π JUWAIRIYYAπ
Zuciyarta cike da fushi tana ta sauri kamar ta tashi sama. Duk wannan saurin tsoronta daya kada Tasi ya shiga gida kafin ta cimmasa. Yau sai ta masa dukan tsiya wallahi don ita bata tsoron ta mutu bare tayi rai. Nafisa ce ta taba ta tace Yaya kinga Tasi chan da abokansa. Kafin ta gama magana yayar tata ta ruga da gudu taci kwalar Tasi cikin fushi tace kai don ubanka me ka fadawa malam dazu a islamiyya. Ya make mata hannu tare da cewa gaskiya na fada masa, ba wani abu yasa kuke makara ba face rike sandar tsohonku da kuke aje bara. Abokansa kuwa sai ihu da dariya suna fadin sai 'ya'yan Idi makaho.
Zuciyar mata fa tazo wuya nan ta rufe ido tana kai musu dukan mahaukata. Da Allah Ya bata sa'a ta kama kwalar Tasi sai kokawa ta kachame. Nafisa da Bidaya suna ganin abin ya baci sai gida da gudu.
Mama tana kwasar tuwo ta gansu a gigice ta fara fadan yau ma tseren kuka yi ko kamar maza. Bidaya tace Mama Yaya Ju ce suke fada da Tasin Baba Ya'u. Nan take ta saki marar dake hannunta tana kwalawa Ismail kira. Ya fito yace mama naji abinda suka ce muje ki raka ni Bidaya.
Akan Tasi ya hango ta tana tula masa kasa a baki yara sun taro ana ta wakar ku casu bamban ku casu. Ismail yayi sauri ya finciko kanwarsa tare da bata kyawawan mari har biyu sannan yaja hannunta gida.
A tsakar gida suka riski iyayenta wanda tun kafin su iso ake jiwo kukanta daga soro don ta maru. Mama cikin fushi itama ta damko ta ta fara duka tana fada. Yanzu Juwairiyya bakya jin dadi sai kin dauko min magana ko. Ta cigaba da cewa shekarunki goma sha hudu fa amma bazaki dena dambe da maza ba. Na fada miki ke macece ba namiji ba yayyanki maza ma wallahi basuyi abinda kike ba. Duk wannan abin da ake Juwairiyya bata ce komai ba kukan ma ta dena ganin yadda babanta yake lalube da hannunsa yana kokarin hana mama dukanta. Yace Mariya kiyi hakuri don Allah ki bar dukanta. Juwairiyya ta kama hannun babanta ta zaunar dashi akan tabarma. Yana zama ya lalubi kunnenta yace wai meyasa bakya jin magana. Ta share hawayen idonta tace Baba zaginmu suke harda cewa bara muke raka ka. Wallahi idan zasu zageka sau dubu zan rama sau dubu ai ba tsoronsu nake ba. Ismail yayi saurin doke mata baki wato ana miki fada ke ko gezau bakiyi ba har kina dada maida martani. Baba yace bari dukanta haka. Ya sake rike mata hannu yace Juwairiyya kinsan dai dani da baban Tasi wa da kani ne ko. Ta kada baki tace ai ba babarku daya ba. Mama ta jefa mata harara tace wai baza kiyi shiru ba. Baba ya cigaba da cewa ki rinka hakuri akan duk abinda zasu fada miki ko yan uwanki. Kinga Ismail da yayanku Najib basa kula su, kuma ma ai duk garin nan babu wanda zaice ya taba ganina da kwanon bara. Nan duk 'ya'yansa dake wurin suka yi murmushi saboda yanayin da ya fadi maganar banda mama da ta ce Alhaji kaine kake sa yaran nan basa daukar maganarka da girma saboda kana musu wasa. Yace to kowa ya kallo ni nan suna kallon shi kuwa ya sha kunu a dole ya bata rai suka sake yin murmushi Ju kuwa har sautin dariyarta ake ji. Yace don Allah ku dena biye musu ko me zasu fada. Lalurar makanta jarabawa ce daga Allah. Da ina da idona rangadau farare kal kamar na Najib da Ismail. Kuyi hakuri yan mata bansan yaya naku suke ba. Amma dai abinda nake so ku gane shine ni bana bakin ciki da niimar da Allah Yayi min da kuma cikin ikon Sa yanzu ma da lalurar tazo bamu kasance cikin kaskanci ba. Zai cigaba da magana yaji kiran sallah sai yace a tashi ayi alwala Allah Yayi muku albarka. Ju ta debo wa babanta ruwa ta zuba masa yayi alwala ismail yayi masa jagora zuwa masallaci
**********************
Bayan kwana biyu da fadan Ju da Tasi tana dawowa daga makarantar boko taci karo dashi a kwanar gidan liman shima ya taso da yan korarsa a baya Lado da Haladu. Suka fara binta da sauri dama yaci alwashin rama abinda tayi masa a rannan duk da rashin mutumcin da babarsa taje tayiwa maman su Ju har gida da wanda babansa yayiwa babanta a kofar gida. Ju dai ko a jikinta data gansu duk da cewar ita kadai ce yau abokiyar tafiyar tata Madina bata je makaranta ba saboda ranar hutu ce garesu yan aji biyar an gama jarabawar kwalifayin zasu dan kwana biyu a gida kafin sakamako ya fito. Tasi da abokansa suka samu suka tare mata hanya yace ke ubanwa kika zubawa kasa a baki shekaranjiya?Tace uhmm wai dani kake? Yace hade girar sama da kasa ya sake maimata tambayarsa. Tace to ubanka na zubawa mai jajayen hakora.
Tasi yace yarinya yau kin gama yawo. Ya cakume ta zasu fara kokawa ta aje jakarta a gefe ta Allah Ya gani bani na takali fadan nan ba.tana fadin haka ta kai masa duka a ciki nan fa maxa uku suka far mata suna dukanta amma bakinta yaki mutuwa sai masifa take tana dukansu itama. Liman ne ya fito yaga abinda ke faruwa yayi musu tsawa suka tsere. Ju kuwa yau an mata taron dangi hijabinta ya yage har kasa ga wuyan riga shima ya yage har kusan cibiyarta. Gashi ita yarinya ce mai garin jiki kirginta ya kusa gama cika. sai da liman yace wuce ki tafi gida ta kula da yadda kayanta suka yi budu budu ga yagewa. Yau tasan ta gama yawo a wurin mama.
**********************
Ju ta bayan gidansu ta zaga ta taka wani kututturen itace ta haura katanga. Tana dira bidaya tana watsa shara nan take ta kwala ihu. Mama ce tazo da gudu tana tambayar lafiya.itama turus tayi yadda ba don jininta bace itama bata gane ju ba. Bidaya kuwa runtse ido tayi tana fadin mama aljani. Mama kam ko baa fada ba tasan yau ma yar tata tayi sanaar da ta saba. Batare da cewa komai ba ta koma da baya taje ta tada Najib wanda bai dade da dawowa daga makatanta ba yana level 3 a jamiar garinsu wato wudil wadda aka fi kira da KUST. Tace fito a hankali kada babanku yaji ina jiranka a wurin shanya. Ai nan ya sameta da wayar redio a hannu ta bashi ta nemi wuri ta zauna a kasa tace zanemin 'yar iskar yarinyar nan wadda bata jin magana. Najib dama haka nan ma cin zali ne dashi bare an bashi license. Nan ya fara dukanta ko tambayar baasi babu. Kamar kullum yauma ba ihu sai hawaye da take zubarwa a zuciyarta kuwa tana kara rayawa wallahi duk wanda zai zagar mata uba Allah ne zai raba ta dashi. Ju kenan ta baba idris.
Tun da ta fara wayo ta gane babanta makaho ne take tausayinsa. Wani lokacin sai ta sami loko tayi ta kuka saboda tausayinsa. Akan baba Ju ta fara qiyamul layl tunda wata rana malamin su yace duk mai yinta komai ya roka Allah zai amsa. Mama da kanta ta fuskanci hankalin Ju kamar baya tare da ita tace wa Najib ya kyale ta. Suna juyawa suka ga baba a tsaye rike da hannun bidaya. Yace idan kun gama dukan ku bani 'yata. Ju wadda kanta yake a durkushe tana jin muryar Baba sai kuka mai tsuma zuciya taje ta kankame shi tace wallahi baba na tsane su kuma bazan yafewa duk wanda ya zage ka ba.
Wannan abu yasa Mama kuka itama. Suka koma dakin Baba gaba dayansu sai yace a fita a barshi da mama da ju. Kowa na fita yace Juwairiyya kina so inyi fushi dake ne. Tayin saurin cewa a'a. Yace to daga yau idan kika sake fada a waje a kaina bani ba...bata bari ya karasa ba tace WALLAHI WALLAHI WALLAHI bazan kara ba.Sai yace tashi kije Allah Yayi miki albarka. Tana fita yace mariya yarinyar nan ta gado fushinki. Ita kanta mama yadda Baba ke magana ya bata tausayi domin tunda ya kamu da lalurar nan baya ko daga murya yace yana gudun kada ladan hakurinsa ya ragu. Mama tace Alhaji yau fa duk kayan jikinta a yage suke gashi kamar an mata wanka da kasa. Yarinyar nan mace ce amma abinda take ko namiji ne dole ayi masa fada.Baba yace mu cigaba da yi mata adduar shiriya da kuma sassautawar zuciya.
********************
Hajiya Asiya ta dubi yar uwarta tace ni tun ranar da kika min waya akan fadan da Juwairiyya tayi hankali na bai kwanta ba don babansu Amal baya nan ne da washegari zaki ganni a garin nan. Idan kin yarda mariya ki barni na tafi da ita kano tunda ta gama jarabawa kafin result ya fito. Mama tace anya yaya ayi haka da dai kin bari sai nan da sati ukun muzo bikin Amal tare. Yarinyar nan kawa zucin gida gareta gashi duk safiya da dare sai tazo taga babanta. Haj Asiya tace wai kin manta yadda kike likewa baba ne da kamar kaska ta fada taba dariya. Kuma yarinyar nan ina ga kawai tausayin babanta take yi. Ga karayar arziki ga makanta lokaci guda dole a tausaya masa. Ki bari mu tafi muyi shirye shiryen bikin yayarta Amal da ita tunda su nafisa basu yi hutu ba ga Alhaji bazaki iya zuwa da wuri ba.
Baba ma ya amince bayan da mama tayi masa bayanin shawarar da yayarta ta kawo. Ju kuwa an gama hada kaya da murnar zuwa wurin yaya amal sai dai kafin ta isha ta lallaba ta fita taje gidan wan mahaifinta wanda shine silar karayar arzikinsa da makantarsa ta sami Baaba mai koko tana tatar gasara ta tsaya ta kama kugu tana murguda baki tace mai koko zan tafi kano gobe nasan duk kowa yana ciki suna sanaar kallo to ki fada musu duk wanda ya zagar min uba ko yan gidanmu Allah Ya isa. Tana fadin haka ta ruga ta koma gida. Mai koko ta bata sami mayar da magana ba ta rike baki tace bari malam ya dawo idan bamuyi da gaske ba yarinyar nan zata tona mana asiri wata rana.
Sai mun sake haduwa da jin rayuwar Juwairiyya (Ju) a kano da asirin da su Mai koko suke tsoron ta bayyana.
π JUWAIRIYYAπ 2
Jan motar su Haj Asiya ke da wuya mal Yau ya fita shima bayan sun gama shawara da maikoko. Bakin titi yaje ya tari mota sai wani kauye. Boka Dillin yana ganinsa yace mugu dan masara yau kuma bayan wa kake son gani. Mal Yau ya zauna a inda ya saba idan tasa ta kawo shi yace yarinyar kanina ke neman ballo min ruwa kasan na fada maka tasan komai don ma kayi kokarin rike bakinta ne. Amma fa bata tsorona yanzu kada wata rana tayi magana. Sannan akwai yayar babarta kusan ita ce gatsnsu yanzu. Itama ina son a hada su duk a tada musu hankali. Tazo ta dauki Zuwairan sun tafi kano bikin yarta. Boka yayi dariyar mugunta yace indai wannan ce matsalar to an gama fadi wata idan akwai.
*************************
Ana bude gate din gidan Haj Asiya wani dadi ya rufe Ju. Ita dai tana son gidan mami kamar yadda yaranta da suma yan gidansu suke kiran Hajiyan. Bari uku ne a cikin tankamemen gidan. Daya na Alh Bashir mijin mamin sai na wansa Dr Umar sai kuma na babarsu Hajja a tsakiya.
Mami tace Juwairiyya muje mu far gaida Hajja ko. Tace to Mami ai ni ina sonta tunda tana zuwa duba Baba. Mami tayi murmushi ita kam ta rasa yadda akayi yarinyar nan take son babanta haka.
Suna shiga Ju taga 'ya'yan wan babansu Amal da take kusan saar su Fauza da Yasmin sun takurawa Hajja wai sai sun daura mata gwaggwaro da biki tunda bikin jikokinta biyu zaayi. ita kuma Hajja ta dage tana turewa abin ya ba Ju dariya tana kokarin karasawa gaban Hajjan su gaisa taji ta taka wani abu, kafin ta ankara ta juyu kuwa aka hankada ta ta fadi kada kanta ya bugu da hannun kujera. Tan take kowa hankalinsa ya dawo gare ta wanda ta taka kuwa cikin fushi ya tashi yace are you stupid? kina tafiya bakya kallon gabanki. Hajja tace Asiya duba min goshin yarinyar nan. Kai Rayyan tun dazu nace ka tashi daga kwanciyar nan kayi hanya kaki. Ju kafin Mami ta taba ta ta shafa goshinta taga jini ai nan taΔ·e ta manta da manya a gabanta tace kan uba ka fasa min goshi. Allah Ya isa, kazo ka kwanta kan hanya kuma ni ina jin na taka maka kafa niyata na juyu na baka hakuri. Mami ta daka mata tsawa tace ke Juwairiyya bana son rashin kunya. Ta juya ga Rayyan tace yi hakuri babban yaya. Sai a lokacin ya durkusa ya gaishe da mami sannan kafin ya fita yace ni dai Mami indai wannan ce mai aikin da zaa daukarwa Amal na mun yafe. Hajja tace kuga yaro mara kunya babar matar taka kake fadawa haka? To yarta ce itama.Mami tace Hajja ya zaki korar min da. Duk suka yi dariya sannan suka gaisa
******* ***************
Bayan anyi sallar azahar Ju da Amal sun cin abinci tare suna hira Mami ta fito daga daki ta zauna kan kujera tace Amal idan anyi laasar ki dauki Juwairiyya kuje ku gaida Dada. Tace to Mami amma motata tun safe Abdul zaije siyo min mai giyar ta makale sai dai mal Garba ya kaimu a taki. Mami tace na aike shi gidan mai turaren wuta. Abdul yace dazu naji Ya Rayyan yace zaije yau. Mami tace to ka fada masa akwai yan rakiya. Amma jira su gama cin abincin ka raka kanwarka ta gaida Umma.
Sunje sun gaida Umma matar Baba Umaru har Ju ta zauna hira wajen su Fauza don ita Mami duk yaranta shida maza ne sai Amal ita kadai.
Bayan laasar sun fito zuwa gwangwazo gidan kakarsu babar su Mami wato Dada sai Ju ta hango Ya Rayyan tsaye jikin mota ai kuwa ta taba Amal tace yaya da wancan mutumin zamu je. Tace eh Ju tace shine fa don wulakanci yace min mai aiki. Amal ta kwashe da dariya tace kin dai rama ko. Tace a'a amma zan rama. Abdul autan mami wanda dashi zaa yace ke Ju shine angon fa. Ta zare ido tace angon wa yace na yaya Amal. Ju sai tayi tsit da baki har sukavkarasa mota. Suna shiga Amal tace Ya Rayyan shine ka kira kanwata mai aiki ko. Yana kokarin ribas da mota yace yi hakuri amarya ai ban sani ba.kanwar taki ce akwai baki kamar reza. Ju dai da tasan angon yayarta ne da tayi shiru da bakinta amma jin yace bakinta kamar reza yasa ta bata rai. Shi kuwa sai ya cigaba da cewa she talks alot, i could hear her voice from my room. To Ju taga abin kamar da rainin hankali wai ana magana da turanci a gabanta tace a ranta wallahi sai na rama. Ko yaya Rayyan kalli mudubin zai duba bayansa sai yayi ido hudu da Ju ita kuma tana lura da hakan da ya kallo sai ta murguda baki a haka har suka isa gidan Dada.
*********************
Kwanan Ju uku a gidan Mami amma duk gidan ya fara isarta. Sau biyu tun zuwants ta hadu da Ya Rayyan amma yana ganinta yake bata rai. Inda sabo ta saba da ganin mutanen da basa sonta a gidan baba Yau amma abinda yasa wannan ke damunta tausayin Yaya Amal take ace mutum irin wannan zata aura mara fara yadda take da son mutane.
Yau gidan Hajja a cike yake da baki 'ya'yanta mata Hassana, Usaina da Habiba na duk sun zo saboda taron gaggawa da Hajja ta kira sati biyu kafin a fara biki. Babu kowa a falon sai yayanta maza da matansu sai matan da kuma Amal da Rayyan. Baba Umaru ne ya fara magana da tambayar yaran shin a falon nan akwai wanda ya taba baku shawarar auren juna? Suka ce a'a. Yace madalla. Ku kuka hada kanku sannan kuka sanar damu sai yanzu saura sati biyu auren ku Amal kice kin fasa. Amal wadda kanta a kasa yake tunda aka fara magana tace wallahi Baba idan na aure shi wani mugun abu zai same ni kila ma na mutu. Rayyan wanda ko daren jiya bayan sun gama hira sun dade kuma a waya abin sai ya zo masa wani iri don shi duk a tunaninsa irin nasihar nan aka zo yi musu. A firgice ya dago kai yace Amal what did you just say?. Mami tace na shiga uku Amal lafiyarki kuwa. Anti Usaina tace ni dai yau bayan asuba ta kira ni ta fada min tana kuka shiyasa nazo na sanar da yaya. Hajja tace zo nan Habiba dayake shine sunan Amal na gaskiya. Me ya hadaki da dan uwanki. Cikin kuka tace ba komai. Babanta wanda ya rasa abin fada ya dafe kai yayi shiru, Mami itama cikin kukan tace Alhaji kana jin abinda yarinyar nan take baka ce komai ba. Nan dai ya dago kai yace Rayyan kana son auren nan? Yace eh Abba amma ..... bai karasa magana ba Abba ya mike ya fita. Baa jima ba ya dawo tare da Sagir dansa da kuma Aliyu wanda yake bin Rayyan ya dubi yayansa yace ni dai indan har kun amince a daura auren nan yanzu naga iya gudun ruwanta. Ya dubi Amal yace uwata yau ba don abin nan na gida bane so kike ki mayar dani karamin mutum. Anti Hassana tace yaya Bashir abi maganar nan a hankali. Ta kalli Rayyan tace ka fada mana gaskiya me ya hada ku. Shi da jin abin nan yake kamar wani mummunan mafarki yace wallahi anti babu komai, Amal tace na gaya muku babu komai auren ne bana so. Nan babanta ya kwada mata mari. Baba umaru yace meye haka Bashir ina wuri kana zartar da hukunci. Hajja kam kuka take sosai don tashin hankali ganin haka dai aka yi shawara akan a daura auren idan ma hure mata kunne ake sa yi maganin abin.
A gabansu Abba Bashir ya bada duba dari a matsayin waliyin Rayyan shi kuma Baba Umaru ya karba sauran yaransu maza suka yi sheda. Sagir na gama addua Amal cikin wata irin murya kamar ta maza mara dadin sauraro tace kun daurawa kanku bala'i. Tana fadin haka ta fadi timmm a kasa. Nan da nan kowa yayi kanta cikin rudewa ana salati.
Wai meke shirin faruwa a gidan Hajja ne daga zuwan Ju?
π JUWAIRIYYA π 3
Sagir da Rayyan ne akan Amal suna kokarin dagata amma duk sun kasa. Baba Umaru yace wai me kuke jira ne ku dago ta akai ta dakin Hajja. Sagir yace Baba mun kasa fa. Nan dai hankali ya sake tashi Abba ya fita ya kira liman aka zo ana ta karatun Qur'ani da adduoi.
Ju da sauran yaran da baa barsu sun shiga bangaren Hajja ba duk hankalinsu ya tashi don ko baa fada ba sun san ba lafiya yadda suka ga manya suna ta shige da fice.
Sai bayan magriba Amal ta farka daga yanayin data shiga ta fara kuka. Anyi anyi tayi shiru abu ya gagara karshe dai gidan Marigayi Tafida Abubakar ranar baayi kwanan farinciki ba.
Duk wannan tashin hankali Mami ko kadan batayi kuka ba don sai a yau ma ta kara yarda kuka rahama ga bawa. Asubar fari ta kira kanwarta Mariya a waya ta sanar da ita duk abinda ya faru, sai a lokacin mami tayi kuka tace mariya ban fadawa Dada ba.Mama tace karki damu in shaa Allah yau zan zo. Bayan sun gama waya tayiwa Baban su Ju bayani shima hankalinsa ba karamin tashi yayi ba kuma yayi mats izinin tafiya. Mama ta barwa su Nafisa da babban yaya Najib sallahun yadda zasu kula da gidan da babansu kafin ta dawo. Fitarta ke da wuya wurin 7:30 na safe taci karo da Lawi dan baba Yau ko kallo bata ishe shi ba ya juya ya koma gida. Yana shiga yace da mahaifiyarsa naga ta fita amma ita da Ismail ne inajin tasha zasu. Har ya juya zai koma daki sai yaga yadda innar tasa ta washe baki. Yace wai inna meyasa tun jiya kika ce nasawa mutannen gidan can ido. Tayi murmushi har wawolunta na hakoran gaba ya bayyana tace kai dai jeka nagode. Da sauri maikoko ta shiga daki ta tashi malam Yau tace inajin fa abin ya tabbata don munafukar ta fita kuma inajin kano ta nufa. Yace ai kinsan aikinsa na kyau a hankali maji wane tashin hankalin ya tura mu.
**********************
Rayyan ba karamin damuwa ya shiga ba da gari ya waye ya shiga bangaren Abba suka gaisa da Mami da Mama wadda take ta sharar hawaye bayan ta ga yadda Amal ta ke ance tunda ta farfado haka ta kwana kuka ba sauti sai hawaye. Rayyan ya zauna a kasa yace Mami Abba ya tashi kuwa kafin yayi shiru Abban ya ce gani Rayyan sannan ya zauna suka gaisa da mama. Rayyan yace Abba ni dai idan babu damuwa ko warware auren nan zaayi don ta sami lafiya. Bazan taba samun kwanciyar hankali ba nasan nine silar ciwon nan. Abba yayi murmushi yace yaro kenan ai rayuwa ba haka take ba. Ni bamu san Amal da lalurar aljanu ba amma wallahi bazan taba yi musu yadda suke so ba indai aure ne basa so tayi to sai dai suyi hakuri don Allah Yafi su. Zamu nema mata magani har Allah Ya bata lafiya. ka bar auren idan har sauki bai samu ba da kaina zan shige maka gaba kayi wani auren. Rayyan sai ya fara kuka kamar yaro wanda hakan yayi daidai da shigowar Ju falon tana ganin
yana kuka tace yi hakuri zata sami lafiya in Allah Yarda. Takaici ne ya kama Rayyan ace sai a weakest moment dinsa yarinyar nan zata shigo harda wani bashi hakuri.
Wasawasa yau sati biyu da fara ciwon Amal kullum zata fadi kamar sumammiya kuma tayi mugun nauyi idan ta farfado kuma sai kuka har cikin bacci tana hawaye. Da farko asibiti aka kaita tayi sati daya tasha allurai da drip amma duk a banza don ma asibitin na Baba Umaru ne so baa biyan kudin treatment. Hajja da Dada ne suka yanke shawarar a dawo da ita gida malamai suyi aikinsu.
Mama dai kwananta goma a kano mami tace ta koma wudil kada abin ya zama rashin hankali ta bar yara da babansu shima kuma da tasa lalurar. A dole ta tafi don tasan hakan ne yafi dacewa amma kafin ta tafi mami ta roki alfarmar a bar mata Ju domin bata da waata mace ita take taimaka mata da ayyukan gida kafin su koma makaranta.
Haka Ju ta zauna sai gashi cikin ikon Allah ita kadai Amal ke yarda ta taba ta ko malami ne yazo ita ke riko hannunta su fito falo don tuni aka barta a dakin Hajja.
kullum safiya zata yi wa Mami shara da yan sauran ayyuka duk da akwai mai aiki. Idan ta gama zata je ta gaishe da Hajja ta bawa Amal abinci.
**********************
Kwana biyu ya rage Ju ta koma Wudil sai amal ta dena magana. Ana zaune zata yi fitsari ko kashi sai dai aji wari dole tasa dena fito da ita. Wannan kukan ya ragu amma ta dena magana sai nuni idan ta ga dama. Ranar da ta fara fitsari a zaune Mami tasha kuka don taga alama yarta ta zama nakashashshiya akayi akayi ta tashi a gyarata taki. Ju tana ganin haka itama sai kuka don babanta ne ya fadu mata a rai ita kuma Amal sai ta zata kwaikwayonta take ta tashi ta dawo kusa da ita, umma ce tayi mata signal da ta ja ta toilet ai kuwa akayi saa ta bita. Ju dai taga ikon Allah don Amal ki tayi kowa ya taba ta karshe dai ita ta gyara mata jiki. Tun daga ranar wankin kashi da fitsarin Amal ya dawo gareta harda wanka domin duk wanda ya taba ta ba Ju ba to zata yini ta kwana kuka.
A hankali Amal ta zama kamar yarinya karama Rayyan kam ra rabu da faraa tun ranar da ta fara ciwon don gani yake laifinsa ne. Malamai kam suna ta aikin magani da addua amma dama ciwo ke shiga farat daya sauki sai a hankali gashi aljanun da ake tunani sune a kanta sunki magana ma. Ranar da Ju zata tafi da sassafe umma ta buga kofar gidan mami don kwana tayi tunani. Lanti mai aiki ce ta bude mata sannan ta kira Mami. Bayan sun gaisa tace Asiya ina Abban yara shawara na kawo mana baki daya.
Abba ya zauna shima sun gaisa da Umma tace to ni jiya hankalina ya tashi kan maganar komawar Juwairiyya gida. Ni dai indai da hali ku barni na roki Mariya ta barta a nan kafin Amal ta sami sauki. Kuna ganin irin artabun da ake da ita idan wani ya taba ta ba yar uwar ba. Na fadawa Baba yace muyi shawara tsakaninmu. Abba ya kalli Mami yace ya kika gani? Nasan yarinyar nan kawaici kawai tayi mana akan babanta.
Shin Ju zata yarda ta zauna a kano kuwa???
π JUWAIRIYYA π 4
Ju tayi mamaki da taje yiwa umma sallama tace mata jiki mota ai tare zamu tafi. Taje ta yiwa Hajja ma sallama harda kukanta, anyi sa'a Amal na bacci bata ga fitarsu ba. Da yake tafiyar ba mai nisa bace basu dade ba suka isa ita dai Ju sai tunani take kala kala game da dalilin biyota da Umma tayi.
Motar na tsayawa Ju ta ruga da gudu ta shiga gida ba ko sallama dakin babanta ta nufa ta fada masa a jiki sai kuka. Mama ta fito ta tari Umma duk suka tsaya kallon ikon Allah yadda Ju ta shige jikin babanta tana ta watso masa tambayoyi. Mama tace Zuwaira ba gaisuwa ai kuwa ta bata fuska Allah ni mama ba sunana zuwaira ba, Umma tayi murmushi tace yo tunda ita kin share ta ai dole tace miki zuwaira.
Baba, Mama da Umma ne zaune a falo sai Ju a kasan kujerar da Baba yake zaune umma tace nasan dai Asiya tayi muku bayani tun kafin mu taho a waya amma duk da haka ina son jin ta bakinku. Mama tace Juwairiyya kalli can tana juyawa sai taga akwatinta ne sai wata ghana must go da ledar viva tace Mama kayan meye wannan. Mama tace mata munyi shawara da su Yaya akan zaki koma kano kafin Allah Yasa Amal taji sauki. Duk munsan yadda tafi yarda dake kuma ko dazu kafin ku iso da muka yi waya ina jin ihunta sun kasa bata abinci. Baba ya mika hannu yana laluben Ju sai ta rike hannun yace baki taba yi mun gardama ba idan ba akan dambe ba don Allah kada ki tashi hankali akan tafiyar nan. Umma tace ni muna komawa zan bayar da kudi a siyo miki waya ki rinka gaisawa da Baba kullum.
*************************
A haka dai aka lallaba Ju suka dawo kano tare da alkawarin zaa saka ta makaranta ranar litinin don ta cigaba da karatun ta. Mami ba karamin farin ciki tayi ba da yadda Ju ta kwantar da hankalinta bayan sun dawo ita ma Umma ta cika alkawari ta bata sabuwar waya karama tace idan aka koma makaranta tayi kokari zata canja mata da mai kyau.
A falon Hajja su Ju suna zaune da Yasmin sai ga Yaya Sagir da Yaya Rayyan sun shigo da ledoji masu dauke da note books,text books da sauran kayan makaranta na kannensu. Rayyan ya kalli Ju da take fama da Amal akan ledar pure water yace ke aji nawa zaki shiga ne. Tace SS 3 ya sake cewa science class ko arts? Tace science. Hajja tace wace makarantar za a kaita. Rayyan yace ta su Fauza, ya dubi yan matan yace kuzo ku ware books dinku ku bar bata sauran notebooks din gobe ku shirya da wuri don ni zan kaiku saboda zan biya kudin nata books din. Abdul autan su Amal yace wai ke Ju nufinki aji daya zamu shiga tace kaima ka kusa candy yaya Abdul? Yace ke fa yar kauye ce meye wani candy ana zaune kalau, graduation ake cewa. Ta murguda baki tace to kawai ka gyara min mana sai kace min yar kauye, ai wudil ba kauye bane. kowa yayi dariya banda Rayyan wanda a halin yanzu damuwarsa tafi farincikin sa yawa saboda ciwon Amal. Magani kullum nema ake kuma Alhamdulillah ta rage yawan kukan nan sai dai behaviours din yara.
Mami ta kawo kudin da Abba ya bata dubu dari ta bawa Rayyan lokacin da suke shirin tafiya makaranta tace gashi babban yaya ku tafi da wannan idan ana bukatar kari sai ka fada min. Yace haba Mami ai tunda dalilin Amal aka dawo da ita kano ni zan biya kudin. A mota kannen nasa suka same shi Fauza mayyar zaman gaba tayi sauri ta shiga sai su Yasmin su uku a baya Ju a tsakiyarsu ita da Abdul. Ya Rayyan yace meye haka zama kusa da namiji tace to ba wa na bane. Yace da Abdul get out ko kunya baka ji zama cikin mata. Ke fauza fita ki koma baya kuma daga yau ko driver ne zai kaiku kada na sake ganinka a baya.
Suna fara tafiya Fauza tace Ju wallahi ki dena magana idan Ya Rayyan nayi don baya so. Tace to Allah Ya bani iko.
An zaunar da Ju a wani empty class da papers biyar da ake son yi mata gwaji ko ta cancanci class din da zaa sa ta na maths, english, biology, physics da chemistry. To fa nan ake yinta Ju dai ba turanci sosai saboda yanayin lalacewar govt schools kafin kace meye wannan dai ta gama maths da physics don tana son lissafi sauran papers din kuma abinda ta fahimta tayi wanda bata gane ba tayi kwabarta.
Ko da ta gama wata malama ce tazo ta mayar da ita office din principal inda Ya Rayyan yake jiranta. Principal din Mr Ayodele yace da Rayyan ya tafi da ita gida gobe su dawo bayan anyi marking. Rayyan yayi godiya yace ta taso su tafi.
Washegari Ya Rayyan ya koma school din shi kadai don principal din yayi masa waya yace ya barta a gida yazo shi kadai. Result din Ju ya gani taci maths da physics ba laifin amma sauran dai ba bayani tun ba English ba. Ko da rashin cin jarabawar bai masa dadi ba wani sentence daya karanta ya mugun bashi dariya ta rubuta ( My ankle is the bery wickedest man in wudil). A zuciyarsa yace lallai yarinyar nan ta tsani wannan kawun nata. Ya ce da Mr Ayodele wane class yake jin zaa sata don ta sami ilimi mai kyau. Mr Ayodele yace idan zai yarda zaa mayar da ita SS1. Ya Rayyan yace shi yafi son JS 3 don yana son a gyara mata turanci yadda zata fahimci karatu sosai.
Sai da ya karbo duk books din da zata bukata da uniform ya biya school fees sannan ya tafi wurin aiki. Bayan magrib Rayyan ya sami Mami yayi mata bayani tace JS 3 Rayyan to wallahi kai da kanwarka ni ba ruwana ta fada tana dariya. Ju da ta shiga daki da tulin littafai zata rubuta suna a jiki sai taga duk ansa JS 3 a jiki ta fito tace Yaya ai duk na JS3 ne Allah Yasa ban riga nasa suna ba sai ka mayar musu. Yayi wani dan murmushi yace ai a nan za a saka ki sunce baki iya turanci ba.
Tabdi wannan ai yafi karfin repeating Ju mai shirin candy bana an maka mata demotion.
π JUWAIRIYYA π 5
Kan uban can shine abinda ya fara fitowa daga bakin Ju sannan tace wallahi bazan yarda ba Mami ce dai ta doke bakin tace haba Juwairiyya kullum sai an miki fadan ki dena magana idan babba nayi . Tace Mami kiyi hakuri kinji wai JS 3 zai kaini. Ajin da Yasmin take fa kenan. Rayyan dai yau dariyar mugunta yake ji ya juya zai fita sai ya dawo yace Allah idan kika sake zagi a gidan nan ranki sai ya baci.
Abin takaici baya karewa don Abdul tsokanar Ju ya rinka yi yana kiranta candy. Ranar da kuka tayi bacci. Da gari ya waye taje ta gaishe da Hajja da Umma sannan ta bawa Amal abinci suka tafi makaranta. Abin mamaki Abdul bai kara tsokanarta ba su Fauza da take tsammanin zasu yi suma kowa bakinsa kanin kafarsa. Ashe Rayyan yayi musu warning duk wanda yayi mata dariya zai gamu dashi.
A makaranta Ju taji dadi sosai da taga ajinsu akwai matan da suka fita tsaho banda maza ma. Dama ita ba wani tsaho gareta ba jikinta madaidaici ba rama ba kiba. Tana da kyau daidai ga dan dimple a kumatunta na dama. A ranar farko yan ajinsu sun fahimci Ju ta iya mmaths don ba su da yawa a ajin kuma malaman suna involving dinsu a ayyukan da suke. A fannin magana dai tunda akayi mata dariya bata sake ba. Su kuma da malami ya shigo ana tambaya sai suce Ju ta amsa yadda suka ji Yasmin na kiranta.
Satin ta daya da fara zuwa duk ta zama a takure saboda yadda yan ajinsu ke damunta har wasu students dinma. Yasmin da abin ya isheta ta fadawa Ya Rayyan wanda kullum yake nuna halin ko in kula a gabanta. Har school din yaje ya sami principal yace idan bazai tsawatar da students akan kanwarsa ba zai canja mata school. Ju bata san me yake faruwa ba taga canji sosai don a assembly Mr Ayodele yace zai dau mataki akan masu takurawa new students.
***********************
Abu kamar wasa term ya kusa karewa kuma su Mami suna kokari every two weeks ana kaita wudil taga iyayenta.
Batun ciwon Amal kam ta rage kuka amma har yanzu bata iya yiwa kanta komai. Ta dai iya kiran Ju kamar ita ta rada mata. Kowa a gidan yana yaba yadda Ju take kokari wurin kula da Amal. Yaya Sagir kuma ya zama mai koya mata assignment don Ju ta dage sai ta iya turanci.
Wata rana tana zaune suna lesson da Yaya Sagir ita da Yasmin sai ga Rayyan ya shigo falon ya zauna yana shan tea. Tana ganinsa ta dena karatun da take Ya sagir yace mata cigaba mana ta dan bata rai ta cigaba da cewa ( wicked, wickeder , wickedest) nan take Rayyan saboda kokarin gintse dariya ya kware da tea. Sagir yace wallahi zamu baku mamaki idan muka fara tsara ku da grammer.
Karshen term Ju tayi ta 23 cikin mutum 25. Tana zuwa gida ta tarar da Rayyan sun dawo daga asibiti da Amal Fauza cikin murna tace Yaya kaga result dina ta 4 nayi yace kinyi kokari akwai kyauta ya kalli sauran ku fa. Kowa yayi kokari dai banda Ju wadda yace zai sa a maida ta JS 1 idan ta dauki sama da ta 20 next term.
**********************
Alhamdulillah Ju ta gama JS 3 lafiya don result dinta na karshe ta 19 tayi. Rayyan yayi farin ciki da hakan duk da bai nuna mata ba. Sai dai yadda ya fuskanta tafi kokari a fannin lissafi gashi bata yi kokori sosai ba ance bazaa bata science ba. Ya dai roki alfarma idan an dawo hutu s sake mata exam a eng don yanzu da kanshi zai koya mata.
Mami ba karamin jin dadin yadda ake Ju ke kula da Amal take ba. Idan tana period ma da kanta take canja pad. Allah kadai zai saka ma yarinyar nan abinda take yawan fada kenan.
Wani malami aka samu irin masu aiki tsakani da Allah Ya tsaya sosai da addua cikin ikon Allah aljanin dake kan Amal yayi magana yace turo shi akayi amma yaki fadan ko waye. idan akayi ruqiya sai ya fita malam na tafiya ya dawo yace shi kawai a kwance auren. Haka dai ake fama da adduar Allah Ya kawo sauki.
Rayyan ya aika yafi sau uku Ju tazo lesson taki don ita tsoronsa ma take yanzu sai da ya hada ta da Abba ta fara zuwa. Idan yana yi mata magana ba amsa idan yayi fada tayi kuka. Daya ga itama akwai taurin kai sai ya rabu da ita da sharadin idan akayi mata exam bata ci ba zaisa a mayar da ita js1. Ju da murna tace ta yarda.
Tun daga lokacin kullum Ju tana karatu da duba dictionary bata tashi idan ba sallah ko kula da wani abin da Amal ke so ba. a dakin Hajja dama take karatun tare da Amal tana yan wasaninta.
Sati biyu da fara karatun nan na Ju suna daki da Amal cikinta ya wani murda saboda bata wani cin abinci kamar wasa da farko ta share sai gashi ya kara da ciwo sosai tana ta yiwa Amal alama da ta kira wani don ta kasa tashi amma ita bata gane ba sai ma ta kwanta a kasa yadda Ju tayi tana kwaikwayonta.
Hajja ce taji shirun nasu yayi yawa ta tashi ta bude kofar dakin abinda ta gani ne ya sata salati da karfi har Umma dake falon ta yi saurin tasowa. Ju ce kwance a kasa sumammiya kamar babu rai tare da ita
Yau kuma me ya sami Ju din Baba Idris.
π JUWAIRIYYA π 7
A falo Ju ta hadu da Mami da Ya Sagir suna hira. Mami tace wa ya taba min ke naga kina ta kumbura bakin nan na tsiwa. Ju tace Ya Rayyan ne ya koro ni, Mami a gabansa fa ya hauni da fada. Ya Sagir da bai gane me akeyi ba yace gaban wa am confused. Ya Rayyan daya shigo a lokacin yace gaban Lawal mai shago mana. Cikin fushi ya cigaba da kallon Ju yace wai ni waye ma ya baki izinin fita. Ya Sagir yace Mami Ju zance take yi ban sani ba. Mami taga yara zasu mata taron dangi tace kwana hudu kenan yana turowa kiranta ina hanawa dazu Hajja tace kada na sake hanata fita don dole tayi aure wata rana. Ya Sagir yace to ni zan mata magana ai su bata gama secondary ba.
Ya Rayyan kwance akan gado yana kallon hotunan Amal cikin zuciyarsa yana dada tausayin halin data shiga dalilin auren su amma abinda yafi damunsa yadda Ju ke neman zama centre of his thoughts. Wai shine har yake fadawa wani shine mijin yarinyar nan mai tsiwa. Ya tashi ya dauko papers din jarabawar da aka yi mata farkon shigarta makaranta ya sha dariya. Karshe dai alwala yayi ya sallah tare dadewa yana addua musamman ga matarsa Amal.
Lokacin WAEC ya matso su Ju an maida hankali ga karatu don ita bata da burin da ya wuce ta zama likitan ido ta taimakawa babanta. Ita da Yasmin sun dage da karatu cikin ikon Allah sunyi sun gama lafiya. Result din Jamb ne ya fara fitowa ita tana da 214 Yasmin kuma 221. Kowa ya tayasu murna. Kanwar Ju ma Nafisa wadda saboda demotion din da akayi mata tare suka gama itama ta sami 187.
***********************
Hajja tasa 'ya'yanta maza a gaba tace shawara na ke son kawo muku wadda kuma zancen gaskiya da Umma muka fara yi don ita tazo da maganar. Abba yace Hajja mu ai umarni zaki bamu ba shawara ba. Tace hmm kaji shi bayan ku akan 'ya'yanku sai anbi a hankali. Baba yayi dariya yace to muna sauraronki. Hajja ta gyara zama tace to ba wani abu bane akan yarinyar nan Juwairiyya ne, idan banyi kuskure ba ta kusa cika shekara hudu a gidan nan kuma duk tsahon lokacin nan a kula da yarmu tayi. Baba yace hakane nima kaina ina tunanin me zamuyi mu saka mata da alkhairi. Hajja maida kallonta ga Abba tace Bashir kana ganin zaka yarda Rayyan ya auri juwairiyya? Gaba dayansu basuyi tunanin jin wannan maganar ba. Hajja bata kula da yadda suka razana ba ta cigaba da cewa yarinyar nan taci kashi da fitsarin yayarta ba tare da ta taba bata rai ba. Allah Ya sani ina tausayin Habiba amma kuma har yanzu bata sami lafiya ba. Idan Juwairiyya tayi aure a wani gidan wa zata yarda ya taba ta. Duk kunsan yadda take kuka idan Juwairiyyan ta tafi makaranta. Abba yayi shiru sai kawai hawaye ya digo daga fuskarsa ya kalli dan uwansa yace Yaya abinda Hajja ta fada gaskiya ne. Shi kanshi Rayyan har kunyarsa nake ji ya gina gida ya kasa tarewa kullum sai dai yaje aiki ya dawo ga shekaru na karuwa. Yaya indai ka aminci to ni bani da matsala akan hadin nan.
**************************
Kowa ya tashi da tunani a ransa amma Abba tsoronsa daya yadda Mami zata karbi maganar. Kwana biyu yana ta juya zancen a ransa karshe dai ya sami dama da ta kawo masa zancen taga alamun Sagir fa yana son Ju. Abba yace ya fada mata ne tace a'a naga alamu ne dai sai ya fada mata shawarar da Hajja ta kawo. Mami sai kuka wiwi kamar yarinya tace yanzu Abban Sagir haka Amal zata kare rayuwarta? Ni bana kin ya auri Ju domin yata ce amma misali Amal ta warke fa. Ni Asiya na shiga uku Abba yace haba yaushe zaki rinka maganar kin shiga uku bayan kinsan babu tsumi ko dabara idan ba abinda Allah Ya tsara ba. Kada muso kanmu mu cutar da wasu. Ki duba yadda yaron nan hatta da abincin da Amal take ci shi yake siya kuma baya tunanin wani aure ya hakura ya zauna da ita a haka. Kada muyi zalunci saboda son yarmu idan hakan alkhairi ne to muyi fatan Allah Ya tabbatar da faruwar sa. Daren ranar dai Abba da Mami kusan kwana suka yi sallah Allah maji rokon bawa sai Ya sassauta musu al amarin a zukatan su..
*************************
Yau Ju an tashi da farin ciki domin kuwa wudil zata ta kwana biyu. Sai da tazo tafiya da kyar aka rabata da Amal duk suna kuka Ju har waje tana jin muryar Amal tana kiranta.
Ya Sagir ne zai kaita dasu Yasmin yan rakiya. Fauza ana exams a buk tana karanta Economics bata sami zuwa ba.
Koda ta isa gida murna take taga Yaya Najib sarkin cin zali don ta kwana biyu basu hadu ba saboda yana aiki a kaduna. Ya yi musu gyara a gida harda fenti Ya Ismail kuma yana bautar kasa a Kwara state. Gida dai sai murna ake da zuwan Ju. Washegari abin mamaki sai ga Abba da Baba da wani Kawun su kanin babansu. Bayan sun gaisa da Baba suka gabatar da abinda ya kawo su na son nemarwa Rayyan auren Ju. Baba yace Alhaji Bashir ban tari numfashinka ba amma yaron nan ba shine mijin Amal ba. Abba ya amsa da shine...sai baba yace to don Allah ku bani mintuna kadan ina zuwa. Sandarsa yasa ya shiga cikin gida ya nufi daki tunda yau da gobe tasa yana iya yawoba gidansa. A daki sautin kukan mama yaji yace Mariya me ya faru? Tace yanzu muka gama magana da yaya da kuma Dada akan abinda ya kawo su Alh. Baba yace to me kuka yanke tace ka amince don duk shawarar da suka bani kenan saboda tunda aka fara maganar auren nan idan ma munki to zasu nema masa wata karshenta ya rabu da Amal din. Kuka yaci karfinta tace ko kadan ba irin rayuwar danake wa Juwairiyya fata ba kenan amma wai mahaifiyarsa ce ta kawo shawarar kada mu aurar da ita a rabasu. Ta share hawaye tace kuna kasan ina tausayawa Yaya kafin najib ya kawo karfi duk dawainiyarsu ta karatu ta dauke mana. Fatana Allah Yasa abin nan ya kara mana zumunci. Yace amin nagode Mariya da dukkan abinda kuke yi min ke da yar uwarki.
Baba ya fita ya koma falon waje yace da bakinsa yaushe kuke son a daura auren kunga ni banyi wani shiri ba ko zaku bani lokaci. Abba yace haba Alhaji Idris juwairiyya ai yata ce don nafi ka morarta idan ka amince a yau zas daura auren. Bidaya Baba ya kira yace ta kira masa Najib da yazo ya tura shi kiran mal Yau da Liman da wasu yan uwansu da abokan arziki. Bayan sallar laasar aka daura auren Rayyan Umar Tafida wanda wurin aikinsu aka tura shi Germany na sati biyu da Juwairiyya Idris Muhammad wadda ke daki suna hira da su Nafisa bata san me yake faruwa ba.
Akwai rigima a gaba daga dukkan alamu
π JUWAIRIYYA π 6
Umma waya ta dauka ta kira Baba ta gaya masa yanayin data tarar da Ju yace to ta sami daya daga cikin samarin gida ya daga ta a sata a mota su taho yana asibiti. Kafin ta gama wayar Hajja ta kira Mami sun shigo tare da Ya Aliyu kowa a rude. Aliyu na kokarin daga Ju sai ga Rayyan ya shigo yace masa ya matsa shi ya dauko ta kamar wata jaririya ya sata a bayan mota Umma na gaba ita kuma Mami sa Ya Aliyu suka biyo bayansu.
A asibitin ma Ya Rayyan bai jira nurses ba ya sake daukan Ju ya shige ciki babansa ya fito daga office tare da Aliyu daya fada masa sun iso ya shiga zai dubata sai wata dr din tace yallabai ka bari naje idan ba kasa zan kira ka don iyaye basa iya duba yaransu sosai. Ba musu ya koma office don ya yarda da ita yace su jira shi a nan reception. Ya Rayyan duk ya kasa zaune ya kasa tsaya ashe duk abinda yake Umma na lura dashi amma bata ce komai ba.
Bayan anyiwa Ju allurai ansa mata drip likitan data duba ta ta wuce office din Dr Umar Tafida tace yallabai yarinyar nan fa yunwa ke damunta don idan ta tashi zansa ayi mata test inajin ulcer ma ta kamata. Ya mike da hanzari what did you just say Dr Rufaida? Yarinyar nan fa 'yace a wurina kuma a gida na ma take. Tare suka fito Baba ya hau fada ko suna maltreating din yar mutane don tana kula da tasu.
**********************
Sai washegari bayan Ju ta dan dawo hayyacinta Mami ta tambayeta meyasa bata cin abinci tace karatu take kuma ita mntawa take da abincin don kada yaya Rayyan ya mayar da ita js1. Mami dai tayi mata fada sannan ta hada ta da mama da baba a waya suka gaisa.
Rayyan ko kadan baiji dadin dalilin da Ju ta bayar ba abin duk ya dame shi harda bawa mami hakuri ya ce bai san zata dauki maganar da gaske ba. Kayan fruits, snacks da sauran kayan kwalama haka ya rinka siyowa kullum yana kawowa Ju bayan kwana uku aka sallameta. Tun daga lokacin kullum ya dawo sai ya tambayi su Yasmin ko taci abinci. Wannan abin ma da yake Umma na kallo tana sake sake a zuci.
Ju dai kwalliya ta biya kudin sabulu don kuwa taci jarabawar eng din saboda haka an bata science class. Rayyan ya daukarwa kansa siyo maltina, hollandia da su viju don kannensa su sha ko su tafi dashi makaranta amma Umma da yanzu bata da aiki sai lura da dan nata tasan saboda Ju ya siya.
*************************
Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah Ju yau sun rubuta exam dinsu ta karshe a SS2. Amma ita farin cikinta biyu ne don kuwa yau zaayi musu walimar sauka a gida Baba da sauran yan gidansu duk zasu zo.
Gidan Marigaya Tafida yau a cike yake yayyen Rayyan mata su biyu Yaya Kubra da Ummi suma sunzo da yaransu. Ju dai hankalinta bai kwanta ba sai da taga shigowar yan gidansu. Baba taje ta rungume ta suma kuka. Hajja tace maimakon kiyi murna sai kuka kuma Zuwaira. Ju ta bata rai Hajja nifa ba sunana Zuwaira ba. Nan dai akaje kowa ya zauna ga kawayensu da suka gayyata da malamin da yake musu karatu a gida. Taro yayi albarka su Ju sun sha wani lace mai kyau da Abba ya dinka musu shi kuma Abdul shadda yasa kalar lace din. Kowa da kyautar da ya basu Ya Rayyan kuwa waya duk ya basu mai kyau.
Ana cikin taro Amal ta fara tari wanda karshe sai da tayi amai a jikin Ju. Bata ko nuna damuwa ba taja hannunta suka koma cikin gida ta gyara mata jiki. Mami ta kalli yadda yarta ta zama babbar mace lokaci guda har tana kula da wata tayi hamdala domin Juwairiyya ta sa ta fita kunyar yayarta.
************************
Yana shigo da motarsa ya haske musu ido. Ba wasu bane Ju ce da wani dan makotansu daya dage yana sonta. Yauma Mami ce ta takura mata sai ta fita. Rayyan ba karamin bacin rai yaji ba wanda shima baisan dalili ba. Yana fitowa saurayin mai suna Lawal yayi saurin miko masa hannu su gaisa. Rayyan ya wani gintse fuska da kyar ya mika hannu. Lawal yace Alh Rayyan yanzu ni ka zama yayana. Ina fata zaka min kamfen wurin kanwwar taka. Ju kuma irin kunyar nan wa ya kamaka kana zance ta sunkuyar da fuska tace Ya Rayyan sannu da zuwa. Yace daka mata tsawa ke da izinin wa kika fito. Come on get inside. Ta zumbura baki ta shige wannan ai dizgawa ne a gaban saurayi Allah Yasa ma bata fara sonsa ba. Tana tafiya ya juya ga Lawal yace Mal kayi hakuri yarinyar nan tana da miji kada ka sake zuwa nemanta. Lawal cikin mamaki yace yallabai na tambaya tace babu kusan minti 30 da fitowarta babu wanda yace ta koma. Rayyan yace to ni nace don ni ne mijin.
Ikon Allah wai dama Rayyan yana son Ju ne???
π JUWAIRIYYA π 8
Rayyan tsaye a reception yana ta kallon agogo ya gaji da jiran abokinsa Abbas wanda suka yi alkawarin haduwa a reception din hotel din da akayi musu masauki zasu je shopping domin sun gama abinda ya kawo a germany saura kwana biyu su koma gida nigeria. Da gudu Abbas ya fito daga elevator yana bashi hakuri. Rayyan sanye yake da wani ash din wando da riga light blue kayan sun masa kyau. Fuskar nan tasha gyara don shi baya aske gemu duka yana barin kadan wanda ya hade da gashin bakinsa. Da yake shi fari ne sai gashin yake masa kyau.
Suna tafiya Abbas wanda tuni ya kawo kudin auren Fauza yace mu shiga kantin kayan matan can kasan mai hada lefe idonsa idon kayan mata. Rayyan yayi dariya to bana son rashin kunya dai kanwata ce. Dukkansu sunyi siyayya shi Rayyan banda Amal harda kannensa ya hada. Zai je wurin biyan kudi ya hangi wata farar night gown sleeveless wadda bazata wuce gwiwa ba kawai sai yayi imagining Ju a cikinta nan da nan yayi tsaki Abbas yace mutumina lfy. Rayyan wanda hannunsa har ya kai kan rigar yace yarinyar nan is getting under my skin and I don't like it. Abbas yace Ju ko. Cikin mamaki yace what do you mean..Abbas Yace ni kaina I cant remember when it started amma baka da zance sai na yarinyar nan tayi kaza ko tayi kaza kana fada kana wani lumshe ido. Rayyan ya kai masa duka yace to tunda ban ambaci suna ba ya akayi kasan da ita nake. Abbas yace sau biyu muna tare da kai zata wuce gaba daya hankalinka sai ya koma gareta. Ka siyo rigar baccin don nasan zata yi rana very sooooon.(fauza ta tsegunta masa auren da aka daura amma tace yayi shiru kada ya fada). Rayyan dai ya dauko irin rigar har biyu duk tsiyar da Abbas ke yi masa sai ya share kawai.
Yau kwana biyu Ju tana aikin kuka ko abinci bata ci tunda Baba ya fada mata zancen auren da aka daura mata da Rayya.
π JUWAIRIYYA π 9
Mama tun tana bada hakuri har abin ya fara bata haushi tana fada. Baba ma yayi nasihar har ya fara fada shi da babu wanda yake jin kansa da Ju. Gidan Baba Idris dai ya zama kamar ana zaman makoki Ju data zo kwana biyu sai gashi tayi kwana takwas. A kwana na taran Ya Najib yasa Ju a gaba yana ta lallabata tayi hakuri don duk fadansa yana son kanwarsa kuma yana tausaya mata. Suna cikin magana sai kawai suka ji sallamar Mami da Umma . Ju tana kokarin tashi ta gudu daki sai taji an kira sunanta. Amal ce fuskarta duk hawaye da gudu Ju taje ta rungumo ta taja hannunta dakinsu Nafisa. Umma tace lallai ana fushi damu yau ko kallo bamu ishi Juwairiyya ba. A falo dai ta barsu tare da Mama suka shiga daki tace da Amal abinci tana mata nuni da baki Amal tace gyada kai alamar tana so, Ju ta tashi zata debo mata sai ta biyota har ta debo iyayensu dai suna kallo. Sai a lokacin Ju ta gaishesu bayan ta dan huce da fushin tace Mami ko kwalΔΊi baa sawa Yaya ba kuma wannan siket din bata jin dadin tafiya dashi ni bana sa mata. Umma tace to Juwairiyya idan baki amince da auren nan ba wace mace kike tunanin zata kula miki da yayarki kamar yadda kike yi. Kuma kina jin akwai mijin da zai yarda ki rinka zuwa kula da ita kullum? Ta cigaba da cewa mu da muka hada auren nan munyi ne bayan tunaninku duk ku ukun kuma da yardar Allah alkhairi muka kulla. Mami tace Ju kiyi hakuri da bamu baki hakkinki na sanar dake ba nayi tunanin bazaki amince bane. Ganin yadda suka taru suna lallaba ta sai taji ba dadi tayi murmushi ta kama hannun Amal suka koma dakin. Hakan ya tabbatar wa da iyayen nata zaa sami nasara a hankali.
************************
Al'amarin Ya Rayyan kuwa tun ranar da ya dawo ya sami labari a wurin iyayensa. Bayan duk iyayen sun taru a gaban Hajja sai Abba yace Rayyan bayan tafiyarka fa an daurawa Juwairiyya aure ai kafin ya kai karshe jikin Rayyan ya fara gumi yace Abba aure kuma? Dama tana da saurayi ne? Ko na dole akayi mata? Baba yace kai wannan irin tambayoyi haka da kai aka daura. Rayyan wani yanayi ya tsinci kansa shi bai gane ba murna ce ko kishiyata. Nan dai iyayen nasa suka yi masa bayanin komai tare da nasiha.
A dakin Umma Rayyan yana nuna mata sayyayyar da yayiwa kowa tana yabawa tace banga ta amarya ba. Rayyan ya wani bata rai ai bansan da maganar ba. Ni an rinka daura min aure a haka kenan babu ko katin gayyata. Umma dai dariya ma take tace zaka iya bagarar da kowa banda ni ba tun yau nake lura da yadda ka damu da yarinyar nan ba sai ka rinka nuna halin ko in kula. Rashin zancen da take ma maigadi ya fada min kai kace duk wanda yazo nemanta ace tana da miji. Shiru yayi don yasan gaskiya ta fada. Can dai yace Umma ko ke kika bada shawarar auren tace eh don nafi kowa sanin meye a zuciyarka. Zai fita ya waigo to nagode tace ba godiya ba itama kayi mata tata tsarabar na gani.
*************************
Sai da su Umma sukayi sallar magrib sannan sukayi shirin tafiya tare da Ju. Sai da ta dake sabon kuka Baba ya dai bata hakuri yace banda abinki ai ba yau zaa kaiki ba abinda ance sai bikin Fauza yazo nan da wata hudu. Kije Allah Yayi albarka. A soro sukayi kicibis da Ya Sagir da Nafisa suna zance tana ganinsu ta gudu shi kuma ya fita yana sosa keya. Umma tace almuri shiyasa kullum Juwairiyya zata zo kake cewa zaka kawota. Mami kuwa a ranta tace ashe naso yin kuskure ba yar yake so ba.
***********************
Kan Amal ne a cinyar Ju tana yi mata tsifa washegarin da suka dawo a dakin Hajja su Yasmin suna ta tsokanar Ju wai tazama dauko wando ita kuma sai kumbura baki take taki kula su. Hajja tace zanci kaniyarku yaran nan. Suna haka Ya Rayyan yayi sallama duk suka yi shiru sai aka fara gaishe shi banda Ju data sunkuyar da kai sai hawaye Hajja tace su Yasmin su fita. Ta juya ga Juwairiyya tace baki gaishe da yayanki ba Ju still bata dago ba tace ina yini bai amsa ba ya dauko kitkat nan da nan Amal ta tafi wurinsa ya bare mata. Hajja tace bazaka amsa ba yace sai da kika rokar min fa Hajja to lafiya tunda kin rokar mata itama.
Wannan zama akwai kallo
π JUWAIRIYYA π 10
Ju bata sake cewa komai ba ta gama tsefewa Amal kai taja hannunta suka tafi daki. Rayyan yana falon Hajja sai ya jiyo kukan Amal. Yana kokarin tashi Hajja tace wankin kai akeyi indai kaji kukan nan amma bata kukan kitso ai. Wata kitkat din ya dauko ya shiga dakin sai ya ga Ju daga ita sai daurin kirji tana gogewa Amal kai. Ai tana ganinsa da yadda tsaya kallonta duk da Amal na kokarin kwace chocolate din da ta gani a hannunsa yasa Ju kwalla kara Hajja ta dogaro sandarta tayi saurin shigowa tana tambayar lafiya yace nima ban sani ba. Ju kuwa cikin karamar murya tace Allah Ya isa.
Kwana hudu kenan da Ju tayiwa Rayyan Allah Yasa tun daga ranar take wasan buya dashi don tasan yaji ta saboda wani kallo da yayi mata. Tana kitchen suna aikin abincin sadaka ita da Mami na juma'a kamar yadda al'adar gidan take. Yau turn din mami ne tayi abinci Umma kuma tayi zobo. Wayar Ju ce take ta ringing taje ta dauka wata classmate dinta ce ta kira take fada mata Waec ta fito taje ta karbi scratch card a makaranta ta duba. Da murnarta ta fadawa Mami tace mata to tunda goma batayi ba taje ta fadawa Yasmin suje driver ya kaisu su karbo.
Gaba dayansu suna da 9 credits don haka da murna suka dawo aka nunawa kowa. Bayan magrib Mami tace Juwairiyya ki dauki abinci ki kaiwa Rayyan tun dazu ya dawo. Ju tace ni kuma Mami tace tace kinga wani a nan ne. Ki tafi da result dinki ma ki nuna masa don tun zuwanki garin nan shi yake biyan kudin makarantarki. Ju cike da mamaki tace ba Abba bane. Mami tace a'a Rayyan ne kuma daga yau kullum rana da dare rinka kai masa abinci daga nan don na riga na fada masa ma.
*************************
Jikin Ju a sanyaye ta dauki abincin da copy din result ta fita. Mami a ranta tana tausayin Ju sai dai tasan dole idan zaayi zaman auren dole su saki jiki da juna shiyasa ta fadawa Umma a dena aje masa abinci.
Tunda ta nufi shashen su Ya Rayyan gabanta ke faduwa. Tana isa kofar dakin ta rasa me ya kamata tayi. Karshe dai ta yanke shawarar ta kwankwasa kofa kafin ya bude ta ajiye ta gudu. Sai dai tana kwankwasawa sau daya taji ance mata come in. Wani dum taji gabanta ya fadi sai tayi saurin dokawa ta ajiye ta gudu sai dai kafin ta dago kofar ta bude ya koma ciki. Turus tayi a gaban tray din har sai da yace ke me kika jira ne.
Yau ce ranar farko da Ju ta fara shiga dakin Rayyan. Kwance ta sameshi yana waya ta ajiye tray din zata fita ya daga mata hannu alamar ta tsaya. Haka ya cigaba da waya kusan 15 minutes tana tsaye. Can dai sai ta fara tsaki ya wani harareta kawai sai ta juya zata fita. Bata ankara ba taga Rayyan a bakin kofa ya rufe ya cigaba da wayarsa. Ai daga nan Ju sai kuka ba shiri ya ajiye wayar ya kalleta ke lafiya me nayi miki tace cikin kuka na gaji. Kin gaji fa kika ce to ai baki ma fara tsayuwa ba punishment dinki kenan. Tace Allah Yaya naci jarabawar ka gani fa. Ya karba very good amma am not punishing you for that. Ju har gumi ta fara ba komai ke damunta ba irin fitsarin daya matseta kamar tayi a tsaye. Ta daure tace me nayi. Allah Ya isa kika yi min ko kin dauka banji ba. Zo ki zuba min abincin ya fada yana canja tasha a tv. Ko da Ju tayi yunkurin motsawa sai ji tayi fitsari ya digo a ranta kawai cewa tayi komai ya fanjama fanjam ta ruga da gudu toilet din dakin tayi fitsarin. Ya Rayyan binta yayi da ido kawai sai yaji shiru kusan 10 minutes da shigarta taki fitowa. Kunya ta gama kamata ta yaya ma zata fito wannan abin kunya da yawa yake.
Nima na tayaki jin kunya Ju
π JUWAIRIYYA π 11
Ke me kike yi ne shiru yaji ya sake maimaita tambayar ba amsa. Kawai sai ya kama kofar zai bude, ba shiri Ju tayi sauri ta danne kofar don ta manta bata sa key ba. Ya Rayyan yace mata kinsan baki fini karfi ba idan baki fito ba zan balle kofar nan. Tace to ka dan fita daga dakin zan fito, lallai yarinyar nan ta raina ni abinda yace kenan a zuci. Tura kofar yayi iya karfinsa ya zare mata ido zo ki fice. Ai da gudu ta fita har tana bugewa da kofa. Sai da ya tabbatar ta fita ya kwashe da dariya Allah Sarki ashe fitsari take ji.
Allah Ya taimake ta a bangaren Hajja take kwana da Amal da bata san me zata gayawa Mami ba matsayin dalilin da yasa ta dade daga kai abinci ba. Daren nan Ju har mafarki tayi Rayyan ya bude ta a toilet tana fitsari.
Washegari tun safe Ju tace kanta yana ciwo don kada taje kaiwa Ya Rayyan abinci da taga bai dawo da rana ba ta ware tana harkokinta magariba nayi ta kwanta harda shan panadol extra ita a dole ga mai ciwon kai kowa yana mata sannu. Kwana uku a jere ana ciwon karya Mami dai har ta gane na rashin son zuwa ne don haka tace zata yi maganin abin. Kamar yadda ta saba Ju ana idar da sallar isha ta nemi magani zata sha bata ganshi ba. Data tambayi mami sai tace ita ta gaji da home remedy asibiti zasu tafi ta kira ance akwai likita. Karya ba kyau Ju dai ta sako hijab tana zuwa falo taci karo da Ya Rayyan. Mami tace jeki mijinki ya kaiki dama tun safe na gaya masa zai kaiki sai kiyi musu bayani sai magriba ciwon yake tashi. Idonta tsilli tsilli tace Mami ai yau baya ma ciwon sosai idan nayi bacci zanji sauki. Dama abinda Mamin tayi tunani kenan ciwon karya ne sai tace gara dai kuje nima zamu dubiya nan makota da umma. Ba yadda zata yi dole ta fita gashi su Fauza sunje gidan kanwar Umma a abuja zasu kwana biyu.
Bayan mota Ju ta nufa zata shiga Ya Rayyan ya ce ke nayi kama da driver dinki ne. Sumsum ta koma gaba ta rabe da jikin kofa. AC ya kunna sanyi ya fara kada ta ga karatun Qur'ani yana tashi tana bi a hankali. Sai da suka kusa isa asibitin ya tsaya a gefen titi yace ke taki amsawa ya maimaita still bata amsa ba sai yace idan baki amsa ba zansa a kwantar dake idan muka je asibitin naga kamar baki tsoron allura. Tace naam cikin karamar murya. Ciwon kan nan ki fada min gaskiya na gaske ne ko na gudu na ne. A hankali tace na gaske ne. Kin tabbata tsakani da Allah. A'a shine kawai abinda tace. Uhmm to bari mu koma gida zan fadawa Baba sun aura min mai shan kwaya. Wallahi bana shan komai ni tana fada sai hawaye. Ke hawaye baya miki wahala ne da anyi magana sai kuka. Akan me kike shan magani kullum. Shiru dai Ju tayi zai sake magana wayarta ta fara ringing sai taga kiran Mami ne. Shi ya dauka yace gamu nan dawowa Mami jikin nata da sauki. Bayan ya ajiye wayar yace daga yau kullum kika kawo min abinci zaki gyara min daki. Tace eyye yace eh ai kinji me nace. Ya juya kan mota suka koma gida.
**********************
Sati uku da faruwar haka kullum Ju zata kai masa abinci kafin ya dawo taje ta gyara dakin duk da kullum taje gado kawai take gyarawa sai ta goge center table da,saman fridge da kan tv. Kullum dakin babu datti. Ya Rayyan akwai tsafta ga kamshi dake tashi a dakin kamar dakin mata.
Baba ne ya kira Rayyan yace tunda ya fara annual leave dinsa ya kamata yaje Wudil ya gaishe da iyayen Ju. Siyayya yayi ta kayan abinci da sauran kayan masarufi ya nemi Sagir su tafi tare sai Hajja tace wai ku yaran zamani yadda ake jan hankalin mace ma sai an koya muku. To ka dauki Juwairiyya ku tafi tare.
Ju ta gama shiryawa Mami tace na fada masa gidan Dada zaku fara zuwa daga nan sai ku wuce. Ki kula da kanki kuma don Allah banda tsiwa. Murmushi tayi ta fice da gudu don taga alama yau Mami kakar take da ita yau.
Bayan sun gaisa da Dada suka danyi hira ya kawo dubu goma ya bata tana ta godiya dayi musu fatan alkhairi sannan suka tafi. A hanya babu wanda ya kula dan uwansa har suka isa tayi mamaki daya gane gidansu. Baba yayi murna sosai tare suka je masallaci da Rayyan. Mama da Baba suka sake musu nasiha tare sannan Baba yace don Allah idan Amal ta sami lafiya ka kwatanta adalci tsakaninsu. Rayyan yace da yardar Allah bazamu sami matsala ba. Sai da suka yi sallar magriba suka kamo hanyar kano. Kafin su iso Ju har tayi bacci. Ko da yayi parking sai ya rasa yadda zaiyi ya tasheta daga bacci. Kallonta kawai yake tayi masa kyau sai da ya hango Abdul ya nufo motarsa sai ya shafi gefen fuskarta ke tashi ki shiga gida. Wani yarrr taji a jikinta ta tashi ta fita.
Har ta kwanta sai taga text ya shigo wayarta
( ina fata kinyi sallah)
tayi reply ( who are you and why do you care)
( hmm i guess your English has improved alot)
( what ever)
( baki ansa min tambayata ba fa)
( malam ina da aure fa ka dena damuna ko in maka Allah Ya isa)
Rayyan dariya ce ta kamashi sosai ( to sarkin Allah Ya isa baki gaji da punishment din tsayawa bane)
Subhanallahi shine abinda Ju tace daga nan bata sake reply ba. Da yaji shiru sai ya kirata kamar ta share sai dai ta dauka tayi sallama. Ya amsa yace wannan number ta ce kiyi saving...goodnight
π JUWAIRIYYA π 12
Tun daga ranar kullum dare Ya Rayyan zai kira Ju yace mata sai da safe. Su Yasmin an dawo daga abuja ana ta bawa Ju labarin wuraren shakatawa tace nima in Allah Yarda zani wataran Fauza tace ki bari ayi biki kice da Ya Rayyan nan zaku je honeymoon ke na tuna ma ai yanzu ma zaku iya zuwa tunda an daura aure. Nan dai hirar ta koma tsokana da abin ya isheta Yasmin na cewa wai kina ma son yayan kuwa? he is very good looking nasan by now kin fara sonsa. Ju har ranta tasan ta fara son Ya Rayyan don kuwa yanzu duk dare bata bacci sai ta jira wayarsa wadda babu abinda yake cewa sai kinci abinci, yaya Amal babu matsala ko daga nan sai yace sai da safe. Kallon Yasmin tayi ta wani kashe ido tace so kai. motsin da taji a bayanta ne yasa ta waiga ashe Ya Rayyan na bayanta a tsaye su Fauza suka yi ta tunzura ta. Bata kara magana ba ta tashi ta koma dakin mami suna mata dariya. Ya Rayyan yace ina wasa daku ne kowacce ta tashi suna masa dariyar shakiyanci.
An fara bikin aminiyar Ju a makaranta Samira dama Mami ta riga tasan da maganar har anko tayiwa musu ita da Yasmin tunda duk ajinsu daya. Ranar kamu tasa ankonta wanda suka dinka fitted gown tayi musu kyau sosai an sha dauri suka kawo mayafi iri daya suka yafa har ka. Sun shiga dakin Hajja yi mata sallama Ju harda sanda kada Amal ta ganta sai Hajja tace wai ni Juwairiyya yayanki yasan da maganar bikin nan ta ce a'a amma duk su Umma sun sani. Hajja tace buga masa waya maza baki san fita ba izinin miji duk taku a wuta mace take yi ba. Ju ta dauka Hajja da wasa take sai taga abin ya wuce wasa dole ta dauki waya ta kira sai aka yi rashin saa yana meeting wayar tana office ta kira ya fi sau goma don bikin Samira ne ko rokonsa ne zata yi. Tace da Hajja bai dauka ba ina ta kira Hajjan tace sai ki hakura Yasmin taje don bazan yarda da fita irin wannan ba. Kafin kace meye wannan Ju sai kuka tana rokon Hajja abu ya hada dasu Umma amma kememe Hajja tace ita bata san wannan tarbiyarba. Umma har text tayi masa shiru.
Yasmin dole ta tafi ita kadai Abdul ya kaita Ju kuwa yini tayi kuka dakin Hajjan ma tayi masa kaura. Ya Rayyan ya fito daga meeting ya tarar da missed calls da tawa. Umma ya fara kira tayi masa bayanin kiran sai ya kira Ju ta kalli waya tayi tsaki karshe ma kashewa tayi gaba daya. Ya kira wayar Mami amma sai ya kasa cewa ta bawa Ju.
Bayan ya dawo ya tarar yau bata kai masa abinci ba ya sake kira still wayarta a kashe sai ya tafi wurin Umma tace ita bata aje masa ba tana dariya yau ka taba amarya zaka yi kwanan yunwa. Girgiza kai yayi anya Umma baki fi son yarinyar nan ba a kaina har dariya kike tace ai ko yadda take kular min da Amal dole na so ta. Fita yayi ya kira Yasmin a waya wadda tana wurin Ju tana bata labarin biki da yadda amarya bata ji dadin rashin zuwanta ba. Tace amma na fada mata baki da lafiya ne. Ya Rayyan cewa yayi tace wa Ju umma na kiranta. Suka fito tare sai suka hadu dashi yace wa Yasmin wuce gida ke kuma biyoni ta wani gatsina fuska umma ke kirana Umma ta kwanta ni nake kiranki. Tsayawa tayi taki tafiya sai kawai yaja hannunta ya koma dakinsa da ita
***********************
Yaya ka sakar min hannu bacci zanyi ko kula ta baiyi ba sai da suka shiga dakin ya rufe kofar harda sa key. Ya bude fridge ya dauko youghurt yana sha ta tsaya tana share hawaye. Ke zauna tace ba sunana ke ba bai kula ta ba ya kuma cewa nace ki zauna da yaga taki yace ashe kina son kwana a dakin nan. da sauri tace Allah Ya kiyaye, ajiye robar yayi yace what did you say...shiru tayi ya biyota tana ja da baya sai da taji bango a bayanta. Maimaita abinda kika ce nan ta fara kokarin gudu yasa hannuwansa biyu ya kafe a jikin bangon ba hanyar gudu. Tuni cikinta ya duri ruwa don ta fara tsorata ya matso da fuskarsa kusa da tata yace me yasa baki fada min kina da biki ba idanunta a rufe saboda yadda take jin numfashinsa dab da fuskarta tace babu komai a hankali. To kinga ba laifina don an hanaki fita ni kuma bana son short notice so ragowar events din ma bazaki ba. Bude ido tayi a hankali ga wasu hawayen na shirin sauka tace don Allah itace babbar kawata idan banje ba zata yi fushi. Tausayi ta bashi to idan na sake ganin hawaye bazaki ba hannu biyu tasa ta goge idonta yace gobe me zaayi tace dinner to ku shirya Abdul sai ya kaiku amma da sharadi daya ina jin yunwa. Ju murmushi tayi har dimple dinta ya fito yace ke kin ci tace a'a amma zanci idan na shiga....wato hunger strike kike saboda kina fushi dani.
Har ta kwanta sai tayi sauri ta dauki wayarta ta tura masa text.
( yaya please ka fadawa Hajja kada ta sake hanani fita)
( idan naki fa)
( don Allah kada ka ki)
( ki taya ni addua gobe ina da case. goodnyt)
Ju bata yi reply ba sai tayi alwala tayi sallah tare da roka masa saa. Sai bayan magrib suka shirya zasu tafi Mami tace kada ku wuce 9:30 amarya tazo ko bata zo ba. Ju tace in sha Allah Mami. Sunyi wa Hajja sallama tace wa Ju yau babu kuka ko tun safe ya fada min. Zuwaira kenan wai an iya fushi jiya kika barni da Amal ta hanani bacci. Abdul yayi ta dariya mu dai mun ganku a rana.
Tara da yan mintuna Ya Rayyan yayi wa Ju text ( ki fito mu tafi) ta nunawa Yasmin ba don sunso ba suka yi sallama da amarya don ma sunyi saa ba ayi african time ba an fara da wuri. A waje suka tarar da Abdul da Ya Rayyan yace ka dauki Yasmin ku tafi na manta bance kada ka dawo daukarsu ba. Ju bata ji dadi ba don yayan nata ya fara bata tsoro.
Ju da Rayyan nice couple ko.
π JUWAIRIYYA π 13
A hankali yake tuki kamar bazasu gida ba kowa yayi shiru da abinda ke ransa. Ju ta kwantar da kai jikin kofa tana hamma Ya Rayyan yace ke kada kiyi min bacci fa ba dama kiji sanyi ac sai ki fara hamma. Mayafin ta taja ta rufe fuska. Au ni bazan ga kwalliyar ba? Sai a gidan biki kike nunawa. shiru tayi har suka iso gida tana kokarin fita taji motar a rufe. Ina zaki yau zance zamuyi na ma fadawa Hajja don kada taji shiru ta rufe kofa. Yaya ni bacci zanyi ta fada tana hammar karya. Bata ankara ba tayi ya janyo ta kusan rabin jikinta duk akan cinyarsa take fuskarta a kirjinsa. Tun tana kokarin kwacewa har ta hakura don ba karfinsu daya ba. Zame mayafinta yayi daga kanta yana shafa mata gashi wanda yasha gyara a salon. Wani irin yanayi suka sami kansu mai dadi can taji yace wa Juwairiyya gabanta har faduwa yayi don bata taba jin ya kirata ba....are you happy with this marriage? Kasa amsawa Ju tayi. Idan baki amsa ba sai mu koma dakina kila zaki fi sakewa a can.A'a yaji tace to give me an answer. Da yaji ta sake shiru ya cigaba I just want you to know ban amince da auren nan ba don kawai kina kular min da Amal. I love my wife kuma kullum ina mata adduar samun lafiya amma you are also special kada ki taba zaton ina tare dake don kina taimaka min kamar yadda aka fada miki a gida. I care about you. Dadi mara misaltuwa Ju taji a ranta gyara mata zama yayi ta koma seat dinta sai ya dauke ta a hoto. Kunya duk ta rufe ta yace idan kin shiga gida ki turo min wasu ina jira. Tana jin alamun ya bude lock din taja dauki dankwalinta ta gyara mayafi zata fita ya sake rike mata hannu gobe ma zaki bikin ta eh,to ki fada min idan kun shirya tunda saturday ne bana son ana kalle min mata....murmushi tayi ta fita. God i love this girl abinda ya fada kenan a fili.
**********************
Ju ta tsinci kanta cikin nishadi bayan ta kwanta taji wayarsa tana dauka ina jira kawai taji yace ya kashe wayar. Nan ta duba wasu hotunanta masu kyau ta tura masa ta whatapp duk da bata taba chatting dashi ba. Kiranta ya sake yi kinyi kyau nagode. Mu kwana lafiya.
Wani malami anti Hassana tazo dashi gidan washegari tace a islamiyyar yaranta yake koyarwa amma taji ance yana ruqiya shiyasa tazo dashi gidan. Ya Rayyan aka taso daga bacci tare da sauran mazan gidan malam yace duk suyi alwala nan ya fara karatu Amal sai ta fara ihu sosai. Su Ju suna side din Mami su duka harda su Mamin suna ta addua. Tuni ma ta manta da yau zaa kai samira. Malam yana ta karatu Amal ta fara fizgar gashinta nan Rayyan da Abba suka danneta ta fara cewa cikin muryar maza zan fita wallahi zan fita dama turo ni akayi. Ku kira uwarta tasan wanda ya turo ni. Malam yasa aka kira su mami Ju ta shigo taga yadda Amal ta fita hayyacinta sai kuka. Malam yace muna sauraronka makiyin Allah azzalumi. Aljani wanda yace sunansa Zazzaq boka ne ya turo ni bisa umarnin mal Yau yace in hana babarta sukuni don ta dena taimakon kaninsa. Ju najin haka kukanta ya tsananta. Shima kanin mu muka rufe masa ido ya dena gani kuma muka ruguza kasuwancinsa amma wallahi zan bude don duk ka kona ni. Wannan yarinyar ma tasan sanda aka binne asirin a kofar gidansu. Duk ranar da tayi niyar fada sai na saka mata wani mummunan tsoro a zuciyarta amma na tuba na bika. Malam yace ni karka bini ina son ka fita daga jikin yarinyar nan kuma makahon nan ma ka bude masa ido idan ba haka ba duk inda ka shiga a duniyar nan zan maka addua kuma kasan baa boyewa Allah. Addua Malam ya cigaba dayi dai Amal tayi atishawa mai karfi....ta dan jima a kwance sai can ta bude ido taga wanda ya rike mata hannu tace Ya Rayyan kai ne?.
To ga Rayyan, Amal da Ju me zai faru da auren su?
.
π JUWAIRIYYA π 14
Farinciki ne ya cika zuciyar kowa da jin yau Amal ta gane wani bayan Ju. Nan 'yan uwanta sai suka rinka cewa nima kin gane ni tana murmushi tana basu amsa. Tana zuwa kan Ju ta tashi ta rungumeta iyakar karfinta tana kuka. Su duka kukan suke har suka bawa mutane tausayi. Amal tace duk duniya babu mai saka miki Ju sai Allah. Wani lokacin ina dawowa hayyacina amma sai na kasa yi muku magana amma duk irin kulawar da kike min nasani.
Malam na shirin fita Ju tace malam mahaifina ne makahon, Abba yace hakane itace yarinyar da ya nuna ai. Malam yace me kika sani game da ciwon mahaifin naki. Ju cikin kuka ta fadi yadda taga baba Yau ya binne zakara mai rai da wasu layoyi a kofar gidansu sannan yace kamar yadda na binne zakaran nan Idris haka na binne arzikinka da ganinka. Yadda gadon mahaifinmu bai amfaneni ba kaima bazaka zauna cikin jindadi ba. Ta cigaba da cewa tun daga ranar duk sanda nayi niyyar fada sai inji tsoro kamar idan na fada din Baba mutuwa zai yi. kowa ya tausayawa Ju sannan malam yace gobe zan dawo da safe muje wurin sa.
Anyi kwanan farin ciki gidan ranar sai dai Juvda zullumi ta kwana don tsoron kada idon Baba yaki budewa. Wurin 11 na safe suka shirya da Abba, ya sagir da Ju sai malam suka wuce wudil. Abin mamaki Ju a tsakar gida taga Baba yana tafiya ba sanda. Mama ce tayi musu bayani ai yau tun asuba idonsa ya bude. Nan dai Malam ya sake basu wasu addu'o'in yace kuma su kiyaye da yawan azkar. Mama ta tayasu murnar samun lafiyar Amal tace zata zo kanon idan an kwana biyu Baba ya kara jin sauki.
Maikoko tazo gulma ta kuma ganewa idonta Baba ya sami lafiya. Taje ta fadawa Baba Yau yace ke banda munafunci babu abinda kika iya. Ina ce zaituna da Lami duk ciki garesu ga Tasi baya da aiki sai shan kayan maye. Ki bari muji da masifar gidanmu yanzu. Tace malam daga kawo labari sai fada. Cikin fushi ya maka mata carbin dake hannunsa ba ke kika rabani da dan uwana ba. Matsa ki ban guri.
********************
Yau kwanan Ju hudu a wudil amma ko sau daya Ya Rayyan bai kirata ba tunda ta taho. Da farko tayi masa uzuri don Amal ta sami lafiya bayan shekara hudu da ciwo. Sai dai a ranta tana sa rai ko sau daya ya kira yaji jikin babanta. Wasa wasa sai da tayi sati biyu a wudil amma kullum suna waya da mutanen kano su mami da Amal. Suna waya da Mami tace zuwan Sagir biyu na dauka zaki biyu shi tace Mami zan tawo da Ya Najib. Washegari Ju ta tashi da matsanancin ciwon mara wato period pain ga zafin gari ya isheta ta shimfida tabarma a tsakar gida ta kwanta daga ita sai wata vest da dogon skirt. Tana kwsnce bayan tayi amai Nafisa ta nayi mata fifita sai suka ji sallamar su Amal. Tare suke da Ya Rayyan suka shigo aka gaisa Mama rungume da Amal tace mungodewa Allah da samun lafiyarki. Amal ta kalli Ju da jikinta kwatakwata babu kwari ta tambayi me ya sameta. Bidaya tayi saurin cewa period pain ne.
Da kyar ta tashi suka gaisa da Amal tana yi mata sannu. Ya Rayyan shima sannun yayi mata ta wani harare shi duk da tana jin jiki. Tana kokarin mikewa sai kawai ta fadi a sume.
π JUWAIRIYYA π 15
Da gudu Ya Rayyan ya tare ta ana ta sallallami yace a bashi ruwa. Shafa mata ya rinka yi a fuska Mama na fifita har ta dawo hayyacinta. Kanta a cinyar Amal ta ganshi sai kawai wasu hawaye masu zafi taji suna fitowa daga idonta. Baba yace azo a tafi asibiti kwana biyu dama ya lura bata cin abinci. Ya Rayyan yace indai ta danji sauki gara su wuce kano kawai. Babu wanda ya musa masa ita Amal da tazo wudil da niyyar sati tare suka juya. Kafin su iso tayi amai sau uku Ya Rayyan tuki yake kamar zai tashi sama. Tafida Clinic suka wuce direct kafin su karasa su Mami wadanda Amal ta kira a waya sun riga su zuwa.
Bude ido tayi ta ganta kan gadon asibiti ga drip a hannunta. Yasmin ce ta fara ganin ta tashi ta taba Amal wadda take rike da hannun Ju har ta fara gyangyadi. Wani hawayen taji suna hada ido da Ya Rayyan ita kanta ta rasa dalilin wannan kuka Mami tace dena kukan mana Ju kefa dadina dake shagwaba. Ina yake miki ciwo yanzu tace ciki ne. Baba likita da kansa yazo yace kowa ya fita daga shi sai su Umma da Ya Rayyan. 'Yata me yake hanaki cin abinci ulcer tayi miki kamu irin wannan ya dubi umma kuma abin ya hade mata biyu harda MP. Ana murna yar uwarki da Alh Idris sun sami lafiya sai ki tada mana hankali. Bata ce komai ba ya bada umarnin a bata abu mai dumi tasha kuma bazai bari ta koma gida ba sai yaga tayi biyun kibarta. Mami murmushi tayi to ke taki ta same ki kullum tuwo zan baki.
Amal tayi nacin a barta ta rinka kwana da Ju Umma taki amincewa tace kema lallaba ki muke yi. Muje gida Rayyan sai ka taho da Fauza. Suna zuwa da Fauza Ya Rayyan yace ta zubawa Ju kunun da suka taho dashi sannan yace ta bashi wuri zasu yi magana. Kunun ya mika mata karbi ki shanye ta karba tana sha kadan kadan. ki bude baki kisha don kara miki zanyi.
Sai da yaga ta shanye yace Juwairiyya what were you trying to do zaki dena cin abinci. Ni ba dena ci nayi ba ta fada bata ko kallonsa. Baba yayi miki karya kenan. Tayi saurin dago kanta a'a. To meyasa kika tafi wudil bada izinina ba nasa miki ido ina jiran ko zaki bugu kice ga dalilinki amma ko sau daya banji wayarki ba. Wani sabon kukan ta fara kinga idan bakiyi shiru ba Allah a dakin nan zan kwana kowa yazo gobe ya ganni. cijin kuka tace Yaya ko sau daya baka kira kaji ya jikin Babana ba kuma ni saboda naga Ya Amal ta samu lafiya shiyasa na tafin. Kusa da ita ya koma ya zauna kice fushi kike yi dani ko ya fada yana murmushi. Saboda haka kika dena cin abinci I believe to kullum sai nayi waya da Mama da Baba ki tambayesu ki ji.Ya goge mata hawaye da hannunsa. Lallai ina da aiki tunda na hadu da sarauniyar shagwaba. Ju tausayin kanta take ji a ranta domin ta san babban abinda ke damunta baya wuce son Ya Rayyan da kuma tsoron rabuwa dashi tunda Ya Amal ta warke don ita kam bazata yarda ta hada miji da yayarta ba.
Satin Ju daya a asibitin su Mama harda Baba sunzo dubata sau biyu daga wudil. Kebewa Mami tayi da Mama tace idan Ju ta sami lafiya sai mu fara shirin biki ko. Mama tace Yaya ban tare ki ba amma inaga a ware auren nan da Juwairiyya kada a sami matsala. Mami tace ko kadan baza ayi haka ba tunda haka Allah Ya kaddara musu auren miji daya dole su hakura.
*******************
Bayan an sallami Ju tana gida Mami bata sata aikin komai wai gara ta huta. Kullum Amal zata kaiwa Ya Rayyan abinci idan taje suyi hirar su. Ko ya kirata suji bangaren Hajja. Wani lokacin a gaban Ju ake hirar ma. Ko idan Amal ta dawo tayi ta bata labarin yadda hirar ta kasance. A wannan lokacin Ju ta tsani zaman gidan Mami domin wani irin kishi take ji a ranta. Ni kam bazan yarda muyi wannan zaman da Ya Amal ba abinda take fada a ranta kenan kullum kuma taga a gidan babu mai zancen auren nasu saboda haka Amal bata sani ba. Ju ta yanke shawarar yiwa Ya Rayyan magana.
Text ta tura masa na tana son magana dashi yayi mata reply idan ya dawo zai nemeta. Ta sake yin wani ita bata son kowa ya gansu. Yace akan meye kike son maganar kawai sai ta tura masa da reply din da ya tada masa hankali
( Yaya ina ganin ya kamata ka sanar dasu Baba a warware auren nan dama anyi shi ne saboda Ya Amal kuma ta warke. Nasan dukkanmu dole aka yi mana gara kace ka fasa ku zauna lafiya da Ya Amal nima sai na auri wani ).
Aikin da bai karasa ba kenan ya baro office. Yana zuwa gida Umma ya nunawa text din tace Rayyan tunda Amal ta warke kake neglecting dinta duk irin halaccin da tayi mana. Nasan ance a bari Amal ta yi wata daya da warkewa kafin ayi mata zancen aurenku amma dole taji ba dadi tunda tasan dama auren hadi ne. Wallahi ina sonta Umma tun kafin ku hada kema kin sani kawai ina kokarin samawa Amal farinciki ne don ta wahala. Umma tace amma kana yi ne at the expense of happiness din Juwairiyya. Ka samu ka lallaba ta har a fadawa Amal din.
Allah Ya taimake shi yau asabar Mami sun fita da Amal sunje gidan Dada lokacin da zasu fita kuma Ju da Yasmin sun tafi yin post UME saboda haka ya sami chance din ganinta bayan sun dawo. Abinci yace ta kawo masa taki zuwa daga karshe da kansa ya bita falon Mami ya sameta tana cin abinci sai ya karbi spoon dinta ya zauna a hannun kujerar da take zaune yana ci. Ju ta ajiye ta bar masa abincin sai ya tashi shima ki biyoni ina jiranki tace bazan zo ba. My Ju nima bakya raga min wannan tsiwar. To akan text dinki zamuyi magana.
Tana zaune a kan kujera shi kuma gefen gado yace naga text dinki kuma kiyi hakuri i got carried away na share ki. Hajja ce ta bada shawarar a bari Amal tayi one month da warkewa sai a fada mata zancen auren ni kuma ina tsoron kada taga ina yawan kula ki ban san yadda zata ji ba shiyasa na hakura gaba daya. Ya mike ita ma ya tayar da ita sai taji ya rungume ta. My Ju dana fada miki you are special i meant it from the bottom of my heart. Ta suma yi masa kuka ni bazan iya kishi da Yayata ba yace nima bana so kuyi amma haka Allah Ya kaddara mana. Bazan taba sakin kowa a cikinku ba you just have to learn to live together. Ni.....sai tayi shiru. Ke me? Kishi gareki haka Juwairiyya ya fada yana shafa mata baya....gaba daya jikinta ya kama rawa Yaya ka barni na tafi yace ba kina kishi bΓ ne ko haka nake wa Amal idan tazo tayi saurin cewa a'a ganin yadda ta tsorata ya bashi dariya. Bata ankara ba taji yayi kissing dinta tun tana kokarin gudu har ta hakura. Sai da ya sake ta yace this is how much you mean to me. Tana kokarin fita don gaba daya a rude take yace Ju ta tsaya cak amma bata juyu ba I LOVE YOU kuma bazan taba sakinki wani ya aura ba.
π JUWAIRIYYA π 16
Yau Ju ji take kamar an mata albishir da kujerar makkah. Ita tasan ba auren soyayya suka yi da Ya Rayyan ba amma indai Allah Ya kaddara musu zama tare tana son ko dan yaya ne ya so ta domin babu abinda take tsoro kamar auren wanda baya sonta. Wai I love you, kai anya kunenta ya jiyo mata da kyau kuwa. Haka ta yini tana sake sake da ta tuna abinda Ya faru a dakinsa kuma sai wani murmushi ya bayyana a fuskarta.
Suna shirin bacci ita da Ya Amal, fauza da Yasmin kowa tana bawa Amal labarin saurayinta. Amal tace Ju wa kika samu mana nan gabanta ya fadi sai kallon kallo tsakanin yan matan Fauza tace Yaya kyale wannan ta fiye boye boye. Ba yadda zaayi su fadi gaskiya don an kwabe su sun san ba huruminsu bane. Ya Amal tace ku barta idan tayi tsami zamu ji ne. Ni dai kowa yasan nawa ta fada tana fari da ido suna ta dariya tace yadda muka tashi gidan nan iyayenmu ba kishiya muma Allah Ya tsare mu da ita. Ju kam kamar an watsa mata ruwan zafi. Sai da kowa ya kwanta ta tashi tayi alwala tana nafila domin ita yanzu a tsorace take. Tana addua tana kuka sai taji an taba ta. A firgice ta juya taga fauza itama hawayen take.
Ju tun ranar da Ya Amal ta warke nake ji miki tsoron makomar auren Yaya. Ju tace amma duk baku yi min zancen cikin kuka gani nake kamar yanzu i am intruding into your lives za ku fi samun farin ciki idan na tafi. Fauza tace ko kadan Ju nasan yadda Yaya ke sonki ko bai fada miki ba kuma kema yanzu na yarda kina son shi. Ki cigaba da addua nasan Allah bazai bari ki tabe ba kuma suma iyayenmu baza suyi miki sakayya mara kyau ba. fadawa jikin Fauza Ju tayi tana kuka sosai i am confused fauza. Kada abin nan ya bata zumunci. Hakuri Fauza ta rinka bata har suka yi bacci.
*********************
Da safe wayar Ya Rayyan ce ta tashi Ju sai tayi mamakin yadda bata farka da wuri babu kowa a dakin koda yake kusan kwana tayi kuka. Me kike har yanzu baki fito ba karfe goma da rabi fa ya tambayeta. Tace Yaya ina kwana. Ban ganshi ba ya bata amsa, haka aka koya miki ana gaishe da miji. Zan koya miki at the right time yanzu dai ki tashi kiyi breakfast kada kizo kina rike ciki anjima.
Ta gama shiryawa zata fito fauza ta shigo dakin tace Ju kinga yadda idanunki suka kumbura kuwa. Ki dan yi kwalliya yadda zata boye idan ba haka ba zaa gane kinyi kuka. Tayi murmushi ta kara gyara fuska Fauza tace Yaya ya dace wallahi.
Sun fito suna dariya suka hadu da Amal tana ta danne danne a computer suka gaisa da Ju tace mata Umma da Mami sun fita da wuri saboda shirye shiryen biki zasu je zabar curtains dina dana Fauza. Ju tace shine baku tashe ni ba ina ta bacci ko gaisawa banyi dasu ba. Ta shiga dakin Hajja ta gaisheta zata fita Ya Rayyan da Ya Aliyu suka shigo ta gaishe su tana daga labule zata fita taji wani abu yayi kara kamar ya fashe tayi saurin fitowa suma su Ya Rayyan din fitowa suka yi a tsatstaye suka tarar da Amal, fauza da yasmin sai laptop a kasa ta rabe gida biyu. Ya Rayyan yace Amal garin yaya kika fasa min laptop. Bata bashi amsa ba sai ji suka yi tas tas ta bawa Ju mari har biyu nan take hancinta ya fara zubar da jini. Tana shirin kara mata Ya Rayyan ya rike hannunta yace wallahi kada ki kara. Ita Ju ta rike fuska tana hawaye Hajja tace Habiba wane irin rashin hankali ne wannan Amal na huce itama hawayen take ta dubi Ya Rayyan amana ta zaka ci ta juya ga Ju ke kuma munafuka shine kika dauki hotuna kika tura masa ko ina kwance ba lafiya dalilin wan ubanki shine zaki min kwacen miji. Wallahi baki isa ba idan ma abinda ya kawoki gidan nan kenan to da kafarki zaki fita. Dama talaka bai san alkhairi ba. Hajja tace rufa min baki a gabana kike wannan diban albarkar. Amal dai rai ya gama baci bata yi shirun ba ta cigaba da cewa Ya Rayyan da kanwata zaka ci amanata shima ya gama kulewa amma ya daure yace Amal ki zauna muyi magana a tsanake sai kawai ta rarumi part din laptop din da ta fasa tana kokarin kwadawa Ju a ka Hajja tace ke Habiba yadda kike matarsa haka itama Juwairiyya matar sa ce.
Amal sakin abin laptop din tayi a kasa tace ME KIKA CE HAJJA
Gidan Alh Tafida akwai kallo
π JUWAIRIYYA π 17
Hajja ta sake cewa Rayyanu mijin Juwairiyya ne kamar yadda yake mijin ki. Amal wata irin kara ta saki ta fita daga falon da gudu ta koma bangarensu. Dakin Mami ra shiga ta rufe kanta ta zauna tana kuka mai tsuma zuciya. Wai ita ce da kishiya? Kishiyar ma Ju.
Rayyan kokarin duba fuskar Ju yayi wadda ke zubar jini ta hanci ta doke masa hΓ nnu. Itama dakin Hajja ta shiga tana nata kukan. Hajja tace wallahi bazaku tada min hawan jini ba ke Fauziyya kira iyayenku su dawo gida. Rayyan haka ya zauna a falon Hajja zuciyarsa na masa suya. Har iyayen su suka dawo.
Amal bata fito daga dakin Mami ba sai da taji Abbanta yace idan bata fito ba ta bari ya shigo jikinta zai gaya mata. A falon Hajja wurin hada ko warware ko wani al'amari aka zauna ga iyaye ga ma auratan guda uku. Baba ne ya fara magana yayi wa Amal fadan abinda tayi wa Ju. Sannan yayi mata bayanin dalilin hada wannan aure. Ya cigaba da cewa Amal duk abinda akayi domin well being dinki ne. Saboda son kanmu ko tunanin meye a zuciyar Juwairiyya bamuyi ba aka daura auren nan. Iyayenta karshen halacci sunyi mana tunda sunsan dalilin zamanta a kano da irin dawainiyar da take dake amma ba musu suka bada auren da muka nema. Yanzu don kin sami lafiya kuma sai tashin hankali? Dama shiru akayi wai ki kara samun lafiya. Sannan muka sake yin shawarar sai kin shekara gidan miji zata tare. Wannan magana gobe nake shirin zuwa sanar da iyayenta sai wannan abu ya faru.
Baba, Umma da Mami suma duk bayanin da suka yi mata kenan. Amal ta gama jinsu cikin kuka tace yanzu da kanwata zanyi kishi Baba? Abba yace ke ki fita idona wallahi duk abinda akayi domin ki idan baki gode mata ba ai bazaki saka mata da tsiya ba. Komawa tayi kusa da Mami tana kuka don Allah Mami ki taimake ni wallahi bana son kishiya. Bazan zauna da Ju ba. Ju wadda tun zamansu banda sharar hawaye babu abinda take sai share hawaye tace Abba sai kowa ya juyu gareta ta cigaba don Allah ku raba auren nan tunda Allah Yasa ta warke. Kowa yaji tausayinta Rayyan kam ya kasa magana amma Ju na ambaton saki yace ni bazan saki kowa ba. Yana fadan haka ya fita.
Tashin hankali dai aka yini anayi a gidan. Mami ta tsare Ju a daki tace kada ta sake ta fadawa iyayenta abinda ke faruwa har ayi resolving issue din. Ju tace to zata fita sai Mami tace garin yaya Rayyan ya sami hotunanki har Amal ta gani. Ju tace cewa yayi na tura masa kuma lokacin ma bata warke ba. Kiyi hakuri Mami shine kawai abinda tace ta fita.
*******************
Dare yayi ana shirin kwanciya yau Amal dakin Mami ta tafi su Ju suna dakin Hajja. Amal dai kukan ta cigaba da yiwa Mami tace ko sau daya Ya Rayyan bai yi tunanin bani hakuri ba. Mami duk tausayin 'yarta ya kamata tace kiyi hakuri Amal nima ko kadan banso hadin nan ba amma da naga it is to your own benefit na hakura. Kuma kinsan Abbanki bazai taba yarda a raba auren kowa a cikin ku ba.
Ju tana dakin Hajja tana aikin kuka don ita wannan abin ita aka fi cuta. Gata cikin tashin hankali kuma an hanata fadawa nata iyayen balle su rarrashe ta. Hajja ta biyo su daki su Fauza suna ta bata hakuri itama hakurin ta bata game da irin abinda take fuskata a gidansu.
Tana shirin tada sallah Ya Rayyan ya kirata a waya taki dauka. Yayi ta kira tana kallon wayar daga karshe sai ta tura masa da text.
( yaya don Allah ka sauwake min auren nan hankalin kowa ya huta )
Tana tura text din tayi saurin kashe wayarta.
π JUWAIRIYYA π 18
Sai bayan asuba bacci ya dauke Rayyan. Da gari ya waye kowa a gidan bashi da cikakkiyar walwala. Ju ta shiga bangaren Mami su gaisa sai taci karo da Amal a falo. Ya Amal ina kwana ko kallon Ju bata yi ba ballantana ta amsa. Ju ta wuce dakin Mami anan ne Mamin ke tambayarta ko zata aminci a raba nata auren da Rayyan. Ju tace Mami ai tun jiya hakan na fada yau ma kuma hakan zan fada musu. Tayi saurin tashi saboda kukan dake kokarin kwace mata. Mami ta tsayar da ita ko kina son sa ne? A'a mami ai dama saboda Ya Amal ne na aminci. Da sauri ta fita har tana karo da Ya Sagir tana kokarin bashi hakuri hawaye wani na bin wani. Yaji tausayin ta sosai bai ce mata komai ba har ta fita ya wuce daki ya dauki key din motarsa. Gidan Dada ya wuce.
Kamar jiya yau ma an sake taruwa falin Hajja da niyyar kawo karshen wannan matsalar sai dai yau kannen su Baba mata suna zaune. Kafin kowa yayi magana Amal tace ni dai na hakura da auren nan Hajja ya sake ni kawai na koma makaranta. Baba yace bana son na sake jin zancen saki a tsakaninku. Anti Usaina tace yanzu ke Amal banda butulci irin na dan Adam har zaki ce ba zaki zauna da Juwairiyya ba? Amal ta suma hawaye Mami tace haba Usaina me ya kawo maganar butulci kuma. Ta koma kan Ju ke kina son zama dashi ne Ju ta girgiza kai alamar a'a. Abba yace ku zaku yanke maganar ne ko kuwa. Nan dai Ju ta tabbatar Mami tafi goyon bayan yarta amma bata ga laifinta ba.
Kowa da irin tasa shawarar karshe dai aka yanke shawarar ya sake duk su biyun indai ba zaayi sulhu ba. Amal sai kuka take ita zaa raba ta da Ya Rayyan a dalilin Ju. Mami itama cewa tayi bata yarda ba ai Ju din ba auren soyayya tayi ba. Rayyan sai ya tashi ya dubi iyayensa Baba ina son Juwairiyya bazan sake ta ba. Nan fa wuri ya kaure da surutun mata kowa tana fadin nata itama umma ta goyi bayan danta ya zauna da wadda yake so.
Ana haka sai suka ji sallamar Dada da Ya Sagir kafin ta zauna Ju ta rungume ta tana ta kuka. Ya Rayyan kuΔ·Γ n nan har zuciyarsa yake ji. Bayan ta gaisa da su Hajja ,Dada tace yanzu Asiya yau kece akan yarki kike neman bata zumunci? Mami ta harari Sagir wanda yace ni naga yarinyar nan babu kowa nata a wurin nan shiyasa na dauko Dada. Dada ta cigaba da cewa Haj Habiba indai ba kwa bukatar wani taimako daga yarinyar nan ni zan tafi da ita. Tazo gidanku ta taimaka muku da abinda ko ke Asiya da kika haifi Amal sai kin kai zuciya nesa zaki jure masa amma ji yadda kuka taru a kanta saboda Amal bata son kishiya. Yanzu ba don yarinyar mai hankali bace kuna tsammanin da tuni bata kira nata iyayen ba.
Hajja dasu Abba suna bawa Dada hakuri Sagir ya lura Ju bata falon. Ina Ju tayi abinda ya tambaya kenan hankalin kowa ya dawo inda ta zauna.
******************
Ju ganin ana ta cece kuce a falon sai ta sulale tayi waje tana tunanin ina zata je ba tare da an gano inda take ba. A daidata sahu ta tara tace masa ya kaita shagari qtrs. Daidai kofar gidan Samira ta tsaya tace ya jira tana zuwa. Tana sallama samira ta tashi da murna ta tare ta. Sai Ju tace Samira bani 200 zan sallami mai adaidaita. Sai data dawo Samira ta kamo hannunta suka zauna lafiya yar uwa? Me ya same ki haka? Ai kamar jira take nan Ju ta fashe da kuka tana yi harda shessheka. Mijin Samira yayi saurin fitowa sai tayi masa signal da hannu alamun ya koma ciki saboda kan Ju a sunkuye yake. Sai da tayi mai isarta sannan Samira tace mu shiga daki muyi sallah sai muyi magana.
Duk suna kan abin sallah basu tashi ba Ju ta fadawa Samira abinda ke faruwa da ita. Tace ina son Ya Rayyan Samira amma abinda yafi damuna yadda zumuncin mu ke neman baci. Wai ni Mami ke goyon bayan a saki. Wallahi da Mama zata zo abin sai yafi baci don tafi Mami zuciya da fada. Ni yanzu so nake idan basu ganni ba asa ya sake ni na koma gaban iyayena.
******************
Wasa farin girki har magriba tayi babu Ju ba labarinta gashi ta kashe waya. Su Mama anki fada musu ana kokarin a gano inda take. Ya Rayyan yafi kowa shiga tashin hankali, bai taba sanin haka yake son Ju ba sai yanzu da yake tunanin rasa ta.
π JUWAIRIYYA π 19
A bangaren Ju kuwa bayan ta gama bawa Samira labari tashi tayi ta hado mata tea mai zafi ta kawo mata. Ki daure ki sha Ju duk kin fada tashin hankalin kwana daya kawai. Allah Yasa lahirar mu tayi kyau. Ju tace ni bana jin Yunwa. Samira ta harare ta so kike ulcer dinki ta tashi ko to ba a gidana ba. Muna tsaka da amarci Ya Rayyan yasa a kama mu. Dan murnushi Ju tayi, Samira tace idan ma baki sha ba kulle ki zanyi a daki na kira yan gidanku.
Ju na zaune a falo tare da Samira da mijinta yace gaskiya na tausaya miki sai dai ya kamata ko mutum daya ne a sanar inda kike saboda halin rayuwa. Yanzu Allah kadai yasan halin da suke ciki.
Hankalin Baba a tashe tun jiya yake kiran Ju baya samu. Itama ma Mama tace tun tana kira wayar na shiga har ta dena shiga. Daga karshe dai Mami ta kira wadda a wannan lokacin sun gama rudewa da rashin sanin inda Ju take. Tana ganin wayar kanwar tata Abba ta mikawa shima yace me zan fada musu, sun bamu amana mun ci? Da suka ji shiru baa dauka ba Mama ta kira Dada tana kuka tace tun jiya na kasa samun Juwairiyya ita ma kuma Yaya bata daukar wayar. Dada dama bata bar gidan Hajja ba tace Mariya gobe ku taho kano. Mama na jin haka sai kuka ta ajiye wayar ta fadawa Baba ya fita ya kira Ismail da Najib. Gaba dayansu a motar Najib din suka gwamutsa harda su Bidaya. 9:47 suka isa gidan Hajja.
*********************
Lallai kudi da 'ya'ya suna iya haddasa fitina a doron kasa domin yau Mama ta fadawa yayarta kalaman da bata taba tsammani ba akan Juwairiyya. Mami shiru tayi domin tasan rabon da suyi fada irin haka da Mariya tun irin fadan sakonni ta tabbatar bata kyauta mata ba. Gaba daya gidan ya hargitse Baban Ju yace ni dai Alhaji Bashir ku taimake ni a raba auren nan kowa ya huta. Hajja dai ranar har kuka tayi yadda al'amarin ya lalace lokaci guda. Tace Mariya kiyi hakuri in Allah Ya yarda zamu ganta domin tana da hankali nasan bazata inda bai kamata ba. Kowa yaje ya kwanta dare yayi gobe sai mu san abinyi.
Su Mama dai gidan Dada suka wuce don tace bazata kwana a gidan ba.
Ya Rayyan kuwa tunda aka fara neman Ju ya fita daga gidan. Ya rasa inda zaije dubata domin kuwa kawayenta kadan ne a kano. Karshe gidansu Abbas ya tafi sai dai cikin dare zazzabi ya rufe shi baya ko iya magana. Wurin karfe uku na dare Abbas ya kaishi asibiti aka kwantar dashi.
********************
Yadda iyayenta basu yi bacci ba itama Ju haka ta kwana kuka, sallah da adduar neman mafita daga Allah. Amal kuwa duk sai ta tsani kanta. Me yasa tabi son zuciya ta cutar da kanwarta? Gashi yau a dalilin ta iyayensu sunyi fada gida ya rasa kwanciyar hankali.
Da safe mijin Samira yace da Ju wa ta yanke shawarar a sanar da inda take. Sai tace zata tafi gidan kakarta. Samira tace kaga gara mu kaita da kanmu don kada tayi wani wurin. Sha daya na safe suka shiga gidan Dada sai dai sunyi rashin saa bata nan. Ju tace nasan ta koma gidan Hajja ku barni a nan zan shiga makotan ta na jira. Samira tace a'a gaskiyq ban yarda ba. Dole suka koma da ita don tace bazata sharada ba gidan Hajja.
A asibiti Amal na tsaye gaban gadon Ya Rayyan tace kayi hakuri yaya bansan kafi son Ju a kaina ba. Ni na hakura idan an ganta a kai maka ita gidanka. Tana fadin haka ta juya zata fita Mami tace Amal ko ciwon da kikayi ne ya taba miki kai ace ko tausayin halin da yan uwanki ke ciki baya damunki. Ya Sagir ne ya ja hannunta suka fita waje.
Cikin mota suka shiga tana masa kuka yace wallahi idan bakiyi shiru ba zan miki dukan tsiya a wurin nan. Yanzu Amal ina iliminki da hankali ya tafi? Na zata ko yau Ju ce ta wayi gari tace tana son Rayyan ke me bashi shawarar aurenta ce. Nan ya rinka yi mata fada da nasiha karshe yace Amal ina ji miki tsoron zama daga cikin mutane masu butulcewa rahmar Allah. Da Yaso fa da kina nan kamar karamar yarinya ita kuma a kaita gidan idan sun so su kula dake idan sunki su cutar dake. Ni shawara kawai na baki kiji tsoron Allah. Amal tace nima abin na damu na Yaya kishi ne yake sani yin hakan.
******************
Washegai Fauza da Nafisa ne a gidansu Samira bayan sun gaisa da Ummansu Fauza tace ni kawar Samira ce tare muka yi secondary school ta fada min zata yi aure amma bana gari shine nazo a raka ni gidanta don wayata ta fadi bani da number dinta. Umman Samira ta kira kaninta tace ya rakasu. A waje Yasmin tace dana biku zata ganeni. Allah Yasa tana gidan dai.
π JUWAIRIYYA π 20
Kamar muryar Fauza nake ji fa Ju ta ce da Samira. Sallamar suka sake ji Samira ta je ta bude kofa. Fauza ce tare da Yasmin da Nafisa. Su hudun rungume juna suka yi suna kuka.
Bayan sun gama bata labarin duk abinda ya faru bayan tafiyarta harda rashin lafiyar Ya Rayyan ,Ju ta share hawaye tace ni ya zanyi ne da raina? Idan na aka bar auren nan zumunci sai ya tabu haka ma idan aka raba. Nafisa tace kiyi hakuri mu koma gidan Dada wallahi Mama ko abinci bata iya ci. Yasmin tace amma dai zaki zo duba Ya Rayyan ko. Murmushin yake tayi wanda yafi kuka ciwo tace in sha Allah.
Yaya mun nemo Ju tana gidan Dada abinda Fauza ta radawa Rayyan kenan a kunne. Yayi kokarin tashi zaune amma jikinsa babu kwari yace kin tabbata ta gyada masa kai. Alhamdulillah yace da har Mami da Ya Sagir suka ji Mami tace me ya faru? Bai iya bata amsa ba sai Fauza ce tace Mami mun nemo Ju dazu mun kaita gidan Dada.
Mama Allah lafiyata kalau abinda Ju ke ta fadawa mamanta kenan wadda tun shigowarsu gidan take ta juyata tana shafa mata jiki tare da tambayar babu inda ke miki ciwo ko. Dada tana daga gefe ta kalli Baba wanda sai murmushi yake tace kaga rashin kunya ko? Da sai ka zata bata son yarta she dai tana zuci.
*********************
Mami da Amal ne suka shigo gidan Dada kowa ya bisu da kallo. Ju ce tayi kokarin gaishe da Mami. Amal sai taje ta rike hannun kanwarta tace Ju kiyi hakuri da abinda ya faru nasan ban kyauta ba. Dama nasan bazan taba iya saka miki ba wannan sai Allah amma yanzu a gaban iyayenmu nayi miki alkawarin bazan taba zama silar mutuwar aurenki ba. Idan har akayi kokarin raba aurenki da Ya Rayyan to nima nayi alkawarin bazan taba zaman aure dashi ba.
Iyayensu mata harma da Dada sai kuka. Mami tace Mariya kiyi hakuri naso na biyewa sharrin zuciya na watsa zumuncin mu. Itama Mama tace nima ki yafe min Yaya. Dada cikin murna tace Allah Yayi muku albarka. Baba Idris baki har kunne don farinciki yace Alhamdulillah tunda Allah Ya korar mana shedan Allah Ya kara hada kawunan mu.
Mami dai ta kawo shawarar a hada su duka ayi biki tare nan Baba yace a'a Haj Asiya ni tawa shawarar shine a fara bikin da Amal bayan shekara daya sai Juwairiyya ta tare hakan zaifi. Mami tace dama abinda Baba likita yace zai fada maka kenan idan ka yarda. Baba yace ni na amince. Allah Ya basu zaman lafiya.
Ju da Amal da suke cikin daki suna jin hirar iyayen nasu. Amal tace Ju kin amince da hakan? Ju tace kai yaya ba dole ba Allah Yasa kafin nan ma kin haihu. Nan Amal tayi mata dundu a baya. Ju ta kwalla kara Mama tayi saurin cewa lafiya? Suna shiga suka gansu suna dariya. Har zuciyarta Mami taji dadi sosai yadda suka hade kansu. Ita kuwa Mama murde musu kunne tayi.
*******************
Yau dai falon Hajja alkhairi aka kulla aka tashi cikin farin ciki da annashuwa. Kamar yadda Baba ya fada Amal ce zata fara tarewa.
Gaban Ju har faduwa yake ta tsaya kofar dakin da aka kwantar da Ya Rayyan. Amal ce ta fito tace to ni zan tafi nayi kanwata na bashi hakuri tare da tabbatar masa mun hada kanmu. Ju ta tsaya kamar an kafe ta don wata irin kunya take ji. Amal kuwa tura ta tayi tace anjima zan dawo sai mu tafi gida yanzu wurin neman venue zamu da Fauza da anti Habiba.
Ju tana shiga dakin taji an rufe kofar an rungumeta ta baya. Tana kokarin gudu taji ya rada mata a kunne keep still. Tsayawa tayi kamar yadda ya umarceta. Sunyi kusan 5 mins a haka sannan ya ja hannunta suka zauna a bakin gado. Duk kunya ta rufe Ju yace ba gaisuwa? Tayi saurin sauka tace ina yini ya jiki? Da sauki tunda kinga damar zuwa dubani. Ju bata ce komai ba ya cigaba da maganarsa da baki dawo ba da aurena zaki mutu ko ina zaki a duniya don bazan sake ki ba. Allah Ya sa na iya hakuri har sai an shekara kafin a kawoki.
π JUWAIRIYYA π 21
Bata ce komai ba yana ta surutunsa shi kadai. Wai dama haka Ya Rayyan yake ta fada a zuci. Sai yayi ta wani shiru shiru kamar baya magana. A nan ta yini abinci ma ranar a plate daya suka ci don cewa yayi bazai ci ba idan bata sa hannu ba. Amal ta dawo tare da Fauza suka dan taba hira sannan suka tafi.
Yau saura kwana uku bikin su Amal gida ya cika da 'yan uwa na nesa harda su Mama. Dinkunan amare duk iri daya akayi ita kuma Ju da su Yasmin da kannenta nasu dinkin iri daya. Mami wani special kulawa take bawa Ju. Ya Rayyan dai ba karamin farinciki yake ba domin yadda yaga matan nasa sun cigaba da rayuwa kamar yan uwa.
Anyi kamu a gidan Hajja ranar ba karamin kyau amaren sukayi ba. Itama Ju tayi kyau sosai tasha gwaggwaro ga kunshi mai kyau kafa da hannu. Washegari yini akayi sannan aka kai amare wadanda suka sha kukan rabuwa da gida. Ju a gayyar Fauza ta tafi daga nan suka shirya zuwa wurin dinner wadda Ya Rayyan da Abbas suka shirya. Kaya Bidaya tazo dasu a leda ta bawa Ju inji Rayyan. Wani lace ne white and purple anyi masa dinkin skirt da riga sai dankwalinsa, mayafi fari mai kyau da takalmi da jaka purple. Ju tana juya kayan tace ya akayi Yaya yasan size dina? Fauza wadda akeyi wa kwalliya tace ni na kai dinkin i hope yayi kyau. Shoe and bag kuwa zabinsa ne. Ju tace to ankon mu dasu Yasmin fa. Fauza tayi dariya zaki fara sabawa miji akan anko ko? To dai an daura miki aure don haka dole abi Yaya da kannen yaya ma ta fada tana kanne mata ido.
Taro ya kayatar sosai musamman shigowar angwayen da amaren su. Ju dake tsaye bayan amaren yau itama taji kishi a ranta amma tayi saurin kawar da abin ta hanyar neman tsari daga sharrin shedan. anyi taro an gama lafiya sunfito duk zasu tafi Abdul ne zai ja motar su Ju. Amal ce ta kula Ya Rayyan duk bashi da sukuni tace Yayana kaje kayi sallama da Ju mana zan jira ka. Harararta yayi kyaleta kawai mu tafi. Kaga dai ka fita nasan kana son zuwa am not that selfish fa. Waya yayi mata tana dauka yace karaso wurin mota ina jiranki. Tana zuwa tace Ya Amal kinyi kyau sosai Amal tace nagode bari na karbi sako wurin Yasmin. Tana fita ta share kwalla gaskiya kishi sai an daure. Ya Rayyan kallon Ju yayi yace sweet Ju Allah Ya kaimu ranar da zaki tare duk da bana jin zanyi hakurin shekara daya. A zuci tace amin amma ya kamata ku tafi haka sai da safe. Korata kike ko? Nagode kada ki kashe waya dai. Tana juya baya taji yace I love you tace me too a hankali sannan ta tafi.
Ju ta fara karatunta a saa tana degree a Nursing sabon department din da aka bude a buk. Ya Rayyan kuwa kullum zai zo gida ya ganta. Ko kadan ta dena bari su hadu inda ba mutane don yana ganinta sai ya taba ko da hannunta ne. Duk dare kuma zai mata waya ko suyi chatting
a whatsapp.
Ju an gama exams tun safe yau ta hada kaya zata tafi Wudil. Ya Rayyan yace zai kaita ya gaisa dasu Mama. Supermarket ya fara kaita yayi wa iyayenta siyayya sannan suka dau hanya. karatu ya kunna musu Ju ta fara rufe ido yace sweet Ju a hankali ta amsa da kyar don bacci ya fara daukarta. Parking yayi a gaba kadan da wani kauye yana kallonta. Jin alamar sun dena tafiya yasa ta farka yaya lafiya kuwa. Yace ina fa lafiya sweet Ju zata haukata ni. Ta zare idanu me nayi maka yace sace min zuciya mana cikin karamar murya. Tace Allah yaya ka fiye shagwaba haka ka koma magana kuma. Yace yarinya ban fara komai ba ma amma bari kiga kadan. Matso da fuskarsa yayi daf da tata tayi saurin rufe ido ya kama hannunta ya dora kan kirjinsa bude idonki tace a'a, musu da miji ko sai ta bude a hankali yace sweet Ju kinji yadda zuciyata ke bugawa akanki? Don Allah kice kina sona ko sau daya ne duk ya marairaice mata. Tausayi ya bata duk da tanajin kunya tace I love you Ya RΓ yyan. Kissing din hannunta yayi yace kinga yadda ake shagwaba kasa mutum yayi abu ko baiyi niyya ba. Lallai yaya kayi min 1-0 amma zan rama. Ya ce eyye ramuwa akan miji tace eh. Dariya yayi suka tafi cikin nishadi.
Sweet Ju ta Ya Rayyan
π JUWAIRIYYA π 22
Yau watan Amal takwas da tarewa amma an hana Ju zuwa gidan sai ranar tarewarta. Sai dai kullum suna waya balle da Amal din ta sami ciki.
A gajiye take tana cin abinci bayan ta dawo daga makaranta Mami ta shigo dakin ta zauna bakin gado tace Juwairiyya wane kalar curtain kike so a falo. Ju ta sunkuyar da kai kai Mami ni kowanne ma. Bikin ma ai akwai lokaci Mami tace mai kwarmin ido da wuri yake fara kuka Juwairiyya ko kin manta ranar asabar zaa kai kayan yayanki Sagir gara ma hada bikin ke da Nafisan kawai.
Ranar asabar ana ta shirye shiryen tafiya Wudil kai kaya Amal ma ta dage zata je Ya Rayyan ya hanata da kuka ta shigo gidan Umma na bata hakuri karshe dai dole aka tafi da ita. Zata shiga mota harda yi ma Ya Rayyan gwalo. Sunje Wudil lafiya sai a hanyar dawowa ne Ya Aliyu ya fada wani rami. Nan fa cikin Amal ya fara murdawa kafin su iso kano jini ya balle mata.
*********************
A asibiti Rayyan ya same su an samu jinin ya tsaya sai dai kuma Amal ta fara nakuda gashi cikin watansa bakwai. Hankalin kowa a tashe yake musamman Rayyan fita akayi aka barsu a gaban gadon ya durkusa ya rike mata hannu tana cizon lebe. Tace Sweet Yaya yana dago kai yaga ta rike kunnuwanta biyu. Nan hawayen da yake rikewa suka zubo tace kayi hakuri banbi umarnin ka ba daga yau dan ba kara. Da hawayen yayi murmushi yace sweet Amal ai ba fushi nayi ba. Allah Ya saukeki lafiya kuma Ya baki lafiya. Tace amin ka fita kuyi ta min addua yanzu zaa kaini dakin gashi,wani murmushin yayi ya ja mata hanci I want a beautiful baby like you Habiba.
Jikin Ju har rawa yake da taga yadda Amal ke gumi ta taba Mami tace haka ake haihuwar to ni na yafe. Mami tayi karfin halin murmushi eh mana Juwairiyya ke da zaki haifo mana dozen.
Nurses biyu ne da wata doctor akan Amal ana ta kokarin ceton ranta dana abinda ke cikin. Da gudu nurse ta fito daga dakin Rayyan yana tambayar lafiya bata kula shi ba ta wuce. Jinin da Ju ta gani a jikin hand gloves din nurse din yasa ta fadi kasa a sume nan Rayyan ya kwasheta ya kaita wani dakin abin duniya yayi mada yawa. Tare da Baba nurse din ta dawo shima baiyi musu magana ba ya shige. Sunyi kusan minti talatin da shiga sai ga nurses sun fito kowacce da baby daya a hannunta. Umma da sauri tazo karba tace dama biyu ne nurse tace eh duk mata ne daya ce bata kwanta daidai ba shiyasa muka kira Baba. Baba shima ya fito yace a wuce da yara SCBU inda ake ajiye jarirai bakwaini ko marasa lafiya.
Sai da Amal tayi kamar awa daya da haihuwa aka turo ta waje dakin hutu. Jikinta duk a mace ba kwari ana ta yi mata sannu. Ya Rayyan ta kalla harda harara tace daga wannan bazan kara ba. Hajja wadda bata zo asibitin ba sai da aka haihu tace haka kowa take fada sai kuma badi a ganta da wani.
Sai da kowa ya fita Ya Rayyan yace Sweet Amal sannu da aiki. Allah Ya baki lafiya Yayi miki albarka. Tace amin amma dai daga wannan sai an kwana biyu na barwa Ju. Dariya yayi sosai su Amal an horu fa wai anyi dinkin nan da kike tsoro yana fada yana cewa bari na gani ta doke masa hanne wallahi anyi baka ji ina ta kiranka ba? Yau Baba yaji zance kala kala don ni daga yau ya zama siriki na.
*******************
Sai bayan sati biyu aka sallami Amal da twins wadanda suka ci sunan Mami da Umma wato Asiya da Aisha. Mama ce tayi jinyarta a asibitin bayan anyi sallama ta koma wudil. Sai da sukayi wata daya sannan akayi taron suna Abba yana ta fada wai son bidiarsu yayi yawa ace suna bayan wata daya.
Ju tana zaune bakin gado dauke da Minal ( Aisha) ita kuma Manal (Asiya) ta bacci sai Ya Rayyan ya shigo yace sweet Ju da babies dinta ina Sweet maijego? Ju tayi dariya tace wanka takeyi. Yauwa to dan matso kiji wata magana tace anya Yaya nifa tuni na dena trusting dinka. Ya kashe ido daya ke bakya cin ribar zance baki ma tsaya kinji me zan fada ba.
Daga bayansu suka ji Amal tana cewa gulmata zaku yi ko? Ju tace Allah ban saurare shi ba Yaya. Dariya suka yi mata Ya Rayyan yace wai dama cewa zanyi itama ta haifi biyu next year ke kuma ki haifi gambo. Amal tace Sweet Yaya yace naam ta dauki takalmi tace sweetly go out tana fada ta bishi da takalmi ya fita Ju tana dariya.
π JUWAIRIYYA π 23
Ance rana bata karya sai dai uwar 'ya taji kunya. Yau ne ake bikin Juwairyya da angonta Rayyan sai kuma Nafisa da angonta Sagir. Taro kam yayi kyau Mami tayi rawar gani sosai don a daki Mama ta sameta bayan an gama jeren Ju taga irin abinda sukayi mata cikin hawaye tace Yaya Allah Ya kara mana zumunci Ya basu zaman lafiya da juna. Babu abinda bakiyi wa Juwairiyya ba mu da muka haifeta ma gudunmawar mu a auren nan kadan ce. Mami tace Mariya kinsan dai kullum nasihar Baba gare mu kenan kafin ya rasu saboda haka muyi kokarin bawa yaranmu shawara mai kyau ta zaman lafiya.
Mami ce ta bada shawarar ayi delaying komawar Amal da sati biyu saboda amarya Ju. Amal din bata musa ba don tasan kazantar da baka gani ba tsafta ce kuma ita ai Ju ta yarda ta bata watanni ma duk da cewa da aure a kanta.
An kai amare dakunan su gidan Rayyan babba ne ba laifi domin kuwa banda falon tsakiya kowace mace harda shi tana da ciki da falo, harda kitchen da toilet. Sai dinning area a falon da wani toilet din guda daya da dakin baki. Gida dai yayi kyau sai fatan zaman lafiya.
*******************
Tunda Ya Rayyan ya fita raka baki da kawayen Ju cikinta ya fara kadawa. Samira tace mata ana shan wahala gashi Anti Hassana ta sata zama cikin bagaruwa wadda samiran tace kara matse mace takeyi. Yana taba kofar dakin ta sake jin cikinta na kuka ai nan da nan ta fada toilet na shiga uku tace a ranta. Ni kuma da gudawa na tare a gidan miji. Sai da ta gama fitowa ta gagara kawai tonu ranar data shigar masa toilet tayi a gida. Yana ta knocking taki magana can da ya gaji yace zan bude fa. Tana jin haka ta fara tube kaya tace ina zuwa wanka nake. Ba yadda zata yi haka watsawa kanta ruwan sanyi tana da rawar dari tayi alwala...da muguwar rawa gwamma kin tashi.
A zaune kan gado ta sameshi yace ana kawo amare sunyi wanka ke daga zuwa zaki karar mana da ruwa. Gabanta ya fadi ba dai yaji tana flushing ba. Ya cigaba to kazamar amarya by the way akwai ruwan zafi ma kuwa? Ga sanyi ya fara zuwa. Sai ta basar ni zafi nake ji shiyasa nayi. Yace to zo na shafa miki mai tace ai zafin dai nake ji amma yanzu da gaske take tunda ya shigo wani gumi ya karyo mata. To dai duk wayon amarya...........
******************
Amal ta fito daga kitchen ta tarar da Ju tayi tagumi a falo tana goye da Manal. Amal tace Ju lafiya kuwa ko result ya fito ne nasanki da zulumi kije ki duba kawai. Ju ta share kwallar data fito mata Amal hankalinta ya kara tashi sai taje ta yiwa Ya Rayyan waya. Bai dade ba ya iso ya dauki Minal dake hannun Amal. Yace lafiya sweet Amal tace tambayi Ju sai sharar kwalla take. Yace sweet Ju ya akayi bata kulashi ba ta tashi ta tafi daki. Amal ta ce Yaya bita i think something is wrong.
Sweet Ju dina wa ya taba ki cikin kuka tace tunda nazo gidan nan wata uku banyi period ba kullum jiransa nake. Yanzu idan ciki ne dani haka zanyi irin na Ya Amal? Da kyar fa ta rinka tafiya gashi harda dinki.
Fita yayi ya kira Amal suka rinka mata dariya Amal tace kin fiye tsoro Ju to sauke goyon nan daga yau an yafe miki kada ki matse musu kanne.
Ju ce a labor room tana ta kiraye kirayen neman taimako. Idan tayi adduar sai ta fara kiran Mami da Mama. Amal har kuka tayi don tace ita bazata taba manta ciwon ba. Kusan awarta biyu a ciki ta haifo katon jaririnta ana kokarin yanke cibiya tace wa nurse din anyi min kari ne nurse tace eh amma ba yawa uku ne Ju tace a garinku uky ba yawa ko. ta ce na ma dena kiranka sweet Yaya tana fada tana kuka. Sister Rabi wato nurse din tace maigidan ne ko? Ai daga yau ki kira sunansa kawai. A haka aka gama aka fito da ita.
Rayyan dai ba karamin dadi yaji ba. Yaro kamar shi yayi yakinsa. Amal tace Ju yaya kika ji akwai zafi... hmmm Yaya ke dai bari sai godiyar Allah gashi nasha dinki.
Ranar suna yaro yaci suna Idris abinda Ju bata zata ba. Ba karamin farinciki tayi ba tace Sweet Yaya ka fadi duk abinda kake so tukwici banda haihuwa next year. Ya rungume ta sannan ya rada mata a kunne ni ke nake so da dan bakin tsiwar nan ya fada yana shafa mata lips.
*****************
Minal da Manal ke rike hannun Baba karami wai yayi tata-ta Amal tace kaji iyayin yaran nan ko yaushe tasu kafar ta gama mikewa Ya Rayyan yace ai gara duk su mike tunda akwai wasu a hanya yana kallon cikinsu ita da Ju. Duk dariya suke Amal tace ni dai daga wannan na dena itama Ju tace ai nima haka. Ya Rayyan yace to sweet matana ai kunsan akwai fili a gidan nan sai na karo biyu. Tare suka rufe masa baki Amal tace Sweet yaya sai sweet Ju ita kuma Ju tace da Sweet Yaya Amal. Ya juya hagu da dama ya kare musu kallo ga yaransa suna wasa yace Allah Ya bamu zaman lafiya da zuria dayyiba. Tare suka amsa da amin.
I realy hope you enjoyed reading Juwairiyya my Sweet friends.
Ku saurari next littafi na.
Taku Batul Mamman
No comments:
Post a Comment