyada kai tayi kamar kadangare, a ransa yace lallai ina da aiki. Ya cigaba da magana kamar yadda aka sanar dake suna na Tahir,  ina aiki da Nigerian airways ni pilot ne. Ina da yayye uku da kanne biyar. Ina fata wannan ya isheki for now, uhm kawai tace. Ganin bata da niyyar magana yasa shi mikewa har ya kusa bakin kofa yace oh ni wane laifi na yiwa Alhaji ya rasa matar da zai nema min aurenta sai bebiya. Kafin ta bashi amsa har ya fice.

*******************

Kwanan Tahir hudu da zuwa Khairi ko zancensa bata so taji anyi a gidansu. Kausar kuwa ta sami abinyi kullum sai ta tsokane ta. Ta kusa gama karatun da take na bayan sallar isha Indo jikar Inno ta leko tace Umma tace kizo inji Tahir.
Ai tuni ta kara karatun, bayan kamar minti goma Umma da kanta tazo cikin fada tace bana son wulakanci Khairi, ganin karatun dai take yi tayi wata 'yar dariya tace haba Khairi ai ko ban fada miki ba kinsan karatunki babu lada don kuwa babu niyya ki tashi tun ranki bai baci ba. Yace sallama yazo yi miki zaiyi tafiya yau. Ko da ta dago kanta idonta cike yake da hawaye. Ta yaya zata fahimtar da iyayenta akwai wanda ta riga ta mallakawa zuciyarta?




Batul Mamman๐Ÿ’–


 ๐Ÿ’• MEYE DALILINKA ๐Ÿ’ž 5

Saroro Umma ta tsaya tana kallonta. Khairi ko dai aljanun ne dake da gaske? Daga magana sai hawaye, to daure kije ki dawo kizo muyi magana kinji 'yar Umma. Share hawayen tayi ta fita Umma ta bita da ido. Bari Malam ya dawo dole asan abin yi.

Yauma sallama tayi a hankali ta shiga falon. A tsaye ta tarad da shi yana sanye da kayansa na matukan jirgi. Sunyi masa kyau don sai yau ma ta kalle shi sosai. Dogo ne sosai don yafi Uncle Ahmad tsayi,kalar fari ne amma har yafi Uncle din nata kai kila ma zabiya ne ban kula ba. Gashi yana da kyau amma dai Uncle ya fi shi. Duk wannan zancen zuci Khairi take shi kuwa Captain Tahir kallonta kawai yake. Ko ba komai tana da kyau kuma 'yar Malamin da yake matukar jindadin tafsirinsa ce. Littafin aljihunsa ya dauko mai suna Sign Language ya dan duba wani page sai yayi mata alama da hannu. Dariya ce ta kwace mata ganin yadda ya dage yana ta motsa hannuwansa. Sai da ta gama tace idan ka gama excercise din ka fada min. Shima dariyar yayi yace ai na zata bebiyar gaske ce.

Kafin ta sake magana Uncle Ahmad ya daga labulen falon ya shigo da sallamarsa rike da ledoji biyu a hannunsa. Gaban Khairi har faduwa yayi da ta ganshi tayi saurin mikewa tsoronta kada ganin Tahir yasa kara lalata chance din ya gabatar mata da soyayyarsa. Su biyun sun mika wa juna hannu sun gaisa Uncle yace Khairi shine baki fada min zanyi inlaw ba. Ya juya ga Tahir gaskiya nayi murna dana ganka Allah Ya tabbatar da alkhairi sai kayi a hankali kanwar tawa akwai kiriniya bata san ta girma ba. Tahir mikewa yayi yace to babban yaya ni zan gudu dama a hanya nake idan Allah Ya dawo damu lafiya zan nemeka. Allah Ya tsare ya fada sannan yace ni sunana Ahmad shi kuma yace Tahir.

Tare suka fita daga falon Khairi ta koma ta zauna tana tunane tunane har Uncle ya dawo. Ga tsarabarki ta Singapore ya fada yana mika mata ledojin hannunsa. Ko dago kai bata yi ba sai alamar sheshshekar kuka yaji. Khairi me ya sameki ko kukan rabuwa da masoyi kike yi? Kamar ya kara zugata ta sake bare baki tana kukan ta mike ta fita daga falon yana kiranta bata amsa ba.

Su Umma ma haka ta wuce su. Uncle Ahmad na fitowa Inno tace masa lafiya? Nima daga na fita raka bakonta ta dawo na tarar tana kuka. Kila ko don zai tafi ne. Inno ta girgiza kai anya kuwa? Yau ne fa zuwansa na biyu, akwai abinda ke damun yarinyar nan. Umma wadda ita kanta abin ya fara damunta tace ka fara tambayarta Ahmad idan abin ya faskara zan sanar da Malam.

*******************

Tun ranar da ya ga wannan kukan Ahmad ya rasa sukuni. It is so unlike Khairi ta bar abu a ranta har ya sata kuka. Duk cikin kannensa yafi shaquwa da ita kuma bata boye masa komai amma wannan karon yayi yayi taki magana. Bayan ya gama ganin last patient dinsa na yau ya yanke shawarar ya sami Malam suyi magana idan bata son Tahir abar zancen. Bazai iya jure rashin walwalar Khairi ba.

Kausar tana ta ban baki da rarrashin kawarta tace Kausar son Uncle ya zame min cuta. Zuciyata kamar zata fashe nake ji tunda ya dawo abin ya karu. Ko kinsan yanzu har waya suke da Tahir tunda ya dawo daga tafiyar da yayi kwanaki sun dinke kamar wasu abokan da suka dade. Kausar gama kwasar tuwon da take tace to Khairi idan abin nan bazaki iya hakura ba why not ki sanar da uncle Ahmad din. Kai bazan iya ba idan har bai fahimta don kansa ba shikenan.

*******************

Kwance yake yana kallon kyakkyawan hatonta a wayarsa. Hakika Jalilah taci amanarsa. Ita din mai kyau ce kuma tasan tana da kyan. Sati uku ya rage ayi bikinsu Yayanta yazo har gida ya dawo musu da kudinsu da kayan lefe wai ta fasa. Ya jima yana maimaita abinnan a ransa yaje gidansu kuma taki fitowa. Sati ukun na cika yaji sanarwar aurenta a kafafen yada labarai  da Senator Bukar Danbuba. Wannan dalilin yasa ya tsorata da lamarin mata domin iyakar so Jalilah ta nuna masa na shekara ukun da suka yi tare. Shiyasa ya dena neman kowacce mace sai yanzu da Alhajinsu ya nemar masa Khairi. Sai dai yarinyar ta zame masa kamar karatun littafin da baa ganewa. Abu daya ya sani shine tun ranar da ya fara zuwa ta shiga ransa




Batul Mamman๐Ÿ’–

๐Ÿ’• MEYE DALILINKA ๐Ÿ’ž 6

Khairi ta duka tana kokarin turawa Malam glasses dinsa Umma ta kallesu tace ni cikinku bansan wanda yafi wani ba, kullum ka turo glass gaba zata mayar maka ciki amma baka fasa turowa. Ke kuma kinsan ko kin tura masa ciki gobe ma zai kara amma ba kya gajiya. khairi ta zauna kusa da Malam tace aini ina jin dadin turawar shima Malam yace inayi ne kawai don jin dadin Ummulkhairi na. Suna cikin dariya suka ji sallamar Uncle Ahmad da Mufida tare da yaransu.

A take taji jikinta ya fara rawa. Ina zata kai son Uncle? Yanzu abin har ya kai tayi loosing composure dinta idan yana kusa?

Sun gaisa da kowa sai dai ta kula da yadda Mufida ta dan daure fuska amma bata kawo komai a ranta ba don tasan ba soyayya take da Uncle ba. Uncle da Malam sun koma daya falon inda Uncle Ahmad ke yi masa bayanin abinda ya kawo shi. Murmushi malam yayi irin na manya yace to Ahmad mai kanwa munyi magana da kanwar taka sai tace min ranar haka nan ta tashi da bacin rai. Na fada mata ta rinka azkar safe da yamma. Ya cigaba da cewa Ummulkhairi ta gama girman da zata yi a gida kuma nasan iyaka abinda Allah Ya hore mana mun bata tarbiya abinda ya rage kawai aure ne. Ina fata Tahir ya zama mijinta. Ahmad ya gamsu da maganar Malam kuma a yadda ya fahimci Tahir yana ganin kamar mutumin kirki ne.

********************

Ajin tun daga waje ake jin hayaniya kasancewar babu malami. Kausar ta dubi Khairi tace 'yar uwa wata shawara zan baki game da maganar Uncle don na lura har yau baki da nutsuwa. Kina istikhara kuwa? Ji wata irin tambaya khairi ta fada to ke yanzu idan nace bana yi ai anyi asarar kudin tara. Kausar tayi murmushi ai nasan kina yi amma da wuya idan ba kina yi ne kawai don samin abinda kike so ba ba domin neman zabin Allah ba tunda kin dade da yankewa kanki wanda kike so. Shiru tayi alamar tunani sannan tace gaskiya ne Kausar amma daga yau zan canza niyya. Banda niyya ina ganin shima Uncle ki koyi dena shiga sabgarsa da yawa kamar wayar da kuke yi kullum da yawan fara'a kamar gonar auduga idan kin ganshi. Khairi tace tohh wani sirrin ne kuma da hakan. Eh ta bata amsa sannan ki dan bawa Captain chance kiga ikon Allah.

Ta karbi shawarar kausar yanzu ba ta kiran Uncle a waya kamar da idan ya kira ma sai taki dauka. Amma hakan ba karamin punishment ta dauke shi ba. Shi kanshi Uncle Ahmad abin ya fara isarsa. Ko haduwa suka yi ta dena rawar kan da take yi.

Tana zaune da Tahir a waje saboda zafi gashi injin gidan yaki kamawa. Yauma ta kasa sakin jiki sosai amma dai tana amsa shi idan yayi magana. Wayarta ya dauka wadda ke kan wani karamin table da ta ajiye masa lemo. Amma dai kasan daukan kayan mutane ba da izini ba babu kyau ko? Eh ya bata amsa tare da cigaba da kokarin kiran wayarsa da tata domin ya sami number dinta. To ai sai ka ajiye min tunda ka sani wannan karon cikin fushi take maganar. Karkari dai ki kirani barawo kuma ba kaina farau ba. Murmushin da yake yi ne ya bata haushi tace me kake nufi? Hmmm Khairi kenan i love your eyes idan kika kalli mutum sai yaji kamar ya gudu dake. Ganin yana neman canja topic din ta tashi zata koma ciki yace barauniya....cak ta tsaya sai kuma ta waigo kafin tayi magana yayi yar dariya barauniyar zuciyata ina zaki ba sallama.

Bata iya yin fadan data yi niyya ba sai ta shige gida. Yana tashi shima gidan ya nufa sai dai a hanya wayarsa tayi ta ringing. Yana parking a cikin gidansu ya duba yana da 13 missed calls. Kira yayi don bai gane nunber din ba.
Hello yaji an fada ana daga wayar.. ko cikin bacci dole ya gane muryar nan duk da ya shekara biyu bai ji ta ba. Katse wayar yayi tare da dafe kirji. Meye dalilin da yasa Jalilah take kiransa a yanzu?



Batul Mamman๐Ÿ’–


 ๐Ÿ’• MEYE DALILINKA ๐Ÿ’ž 7


Yau kuma me ya faru kika shigo da fushi 'yata? Khairi ta kalli Inno idanunta cike da hawaye tace Inno ko sau daya Uncle bai taba kallo na da wata manufa ba bayan kanwarsa da ya daukeni. Kada ki manta na fada miki ki bin iyaye wajibi ne idan kika bi su zaki ga amfanin yin hakan 'yata. Ki daure ki bawa Tahir din dama kiga abinda Allah Ya tsara miki. Share hawaye tayi da dankwalinta Inno in Allah Ya yarda zanyi kokari na cire Uncle a raina. Zan koyawa zuciyata son zabin Malam. Ni dai ki taya ni addua.

Yana shirin kwanciya ya sake jin waya ta shigo ko da ya duba number din da Jalilah ta kira shi da ita ce dazu. Wannan karon ya dauka yayi sallama.

Tahir nice Jalilah. Ta fada cikin siririyar muryar jan hankali.

Lafiya kike kirana a daren nan?

Lafiyar kenan my one and only. Shiru tayi tana jiran amsar shi.

Yaushe rabon da yaji muryarta balle ma ta ambace shi da wannan sunan. Disconnecting din call din yayi ya kashe wayar gaba daya. Me Jalilah ke nema tare dashi bayan irin cin fuskar da suka yi masa?

********************

Gidan Baba Aliyu Umma da Khairi suka nufa kafin azahar bayan Hajiya ta kira su bayan asuba ta sanar dasu haihuwar Rahma. Yakumbo ta gani tana yiwa baby wanka tace to yar tsohuwa ki wanke ta da kyau dai kuma kada ki fesa mata goro. Hajiya dake ta fama da Rahma taci abinci tace to yar nema daga shigowarki zaki fara ko. Da kin kyale ni da ita Karimatu in gama da 'yar ta ta in buge bakin. Wa zai buge miki baki khairi taji ana fada daga bakin kofa. Tana juyawa suka hada ido bata bashi amsa ba sai ta gaishe shi ta mike zata fita. Au yau bakya son na tare miki fadan ne? Ya tambayeta sai dai bata bashi amsa ba tace bari naje wurin Baba Hashim mu gaisa. Kallonta kawai yayi gaba daya Khairi ta canja masa ya rasa dalili amma ko kadan abin baya masa dadi.

Dariya suke ita da Umaima suna zaune gaban wheel chair din Baba Hashim yana basu labari. Duk basu kula da tsayuwarsa a wurin ba sai da ya danyi knocking kofar yace Baba Hashim wane labari kake basu ne ba'a hada damu ba? Shigo Ahmad ya fada yana murmushi. Labarin kiriniyar ka nake basu. Ai mun sami na tsokana ko Khairi? Umaima ta tambayeta ita kuwa kokarin tashi take tace ina zuwa zanyi waya ne.

Idan wasa ne ya soma yin yawa. Uncle Ahmad ya fara gajiya da yadda Khairi take share shi. ko a waya amsar maganarsa bata wuce eh ko a'a wanda ko kadan ba haka suka saba ba.

******************

Toilet ta shiga tayi kuka mai isarta sannan tayi alwala ta diga maganin ciwon ido mai sa ido yayi haske. Ba tun yau take amfani dashi ba indai tayi kukan Uncle sai ta diga. Khairi kenan
Rashin kula shi ba karamin damunta yake ba sai dai tasan hakuri ya zame mata dole. Kamar ba ita ba ta fito ta shiga dakin Momi tayi sallah.

******************

Shi kan shi bai sani ba amma bayan mintuna kadan yake dauko waya ya duba ko text dinta ya shigo. Sau uku kenan yana mata text yau na tsokana ta share. Wai ni wayar wa kake jira ne Abban Iman? Tun dazu kake abu daya. Abu daya kamar me fa Mufida. Kallon ka raina min hankali tayi mishi kafin ta bashi amsa kallon wayarka mana.  Its nothing to worry about bani ruwa mai sanyi dai. Ita tasan akwai abinda ke damunsa amma idan bazai fada ba zata jira.




Batul Mamman ๐Ÿ’–

 ๐Ÿ’• MEYE DALILINKA ๐Ÿ’ž 8

Sati biyu kenan da khairi ta fara ja da baya da Uncle Ahmad kuma ta daure tana kula Captain sai dai ta rasa sukuni da walwala kamar yadda ta saba. Wannan abu kuwa babu wanda baya damu a gidansu. Babbar matsalarta yanzu bata wuce zafi da kirjinta yake yawan yi sai taji kamar zuciyarta zata cika mata kirji. Babu wanda ta iya sanarwa wannan hali da take ciki iyaka ta dage da yawan addua.

Ba irin wayar da Jalilah bata yiwa Tahir amma yaki saurararta daga karshe tayi masa text wanda a ciki take ta sanar dashi aurenta ya mutu tana so su dawo da soyayyarsu. Ji rainin hankali..tamkar ta aikawa dutse haka ya share zancen.

Iyaye sun gama magana an yanke shawarar yin bikin khairi bayan babbar sallah lokacin Tahir zai dauki hutunsa na shekara. Yana jindadin yadda khairi take bashi hadin kai suyi hira wadda bata wuce zancen makaranta, kausar da uncle Ahmad. Bai taba kawo komai a ransa ba sai dai ya fahimci kamar tana cikin damuwa wadda bata so a sani.
*****************

Ina kuma zaka je daga dawowarka Abban Iman? Wani kallo yayi mata bai amsa ba ya cigaba da saka safa a kafarsa. Abban Iman magana fa nake yi maka 'yan kwanakin nan na kasa gane kanka idan anyi magana kace ba komai. Tashi yayi ya dauki keys dinsa ya fita ya barta tsaye saroro. Shirun nasa shi yafi bata tsoro don a yadda take da Ahmad bata magana biyu baiyi abinda take so ba. Idan ma wata yar isakar ke neman daga mata hankali to wallahi tayi kadan. Dole ta koma wurin Mai Dafai ya bata wani sirrin malakar. Ahmad baya cikin mazan da mace zata sameshi taso rabuwa dashi.

A hanya yana ta sake sake a zuciyarsa. Damuwarsa bata wuce ta Khairi da yadda ta canza masa lokaci guda.

Khairi ki fada min gaskiya ko baki son aurena ne? Wani murmushi tayi wanda ya kara haska kyawunta wa ya fada maka Captain? Kefa kin saba amsa tambaya da wata tambayar. To ai kaine kamar wani lauya ka cika tambaya baka san ance wala ta jassasu ba. Tana magana tana yar dariya sai dai Tahir ba yaro bane yasan dariya kuma ya san yake. Lemo ta zuba a cup zata mika masa Indo da Uncle Ahmad suka shigo falon. Sakin cup din tayi ba shiri da jin muryarsa yana sallama. Duk su ukun kanta suka yi suna tambayar ko bata ji ciwo ba don ya tarwatse ko ta ina.

Allah Captain babu abinda ya same ni ta duka tana matse kasan skirt dinta. Abin ya bawa Ahmad mamaki kamar bata ganshi ba taki amsawa yana magana. Tahir ya lura da abinda tayi sai ya mika masa hannu suka gaisa. Mikewa tayi bari na gyara jikina na dawo. No ba sai kin dawo ba Ummulkhairi zan tafi kinga tara tayi. Wani murmushin tayi to kana tsoron dare ne? Gidan uncle fa yafi naku nisa amma kaga yanzu yazo. Ahmad kaji kanwarka ko wato gidanmu ne banda ita. Ganin yadda suke wasa yasa yaji ransa ya kara baci. Da shi kadai khairi ya kamata tayi wasa irin haka. Kuji karfin hali. Wato ko kunyata ba kwa ji ko. Tahir yana dariya yace tuba muke yi Uncle. Sai da safe Khairi.

Yana fita ta kama hanya zata fita daidai lokacin da Indo ta dawo da tsintsiya da tsumma zata gyara wurin da khairi tayi bari. Ke ina zaki ya tambaya fuskarsa babu fara'a. Da yasan yadda ta kidime da ganinsa da bai tsayar da ita ba.




Batul Mamman ๐Ÿ’–

  ๐Ÿ’•  MEYE DALIINKA ๐Ÿ’ž 9

Yanayin da taga fuskarsa ya bata tsoro don da gani ransa a bace yake. Indo ya jira ta gama sharar da take bayan ta fita a hankali ya rinka tafiya ita kuwa yana matsowa tana kara tsorata. Sai da yazo daf da ita sannan ya tsaya yace Khairi wai menene matsalarki ne these days i dont understand you. Bakinta na rawa ba...ba kkkomai Uncle. Sami wuri ki zauna, ba musu ta koma ta zauna. Kada ki bata lokacinki wurin yi min karya irin yadda kike min kwanakin nan nasan akwai wani abu. Kanta a kasa don ba zata jure kallon da yake mata ba. Babu komai da gaske kawai yanzu ina dan jin kunyarka ne. Kin manta nine ma sirikinki Alh Mahe, malama ki saurare ni da kyau Allah idan na sake kiranki kika ki dauka ranki sai ya baci...kuma the next time kika yi pretending baki ganni ba..hmmm kada ki sake kawai. Yana gama magana ya fice ba ko sallama.

Da gudu ta tafi dakinta tana shiga tayi jifa da hijab da dankwalinta ta kwanta tana kuka. Yanzu haka Uncle Ahmad zai rinka yin abinda zai kara daukan hankalinta amma yana nuna halin ko in kula a kanta. Wani irin tari ne ya sarke ta tana cikin kukan tasa dankwalinta ta rufe baki sai dai tana cirewa ba karamin razana tayi ba domin kuwa jini ta gani a jikin dankwalin.

*******************

Mufida zaune a gaban Mal Mai Dafa'i ta fada masa duk matsalolinta da mijinta yace kada ki damu ga wannan kwalli da hodar da zarar kin yi amfani dasu kun hada ido to an gama magana. Tana ta washe baki ta mika hannu zata karba ya noke tare da mika mata daya hannun nasa. Haba ranki ya dade ai sai naji kafin alkalami a tukunna. Da sauri ta bashi kudin ta mike , a ranta kuwa tayi kwafa tace dani kake zancen Ahmad.

Yaya Kausar wai ki zo inji wani Tahir. Tahir kuma ta maimaita cike da mamaki. Ni yace ka kirawo Hassan? Eh ya gyada kai. To kace ina zuwa kuma ka gaishe da mamanku. Neman izini tayi a wurin mahaifiyarta sannan tace ya shigo. A farfajiyar gidan ta ajiye musu kujeru yazo ya zauna. Nasan zaki yi mamakin ganina duk da bamu taba haduwa ba ko. Haka ne ta amsa da 'yar fara'arta. Yanayinsa ya nuna alamun damuwa yace Kausar nine Tahir din da zai auri kawarki Allah baiyi mun hadu ba sai yau. Nan da nan ta mike Allah sarki ai ban gane ba...ina fata lafiya dai ko? Lafiya kalau in sha Allah. Ya nuna mata kujera dawo ki zauna magana nazo muyi akan Khairi. Jin haka ta dan sha jinin jikinta, ita kanta ta san khairi ta canja yan kwanakin da suka gabata.

Canjin da Uncle  Ahmad yace yana son gani daga gareta ya gagara domin kuwa Khairi yanzu yawncin kullum bata jindadi daga zazzabi sai ciwon kai. Malam ya shiga damuwa kwarai itama Umman khairi abin ya isheta domin gidan ya zama shiru ba hayaniyarta. Suna zaune a falo zasu yi karatun asuba da Malam ya turo glasses dinsa gaba sai dai sabanin yadda ta saba yau Khairi kwantar da kanta tayi a jikin kujera bata da niyyar tashi. Malam da Umma sai kallon kallo.


Batul Mamman ๐Ÿ’–

 ๐Ÿ’• MEYE DALILINKA ๐Ÿ’ž 10

Kasa karatun tayi ta tashi ta koma daki. Ba komai take gudu ba face tarin da ya taho mata kada su ga jini su tsorata. Ita kadai tasan yadda take ji a jikinta. Su Malam da ta baro a falo kuwa hankalinsu ya tashi. Gari na karasa wayewa Malam ya kira yayansa ya sanar dashi halin da ake ciki.

Uncle Ahmad yana ta sauri ya shirya saboda yana son fara biyawa ta sabon asbitin hadin gwiwa da suke shirin budewa shi da abokinsa wayarsa tayi kara. Momi ce ta sanar dashi Baba yana nemansa idan har bashi da patient da safe yazo yanzu. Yana ajiye wayar ya fita da sauri ko breakfast baiyi ba. Mufida tasha takaici domin maganin dubu ashirin zuba masa a abincin.

********************

Mamakin ganin Malam yayi a gidan da safe haka sai Baba Hashim da Yakumbo. Malam ya zayyana musu halin da Khairi ke ciki hankalin Uncle ba karamin tashi yayi ba. Kowa a wurin yana fadin irin canjin da ya gani a tare da ita. Baba ya dubi Ahmad yace to kaine babba wanda idan babu mu dole kasa ido kan kannenka kuma gaka likita dole kayi wani abu a kai. Kansa a kasa yace in Allah Ya yarda zanyi iya kokarina. Kuma tunda kun shaku sosai kayi kokarin sanin ko wata matsala gareta inji Yakumbo.

'Ya'yan Alh Mahe ne suka zo duba Khairi domin Tahir ya sanar dasu bata jindadi. Wata kanwarsa tace antinmu anya ba ciwon tafiyar yaya kike yi ba. Duk suka yi dariya cikin karfin hali tace ai duk inda yake tare muke banda abinki. Haka suka tafi suna ta yabonta.

Daga wurin aiki gidan Malam uncle Ahmad ya wuce. Ya gaisa da Umma da take kitchen tace masa Khairi tana falo. Kamshinsa mai dadi ne ya fara dokan hancinta ta yunkura ta tashi zaune Uncle dina sannu da zuwa. Yauwa kanwata ya amsa mata a sanyaye. Khairi kin rame ji idanunki a loko. To kada dai kace min mujiya don ita ce mai ido a loko. Yana dariya yace ai fa ke din nan da bakinki. Ko ciwon karya kike yi ne duk kin wani tayar mana da hankali. Tsayuwar da yayi a gabanta yasa duk jikinta yayi sanyi shi kuwa wani irin kallo yake yi mata. Yadda yake ji game da kanwar tasa yau daban ne,yana tausayinta sanan yana tsoron rabuwa da ita. Rashin kula shi da take yi yasa ya kara sanin cewa Khairi is an important part of his life.

Uncle ka zauna mana ta fada kanta a sunkuye.kujerar da ke kallonta ya zauna. Khairi kafin ayi zancen asibiti don Allah ki fada min abinda ke damunki. Hawaye taji yana taruwa a idanunta sai ta kasa bashi amsa. Kinsan yadda muka damu da ke gaba daya amma cikin kankanin lokaci kin canja ga rama kamar ana tsotse ki. Murmushin da tayi sai da yasa zuciyar Ahmad bugawa da karfi...God Khairi is so beautiful. A zahiri kuwa cewa yayi ko aure ne baki so ko Tahir din? Babu ko daya Uncle malaria  ce ta sani a gaba. Duk kin zama makaryaciya ya fada yana kallon ta ido cikin ido tana kokarin kawar da kanta yace Khairi...wani iri taji har tafin kafarta. Ki kalle ni da kyau ki rantse baki da matsala...

Kafin ta bashi amsa tari ya sarke ta ga hawayen da take kokarin mayarwa. Uncle Ahmad tashi yayi da sauri ya dauko mata tissue yana cewa wanke ni zaki yi da virus din mura ko? Yana mika mata tissue din tayi wani tari mai karfi sai jini ya watso masa a gaban riga. Ita kuwa Khairi faduwa kasa tayi a sume.
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun shine abinda ya fada da karfi har Umma, Inno da Indo suka shigo falon da sauri.



Batul Mamman๐Ÿ’–


 ๐Ÿ’• MEYE DALILINKA ๐Ÿ’ž 11

Ganin halin da Khairi ke ciki Umma ta soma kuka ina zan sa kaina ni Munnira ta koma ga Uncle Ahmad don Allah kayi wani abu ita kadai gareni. Yadda suke ta kuka yasa shima ya dada rudewa. Daukarta yayi ya fita Indo tayi saurin bude masa mota yasa ta a ciki. Umma ta shiga gaba kan Khairi a cinyar inno suka nufi asibiti.

Tun kafin su isa ya kira wani abokinsa ya kwatanta masa halin da take ciki domin a tanadi kayan da ake bukata kafin su iso. Umma a gefe daya ta kira Malam sai da taji shiru bai dauka ba ta tuna yau alhamis yana yin karatu a masallacin Mus'ab ibn Umair a nan unguwarsu. Driver dinsa ta kira Lado ta sanar dashi idan Malam ya fito ya fada masa.

Ko da isarsu asibitin sake daukarta yayi abokan aikinsa suka yi masa jagora zuwa dakin da zai kaita. Yana dora ta akan gado sai ta fara aman jini idan tayi yunkurin aman sai kirjinta ya amsa. Haka Uncle ya rirrike ta tana amai tana hawaye duk kayansa sun baci sai dai ba ta su yake. Yana daga zaune bakin gadon ya rike ta yana bada command kamar wani soja. Daya ga kamar ta fara fita hayyacinta sai ya fara marin fuskarta da sauri Khairi stay with me, wani gumi ke karyo masa hasbunallahu wa ni'imal wakil open your eyes please. Karshen maganar dai da kuka ya kare ta. Dr Maina ne yaja hannunsa da kyar ya fitar dashi daga dakin. Tamkar karamin yaro haka ya zauna a kofar dakin yana kuka. Umma na ganin haka ta fadi a sume.  Ana kokarin dauke ta Malam da iyalan gidan Baba Aliyu suka shigo.

********************

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un shine kawai ake fada. Inno ce ta iya yi musu bayanin abinda ya faru domin Uncle Ahmad kai kawai ya rike yana zubar da hawaye saboda baya tunanin Khairi zata tashi. Bayan an sami kanta Umma ma ta farfado Malam da Baba suka tafi office din Dr Maina. A can suka tarar da Ahmad fuskarsa duk ta nuna alamun damuwa.

Baba ya sake kallon likitan cikin fushi wai nufinka karamar yarinya kamar Ummulkhairi ita ce da hawan jini da ciwon zuciya? Dr Maina ya dubi Uncle yace Dr Saraki ai na nuna maka dukkan binciken da mukayi. Malam yace to ni ba wannan ba ku fada min meye abin yi. Ina ganin ina maganin da aka bata ya sake ta sai mu tambayeta menene problem dinta. Me ta sa a ranta har ta kamu da wannan ciwon cewar Baba. Uncle Ahmad yace zan tambayeta Malam. Ku daure ku tafi gida a kawo abubuwan da zata bukata da mai kwana daya. Nima ba tafiya zanyi ba.



Batul Mamman ๐Ÿ’–
๐Ÿ’• MEYE DALILINKA ๐Ÿ’ž 12

sai da ta kwana uku ta dan fara dawowa hayyacinta. Duk yadda ake ta rarrashinta ta fadi matsalarta abu yaci tura domin kuwa cewa take babu komai. Ai da kunya tace tana son wani da namiji da bakinta. Musamman Uncle wanda bata taba ganin alamun zai mata son aure ba.

Kausar suna ta fada da mai adaidaitan da ya kawo ta asibiti saboda bata da chanji sai ta hango shi yana fitowa daga mota. Kaf idanunsu suka hadu sai kallon kallo. Ko me ta tuna tayi saurin dauki ido tare da cewa a'uzubillah. Tun kafin karaso kamshinsa yayi masa iso yana zuwa dubu daya ya mikawa mai dan sahun yace mata muje ko. Ko sauraron godiyar mai dan sahun baiyi ba. Itama dai godiyar tayi masa tare da gaishe shi. Kafin su shiga wayarsa tayi ringing ya dauka yana magana da kyar. A ranta kausar tace idan namiji yasan ya hadu wulakancinsa karuwa yake. Jalilah na fada miki ki dena kirana kuma idan kika sake zuwa gidanmu zan sa kannena suyi miki duka. Kausar dai dariya ma take yi. Yana gamawa ya harareta ku mata kun iya rainin wayo.

Khairi yaya jikin naki? Dan murmushi tayi sai idanu da suka fada ga rama. Kausar tace ai baka ganta ba lokacin da bata gane waye a kanta. To dadin abin dai banyi surutai irin naki ba...ina jinki kina cewa khairi kada ki mutu ki barni wayyo yar uwata. Lallai kin warke amma ba don kina gadon asibiti ba dundu zan miki. Ai dama ki saba min mugunta. Shi dai Tahir abin dariya ya bashi to ko zaku kara ne nayi refree. Uncle Ahmad ne shigo dakin da sallamarsa. Yayi mata kyau sosai har taji zafi a zuciyarta sai tayi shiru ta dena magana shi kuwa ido ya zuba mata kamar ya manta da mutane a dakin. Tahir da Kausar suka hada ido irin kallon you see what I told you din nan.

Sun dan taba hira wadda Khairi tayi shiru. Tahir yace doctor ina son ganinka idan ka gama. Khairi wadda tun dazu bata kula kowa ba tace gulma zaku fara? Sai a lokacin Uncle yayi murmushi fuskarsa ta kara yin kyau. Khairina ta fara dawowa kenan. Ya maida dubansa ga Tahir muje ko Captain.

********************

Kafin Dr Ahmad ya rufe kofar office din Kausar ta shigo ya kalleta da mamaki a fuskarsa Tahir yace ai maganar da ita zaayi. Bayan duk sun zauna Ahmad yace kun barni a suspense fa don Allah me ya faru. Tahir ne ya soma magana tare da fada masa irin yanayin dayake ganin khairi tun farkon zuwansa ya lura tana da damuwa. Dalilin haka yasa ya nemi kausar wadda da kyar ya shawo kanta ta fada masa matsalar khairin. A takaice dai doctor Khairi is in love with someone else. What??? Kausar da gaske kike yi. Eh Uncle ta bashi amsa. Wannan abu tun muna yara ya fara har yanzu kuma mutumin bai ma sani ba. Ko kadan zancen bai masa dadi ba. Yanzu khairi wani take so....to waye ma wannan mutumin karshe dai wani kishi mai tsanani yaji ya turnuke shi ya kasa magana. Tahir wanda yake lura da abinda yake yi yayi murmushi ashe dai Khairi ba son maso wani takeyi ba. Yace kada ka damu dan uwa ai sanin irin matsalar tata zai kawo saukin lamarin. Sai ka dage wurin jin ko waye take so din. Kausar kallon shi tayi da mamaki don a yadda sukayi shawara zasu fada masa ko waye. Ni dai zan sami Alhajinmu nayi masa bayani na janye daga maganar auren.


A waje yace kausar kinga na canja plan ko? Na kula kamar yana sonta ne shima gara mu bari suyi resolving din issue din da kansu. Mungode sosai Captain domin badon kayi hakan ba bazamu taba iya fada ba. Ba komai Kausar sai dai tunda kin hanani kawarki sai ki nemo min wata matar.

Ahmad ya rike kansa wanda ke masa matsanancin ciwo. Waye yasa khairi wannan ciwon, ina ma dai ace.....Khairi bazan iya jure rashinki ba ya fada a sarari



Batul Mamman๐Ÿ’–


๐Ÿ’• MEYE DALILINKA ๐Ÿ’ž 13


Bayani Ahmad yayi musu game da abinda Tahir ya fada musu. Malam yayi matukar mamaki domin ko da wasa bai taba ganin alama ba, uwa uba kuma shi a yadda ya santa ko saurar samari bata yi. Baba dai cewa yayi a bita a hankali kuma su fara tambayarta kafin a yanke hukunci.

Babban yaya aka barwa aikin tambayar kanwar tasa sai dai abin yaci tura domin kuwa kuka take saka masa idan ya tambayeta. Shi dai yana son ta sami lafiya amma tsakani da Allah yana tararrabin wa zata ce. Wasa wasa sai da tayi sati a asibitin. Duk iyaye da lallami da rarrashi anyi anyi taki magana sai kuka. Ga ciwo yana neman dawowa sabo. Inno abin duk ya ishe ta kullum ita da kausar suna aikin bata shawara tace ita bata yafe ba ma duk wanda ya fada a cikinsu. Tahir dama bai taba nuna mata ya sani ba.

Sai da ta tabbatar babu kowa a bakin motar sai shi kadai yana jiran dreban sa ya idar da sallah Inno taje bakin motar ta durkusa har kasa. Baba Aliyu yace haba haba don Allah tashi yana magana yana waige waige. Ya zaki durkusa min haka bayan ko ba'a fada ba nasan kin girmeni ko so kike babban Malam ya fara min waazi? ya kare zancen da murmushi. Inno ta mike ta sunkuyar da kai kasa. Ranka ya dade akan maganar ummalhairu ne. Ina jinki Inno ya fada hankalinsa na gareta. Alhaji tun yarinyar nan bata san kanta ba take son shi har girmanta. Saboda shi wallahi bata fita fira da wasu mazan gashi bai ma san tana yi ba tana fadin haka sai kuka. Baba yace bangane ba waye shi din. Ta face hanci yallabai Amadu nake nufi na wurinka. Wani irin farinciki ne ya saukar masa a zuciya har fuskarsa ta nuna. Ahmad kika ce fa? Kin tabbata? Alhaji wallahi bazan maka karya ba. Bandir din 'yan dari biyu ya dauko daga aljihunsa ya bata. Murmushi tayi irin nasu na tsofaffi Alhaji bani da burin da ya wuce naga auren Ummalhairu da Amadu shine kawai abinda zaka bani tukwici.

Bai taba zata haka abin zai kasance ba. Sai dai yayi murna mara misaltuwa. Alhaji Aliyu yana son kannensa sosai. A dalilin su ya hakura da jami'a a shekararsa ta biyu don kudin da yake samu bazai isa ya ciyar da gidansu kuma duka suje makaranta ba. Dr Abdallah 'ya daya gareshi idan dansa ya aura yasan ya gama hada kan 'ya'yansu tunda Hashim lalura tasa ko auren baiyi ba. Karshe sai ya yanke shawarar bazai fadawa kowa ba sai ya sami hanyar bullowa lamarin.

******************

Ahmad zaune a dakin mahaifinsa ya sunkuyar da kai kasa ga mahaifiyarsa a gefe. Kalon agogo yake yi domin kuwa yabar khairi jikin babu dadi sauri yake ya koma. Baba yayi gyaran murya yace Ahmad idan na baka umarni za ka bi? Baba bana fatan Allah Ya nuna min ranar da zan ketare maganarka. Alhamdulillah yace sannan ya dubi Haj Karima duk abinda muka zanta da Inno ke kadai na fadawa saboda na aminta da cewa kema bazaki bijire min ba, Ahmad ko kasan cewa kanwarka ciwon nan da take yi dalilinka ne. Da sauri ya dago kansa...ni kuma Baba ya fada cikin rudewa. Eh Ahmad kai. Dazu Inno tayi min gamsashen bayani ashe ka taba cewa kaine mijinta tun tana karama. To tasa abin a ranta ta kuma girma da sonka. Ikon Allah haka kawai yake fada a ransa. Ko shiyasa ya zama restless akan lamarinta? Lallai kuwa idan haka ne zai share mata hawaye domin ko ba komai a cikin kannensa daban khairi take. Baba ya katse masa tunani da cewa ina son kayi min alkawarin zaka aure ta kuma bazaka taba wulakanta min 'ya ba. Kafin ya bada amsa Hajiya tace Alhaji ina ganin abinda yafi shine kace kai ka hada auren kawai kasan mu mata da gutsiri tsoma ko da wasa wata zata iya fada mata magana nan gaba. Ahmad ya kalli mahaifiyarsa Hajiya akwai tunani. Baba ma yaji dadin shawararta..yace kaga jiya Abdullahi ya tafi madina taron malamai na sati uku daga nan zaiyi umra kafin ya dawo. nasan shima ciwon yarinyar nan ya tsorata shi fada ne kawai baya yi. Idan ya dawo zamu yanke lokacin aurenku da su Kawu Hadi.

******************

Kausar da Inno sun sami Umma a barandar asibitin sunyi mata bayanin komai. Suna haka Baba ya kira yayi mata zancen tare da sanar da ita cewa kada ta fadawa Malam wannan aikinsa ne idan ya dawo. Ya sanar da ita ne domin yana son a samin kan Khairi kafin ya dawo.  ita Hajiya tace bama zata nuna tasan komai ba kada Umman taji babu dadi shiyasa ita bata kira ba.Kaji manya masu tunani.




Batul Mamman๐Ÿ’–


 ๐Ÿ’• MEYE DALILINKA ๐Ÿ’ž 14

Uncle Ahmad gida ya wuce ya tarar yaransa sunyi bacci a falo ya dauke su ya kai daki. Mufida wai meyasa kike son barin yaran nan a falo su kadai? Gashi har sunyi bacci. A fusace ta juyu zata bashi sai taji tsoron kada ranshi ya baci yaki kwana da ita ta sake asarar maganin mallakar da Mai Dafa'i ya bata ta shafa a kirji da mara. Abban Iman nasan kanwarka tana kwance a asibiti amma hakan ba yana nufin ka dena dawowa da wuri ba ko ka dena cin abinci. Rungumota yayi amma hankalinsa yana wurin khairi.  fuskarta ya shafa yi hakuri Mufida kinsan dole hankalina ya tashi ita kadai Malam ya mallaka kuma idan zaki tuna ko kafin aurenmu mun shaku sosai. Itama sakin fuska tayi tana kokarin su hada ido yayi arba da kwallin data sa. Sai dai hakan bata samu ba domin sakinta yayi tare da bata hakuri. Mufida wanka zanyi na koma asibiti jikin khairi babu dadi na barta dazu. Kai wannan yarinya ko jaraba tana asibitin ma ta hana ruwa gudu.. gara a aurar da ita kowa ya huta.

Bakin wando da maroon din shirt ya saka sunyi masa kyau sosai. Sai turare yana fesawa yana dan humming din wata waka. Mufida ta harare shi ni wannan abin da kake yi sai na zata zance zaka ba wurin patient ba. Dariya yayi don baya so suyi fada kada ta bata masa lokaci. Daren yau na Khairina ne ya fada a ransa.

Yana tuki cike da farinciki kamar wani sabon shigar soyayya. Shima abin mamaki yake bashi.

Fada suke da Inno akan cin abinci Uncle Ahmad yayi sallama sai da suka masa izini ya shiga. Tare da wata nurse suka shigo dakin ta gaishe shi kanta yana kallon plate din abincin. Inno allura zan mata har biyu ina fata taci abinci. Yana maganar ne cikin zolaya inno tace bata ci ba ai rigimar da muke yi kenan kafin ka shigo. Nurse din ya sallama dama yana sane wurin yin rounds dinsa yabar dakinta ya zama na karshe. Kujerar gaban gadon ya jawo kusa da kafafunta ya zauna sannan ya kalli inno nifa zance nazo Inno gaskiya ki bamu wuri. Eyye dan nan lallai yaran zamani ba kunya. Ita kanta khairi ji tayi kamar gadon ya tsage ta shige. Lafiyar Uncle kuwa?

Inno na fita ya dauke plate din daga cinyart. Bude bakin in baki a baki kinji khairina. Kallonsa take galala ikon Allah. Dan zare mata ido yayi da gaske nake fa. Ni zan iya ci da kaina....shima kwaikwayon muryarta yayi ya maimaita abin da ta ce har tayi dariya gaskiya Uncle da kai mace ne saboda muryarka zaka rasa miji. Wai!!! Garmaho kenan. Ganin yadda har ta sake tana dariya ya sanyaya zuciyar Ahmad. Khairi will never sieze to amaze him. Matso da fuskarsa yayi kusa da tata. Tell me something khairina.. ina jinka ta bashi amsa sai dai cikinta har kadawa yake don tsoro. Gaba daya nauyinsa yake ji bare ya matso kusa da ita gani take ya kara girma. Katse mata tunani yayi bakya son muryar tawa ne? Ina so mana,  tana fada taji kunya sai tayi saurin rufe fuskarta. Shi kanshi dadi yaji a ransa bude fuskar ki ci abinci akwai allura da zan miki. A ina ta tambaya a tsorace. Yau ba tsoron allurar bane kadai harda tsoron wanda zaiyi domin kullum nurse ke yi mata. Indai kin cinye duka zan kira Sister Shukriya tayi miki. Ai kuwa tana da kirki Uncle zan cinye.

Tana ci suna hira abin gwanin shaawa shine nima har nayi addua Allah Ya kara mana so, kauna, tausayi, mutuntawa, da girmamawa tare da dunbin romanciyya tsakanin mu da mazan mu. Amin

ta cinye abincin tas sannan Uncle Ahmad yace to Khairina sai da safe na korar miki inno ko. Ai nasan zan sha mita. Sai da safe kanwata ya fada yana bude kofa...sai da safe Uncle dina. Yaushe rabon da ta kira shi da wannan sunan? Yana fita Inno ta shigo da nurse yau khairi ko ihun allura bata yi ba. Bayan ta fita ne Khairi cike da nishadi tace Inno yau Uncle Ahmad ya canja min sosai. Ai naga kina ta faraa kamar kin tsinci hakori amma tuntuni baki kula bane haka yake miki tunda kika fara ciwon nan har kuka fa yayi. Da gaske? Zan miki wasa ne 'yata. Ki cigaba da addua kila bukatar ki ce zata biya. Dama ta samu an cire mata drip saboda haka alwala ta dauro ta yi nafila tare da kara addua indai akwai alkhairi Ya Allah Kasa Uncle Ahmad ya zama mijina.


Batul Mamman๐Ÿ’–

 ๐Ÿ’• MEYE DALILINKA ๐Ÿ’ž 15

Tun daga lokacin da Uncle Ahmad ya fara nuna kulawarsa ga Khairi. Kulawa irin ta soyayya sauki ya fara samuwa sosai dama ciwon nasa ne. Umman khairi dai farincikinta baya misaltuwa domin tilon yarta ta sami lafiya.

Alh Aliyu duk da ya hana a sanar da Malam halin da ake ciki amma har gida yaje ya sami Alh Mahe akan maganar Tahir. Hakika duk mutum mai halin kirki ya kan dace da abokin kwarai. Alh Mahe yace kada ka damu Alhaji kafin yayi magana da Ahmad din ma sai da ya sanar dani halin da ake ciki. Idan Malam ya dawo shima nasan zai fahimta. Allah Ya yi mana jagora.

Tun safe suke baki kasancewar yau asabar babu aiki masu zuwa dubiya sun karu. Ganin har wurin takwas na dare da baki Uncle Ahmad yazo da kanshi ya sallami kowa domin a cewarsa Khairi na bukatar hutu sosai. Umma da Indo ne karshen tafiya yaje rakasu mota. Yana dawowa ya tarar khairi tayi bacci. Abin ya daure masa kai. Inno ba yanzu na fita tana hira ba ya kika bari tayi bacci bata sha magani ba. Kasan dai bata son maganin nan na dare kullum ta sha sai tayi kakarin amai, wai wari yake yi. Murmushi yayi don yasan sarai idonta biyu. To tunda bata so ai akwai allurarsa sai nayi mata. Yana fita ta mike ta gyara kwanciya harda rufa har kanta duk da zafin da akeyi saboda hadarin da ke haduwa. Inno dai dariya take yi. Ko da ya dawo ta fara gumi a karkashin bargo yace kinga ban sami karamin syringe ba sai wannan babban shi kuma allurarsa akwai girma. Kallonta yake yi yana magana don sai mutsu mutsu take daga cikin bargon....hmmm yarinya zafi zai koro ki ya fada a ransa. Inno sai kin dan danne min ita fa don allurar nan idan aka yiwa mutum yana dadewa bai motsa ba. Jin hannun Inno yasa ta bude kanta ba shiri shi kuwa ya dage sai yayi. Kuka ta sa masa da rokon yayi hakuri zata sha. Komai na khairi shaawa yake bashi. Har yanzu dai zancen soyayya bai hada su ba amma kana ganinsu tare zaka gane akwai wata a kasa.

Malam yayi matukar farinciki yadda yake jin muryar khairi a waya. Umma ta fada masa an kusa sallamarta ma.
******************

Dakinta yasha gyara don yau Umma da kanta ta gyara shi ta fitar da kayan wanki sannan ta gyara mata wardrobe. Gida yana ta kamshi kamar wata amarya zata tare. Gidan Baba aka fara kaita ta gaishe da yakumbo da baba Hashim wanda ya damu kwarai da ciwonta sai dai sau biyu aka kaishi dubuta. Daga nan kuwa gida suka wuce Umma baki har kunne. Ashe dai tana ji da khairin ta ta. Wanka tayi tasa wata dogowar rigar atampa tayi kwalliya kausar tace khairi irin wannan ado kamar ba daga gadon asibiti kika taso ba. Dariya sukayi harda tafawa sai wayar khairi tayi ringing tana dauka ya fara fada. Ina kika shiga ina ta waya baki dauka ba? Duk kin daga min hankali. Yi hakuri Uncle dina ta bashi amsa a sanyaye. Na shiga wanka ne kuma dana fito ban duba wayar ba.
Jin yanayin maganarta yasa baiji dadi ba ko ya bata mata rai. Khairina ba fada nake miki ba kinji ko. Naji tsoro ne ko wani abu ya same ki. Murmushi tayi har yaji sautinsa wanda hakan yayi masa dadi. I am already missing you here. Na saba ganinki kullum kwanakin nan. Shiru tayi tana sauraronsa. Khairin Ahmad kina ji na?

Wayyo dadi har wani juyi tayi a kan gado. Kausar tana gefe tana kallon ikon Allah. Ina jinka Uncle dina ta bashi amsa.

Ki shirya yau zanzo zance na gaske after magrib.

Zance kuma Uncle?

Eh ko zaki hanani ganin mata ta ne?

Wace matar ta tambayeshi cike da murna.

Ummulkhair Abdallah Saraki


Batul Mamman๐Ÿ’–

 ๐Ÿ’• MEYE DALILINKA๐Ÿ’ž 16

Tana ajiye wayar ta rungumo kausar nagode da adduarki yar uwa. Allah Ya saka da alkhairi. Ture ta tayi tace duk nasan saboda uncle Ahmad ne kike wani tarairaya ta. Dariya tayi kafin ta zauna bakin gado. Ki fada min gaskiya tsakani da Allah baki da hannu a lamarin nan? Ni Allah Ya isan ma da nayi idan kika fada na yafe fa. Yadda take magana yasa kausar yin murmushi sannan ta fada mata duk yadda sukayi da Tahir da Uncle din nata. Karshe tace mata Allah Khairi shima yana sonki don baki ga fuskarsa ba lokacin da Captain yace masa kina da wanda kike so. Da kina ganiyar ciwonki kuwa ai yadda ya rinka yi ko Umma albarka. Ke dai mu dage da addua a kodayaushe. Khairi dai bata tsaya jin karshen maganar kausar ba ta daga gira daya wato Captain ta wani ja sunan yadda kausar tayi. Lah wallahi kada ki fassara ni. Me kika ji nace har kin tsargu kamar mara gaskiya. Khairi ki kiyaye ni fa. Ganin kausar ta yo kanta yasa ta mike itama zata gudu  idan naki fa...

Umma tana daga falo tana jin hayaniyarsu. Zuciyarta fes ta Inno Allah Ya biyaki. Ji yau kadai da khairi ta dawo gidan nan har ta cika min kunne. Ai Hajiya idan da rabo sai kiga ta cika miki gida da yara nan gaba.

******************

Uncle Ahmad ya cika alkawari domin kuwa a masallacin kusa da gidansu khairi yayi sallar Isha sannan ya kira ta a waya. Ya sanar da ita zuwansa. A falo ta makale saboda Umma tana kallon news. Yana ta kira tana rejecting calls din. Umma kuwa tana lura da ita idan bazaki tashi ba nima bazan baki wuri ki sami damar fita ba zan ga karshen gulma. Gajiya yayi ya shigo falon bayan an amsa masa sallama. Gaban Umma yaje ya zauna. Anti Munnira barka da yamma. Mun wuni lafiya Ahmad? Ya zirga zirgar ku, Allah Ya kara zumunci Ya saka da alkhairi. Amin ya bata amsa. Khairi ko kallonsa taki yi duk yadda yaso su hada ido. Umma har ta fara jin kunya ganin haka ta tashi ta tafi daki.

To ai sai ki tashi tunda nayi miki hanya ko a nan zamu yi hirar? Kunya ce ta kamata. Yanzu sai ta bishi falon baki...anya zata iya kuwa. Ganin bata da niyyar tashi yasa ya miki 5mins na baki idan baki zo ba zan tafi.

A hankali ta shiga falon kamar wadda zaa kama. Yana daga zaune yana dariya ashe dai kina son mijinki. Mayafin jikinta tasa ta rufe fuska a haka taje ta zauna.

Kin dena magana ne khairi na. A'a ta bashi amsa cike da kunya. bazan hanaki jin kunya ba yanzu khairi amma very soon zanyi maganinta. Janye mayafin tayi ayi maganinta fa kace Uncle? Babu inda za ta. Hmm..... akwai ranar da zan kashe bakin nan. Mu kashe na juna dai ...tana fada kuma sai ta tuna da wa take magana ba shiri ta mike Uncle sai da safe..
Shima tashin yayi ina zaki kike wani sauri? Sai kin fada min yadda zamu kashe bakin juna. Da gudu ta fice zuciyarta tana bugawa da sauri. Shima Ahmad ta barshi cikin wani irin yanayi mara misaltuwa.

Gidan su Khairi yau an tashi da gyara da girke girke Malam yana hanya. Kwananta uku da dawowa daga asibiti. Cike da doki ya shigo gidan Khairi ta kankame shi tana ta murna. Yayi mata addua tare da bata guzurin zamzam da yayi mata. Da murna ta shiga daki ta kira Uncle tana sanar dashi dawowar Malam. Ita kuwa Umma tsabar murna bayan ya gama cin abinci tace Malam albishirinka. Goro fari Munnira yana magana cike da nishadi. Ba dole ba khairinsu ta warke. Tace to bani tukwici don nasan sai ka fi Alhaji murnar abinda zan sanar da kai. Allah Yayi miki albarka uwargidana. Amin ta amsa sannan ta bashi labarin khairi da Uncle Ahmad. Tunda ta fara gabansa ke faduwa ai kuwa abinda yake tsoron ji ta fada. Ummulkhair da Ahmad. Tana gama bayani ya mike a sanyaye Munnira...naam Malam ta amsa masa cikin jindadi. Mikewa yayi idanunsa fal da hawaye yace kiyi hakuri amma ko na mutu kiyi min alkawarin Ahmad ba zai taba auren Ummulkhair ba.



Batul Mamman๐Ÿ’–


 ๐Ÿ’• MEYE DALILINKA ๐Ÿ’ž 17

A tsorace ta miki har wayar da ke kan cinyarta ta fadi ta tarwatse. Malam meye dalilinka na fadar wannan maganar. Bai iya bata amsa ba don bashi da bakin magana. Dakinsa ya shiga ya rufo kofar. Haj Munnira ta shiga tashin hankali saboda sabanin reaction din da tayi tsammani ta gani a tare da shi. Ko dai Ahmad yana da wani mugun hali ne da basu sani ba?

Shi kuwa Dr Abdallah ko da ya shiga daki alwala ya dauro yazo ya fara nafila wadda bai san adadinta ba.  Yana yi yana kuka tare da tsananta addua ga Allah SWT kada ya nuna masa wannan bakar rana da Ahmad zai auri Khairi.

Ita kuwa khairi da bata san abinda ke faruwa ba baccinta tayi mai dadi domin kuwa sun dade sun hira da uncle Ahmad a waya. A nasa bangaren bayan yaje gida ya tarar Mufida tana wanka. Cire kayansa yayi daga shi sai singlet da gajeren wando ya zauna a kan gadon yana jira ta fito shima yayi. Tunawa yayi wani abokinsa ya bashi gift din pack din necktie bai sami damar dubawa ba sai ya tashi ya bude wardrobe dinsa yana nema bai san inda Mufida ta ajiye ba. Garin dube dubensa yaga wata bakar leda a bangaren kayanta. yana budewa wata takarda ta fado sai ga wasu kananan kwalabe da kulle kulle a leda. Tattatawa yayi zai mayar mata don ya zata irin kayan matan nan ne da take sha ya dai yi mata fadan ta tabbatar ta san me take sha saboda lafiyarta ma. Haka nan ya bude takaddar ya fara karantawa domin rubutunta ne a jiki yana  yar dariya...

1. Farin kulli hodar fuska idan miji ya gani komai kika tambaya zaki samu
2. Kwalba mai jan ruwa na shafawa a goshi, mara da kirji miji yaji tsoronki
3. Kwallin mallaka a saka lokacin kwanciya bacci

Dama ga zafin gari amma wani gumi ta fara yi. Ita kuwa mufida me na rage ta dashi take neman fadawa shirka. Ko da ta fito bai nuna ya gani ba yaje yayi wanka ko mai bai shafa ba yaji ta rungume shi harda riko fuskarsa da hannayenta don su hada ido. Shi kuwa sai nokewa yake yana karanta Ayatul kursiyy. Ranar dai bai yadda anyi abinda take so ba don yana tsoron wanda ake shafawa mara kada ya hadu dashi ya fara tsoronta. Baccin karya yayi kafin na gasken ya zo tare da yanke shawarar fadawa Malam don ya bashi shawarar abinda ya kamata yayi.
******************

Malam bai sami kansa ba sai bayan isha ya tafi gidan yayansa. Alhaji Aliyu yace ai nasan kana samun labari zaka zo. Baba Hashim da yake gefe yace ai yaran nan sun gama mana komai. Allah Ya tabbatar da alkhairi. Amin, amin Baba ya amsa. Malam ya tattaro courage dinsa yace amma Yaya ka manta da maganar yaron wurin Alh Mahe? Yar dariya yayi nasan zaka ce ana neman aure cikin neman wani ko? To kwantar da hankalinka har gida naje na sameshi kai shima Tahir din da kansa yace ya janye. Ba haka Malam yaso ji ba amma yasan idan ya bari aka yi auren nan Allah bazai barshi ba. Saboda haka ya dake yace Yaya ni dai gaskiya kayi hakuri kuma na baka damar nemawa khairi miji amma banda Ahmad.

Yayi kusan minti biyar a bakin kofar yana sallama basu amsa ba shiyasa bai shiga ba amma maganar Malam wadda ba karamin razana shi tayi ba yasa ya saki kwalaben asirin mufida har suka waigo suka ganshi.



Batul Mamman๐Ÿ’–


 ๐Ÿ’• MEYE DALILINKA๐Ÿ’ž 18


Yayi yayi amma ya rasa me zai ce karshe dai shigowa yayi ya zauna. Baba yace Abdullahi fada min me yake faruwa. Ahmad yayi maka laifi ne ko akwai halinsa na sabon Allah da bamu sani ba. Fuskar Ahmad kawai yake kallo a ransa yana cewa ka yafe min Ahmad. Ganin yayi shiru abin ya fara batawa Baba rai yace muna sauraronka kayi shiru. Baba Hashim yace Ahmad tun kafin abu yayi nisa ka fada mana gaskiya domin naga baban naka baya son yin magana kada ya fadi sirrinka. Kana kallon shi kasan a rude yake. Wallahi baba Hashim bansan me nayi ba. Malam yayi ajiyar zuciya babu abinda kayi kada ma ka zaigi kanka auren ne kawai bana son ayi na zumunci. Allah Ya baku wasu ku aura. Baba ya dago kai cikin bacin rai yace Ahmad bamu wuri. A sanyaye ya fita ya koma dakin mahaifiyarsa. Tana ganin yanayinsa tasan ba lafiya ta fita ta kira Momi da yakumbo suka shiga falon tare.

Ni Ahmad baiyi min komai ba amma Yaya kayi hakuri auren nan wallahi baza ayi shi ba. Yana fadin haka ya fita.

Yauma rufe kansa yayi a daki Umma ta rasa yadda zata yi gashi bata so khairi tasan abinda ke faruwa. Waya ya dauko ya kira Baba  malam mahaifin Umma yana magana yana kuka ya sanar dashi halin da ake ciki. Ka taimaka kasa baki kada muyi abinda Allah zaiyi fushi damu amma kafi kowa sanin dalilin da yasa bazan bari ayi auren nan ba. Baba Malam yace ka kwantar da hankalinka ranar juma'a in sha Allah zan zo kanon. Amma kafin nan kada ka bari ayi auren kaji ko Abdallah. To Malam ya amsa masa cikin kuka.

Haj Karima da su Yakumbo kowa kansa a daure. A daki ta tsare Ahmad lallai ya fada mata abinda yayi wa Malam. Karshe tace ko dai kana da cutar nan ne ka boye mana. Wace cuta kuma Hajiya ya tambayeta a razane. Kanjamau mana. Haba hajiya wallahi bani da ita. To ba komai nasan babanku bazaiyi shiru da maganar nan ba. Ni dai babu komai a tsakaninmu na fada da zai sa yaki jinina amma da safe zan kira Munnira naji ko tasan dalili.


Khairi tana dafa indomie zata ci ta tafi makaranta ta ji muryar Umma tana cewa wallahi haj karima nima yadda kika ji maganar nan haka naji ta. Ko kinsan yanzu ko dakinsa baya bari na shiga da sassafe yake fita sai khairin ma tayi bacci yake dawowa. Ni tsoro na daya kada taji cewa mahaifinta ne baya so ta auri Ahmad. Kirji ta dafe sakamakon wani zafi da taji zuciyarta tana yi.

Batul Mamman๐Ÿ’–


๐Ÿ’•MEYE DALILINKA๐Ÿ’ž 19

Da gudu ta ta shigo falon Umma na ganinta tayi saurin katse wayar. Khairi tace Ummana me ya faru? Meyasa Malam baya son auren tana magana hawaye suna wanke mata fuska. Umma bata da amsa ta fara rarrashinta duka duka yaushw ta fito daga asibiti malam zai janyo musu tashin hankali.

A kasa ta zauna tana ta kuka Umma na bata baki sai ga indo ta shigo daga baya da gudu ta nufi kitchen saboda kaurin indomie din da khairi ta dora. Daki ta koma ta dauko waya ta kira Uncle Ahmad tana kuka yana jin yanayinta yasan abinda ya faru yace khairina kina ji na? Da kyar ta iya amsawa. Bana so ciwonki ya kara tashi kiyi hakuri ki dena kuka Baba zai masa magana. Ni kaina bansan ma abinda nayi masa bane but dont nasan Allah zai mana magani.

Makaranta dai tasha ruwa haka tayi ta jiran Malam sai can dare ya dawo. Jugum jugum ta gansu ita da Umma yace me ya faru Munnira? Dole kace me ya faru mana kana neman kashe min 'ya da fada take maganar don kokarinta yaji haushi ya fadi dalili kowa ya sani. Bai kula ta ba ya dubi khairi yau ko sannu da zuwa bata yi masa ba yace  Ummulkhairi...ta dago fuskarta idanunta sunyi ja kamar gauta kiyi hakuri ki cire Ahmad a ranki. Bai ma jira ta amsa ba ya shige daki. A dakin umma ta kwana tana ta aikin kuka.

***************

Ahmad bai taba shiga tashin hankali ba kamar yanzu da yake ganin zai rasa khairi da gaske. Baba da su Yakumbo sunyi iya yinsu amma ya dage kan bazaayi auren ba. Gashi uwa uba yaki fadin dalilinsa.

Zuwa yanzu duk 'yan gidan sun san abinda ke faruwa Mufida tayi murna sosai jin malam yaki yarda. Wato da don munafurci babu wanda ya fada mata zancen auren, maganinsu kenan. Kawu Hadi wanda shi kadai ya rage a kannen babansu Malam shima har ya gaji da magana. Malam yace sai dai suyi hakuri shima ba a son ransa bane.

Yana kwance a daki yau kwanansa biyu baije aiki ba don bashi da nutsuwa da kwanciyar hankali. Mufida bata gabansa tun ranar da yaga kulle kullenta. Waya ya dauko ya kira ta

Khairina...kana jin muryarsa abin tausayi.
Naam Uncle Ahmad sai kawai ta fashe da kuka.

Tamkar tana watsa masa ruwan zafi haka yake jin kukanta. Ki yarda dani Khairi bazan taba bari a raba mu ba indai ba auren namu zai zama hatsari bane a rayuwarki.

Bata ce komai ba sai shesshekar kuka...kiyi min magana mana. Uncle kada ka bari a rabamu tana fada muryarta na rawa.

I won't, I promise

Bayan ya ajiye wayar text yayi mata

( I Love you Ummulkhairi ina fata you feel the same way about me.)

Text dinsa dai kuka ya kara mata tana cikin yi kirjinta ya fara bugawa numfashi yana sama sama. A haka Inno tazo ta ganta ta yi saurin kiran Umma. Kuka ta saka tana wargaza magungunan khairin ta rasa wanda zata bata. A haka Malam ya shigo hankali a tashe zai daga khairi ,Umma ta daga masa hannu tana kuka dakata Abdullahi kada ka taba min 'ya. Ba so kake ta mutu ba kowa ya huta ai gara ta mutun. Amma wallahi kaji na rantse maka idan na rasa 'yata na gama aurenka. Ana maka kallon malami a waje amma ni yanzu nasan cewa ina tare da mutum mara tsoron Allah. Shi kanshi idan ka kalle shi sai ka tausayawa yanayin da yake ciki. Munnira kada kiyi sabo saboda fushi. To Dr Abdullahi Saraki sai ka fada min MEYE DALILINKA na hana auren khairi  da Ahmad ta fada tana rike kugu kana ganinta kasan bata cikin hayyacinta sosai.



Batul Mamman๐Ÿ’–


 ๐Ÿ’•MEYE DALILINKA๐Ÿ’ž 20

Shima magungunan ya rinka dubawa da ya rasa yadda zai yi waya ya ciro da aljihunsa ya kira uncle Ahmad. Cikin bacci ya dauka jin muryar malam yasa ya ce me ya faru don wayar malam a daren nan yasan ba lafiya. Khairi ce ciwonta ya rashi ya bashi amsa a gigice.

Doguwar riga ya dora akan kayan baccinsa gaba a baya ya suri keys din mota ya fita. A kan gado ya ganta kamar ta suma. Allurai yi mata har uku sannan yasa mata drip. Umma kallon malam take kirikiri yace bai yadda da aure ba amma da yaga babu yadda zaiyi ai ya kira shi ya ceci ran 'yar sa.

A falon gidan ya kwana da asuba Malam yazo ya tashe shi. Tare suka je masallaci yana son tambayar Malam amma yayi masa kwarjini. malam dai bai ce komai ba har suka koma gida. Ya sake shiga tana kan abin sallah. Fita yayi bayan ta idar ta zo falo ta same shi. Ya tambayeta ya take ji tace masa da sauki daga nan ta koma daki domin malam yana zaune yana kallon su. Bayan yaje gida yayi wanka gidansu ya tafi ya yi saa Baba bai fita ba. Ya sanar dashi abinda ya sami khairi Baba yace Ahmad kayi hakuri bana son tashin hankali da Abdullahi amma kasa a ranka zanyi maganin abin da yardar Allah.

Gwaggo baki ga halin da khairi take ciki ba kamar baya tausayinta. Ni ba don ina tsoron Baba Malam ba wallahi gida zan taho. Gwaggo mahaifiyar Munnira  tace kul na sake jin zancen tahowa kiyi hakuri babanki yana hanyar kanon ma. Umma ta share hawaye me zaiyi a kano kuma? Akan maganar auren ne dai, Allah Yayi miki albarka. Tana ajiye wayar itama hawayen take yi tana tausayin 'yarta. Lallai yau kila asiri zai tuno me zasu fadawa Munnira bayan sun san komai.

Ana idar da sallar Juma'a Alh Aliyu ya matsa kusa da liman ya sanar dashi akwai daurin aure suyi hakuri abin yazo a haka. Liman yayi sanarwa ta loudspeaker saboda haka wasu daga cikin mutanen suka tsaya. Ya dubi Baba Hashim ya ajiye masa kudi a kan cinyarsa yace kaine waliyin Ahmad yace to yana cike da mamaki wato shirun da Alh Aliyu yayi ba na wasa bane ashe . A take a nan yayiwa khairi walicci aka daura aurenta da Ahmad akan sadaki dubu hamsin mutane suka shaida.

Text ya turawa kaninsa yana sanar dashi daurin auren kuma yazo yana jiransa a gida. Shima Ahmad text din ya gani murna da farinciki suka rufe shi.

Gumi ne ya rinka karyo wa malam yana ta salati Umma ta dauki wayar tana karanta text din ta rangada guda tace Allah Ya saka wa Yaya da alkhairi. Dakin khairi ta shiga ta same tana karatu. Khairi ki gode Allah yanzu Baba ya daura muku aure da Ahmad. Tana kai karshen aya ta rungume umma tana kuka. Suna tsaye a haka sai jin muryar Malam suka yi yace su fito zasu tafi gidan Baba.

Umma ko a jikinta domin dai bukata ta biya. Yana parking din mota a kofar gidan sai umma ta lura da kaninta Umar shima yana gyara parking yace mata tare suke da Baba Malam yanzu ya shiga ciki. Khairi har kasa ta durkusa tana gaishe shi tace kawu umar ina su ibty da zainab. Suna nan kalau ya bata amsa kafin itama ta bi bayan iyayenta.

Baba Malam ne zaune kan kujera sai iyalan gidan Baba dana malam tare da Kawu Hadi. A yara kuwa daga Uncle Ahmad sai khairi. Bayan sun gaggaisa Baba ya nuna mamakinsa na ganin babban Malamin a gidansa wato Shiek Hamza Samaru daya daga cikin malaman da kasa ke ji da su.
Baba Malam yace naji dadi sosai Aliyu yadda kake kokarin habbaka zumunci tsakaninka da 'yan uwanka. Hakika abinda kayi yau na kokarin ceton rayuwar 'yar kaninka aikin lada ne babba sai dai akwai kuskure a yin hakan. Umma wadda dama ganin baban nata a gidan itama yasa tasha jinin jikinta ta fara tsorata. Ya mayar da kallonsa ga Malam, yace Abdallah ranar wanka ba'a boyon cibi.

Malam gumi yake ga jikinsa har tsuma yake yau sirrin boye zai fito fili. Ji yayi bakinsa gaba daya babu yawu idanunsa sunyi ja saboda firgici. Yakumbo tace yi magana mana ka barmu da zulumi.

Hmmm yayi ajiyar zuciya kafin yace kuyi hakuri amma Ahmad...............................
.........shirunsa ya kara tada musu hankali. Ahmad.....dana ne ya karasa da kuka.


Batul Mamman๐Ÿ’–

๐Ÿ’• MEYE DALILINKA๐Ÿ’ž 21


INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN kowa abinda yake fada kenan. Lokaci guda tsanin rudani ya shiga tsakanin 'yan uwan. Haj Karima ta kadu sosai da kyar ta iya mikewa tana nuna Malam kamar zata yi magana sai dai kafin ta iya takawa ta fadi kasa a sume. Nan da nan hankali ya koma gareta. Umma tace Malam wallahi na gama auren nan. Ka sake ni gidanmu zan tafi. Tana magana kamar mai sumbatu sai da Baba Malam ya daka mata tsawa. Ta koma ta zauna tana kuka. A wannan lokacin kuwa Ahmad ji yayi inama ya mutu ya huta ga tashin hankali ga hajiyansa a kwance. Khairi kuwa kirjinta ta dafe idanunta babu ko digon hawaye....ashe kuka ma rahma ne. Baba kuwa kallon kowa yake dai dai zuciyarsa na sake sake.

Baba Malam da Kawunsu Baba da kyar suka shawo kan jamaar wurin aka yi shiru. Haj karima tana tashi ta dubi Malam tace Abdullahi ba sai kayi min sharri ba don baka son auren nan...ta juya ga Ahmad idan ka haifu cikin uwa da uba ka saki yarinyar nan a yau, a yanzu saki uku. Shi kam jikinsa babu kwari ko kadan bashi da sauran katabus bai iya cewa komai ba. Dattijan suka ce kowa ya saurara Baba Malam yayi gyaran murya. Nasan kowa a nan ya shiga cikin rudani da tashin hankali amma yana da kyau ku saurari uzurin Abdallah kafin a yanke hukunci.

Malam dai kuka yake yau din da yayi ta gudu for the past 36years tazo ta cimmasa.

Yaya idan ka tuna shekarunku hudu da Hajiya baku haihu ba. A lokacin dukkanmu gida daya muke tare da ku. Muna karatu ni da Hashim kana kasuwancinka.

(Tana jin haka tasan karshenta wannan maganar dalilin makircin da ta kulla ne shekarun baya)

Malam ya cigaba da bayani to wata rana na dawo gida ina cin abinci sai ta shigo falon da zobo ta zuba min itama ta sha. Daga nan na farka na ganni a dakinta kan gadonta. Tana daya gefen a kwance....kuka yaci karfinsa. Sai da ya numfasa ya cigaba. Har na fita bata sani ba. Kuma a ranar ne hashim ya fado daga bene. Bayan wata uku ka sanar dani tana da ciki wannan dalilin ne yasa na koma zaria har na hadu da Baba Malam. Yasan komai don ban boye masa ba.

Bayansa ya kwaye musu shatin bulala ne ya dai yi fading baa gani sosai. Zuwa nayi aka yi min bulala dari a matsayin kaffara. Wannan shine dalilin da yasa nake da yakinin Ahmad dana ne.

Wallahi Abdullahi kayi karya haka take fada cikin gunjin kuka. Baba haki ya fara Malam yayi yunkurin kamashi ya mike ya doke masa hannu. Uncle Ahmad ne ya fitar dashi da kyar ya sa shi a mota domin falon tamkar kurkuku kowa yake jinsa. Umma ta kama hannun Khairi fuuuu ta tashi suka fita. Ita dai khairi binta kawai take yi idanunta a bude amma bata ganin inda take takawa. Sai da suka fito Umma ta suma kuka ina suka nufa? Ita dai bazata koma gidan Malam ba. Ace wai Ahmad wan khairi ne uba daya???

Shiru taji daga bayanta tana juyawa don taji shiru khairi ba magana sai taga jini ke fita daga bakinta. Ihu ta kwala don ta shiga tashin hankali. Da gudu Malam ya fito ya ciccibe ta ya dora a kan kafadarsa yasa ta a mota sai asibiti.




Batul Mamman๐Ÿ’–


๐Ÿ’•MEYE DALILINKA๐Ÿ’ž 22

Kwana biyar kenan ana faman abu daya, kokarin ceto rayuwar Baba wanda jininsa yayi mugun hawa da Khairi mai fama da ciwon zuciya.

Kausar kullum tana asibitin amma khairi bata gaya mata ainihin abinda ke faruwa ba domin wannan sirrin gidansu ne. Tahir ma yazo dubiya rabonsa da duk su biyun tun ranar da ya sanar da Uncle Ahmad zancen khairi na da wanda take so.

Kausar ina kyautata zaton akwai matsala a tare da friend dinki. Ina fata ba hanata auren aka yi ba. Ya gyara tsayuwa kuma naga kusan dukkansu kowa yana tattare da damuwa. Kausar  tace to Captain nima haka na gani mu taya su addua dai. Haka ne ya bata amsa. Sai kuma yace kina ganin ya dace na tafi na barki kina jiran abin hawa? Ah haba kada ka damu ai basa wuya. No ya fada yana girgiza kai. Kizo na ajiye ki.  Kememe taki yarda karshe dai kudin mota ya bata yace idan bata karba ba zai hana kowa daukarta. Yana wurin ta sami taxi ya biya kudin tare da kashedin kada a dauki kowa.

Khairi ta fara samun sauki sai dai har yanzu jinin Alh Aliyu yaki sauka. Baya kaunar Malam ya shiga dakinsa da sunan dubiya. Ita kanta khairin girman babanta ya sauka a idonta. Abin duniya yayi masa yawa gashi ko sau daya Umma taki sauraron sa. A corridor din asibitin ya hadu da hajiya Karima ta dawo daga raka 'yan uwanta. Niyarsa ya wuce don bashi da idon kallonta tace Abdullahi....yau ba malam din...tsayawa yayi cike da fargaba. Idanunta fal hawaye kayi min tabo wanda baya taba bacewa ka sheganta min da daya da Allah Ya bani.. ka cutar min da rayuwa. Ajiyar zuciya yayi ki sani da mutumci na bazan so na jawowa kaina mummunar matsala irin wannan ba. Sai dai idan na bari akayi auren yaran azabar da zan gamu da ita mai radadi ce. Duk abinda nayi na yi shi ne domin mu rabauta a wurin Allah. Ta sa mayafi ta goge hawayenta ba komai Allah zai mana sakayya jira nake Alhaji ya sami sauki ayi gwajin jini  amma duk da haka ka bata min suna. Har ta shige yana jin sautin kukanta...shima hawaye ya share da hannunsa. Duk abinda yayi yasan saboda tsoron Allah ne.

(Tana labe tana sauraronsu ita ma ta rasa farinciki tunda aka fara maganar nan. Wai da wane bakin zata tona gaskiyar da ta binne tsahon shekarun nan?)

Yau aka sallami Khairi suna shirin fita ta kalli Ummanta. Umma ina muka nufa? Zaria zamu je idan Baba Malam ya hana mu zama ina da gidan haya a ja'in sai na sallame su mu koma. Yakumbo ce ta shigo bayan sun gaisa tace Mannira ku shigo dakin Alhaji mana ina son ganin ku.

A raku be suke a dakin wannan ya kalli wannan. Tun ranar da abin ya faru sai yau ta ganshi sati biyu kenan. Uncle Ahmad ya rame sosai. Hajiyansa tana kan tabarma ita da Momi sai Malam dake tsaye bayan wheelchair din  Baba hashim. Baba dake kan gado juya musu baya yayi.

Yakumbo tace to  Alhamdulillah tunda duk mun taru a nan. Lokaci yayi  da zan fadi sirron boye. Baba yayi saurin.juyuwa a tsorace yace Yakumbo kada dai kice ni ko daya daga cikin kannena ma ba mu da uba.

Dariyar da tayi mai cike da nuna takaici ce da damuwa. Aliyu, Abdallah, Hashim kowanne tana kiran sunansa tana kallonsa. Ku yafe min abinda nayi muku amma hakika Ahmadu ba danka bane Abdallah. Aliyu ne ubansa. Wata irin ajiyar zuciya Uncle Ahmad ya saki. Haj Karima kuwa cewa tayi uhmm kunji ko? Ai na fada muku wallahi dannan dan aure ne.

'Yar tsohuwa tasa kuka ta fayyace musu gaskiyar abinda ya faru shekaru 36 da suka wuce.


Nima nace ku biyo ni don jin wannan labari



Taku Batul Mamman


 ๐Ÿ’• MEYE DALILINKA๐Ÿ’ž 23

AINIHIN ABINDA YA FARU SHEKARU 36 DA SUKA WUCE


Mahaifinsu sunan sa Ahmadu amma jamaa sunfi kiransa da Saraki. Sana'ar dinki yake yi wadda ya koya wa 'ya'yansa Aliyu da Abdallah domin lokacin Hashim yana karami. Bayan rasuwar mahaifiyarsu ne ya auri Yakumbo Larai. Ta rike su da gaskiya kuma ita Allah bai bata haihuwa ba. Aliyu yana aji biyar a sakandire baban nasu ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya. Ko da aka raba gado sai ya kasance Yakumbo bata da rabo a cikin  gidan, gasu maza sun fara tasawa basa son a rabasu tsakanin gidajen yan uwan babarsu ko babansu. Dalilin haka suka roki Yakumbo kuma akayi sa'a ta amince ta cigaba da zama dasu. Da dadi ba dadi haka suka cigaba da zama, itama tana dan sanaar sayar da kayan kamshi kamar su citta da kaninfari. Aliyu da Abdallah kuwa sun cigaba da dinki.

Lokacin da Aliyu zai shiga aji biyu a jamia Abdallah yake bukatar kudin jarabawar gaba da sakandire. Kudin hannunsu kuma mutum daya zai isa har ma da ciko.

Aliyu na zaune gaban Yakumbo yake fada mata yaje wurin Kawu Hadi amma kudin basu samu ba. Nima nasa akuya ta a kasuwa Ali har yau ba'a siya ba ta fada tana share hawaye. Ni shawara gareni idan zaka yarda. Ina jinki ya bata amsa. Da kanka kake cewa Abdullahi akwai kwakwalwa ga hadda a kan nan nasa. Mu shaida ne kullum na daya yake yi. Ka daure a biya masa idan yaso ina sayar da akuyar da dan kudin dinkinku sai ka biya. Mutmushi yayi haba Yakumbo bazan taba musa miki ba. Allah Yasa kada ya bamu kunya ni zan hakura in jira.

Abdallah yayi jarabawa kuma cikin ikon Allah sakamakonsa yayi kyau sosai zai sami gurbin karatu a jamiar bayero ta kano. Zuwa wannan lokacin Aliyu yayi nisa a kasuwanci ya ma bar zancen makaranta. Kokarinsa duk bai wuce kanen nasa su sami ilimi ba. Bayan shekara daya ya auri Karima 'yar makotansu. Kuma daga lokacin ne suka fara samun sabani da Yakumbo. Ita a ganinta ta sha wahalarsu dole tafi Karima jindadi a gidan duk da cewa babu abinda aka rage ta dashi.

Shekaru hudu kenan babu haihuwa Yakumbo kullum gori da bakar magana. Sai dai Aliyu yayi ta bata hakuri a daki domin yace bazai iya sa in sa da Yakumbo ba. A dalilinsu taki kara aure duk da bata rasa manema ba.

Abdallah ya samu nasarar gama karatunsa na jamia inda ya zakara a wannan shekarar na daliban da suka karanci Mass Communication. Karatun ya dace dashi saboda akwai shi da baki ga iya tsara zance. Yana jiran a kirasu bautar kasa ne tsautsayin ya faru.

Yakumbo ta jima tana bawa Aliyu shawarar ya auri Abu 'yar kaninta saboda zuwa lokacin arziki ya karu gareshi har mota ya siya ya kuma sayawa Abdalla vespa. Kullum korafinta ai karima bata haihuwa shi kuwa Abdallah idan yaji haka ranar zai wuni nasiha ga 'yar tsohuwa. Hakan yasa ta fara tsanarsa saboda yana shigar wa Karima fadan da ba nasa ba.

Basiru dan autansu ta samu suka yi shawarar yadda za'a kori Karima da Abdallah gaba daya daga gidan. Abdallah ya dawo daga shago saboda har yanzu basu tafi bautar kasa ba yaje ya dauko abincinsa ya zauna a falo yana ci.

Ah ah malam Audu yunwa ta koro ka ne? Ta tambaya tan a kokarin zaunawa.  Ke dai bari babbar yaya meye a jug din ne? Zobo ne ta bashi amsa. Shine ko ki dan sammin. Zuba masa tayi yana sha yace sukari bai ji ba. To shazumamu sarkin zaki ni kadan nasa saboda yayanka da Hashim basa son zaki da yawa. Ni ko oho kenan.

Tana bayan kofa tana saurarensu.

Jim kadan Karima ta fara gyangyandi, Abdallah yace shima cikin muryar me kama da ta maye ki shiga daki mana. Da kyar ta mike ta tafi. Ba'a jima ba shima ya fara baccin.

Dariya tayi sannan ta fita ta kirawo kanin nata. Sun sha wahala kafin su ka iya kaishi dakin suka kwantar dashi a kan gadon. Yaya bari kiga na cire masa riga. Itama ki cire mata dankwali. Haka suka aiwatar kafin su fita tace ai in Allah Ya yarda sai ya auri Abu. Haka kawai ya ajiye juya a gida ga kudi ya fara samuwa wata sakarai tana ci. Tana gama magana ta juya kawai ta ga Hashim wanda yake SS3  a lokacin yana masu wani irin kallo.




Batul Mamman๐Ÿ’–

๐Ÿ’• MEYE DALILINKA๐Ÿ’ž 24

Gaishe su yayi ya wuce dakinsa domin ya cire uniform sai dai yana ta mamakin me suke yi ita da kaninta a sama bayan nasu bangaren a kasa ne.

Wani irin ciwon kai ne ya kama shi kamar kansa zai fashe ya farka a razane. Kansa ne ya yuye domin bai ma gane a ina yake ba. A hankali ya fara tuna me yayi karshe kafin ya ganshi anan. Ganin jikinsa babu riga ga Karima a gefe ba karamin razana shi yayi ba. Me suka yi? Garin yaya ya biyota daki? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Yana ganin ta fara motsi yayi saurin fita daga dakin. Kasa ya sauka ya shiga wanka don kansa yayi clearing. Wani irin yanayi ya tsinci kansa saboda bai san me ya faru ba a dakin. Haka ya zauna har laasar ga matsanancin ciwon kai.

A tsakar gida Yakumbo ta ganshi yana alwala. Saboda tsabar gigita da tayi ruwan da ke bakinta har kware ta yayi. Garin yaya ya farka da wuri bayan maganin da ta zuba a zobon wanda zai sa su bacci har na awa biyar ne. Gashi Aliyu ya kusa dawowa. Ita kuma bata isa tace ta gansu ba. Dama niyarta Aliyu ya dawo daga kasuwa da laasar idanunsa su gane masa.

Fakar ido tayi ta koma saman tana neman inda ta jefar da ledar maganin wadda ta yar cikin sauri don kitchen din karima a sama yake. Motsi taji a bayanta tana juyuwa ta sake ganin hashim ai kawai sai ta kwalla kara wai ga gizogizo nan don tasan akansa Hashim ya taba suma saboda yana tsoronsa a kokarinsa na guduwa yayi missing step ya fado daga benen.

Ita tayi haka ne don ya dena binta shi kuma yadda yaga tana sanda ne yasa ya bi bayanta. A sume ta sauko ta sameshi ta fara ihu.

 Gidan nasu ya hadu da tashin hankali a lokacin da likitoci suka tabbatar musu da cewa bazai iya kara motsa wata gaba a jikinsa ba banda kansa. Yakumbo tayi nadama mara misaltuwa. Garin son zuciya ta cutar da dan maraya. Wannan tashin hankalin yasa Abdallah mantawa da abinda ya faru sai dai bayan wata uku Aliyu cike da farinciki ya sanar dashi karima na da ciki. Wannan dalilin yasa da posting dinsu ya fito ya tafi kaduna sai da yayi shekara guda bai dawo ba. Shi niyarsa ma ya tafi kenan don bazai iya cigaba da ganin karima da abinda zata haifa ba.

A garin kaduna an tura shi wata makaranta a zaria bautar kasa wadda take kusa da masallacin da Baba Malam mahaifin Munnira yake koyarwa. Kullum bayan magariba ake karatun. Wata rana ana karanta suratul Nur yaji irin hukuncin da Allah Ya tanadar wa mazinata. Ranar yayi kuka sosai bayan sunyi isha ya tari Malam a hanya ya sanar dashi yana da matsalar da zaiso su tattauna a kai.

Washegari yaje gidan malam din kamar yadda sukayi alkawari ya sanar dashi halin da yake ciki. Malam yayi masa nasiha yace ai ba da gangan kayi ba kaje ka yawaita istigfari. Yace to Malam maganar haddi fa? Idan baayi min ba bazan taba samun kwanciyar hankali ba ko da ita ce ajalina. Ba yadda Baba Malam baiyi ba ya dage sai an yi. Anyi masa bulala dari tunda da bakinsa yace ya aikata.

Baba Malam ya tausaya masa sosai ya bashi daki a gidansa ya sanar da matarsa komai domin mace ce ta kwarai me rikon sirri. Da kansa yayi jinyar Abdallag har ya warke kuma a nan ne ya nuna shaawarsa ta son juya akalar kartunsa ga addini. Yayi karatu sosai tare da Baba Malam har aka gama bautar kasa ya kara lokaci. Da malam yaga bashi da niyyar komawa gida yayi masa nasiha sosai. A dole ya koma 'yan uwansa bayan doguwar mita suka hakura. Bayan wasu shekaru ne lokacin da Munnira ta gama secondary Baba Malam ya bashi aurenta saboda ya yaba da hankalinsa kuma yaga bashi da niyyar aure sai karatu.

A lokacin ne kuma Aliyu da kansa ya nemi auren Abu wato haj zainab ko muce Momi matarsa ta biyu. Yakumbo ta dada tsorata da lamarin Allah. Wato zafin nema baya kawo samu. Gashi da kansa ya nemi auren. Ta kira Basiru ta roke shi da su binne maganar abinda ya faru zata cigaba da kulawa da hashim har mutuwarta. Kuma ba zata taba tona wannan abin ba tunda basu sani ba. Sannan ta gargade shi da kada ya bari baban Abu ya sani domin shi mafadaci ne akan abinda yake gaskiya ita ma yayarsa tsoronsa take ji.



Batul Mamman ๐Ÿ’–



๐Ÿ’• MEYE DALILIKA๐Ÿ’ž 25

Ko da Yakumbo ta gama bada nata labarin shima Malam ya fadi abinda ya faru a zaria. Dakin sai sautin kuka da salati ake ji. Har kasa Yakumbo ta tsuguna neman gafara. Baba ya sauko daga kan gadonsa yace ta tashi. Ai ni Yakumbo tunda dai ta tabbata Ahmad dana ne wallahi na yafe miki sai dai wadanda kika yiwa laifi suna da yawa. Komawa tayi gaban Baba Hashim wanda yake ta zubar da hawaye ka yafe min dana, ka yafe min. Ita ma kukan take yace Allah Ya yafe mana baki daya....ya tuna yadda ko sau daya bata taba nuna kyama ko gazawa akansa ba duk da tsufanta.

Momi ta kalli Yakumbo yanzu duk a kaina kika kusa tarwatsa gidan nan? Nata kukan yafi na kowa bata taba tsammanin wannan badakalar ta shafe ta ba. Ita dai Yakumbo kuka take yi duk wanda ke wurin dole ya tausayawa tsohuwar.

Kafin su fita daga dakin kowa ya yafewa dan uwansa. Malam ya kira mahaifin Umma ya sanar dashi komai.....ikon Allah yafi karfin wasa Abdallah,  hakika Allah Yaso cire maka wannan tunanin na ka aikata zina shiyasa Ya hada zukatan yaran nan don gaskiya tayi halinta. Allah Ya kara mana imani.

Khairi da Ummanta gida suka wuce tare da Malam. Umma kamar ta ari baki wurin bashi hakuri ranar. Sai da suka kebe yace Munnira ban taba jin haushinki ba duk abinda kika yi akan gaskiya ne.

Bayan kwana biyu Baba ya matsa a sallame shi daga asibiti saboda yana son ayi ayi bikin Ahmad da khairinsa.

Bayan ya kai babansa gida, gidansu khairi ya taho. Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta shigo falon. Shiru shiru babu mai niyar magana rabon da su hadu tun ranar da aka fasa kwai a gidan Baba. Ita carpet ma take ta kallo yau. Bata ankara ba taji shi a kusa da ita. Tana dago fuska suka hada ido...gaba dayansu sunji wani irin yanayi a tare dasu. Tayi kokarin matsawa yasa hannu ya riko ta gaba daya ji tayi kamar bata taba shiga yanayin farinciki kamar wannan ba. Bata ki su zauna a haka ba sai kuma ta tuna kada ta bada mata...uncle ka sake ni.  Daya hannun yasa yana shafa fuskarta.... aure ni da ke mutu ka raba kinji ko. Ganin bai fahimce ta ba tace ba haka nake nufi ba. Daga gira yayi yana kallonta me kike nufi? In bari ki zauna kina kallon kasa kamar baki da abin kallo. Kafin ta bashi amsa wanda ita duk a rike ce take saboda yadda yake zagaye fuskarta da dan yatsan sa yace kin rame sosai khairi na. Bana son motsatstsiyar  mace. Lallai ma nice motsatstsiyar? To ni kuma bana son kajamemmen miji. Dukkansu dariya suka yi. Sannan ya hada goshinsa da nata a hankali yace mata I love you Ummulkhair... khairin Uncle Ahmad. Dadi ne ya ratsa zuciyarta. Tayi saurin tashi ta gudu sai wayarsa ta fara ringing. Yana dubawa sunan Mufida ya gani.


Batul Mamman๐Ÿ’–

 ๐Ÿ’•MEYE DALILINKA๐Ÿ’ž 26

Yana dauka ta fara masifa. Na kira Umaima tace tun dazu ka mayar da Baba gida...ina ka tsaya? Ta tambayeshi cikin bacin rai. Bata jira ya bata amsa ba tace ina jiranka maza ka dawo gida. To kawai ya ce ya ajiye wayar domin shi mamaki yake yadda ta sami kwarin gwiwar ya masa magana a haka. Can ya tuna maiko-maikon daya gani a goshinta da kirjinta a daren jiya. Dariya ce ta kubuce masa daya gane kayan mallaka da juya miji akayi amfani dasu shine take gwadawa yau,Allah Yasa khairi ta fice ma yayi mai isarsa. Shegiya to ta Allah ba taki ba ina karanta Ayatul kursiyy har wani surkullen banza zai kamani.

Daga kofar falo Sadiq ya rugo da gudu ya rungume shi. Yana shirin daukarsa ya kula gaba daya hannuwansa da bakinsa harma da gaban rigarsa duk sun baci da miya. Da fada ya shiga gida Mufida tana zaune tana kallo ta galla masa harara. Dama jira nake ka dawo ka wanke masa....ga wurin da yaci abincin ma duk ya bata min ka goge don Atine mai aiki bata nan. Kallonta yayi shekeke sai kuma ya tuna yanzu fa tana tunanin aikin bokanta yayi. Daukan yaron yayi yayi masa wanka ma gaba daya sannan yazo ya gyara wurin. Ranar mufida sai faraa da farinciki. Uncle Ahmad kuma sai dariyar mugunta idan ya faki idonta. Yaro bai san wuta ba sai ya taka...ranar da zan damke ki a hannuna zaki wahala ya fada a ransa.

Sati biyu aka sa bikin Khairi sai dai sam Baba yaki yarda yace shi akwai shirye shiryen da zaiyi. Malam ya dube shi haba Yaya wane shiri kuma ya rage ai kawai  a kaita dakinta. To nuna min iko zaka yi kuma Baba ya tambaya. Allah Ya baka hakuri ya bada amsa. Yana gyara karin hularsa yace ai nasan zaka ce baka son bidia sai dai kada ka manta bikin aure yana da bambanci da taron mutuwa kuma dole mu gayyaci mutane su taya mu murna. After all we have been through Abdallah dole muyi abinda ran kowa zaiyi dadi. Baba Hashim yace duk abinda ya faru da khairi ai baza mu kaita daki ba kamar ladan noma ko yakumbo. Haka ne ta bashi amsa a hankali. Har yau ta kasa sakin jiki da su kamar da.

Mahaifiyar Kausar ita ce ta dauki nauyim gyaran amarya ciki da waje domin mutuniyar nijar ce kuma sana'arta kenan. Hatta turaren wuta na gida duk ita ce take yi. Kwanaki uku kawai da fara gyaran jiki Khairi ta soma canjawa ga wani kamshi da take yi. Abincin da take ci ma ita take bata don a cewarta khairi ta rame saboda ciwo ita kuwa bata son ganin mace a tsamure kamar kudin guzuri. Tana zaune kan kujera  umman kausar ta sa mata kaskon turaren jiki ta lullube ta da katon bargo wayar kausar ta fara ringing sai ta katse. Haka take ta yi da an kira sai tayi rejecting khairi kuwa ta sa ta a gaba da kyar ta fada mata wai Tahir ne yake yawan kiranta a waya. Khairi tayi murmushi to meyasa bakya son dauka ko don ina wurin ne? Lah wallahi ko baki nan bana dauka. Khairi tace to kinsan wulakanci ba halin mu bane. Kika sani ma ko ya fada ne...eyye eyye Kausar ta captain tahir. Nan suka fara aikinsu na cacar baki kamar kananan yara.

Umma ta zage da shirin aurar da tilon yarta su inno ma baa barsu a baya ba. Mufida dai ta cigaba da sa maigida aiki yana biye mata. Ko sau daya taba ce ya fasa auren ba don tasan ko a wurin danginsa bata isa ba. A cewarta zata yi maganin ta idan ta iso.


Batul Mamman๐Ÿ’–
๐Ÿ’•MEYE DALILINKA๐Ÿ’ž 27

Anyi biki na gani na fada sannan kuma ayi abin a tsaftace kamar yadda Malam yaso. Babu kwadon maza da mata ayi ta rawar rashin kunya ko kaga budurwa ta tafe kamar sanda wani lokacin harda masu aure a wurin biki babu mayafi sai gwaggwaro. Ayi dinkin nan riga ta matse duk kayan kirjin su rinka neman fitowa ta sama. Wani katon banza ya kalle ki a bati siddan. Wallahi mu kiyaye mata mu saya wa kawunanmu mutumci.

Ranar asabar za'a kai amarya tasa wani farin material me adon lemon green flowers. Takalminta da 'yar karamar jaka harda katon mayafin da ta lullube jikinta duk lemon green ne. Kamshi take me dadi Anti Rumana da Anti Sadiya kannen ummanta su suka shirya ta. Wata matar wan umman kuwa da suke kira Umma Zainab mouth freshner ta bata kafin ta fito daga daki tace ki fesa yaji kamshi mu ma iyayenki duk a haka muke gyara tsufanmu. Kunya ce ta kama Khairi. Ranar sun sha kuka ita da Ummanta dakyar aka raba su.

Gidan Baba aka kaita yayi mata nasiha. Ana shirin tafiya yace ai Malam ya sanar dashi a bar mijinta yazo ya dauketa saboda haka kowa ta je ganin daki daga baya. Momi dai sai mita don ta gama shirin kai amarya tunda Umma da Hajiya duk babu su. Ko da Uncle Ahmad ya iso da abokinsa daya Baba har waje ya rako su jikin wata sabuwar mota kirar honda silver colour mai kyau. ya kama hannun Khairi ya sa mata makulli a hanunta...cike da mamaki ta dago kanta yace  Ummulkhairi wannan kyautar ki ce fatana ku zauna lafiya da dan uwanki. Sai ka daure ka koya mata don ba taka bace yace da Uncle Ahmad. Godiya suka yi masa yace maza maza ku tafi dare na kara yi. Ahmad ka bar motarka a nan gobe Hashim karami sai ya kawo maka ku tafi a wannan.

Tana kuka baba ya bude kofa da kansa ya zaunar da ita a ciki suka tafi. Kusan mintuna biyar yana tuki sai sautin kukan khair ake ji. Can sai taji shima kamar yana kukan ta dago kai murya duk ta dakushe saboda kuka Uncle lafiya? Shiru yayi ya cigaba da abinda yake yi. Hankalinta ya fara tashi....uncle dina me ta faru? Kwaikwayon muryarta yayi yace Khairina ce bata so na. Bude idanunta tayi wadanda suka yi ja tace wallahi ban fada ba, waye ya gaya maka. Ganin ta rude yasa shi yin dariya ashe kukan gulma kike yi ana turo ki kina wani makalewa. Kin bashi amsa tayi wai ita tayi fushi. Haka yayi ta tsokanarta har suka iso gidan.

Ta kofar kitchen ya shiga da ita sannan ya wuce da ita part dinta. Ita dai bata tambayeshi dalili ba shi kuwa yayi haka ne saboda Mufida da kawayenta da suke babban falon gidan  wanda take sada mutum da dukkan parts din gidan. Suna zaman jiran kwakwaf.

Tun daga falo take jin kamshi lallai su kausar da umaima sunyi aiki. Tana shirin zama ya kama hannunta suka shiga daki. Wani guntun zazzabi taji ya kama ta lokacin da ya rufe kofar...wai itace a daki daya da Uncle dinta. A darare ta zauna a bakin gado ta sake jan mayafi ta rufe fuska. Hmm wai ko wacce amarya don gulma sai tayi ta rufe rufe da an kwana biyu ta fi ruwa iya gudu. Sarai ta fahimce shi amma sai tayi shiru. Hula da rigarsa ya cire daga shi sai dogon wando da singlet ya dawo gabanta ya zauna. Tun dazu kamshinta ke tada masa hankali amma yanzu da ya zauna gabanta abin karuwa yayi....da kyar yace khairina yau ya akayi baki da amsar bayarwa idan nayi magana? Ko har an zo ranar da zan kashe bakin aku ne....tsit ya sake ji sai ya mike ya shiga toilet. Alwala ya dauro ya fito yace itama taje ta yi.

Bayan sunyi sallah ne ya dafa tsakiyar kant yayi addua sannan yayi musu doguwar addua da fatan zaman lafiya. Kazar amarci ta al'adar bahaushe ya kawo mata da lemo, ruwa tare da shawarma don yasan tana son ta. yau dai khairi jiki ba kwari kadan ta ci bayan ya matsa mata. Tashi yayi bayan sun gama yace zaije ya rufe gida tana iya yin wanka kafin ya dawo.

Ko da ya shiga falon mufida ya tarar da kawayenta biyu suna ta shewa. Tayi mamakin ganinsa sai kuma tace ko an fasa kawota ne munji shiru tun dazu...tafawa kawayen suka yi. Shi bai ma taba ganinsu ba kila a gidan boka suka hadu ya fada a zuci. Ku tashi ku tafi zan rufe kofa dare yayi. Kai!!! Mufida tace daga zaune. Kawayen nawa kake kora to babu mai fita sai an kawo wannan ragowar asibitin. Tsawa ya daka musu yace idan basu fita ba zai kira maigadi yayi waje dasu. mikewa tayi cike da mamaki . Yau ita yake wa haka kuma a gaban wadanda ta gama cika baki a gabansu. Suna fita ya rufe kofar gidansa sannan yace mata sai da safe. Kafin tayi magana yayi gaba.

A bakin gadon ya sake ganinta ya wuce ya shiga toilet yayi wanka. Ko da ya fito daga shi sai tawul a kugunsa ya tarar ta juya baya tana ninke mayafi. Niyyarta ta kwanta baccin karya kafin ya fito. Tsayawa yayi yana kare mata kallo ta baya. Riga da skirt din duk sun matse ta ga gashinta da ya fito ta dankwalunta ya kwanta wurin kafadunta. Ji tayi kawai yayi hugging dinta ta baya...nan da nan jiki ya fara rawa. A  ya dawo da kansa daidai kunnenta yayi mata rada a kunne. Zaki yi wankan ne ko nayi miki ya fada bata ma iya bashi amsa ba domin ji tayi yana mata kiss a wuyanta. Duk isakar dakin ita zafi take ji. Juyu da ita yayi ya sake jawota jikinsa ya sake yi....Khairina shiru ba amsa. To ta ina ma zata yi magana bayan yau uncle din nata ya sauya gaba daya. Shi kuwa kasa hakura yayi ji yayi idan bai rike ta ba bazai iya shirin bacci ba. Da kyar ya sake ta ya koma ya shafa mai a jikinsa....a sace ta rinka kallonsa har ya gama ya sa kayan bacci itama ya miko mata wasu riga da wando. Bari na saka miki tunda ke baki iya tattalin miji ba. Ba shafa min mai babu saka min kaya . Sai yanzu tayi magana tace kamar wani baby? Bata ma san maganar ta fito ba. Karbar kayan hannunta yayi yace idan na bazaki min kamar baby ba ni zan miki. Nan suka fara kokawa ya dage shi zai cire mata kaya ya sa mata kayan bacci.

Suna haka suka ji wani irin bugun kofa kamar zaa ballata.



Batul Mamman๐Ÿ’–


๐Ÿ’• MEYE DALILINKA๐Ÿ’ž 28

Bugun aka sake yi kamar maiyi na da tabin hankali. Fita Uncle Ahmad yayi yaje ya bude kofar ita kuwa khairi tana cikin daki. Yana murda mukulli ta banko kofar dakin. Don wulakanci sai ka dawo dakin nan ka zauna idan ba'a kawo amaryar ba sai ka hakura. Yana kallonta fuskar nan tasha hoda har ta so tayi yawa ga uban kwalli ido rambajau. Lallai mufida ta dage da son juya miji. Daga daki Khairi na jiyo maganganun da take ita mamaki ne ya kamata dama haka Anti mufida take. Lallai zata koya mata hankali don ko bata auren Uncle bazata jure matarsa taci mutumcinsa ba a matsayinsa na yayanta.

Mufida ki koma dakinki khairi na ciki. Me ka ce? To ta ina ta shigo wannan karon cikin ido take kallonsa. Tare muke Mallam baya son taron kai amarya ya bata amsa. Ganin ya kalli fuskarta da idonta yasa tace kaga Abban Iman nifa ban yarda ka kwana a dakin nan ba ka wuce kawai mu tafi. Yana kokarin magana tace dakata bana son jin komai kawai ka wuce. Khairi dai abin duniya ne ya isheta lallai uncle ya bari ake masa haka. Muje kawai yace da ita Khairi tayi saurin fitowa daidai lokacin da yake jan hannun mufida. Wani azababben kishi ne ya kama ta suna fita ta kama kofar dakin ta kulle ta ciki. Ta fada gado tana kuka.

Dakinsa ya wuce da ita don baya son tashin yaransa a dakinta sannan baya son yin hayaniya gaban khairinsa saboda bata da ishasshiyar lafiya. suna shiga yace ke ni kike wa tsawa saboda baki da kunya? Ko kina zaton ban san abinda kike yi ba? Wallahi idan kika sake kokarin maimaita abinda kika yi yanzu sai na fasa miki jiki. Shashashar banza da iliminki da wayonki kin mayar da kanki mahaukaciya. Ganin yadda ya rufe ido yana mata fada yasa tayi shiru har ya gama fadansa ya fita. Da sake wallahi damanasan zaa rina kishi da yar malam . wato itama tazo da shirinta.

Ko da ya koma sai ya shiga falon nata ya kulle kofa ya kama kofar daki yaji a rufe. Murmushi yayi wato tayi fushi tun yanzu kenan. Khairina please ki bude kofar. Tana daga kan gado ta share hawaye anki din....tohhh rashin kunya kika fara kema? Shiru yaji tayi. Idan baki bude ba zan koma wurin mufida. Sai ka dawo ta bashi amsa amma a zuciyart tana tsoron kada ya tafin da gaske. To ki taso ki kulle kofar falon sai da safe. Tasowa tayi ta dauki mayafinta ta yafa kan rigar baccin da ta saka ta dawo bakin kofar da sabon kukanta. Yanzu maimakon ka bani hakuri sai ka koma? Ashe fushin karya kike ma tunda har kin karaya ya bata amsa. Sweet dreams kinji khairina. Alamar an bude kofa an rufe taji hasken fitilar da take hangowa ya bace. Cike da takaici ta bude kofar daki da gaske ka tafi take magana cikin muryar kuka tana shafa bango don bata san inda makunnin filar yake ba. Lallai ma sai na fadawa Umma gobe ta sake fada. Ji ta yi an daga ta gaba daya ya shiga dakin ya ajiye kan gado.

Kulle kofar dakin yayi tare da kashe fitila ya dawo ya kwanta tare da jawota jikinsa. Me zaki fadawa Umman? Uhmmm tace a hankali. Baki ji me nace ba zo na maimaita miki. Kwacewa tayi ta koma gefen gado ka koma wurin anti mufida. Allah Ya baki hakuri khairina yace tare da sake janyota jikinsa. A haka suka yi bacci. Kamshin da take yana dada tada masa hankali sai dai yasan yadda take rai a bace ta wani kankame jiki gara ya barta ta huta.


Batul Mamman๐Ÿ’–



 ๐Ÿ’• MEYE DALILIKA ๐Ÿ’ž29


Har yadawo daga masallaci tana bacci. Ji tayi ana ja mata yatsun kafa ba shiri ta tashi tana dariya don ita  ana taba mata kafa ji take kamar cakulkuli ne. To shashashar madina daga taba kafa ya fada yana zama kan gadon. kinyi sallah kuwa? Saurin mikewa tayi tace a'a meyasa baka tashe ni ba ta fada tana tabe baki. Har dundu nayi miki ashe haka kike da nauyin bacci. To daga yau da ruwan sanyi zan rinka tashinki. Wucewa tayi toilet tayi alwala bayan ta idar da sallah ta jira ya kammala karatun Qur'an ta gaishe shi. Kin amsawa yayi sai da ya ajiye Qur'anin yace wa ya fada miki haka ake gaishe da miji. To ya zan gaisheka Uncle? Lips dinsa ya nuna mata tayi kamar bata gane ba. Bushewa yayi ne kake son na miko maka mai. Kin manta tsagewa yayi ki miko allura da zare. Biyota yayi tayi saurin shiga toilet ta rufe.

Bayan ta fito daga wanka ta tarar baya dakin. Riga da skirt ta saka na atampa dinkin yayi mata kyau. Turare da humra kuwa sunyi aiki. Tana fitowa falonta ya shigo shima yayi wankan yana ta kamshi. Fito muyi breakfast yace tare da komawa. Biyo bayanshi tayi. Tana shiga babban falon taji an rikota ta baya. Anti Khairi wai kin zama maman mu kema? Iman ce yar shekara hudu me sunan hajiyar uncle. Na zama ta amsa mata sannan ta daga ta sama yadda ta saba yi mata. Sadiq ne ya taho yana cewa nima nima. Shima daga shi tayi yana ta dariya. Uncle Ahmad yana  kan kujera yana musu dariya. Suna haka Mufida ta fito da tray a hannunta. Khairi tace Anti Mufida ina kwana....wace irin anti kuma ana zaune kalau? Idan ni antinki ce ai bazaki aure min miji ba. Shiru khairi tayi bata ba ta amsa ba. Mufida ta dubi mijinta  ina fata ba zuwa kayi da ita ku ci abinci ba don wallahi bazanyi mata girki ba Kura da shan duka gardi da kwashe kudi. Uncle Ahmad yace Khairina muje dakina akwai kayan tea.

Bayan sun gama ya kira mufida a waya. Sai da ta fi 20minutes kafin ta zo ran Uncle duk ya gama baci. Khairi tana ta kallon yanayin fuskarsa ranta yana sosuwa. Ita tasan har ga Allah bata zo da niyar fitina ba gidan amma tana ganin zata saitawa Mufida zama indai ta nemi batawa mijinta rai. Banko kofar tayi ta shigo ta sami wuri ta zauna tana ta kumburi fuskar nan tasha hoda. A ransa Uncle yace narambada wannan boka ya cuceni. To dama magana zanyi muku game da yadda nake son tafiyar da gidana. Bana son rigima ko tashin hankali saboda haka ku kiyaye....abu na biyu kowa nayi mata kitchn dinta duk me girki ita zata dafa abincin duka gida. Ga store nan duk abinda babu magana zaku yi. sannan zaku rinka raba kwana bibbiyu bayan an gama kwanaki bakwai na farko. Idan da mai tambaya sai tayi. Mufida mikewa tayi kayi ka gama rawar kafarka akan wannan yarinyar da ta rasa miji. Wani takaici ne ya kama khairi tana ganin Uncle Ahmad ya tashi da niyar fada sai kawai ta ja hannub rigarta daya zip dinta ya bude ta baya ta tashi ta tafi gabansa. Uncle dina zuge min zip dinnan please. Yadda take maganar yasa yayi murmushi ya tashi. Ai da gudu Mufida ta fita tana kuka. Iskancin har a gabana Allah Ya isa.



Batul Mamman๐Ÿ’–


 ๐Ÿ’•MEYE DALILINKA๐Ÿ’ž 30

Tana fita suna jiwo muryarta tana ta fada. Ina kokarin daidaita matsala kina karawa ko Khairina...ashe kin iya rigima. Don Allah kada ki biye mata kema kila kiyi abinda ya fi nata idan kika ji zanyi aure. Yana magana yana jan hancinta.

Karar mota suka ji yayi saurin sakin khairi tare da lekawa waje ta window. Mufida ce taja mota ta fita da yaranta a ciki. Yadda ya juyo ransa a bace ya nuna khairi wallahi duk yarinyar da ta yi min yaji sai dai iyayenta su kawota. Ba 'yar da zanyi biko. Yadda yake fada sai ka ce khairi ce tayi laifi. Ficewa tayi daga dakin itama rai a bace.

Ranar haka ta wuni sukuku shi kuwa Uncle ko dakinta baije ba. Ko da wasa bai taba tunanin rabuwa da mufida ba saboda yana sonta amma ya rasa waye ya bata gurguwar shawara har ta fara neman hanyar bata. Mukullinsa ya dauka shima ya fita daga gidan. Har ya kusa kwana ta tuna baiyi wa khairi adalci ba. Dawowa yayi ya tarar tana toilet. Duk yadda ya buga taki budewa. Dakin Mufida ya koma ya nemo yan tarkacen mallakar da take amfani dasu ya nufi gidan Malam.

Girgiza kai Malam ya rinka yi da yaji bayanin Ahmad. To ka kira ta a waya kaji inda ta tafi ne? A'a malam amma nasan gida zata je. Wayar babanta Malam ya kira ya tabbatar da zuwanta. Ai nima kiranka nake shirin yi ka rigani. Daga anyi mata kishiya sai yaji. Abinda nake so ka kyale ta har sai tayi sati taji uwar da ake ji a gidan sai muyi maganar. Malam yace ai bazaayi haka ba ni ina da karatu ne yau na kusa makara amma gobe in Allah Ya yarda zanzo mu tattauna. Godiya yayi masa sosai. Bayan ya ajiye wayar ya sanar da mahaifiyarta. Itama ko kadan bata goyi bayanta ba.

Khairi dai ana fushi da  angon saboda haka da ya dawo bayan laasar ta hade masa fuska. Dariya yayi Khairina kinyi fushi ne...ko dago kai bata yi ba tana daddana waya a kan kujera. Zama yayi ya kwashe kafafunta ya dora kan cinyarsa. Tana jin haka ta fara murmushi sai kuma ta dake kada tayi saurin sauka. Tafiyar tsotsa ya fara mata sai dariya tana kokarin kwacewa. Rungume ta yayi yana mata magana a kunne. Kiyi hakuri kinji khairina. Bata bashi amsa ba jin yadda yake shafa mata baya. Can taji yace nifa yunwa nake ji. Ta tura baki bayan baka bani komai naci ba ka fita. Da sauri ya tashi tun safe haka kika zร una. Don Allah kiyi hakuri. Bari na dafa miki indomie da kaina sai na hada miki gas cooker dinki ta baya. Ganin ya rikice tace kai dai wasa nake. Naga zaka min horon yunwa ne shine na hada ai ba wuya. Ga naka abincin can amma ba nama don ban gani ba. Kissing din goshinta yayi duk da haka kiyi hakuri.

Daren ranar kuwa anyi kwanan farinciki tsakanin ma'auratan. Khairin Uncle har Allah Ya isa tayi masa karshe tace masa mugu saboda ganin yadda ta wahala yayi mata allurar bacci. Da taimakonsa ta tashi ya cika mata bucket da ruwan zafi tayi wanka. Sai da tayi sallah ta shirya tsaf ya dawo dakin. Tana ganinsa jiki ya fara rawa. Dariya yayi harda hawaye ta mugunta. Haka kike da tsoro dama...harararsa tayi kai amma kinyi kyau kamar a sake. Sai hawaye ya gani sharrr. Ikon Allah na auro mai arhar hawaye. Rarrashi ya zauna yi bayan tayi shiru yace yanzu khairina jiya fa kin min Allah Ya isa. Bude idanu tayi ni din? Kwarai kuwa harda kirana mugu. Gaskiya bani bace ta fada tana dariya. Ni har ina tunanin irin rakin da zaki yi lokacin haihuwa.


 ๐Ÿ’•MEYE DALILINKA๐Ÿ’ž 31

Bai bari tayi komai ba ranar duk. Da kansa ya sama musu abinda za su ci. Yana dawowa daga sallar laasar yace mata zaije wurin Malam. Ta so binshi yace idan ba so take ayi musu fada ba su bari ko sati ta cika.

Har bakin kofa ta rako shi yana rike da hannunta. Sai ka dawo Uncle dina kada ka dade...kashe mata ido yayi akwai abinda zaki bani ne ko salon na dawo a bini da Allah Ya isa. Hannuwanta biyu tasa ta rufe ido cike da kunya ta koma ciki da gudu.

Kana ganinshi kasan yana tare da nishadi. Yana zuwa bayan ya gaisa da mutan gidan Malam yace ya tashi su tafi gidan su Mufida. Bata rai yayi ni fa har rantsuwa nayi bazan taba zuwa biko ba duk ranar da tayi yaji. Murmushi Malam yayi ai ba biko zamu ba. Ina son muje iyayenta su san abinda take yi ne domin suyi mata fada. Idan aka kyale ta zata cigaba da shirka ne. Ni fa shiyasa naji na ma gaji da zama da ita Malam. Tunda har take iya zuwa wurin bokaye ko yan tsibbu. Ai tasan hakan ba karamin sabo bane. Eh lallai zaka ce haka mana tunda ka kwashi budurwa. Kunya ce ta kama shi jin malam  ya fadi haka. Suna shiga motar Ahmad, malam yace ban aminci ko Yaya yasan maganar nan ba balle Ummulkhair. Shi rike sirri yana da kyau kuma rufin asirin matarka rufin asirinka ne.

Hotoro suka nufa gidansu Mufida. Mahaifinta ne zaune da Uncle Ahmad da Dr Abdallah. Sun gaisa cikin girmama juna sannan suka fara abinda ya kawo su. Mufida aka kirawo tare da mahaifiyarta wadda ta shigo ne don ta gaisa da Malam. Tana shirin fita yace ai gara ta zauna.

Malam yace me akayi miki kika dawo gida Mufida? Rainin wayo tace a ranta kamar ba yar cikinsa ya turo mata suyi sharing miji ba. A zahiri kuwa cewa tayi babu komai. Ashe baki san cewa duk matar da take fita ba tare da izinin mijinta ba duk taku daya a wuta take yinsa ba. (To yan uwana mata masu tambayar fita daya suyi biye biye ko ayi satar unguwa. Don Allah mu kiyaye domin haramun ne).

Da bata bada amsa ba sai ya fiddo ledar da Uncle ya kawo mishi. Tana gani ta razana sosai Malam ya hade fuska yana mata magana a matsayinsa na malami ba uban miji ba. Kuka ta fara yi iyayenta basu gane me yake faruwa ba sai da uncle yayi musu bayani. Kuma ta fara amfani dasu ne kafin ma zancen aurensa ya tashi. Mahaifiyarta ce ta rinka dukanta yanzu zubar min da mutumci zaki yi mufida? Ashe ban miki tarbiyar arziki ba. Tana magana tana kuka. Babanta duk kunya ta kamashi. Shi dai Ahmad baice komai ba.

Babanta ya dago kai Mufida wa ya koya miki zuwa gidan boka? Baki san sallarki ta kwanaki arbain bazasu karbu ba banda shirka ta yadda da su. Cikin kuka tace wallahi Baba ba boka bane. Malami ne shima sunansa Mai Dafa'i. Sunansa mai uwarki dai inji mamanta. Malam yace haba hajiya ya zaki zage ta. Huci kawai take yi don takaici so tayi a barta ta jibgi yar banza. Cikin kuka ta kwatanta gidansa a wata unguwa. Dabara ta fadowa malam yace ai kawarki da kuke zuwa tare ce ta tona miki asiri. Ta kalle shi tana sharar hawaye kuma fa wallahi malam ita ce ta dage sai munje. Lallai Laraba ta cuceni. Yace to ya kamata kusani akwai bambanci tsakanin boka da malam. Duk wanda zai zauna yana bugun kasa ko a baki dogon carbi ace ki kama daya duk ba hanyar Allah bace. Yanzu an baki hoda da kwalli ki mallake miji to daga mallakar sai me. Karshe bazaki taba jin dadin zaman ba tunda kinsan ba don Allah yake miki ba kuma tun daga kabari a fara azabtar da mutum kafin aje lahira. Suna amfani ne da son duniyarku sai su kira kansu malamai a wurin irinku masu sauran imanin da basa son zuwa wurin boka.
Mufida tayi shiru maganar ta shigeta ta bawa iyayenta da mijinta hakuri. Malam yace ta shirya yaranta ta koma gida tunda ba sakinta mijinta yayi ba.

Tana fita Malam yace da Ahmad ka nemi laraban nan ko wace kayi mata nasiha idan bata ji ba ka hanata shiga gidanka. Baban Mufida yace au baka santa ba dama. Wayo kawai nayi mata nasan dole kaita aka yi.

Tunda ta koma gidan Uncle Ahmad ake zaman lafiya. Rayuwarsu abin shaawa. Lokacin da khairi ta sami ciki Uncle Ahmad ya ga shagwaba iri iri. Mufida tana biye mata suna tsula tsiya son ransu.

Tun safe take jin ciwo kadan kadan tana daurewa. Suna falo Mufida tace anya Khairi ko abin yazo ne. Khairi tace a'a saura sati uku fa. Cikin dare kuwa ciwo yasa ta farka daga bacci ta dumawa Uncle dundu ya tashi ba shiri. Kai khairina me ya faru. Jin tana numfashi da kyar yayi saurin tashi ya kunna fitila. Cikinta ta nuna masa yace yana zuwa ya tafi ya dauko handgloves zai dubata sai mamaki ya kamashi ganin har kai ya fara fitowa. A daki su kadai ya taimaka mata ta haifo masa santaleliyar budurwa. Sai da ya yanke cibi ya jira mahaifa ta fito sannan yaje ya taso mufida. Tana ganin jini jikinta ya fara rawa na shiga uku Abban Iman meye wannan? Wani kuka taji baby tana sanar da zuwanta. Ai bata tsaya daukan baby ba ta tafi neman ruwan zafi. Ta wanke baby tas tasa mata kaya. Itama khairi tayi wanka mufida ta hada mata tea mai zafi tasha. Sai da asuba suka rinka buga waya Umma da kyar ta jira takwas na safe tayi. Malam yana ta mata tsiya yar fari ce fa. Tace ai yau duk mai iyawa ya kirani mara kunya amma sai na je.

Khairi na kwance a daki ya shiga. Khairin Uncle a zama mama. Tayi dariya dama jira nake kazo. To gani wani cikin zan miki ne...an gaya maka ina tsoro ne ....yanzu dai kaga banyi raki ba kyauta zaka bani. Kin manta naci dundu a baya. Kinsa ina tafiya kamar tare mukayi nakudar. Rungume matarsa yayi Allah Yayi miki albarka. I love you...love you too uncle dina. Nan suka yi shawarar sunan baby da zaa sawa baby.

Suna ta boye boye sai ranar suna kowa yaji sunan yarinya Hawwa amma zasu kirata Jiddah saboda sunan Yakumbo ne. Ita kam Yakumbo har kuka tayi yaran da taso bata tsakanin iyayensu ne suka yi mata wannan karar.

Jiddah na bacci Uncle ya fara mintsinin khairi tana juyuwa yace Khairina tashi ayi sabon baby please. Yadda yayi maganar yasa tayi dariya yana fara kissing dinta Jiddah ta tsala ihu. Duk suka juyo suna lalubenta don har an kashe fitila.....

To daga nan zamuyi sallama da iyalan Dr Ahmad Aliyu Saraki. Sai muce Allah Ya bawa kowace mace mijin kwarai Ya zaunar damu lfy da mazanmu Ya bamu zuria dayyiba.




Taku Batul Mamman๐Ÿ’–